Showing 21001 words to 24000 words out of 61652 words

Chapter 8 - YARE BIYU COMPLETED BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Nil   

01 Jul 2025

4033

dogon tsaki ta wuce cikin gida!

Su funmilayo suka kwashe da dariya ,hashim ya ciro kud'i ya rarraba masu yana kuma masu
godiya bisa tayashi girbi da sukayi!

Hashim ya wuce gidan MD ,ya had'a kan kayansa kakaf domin gobe hutunsa da ya d'auka zai
'kare,kuma yana so a goben ya wuce da matarsa!

Da yamma hashim da MD suka je gidansu bolaji ,suka aika aka masu sallama da bamidele
,bayan ya fito ,MD ya shaidawa bamidele kud'irinsu akan cewa gobe suke son a d'aura
aure,hashim ya wuce da matarsa,tunda ya kamalla noma kamar yadda bolajin ta
bu'kata,bamidele jiki na rawa ya amsa masu da bakomai,gobe su turo magabatansu a d'aura
auren ya wuce da ita!

Ko da bamidele ya shaidawa bolaji yadda sukayi dasu MD ,hankalinta ya tashi matu'ka tana ta
cewa haba ya zaiyi mata haka,kar fa ya manta shine fa wanda yayi sanadin mutuwar
iyayensu,taya zata aureshi!
Bamidele ya nuna mata cewa shi ba ruwanshi,ita takama tasa d'an mutane noma tare da
d'aukan al'kawarin aurensa idan yayi noman ,aure kam yazama dole ta auri oga soldier,domin
bazai zuba mata ido ta sa6a alkawari ba,kuma oga soldier yana sonta matu'ka,idan ya rasata
Allah kad'ai yasan abinda zai aikata a garesu,shikuma ba zai iya da jarabar sojoji ba!
Hashim ya buga ya shaidawa mai martaba yadda sukayi da bamidele,mai martaba ya tayashi
murna ya kuma ce masa suna nan tafe washegari insha Allah!

Maimartaba ya shaidawa fulani cewa gobe zasuje su dawo da hashim!

Fulani sai murna take,hakan yasa ta bugawa yayarta waya akan cewa a turo mata nawwara
gobe da safe!

¤¤¤

Washegari misalin 'karfe 8 na safe mai martaba da tawagarsa suka wuce lagos daganan zasu
wuce can osun yankin erin!

'karfe goma na safe nawwara ta iso fada ,fulani taji dadin isowarta,domin tana son wannan
karon idan hashim ya dawo ayi bikinsa da nawwara kowa ya huta!

Haka aka cigaba da gyare gyare da dafe dafe a cikin fada ,duk na tarbar cap.t Yarima hashim,
bisa jagorancin fulani!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/16, 11:17 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

~25~

Misalin 'karfe 8:00 na safe hashim ya gama shiryawa cikin uniform,ya kuma had'a kayansa
kakaf yasa a mota ,sannan yayiwa MD godiya ga bashi masauki da yayi a gidansa na tsawon
watanni!

Sannan suka d'unguma dashi da MD suka wuce gidansu bolaji a motarsa,domin a can 'kofar
gidansu bolaji zasu jira isowar mai martaba!

Bolaji kuwa ko rintsawa batayi ba,haka zalika bamidele,kwana sukayi yana bata baki ,da kuma
hakuri akan aurenta da hashim!

Su iya folake dasu iya ayomide da sauran mata sukayi gangami guda suka taho gidansu bolaji
da sassafe,da isowar su kuwa suka fara cece kuce akan auran bolaji da hashim,taya zasu zuba
ido a aurawa bahaushe bolaji,bahaushen da yayi sanadin mutuwar iyayenta!

Bamidele ya koro masu bayani ga alkawarin da bolaji ta d'auka, amma mirsisi suka 'ki yarda!

Hakan yayiwa bolaji dad'i sosai domin ko kad'an ba ta son aurenta da hashim !

Misalin 'karfe 12:00 na rana ,mai martaba da tawagarsa,tare da kuma oba [sarkin osun] da tashi
tawagar suka iso 'kofar gidansu bolaji!

Bamidele yaje ya kwashi gaisuwa a gunsu,ya kuma sanar dasu halin da ake ciki!

Oba ya nemi 'karin bayani a gun mai martaba,mai martaba ya labarta masa abinda yasani
game da tarihin had'uwar hashim da bolaji!

Bayan Oba yaji wannan labari,a take ya nunawa hashim kuskurensa game da abinda ya aikita

ga maami,sannan ya umarci bamidele ya turo masa bolaji da su iya folake!

