Showing 3001 words to 6000 words out of 61652 words
da alkunya,magana wuya yake mata,bata da tashin
hankali ,gata da sanyin rai da kuma ha'kuri!
Bayan ansha biki ta tare a sokoto government house,suna zaune lafiya da fulani,babu matsala
ko kad'an a zaman nasu!
Bayan Wata goma sha d'aya[11] da auran,naja'atu ta haifo santalalen d'anta ma'aboci kyawu da
kwarjini!
Kowa ya yi farinciki da wannan haihuwar musamman Attahiru da fulani!
Ranar suna aka rad'awa yaro suna HASHIM!
Watan hashim goma shad'aya ,naja'atu ta cireshi daga nono,ta had'a kayansa kakaf ta mi'kawa
fulani shi kyauta!
Fulani tayi murna da wannan kyauta da naja'atu tayi mata,domin har kuka sai da tayi,kuma
daman Allah ya d'aura mata 'kaunar hashim tun ranar da aka haifeshi!
Attahiru yayi ta shi wa naja'atu albarka!
Hashim yana da shekara d'aya,tenure d'in mahaifinsa ta 'kare! Suka tattara suka bar state
government house, bayan tsohon governor attahiru yayi handing over ga sabon