Oba ya dubesu yafara da basu ha'kuri ga abinda hashim ya aikata wanda faruwar hakan,
mu'kaddari ne,kuma Allah ya riga ya 'kaddara mutuwar babalaji da maami a wannan ranar ko
da kuwa hashim bai zo ba,sannan yayi masu nuni da sakayyar Allah akan hashim na jarabtarsa
da Allah yayi da soyayyar bolaji! Oba ya cigaba da masu nasiha,har sai da jikinsu yayi sanyi!
Mai martaba shima ya 'kara basu èa'kuri,sannan ya umarci hashim da ya nemi yafiyarsu!

Hashim ya basu ha'kuri ya kuma nemi yafiyarsu,a take suka ha'kura suka fawallawa Allah
lamarin,ita ko bolaji bataso faruwan hakan ba!

Mai martaba ya ciro awarwaron zinare guda uku daga aljihun alkyabbarsa ya mi'kawa bolaji a
matsayin sadakinta!
Bolaji tana ji tana gani aka d'aura aurenta da hashim!

Jiki a sanyaye ta shige cikin gida,bamidele ya bi bayanta ,yana shiga gidan,ya tarar da bolaji
zaune a tsa'kar gida tana risgar kuka,bamidele ya zauna kusa da ita ,ya kamo hannunta yana
bata hakuri,ya kuma yi mata nasiha sosai akan ta zauna lafia da mijinta da danginsa ,kuma
yana da tabbacin cewa hashim bazai ta6a wula'kantata ba,tunda yana sonta!
Hashim kuwa ya kwashe kayansa daga motarsa ya zuba a booth din motar da maimartaba
sukazo da ita,sannan ya dam'kawa MD mu'kullin motar,wato ya bashi kyautar motar!

A haka su iya folake da funmilayo suka shirya ta cikin buba da iro ,suka kafa mata d'aurin
ashoke ,sannan suka lullu6eta da mayafi,suka fice da ita!
A motar maimartaba suka sata,bolaji sai kuka take,shi kanshi bamidele ya tausaya mata ,jaka
ya mi'ka mata mai dauke da takardunta da album d'inta!
Maimartaba ,oba ,da hashim sukayi sallama da mutanen yankin bayan sun raba masu kud'i
,sannan suka shige mota,suka wuce tare da bolaji masarautar osun suna masu d'agawa yan
yankin hannu!

A masarautar osun ,kuyangu da hadimai suka gyara bolaji,sarauniya ta bada umarnin a shirya
bolaji cikin leshi da ashoke masu kyau da tsad'a,da kuma yari da sar'ka na coral beads masu
kyau da she'ki,sannan mai make up itama tayi nata aikin!
Bolaji ita dai nata idanu,hannunta ri'ke da jakar da bamidele ya bata d'azu!

¤¤¤¤
Misalin 'karfe 5:00pm jirginsu mai martaba ya sauka a filin airport na sultan bello dake sokoto!

Maimartaba ne a gaba wajen saukowa daga jirgi,sai hashim wanda yake rungume da bolaji,sai
sauran tawagar sarki !

Royal chaffeurs daman suna jiransu da motoci a bud'e , mai martaba da hashim &bolaji suka
shig mota d'aya,tawagar sarki suka shige sauran motocin,dogarawa hannunsu ri'ke da jakar
bolaji dakuma jakar kayan hashim suma suka shige tasu motar!

Motocin a jere [convoy] suka fice daga airport tare da wucewa yankin yabo,masarautar moddibo
,inda fulani da nawwara suke jiran isowar maimartaba da yarima cap.t hashim!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/16, 12:16 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

~26~

Fulani da nawwara sun shirya cikin kaya na alfarma,sai zuba 'kamshi suke,ita kuwa ummu ko
a jikinta tunda ba sultan bane zai dawo,tana d'akinta tana karatun al'qur'ani!
Bayan fulani ta tabbatar da kamalluwar komai tun kama daga abinci,abinsha,da kuma da'kin
kwanansu,hatta ruwan wanka sai da tabbatar da ancika bath tubs da ruwan turare!

Misalin 5:00pm motoci suka fara shigowa harabar masarautar modibbo!
Da sauri royal guards suka bubbud'e masu 'kofofi suka fito,mai martaba ne ya fara fitowa sai
hashim da bolaji,sai kuma sauran yan rakiya, bayan mai martaba ya sallami tawagarsa sun
watse,sai ya maido da dubansa ga bolaji fuskarsa d'auke da murmushi yace ' welcome to our
palace my daughter',kanta a sunkuye ta amsa da 'thank you sir',mai martaba ya dubi hashim
yace 'kai kuma ko da munshiga ciki,kar ka kuskura ka shaidawa ummanka batun aurenka ,ko
da kuwa ta tambayeka wacece ita,kar ka ce mata komai ,ka bari da kaina zan mata bayani idan
mun huta',hashim ya amsa da 'angama ranka shi dade!'
A haka suka d'unguma cikin gida bisa rakiyar royal guards wanda hannunsu ke ri'ke da jakar
bolaji da hashim!

A kofar shiga main palace palour suka tadda fulani da nawwara da hadimai suna jiransu,mai
martaba ya amsa gaisuwar fulani da nawwara da sauran hadimai,sannan ya wuce ciki ya barsu!

Bayan Wucewar maimartaba fulani tasa hannu ta rungumo hashim tana ce masa 'welcome
home my souldear,my charming prince,the soldier of the nation! Murmushi hashim yayi yana
cewa 'thank you my gorgeous mother ,dafatan na sameku lafiya', fulani ta amsa da 'lafiya lau'
sannan ta nuna nawwara da yatsa tana cewa 'ga nawwara nan danake maka
zancenta',nawwara cike da kwarkwasa da yanga,ta karkace hanci kamar wata kuturwa tana
cewa 'welcome yaya hash,how's the journey',tana mai juya idanu!
Hashim yasa hannu ya jawo bolaji[wacce kanta ke sunkuye] ,jikinsa yana mai cewa
nawwara'the journey was awesome',sannan ya dubi bolaji tare da cewa 'lets go in,it seems like
you are exhausted'!
Fulani baki hangame ta dubi hashim sannan ta dubi bolajin da sai yanzu ta lura da ita,ta jinjina

kanta kamar kad'angaruwa tana mai cewa 'souldear wace kuma wannan',hashim ya murmusa
sannan ya 'kara rungumo bolaji ta gefensa da kyau ,sannan yace 'umma ,sunanta bolaji!'
,'gwalagwaji' fulani ta maimaita a firgice hannunta akan kirji ,hashim yace 'a'a bolaji
sunanta,sauran bayani zakiji a gun abba anjima',sannan ya dubi bolaji yana ce mata 'meet my
mother' ,bolaji ta d'ago idanunta ,fuskarta ba yabo ba fallasa tace'good evening ma',fulani kasa
amsawa tayi domin kwata kwata noturan kanta sun kunce,ganin haka yasa hashim ya ja bolaji
suka shige ciki tare da wucewa d'akinsa!

Nawwara ce ta ta6a fulani,wanda hakan yasa fulani tayi firgigit ta dawo hayaccinta, kamar
wacce ta tashi daga bacci,sannan ta sauke numfashi tana cewa 'tir'kashi,yau naga abinda zai
hanani bacci',ta cigaba da cewa 'nawwara YARE fa idanuna suka gane mini',nawwara ta amsa
da cewa 'ni ba wannan ba,ala'karsu da yaya hash nakeson insani ',fulani ta amsa da 'nima ban
sani ba,amma mu jira muji sauran bayani a gun mai martaba kamar yadda souldear d'in ya
fad'a,na tabbata zamu samu amsoshinmu acikin bayaninsa!'

¤¤¤

Bayan hadimai sun ajje jakar kayan bolaji da hashim sun fice,hashim dake zaune akan
couch[kujera] ya dubi bolaji data tsaya a tsaye 'kerere tana 'karewa d'akin kallo,murya a
tausashe hashim yace 'my better half,please sit down',harara ta watsa masa tare jan dogon
tsaki ,hashim ya murmusa kawai ,a fusace ya fisgo hannunta ta fad'o kansa,ya gyara mata
zamanta sosai akan cinyarsa,hannu yasa ya d'auko glasscup dake gefensa mai d'auke da
ruwan sanyi,ya kai bakinta,sanin cewa yanzu zai murd'e mata hannu yasa ta fara shan ruwan
,kuma sanyin ruwan da ya ratsa ma'kogoranta yasa ta shanye ruwan tas!
Hashim ya ajje cup din,sannan ya fara cire mata d'ankunne da sar'ka,ya kuma warware mata
d'aurin ashoken dake kanta!
Bolaji ji take kamar ta fasa ihu ,sai tsaki kawai take!
Hashim ya tureta daga kan cinyarsa a hankali,ya zaunar da ita akan couch d'in,mi'kewa yayi
yana cire kayan jikinsa,sai da ya saura daga shi sai singlet da boxer ,sannan ya shige toilet!

Bolaji tayi 'kwafa ta tallafo kumatunta da hannu biyu ,tace 'chai,i don suffer,me bolaji don
become oga hitler wife by force by fire,chai chai,na my mouth cause am,i go carry my big mouth
promise am marriage if e go farm,i think sey the mumu no go fit farm,see the wahala wey this
promise come land me into,but no lele,GOD dey'
Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL=YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

~26~

Fulani da nawwara sun shirya cikin kaya na alfarma,sai zuba 'kamshi suke,ita kuwa ummu ko
a jikinta tunda ba sultan bane zai dawo,tana d'akinta tana karatun al'qur'ani!

Bayan fulani ta tabbatar da kamalluwar komai tun kama daga abinci,abinsha,da kuma da'kin
kwanansu,hatta ruwan wanka sai da tabbatar da ancika bath tubs da ruwan turare!

Misalin 5:00pm motoci suka fara shigowa harabar masarautar modibbo!
Da sauri royal guards suka bubbud'e masu 'kofofi suka fito,mai martaba ne ya fara fitowa sai
hashim da bolaji,sai kuma sauran yan rakiya, bayan mai martaba ya sallami tawagarsa sun
watse,sai ya maido da dubansa ga bolaji fuskarsa d'auke da murmushi yace ' welcome to our
palace my daughter',kanta a sunkuye ta amsa da 'thank you sir',mai martaba ya dubi hashim
yace 'kai kuma ko da munshiga ciki,kar ka kuskura ka shaidawa ummanka batun aurenka ,ko
da kuwa ta tambayeka wacece ita,kar ka ce mata komai ,ka bari da kaina zan mata bayani idan
mun huta',hashim ya amsa da 'angama ranka shi dade!'
A haka suka d'unguma cikin gida bisa rakiyar royal guards wanda hannunsu ke ri'ke da jakar
bolaji da hashim!

A kofar shiga main palace palour suka tadda fulani da nawwara da hadimai suna jiransu,mai
martaba ya amsa gaisuwar fulani da nawwara da sauran hadimai,sannan ya wuce ciki ya barsu!

Bayan Wucewar maimartaba fulani tasa hannu ta rungumo hashim tana ce masa 'welcome
home my souldear,my charming prince,the soldier of the nation! Murmushi hashim yayi yana
cewa 'thank you my gorgeous mother ,dafatan na sameku lafiya', fulani ta amsa da 'lafiya lau'
sannan ta nuna nawwara da yatsa tana cewa 'ga nawwara nan danake maka
zancenta',nawwara cike da kwarkwasa da yanga,ta karkace hanci kamar wata kuturwa tana
cewa 'welcome yaya hash,how's the journey',tana mai juya idanu!
Hashim yasa hannu ya jawo bolaji[wacce kanta ke sunkuye] ,jikinsa yana mai cewa
nawwara'the journey was awesome',sannan ya dubi bolaji tare da cewa 'lets go in,it seems like
you are exhausted'!
Fulani baki hangame ta dubi hashim sannan ta dubi bolajin da sai yanzu ta lura da ita,ta jinjina
kanta kamar kad'angaruwa tana mai cewa 'souldear wace kuma wannan',hashim ya murmusa
sannan ya 'kara rungumo bolaji ta gefensa da kùau ,sannan yace 'umma ,sunanta bolaji!'
,'gwalagwaji' fulani ta maimaita a firgice èannunta akan kirji ,hashim yace 'a'a bolaji
sunanta,sauran bayani zakiji a gun abba anjima',sannan ya dubi bolaji yana ce mata 'meet my
mother' ,bolaji ta d'ago idanunta ,fuskarta ba yabo ba fallasa tace'good evening ma',fulani kasa
amsawa tayi domin kwata kwata noturan kanta sun kunce,ganin haka yasa hashim ya ja bolaji
suka shige ciki tare da wucewa d'akinsa!

Nawwara ce ta ta6a fulani,wanda hakan yasa fulani tayi firgigit ta dawo hayaccinta, kamar
wacce ta tashi daga bacci,sannan ta sauke numfashi tana cewa 'tir'kashi,yau naga abinda zai
hanani bacci',ta cigaba da cewa 'nawwara YARE fa idanuna suka gane mini',nawwara ta amsa
da cewa 'ni ba wannan ba,ala'karsu da yaya hash nakeson insani ',fulani ta amsa da 'nima ban
sani ba,amma mu jira muji sauran bayani a gun mai martaba kamar yadda souldear d'in ya
fad'a,na tabbata zamu samu amsoshinmu acikin bayaninsa!'

¤¤¤

Bayan hadimai sun ajje jakar kayan bolaji da hashim sun fice,hashim dake zaune akan
couch[kujera] ya dubi bolaji data tsaya a tsaye 'kerere tana 'karewa d'akin kallo,murya a
tausashe hashim yace 'my better half,please sit down',harara ta watsa masa tare jan dogon
tsaki ,hashim ya murmusa kawai ,a fusace ya fisgo hannunta ta fad'o kansa,ya gyara mata
zamanta sosai akan cinyarsa,hannu yasa ya d'auko glasscup dake gefensa mai d'auke da
ruwan sanyi,ya kai bakinta,sanin cewa yanzu zai murd'e mata hannu yasa ta fara shan ruwan
,kuma sanyin ruwan da ya ratsa ma'kogoranta yasa ta shanye ruwan tas!
Hashim ya ajje cup din,sannan ya fara cire mata d'ankunne da sar'ka,ya kuma warware mata
d'aurin ashoken dake kanta!
Bolaji ji take kamar ta fasa ihu ,sai tsaki kawai take!
Hashim ya tureta daga kan cinyarsa a hankali,ya zaunar da ita akan couch d'in,mi'kewa yayi
yana cire kayan jikinsa,sai da ya saura daga shi sai singlet da boxer ,sannan ya shige toilet!

Bolaji tayi 'kwafa ta tallafo kumatunta da hannu biyu ,tace 'chai,i don suffer,me bolaji don
become oga hitler wife by force by fire,chai chai,na my mouth cause am,i go carry my big mouth
promise am marriage if e go farm,i think sey the mumu no go fit farm,see the wahala wey this
promise come land me into,but no lele,GOD dey'
Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/16, 12:22 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

~27~

Fitowar hashim daga toilet ne ya katsewa bolaji zancen da take,d'agowa tayi takai duba
gareshi,sauran 'kiris ta sume lokacin da idanunta suka mata tozali da hashim sanye da towel
kawai a 'kugu,jikinsa smooth babu d'igon tabo,faffad'an kirjinsa a cike tam yake da tsoka amma
babu suma,cikinsa a tsu'ke wanda six packs suka 'kawata,bolaji ita kanta tasan hashim namiji
ne mai kyau da tsarin halitta!
Hashim ne ya 'karaso ya hure mata idanu,tayi firgigit ta dawo hayaccinta,ta harareshi taja
tsaki,bai bi takanta ba,ya tayata cire kayan jikinta,ya cicci6eta ya kai ta toilet,ya fito ya shirya
cikin wata ba'kar jallabiya !
Bolaji ta fito daga toilet ,jikinta rufe da towel,hashim ya mi'ka mata jallabiya ta saka,sannan ta
jawo jakarta ta ciro hijab tasaka,sannan ta d'aura zanin leshin da ta cire!
Hashim ya jasu sallar maghrib,bayan sun iddar ya ja hannunta suka fice !
A kan dinning suka iske maimartaba,fulani,ummu da nawwara!
Kujera hashim ya jawo, bolaji ta zauna,sannan shi ma ya zauna a kujerar dake kusa da kujerar
bolaji,kuyanga ta yi serving d'insu !

Misalin 'karfe 8:50pm na dare,maimartaba yana zaune da fulani da ummu a restroom!
Mai martaba yayi gyaran murya ya fara yiwa fulani fad'a akan abinda tasa hashim yaje ya

aikita,fulani ta tsure tana bashi ha'kuri,mai martaba yayi mata tatas ,sannan kuma ya labarta
masu komai da yasani game da ala'kar hashim da bolaji har izuwa aurensu a yau,suka taho da
ita!
Fulani 'kiris ya rage zuciyarta ta tarwatse,amma haka ta tattaro nutsuwa da fara'a ta shimfid'a
akan fuskarta tanuna tsantsan murnarta ga auren hashim da bolaji!
Ummu itama taji dad'in wannan aure a zuciyarta ,amma a fili sai tayi addu'a kawai!
Kasancewar ummu ke da girki,hakan yasa fulani ta mi'ke ta fice ta nufi d'akinta!

Hashim ya gama shigar da duk wani informations ta laptop d'insa,kasancewar gobe zai wuce
liberia inda aka turasu wani aiki har na tsawon wata d'aya,kuma sunada damar tafiya da
matayensu at thier own risk,bayan ya gama da laptop d'in,kashewa yayi ya mi'ke ya cire kayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login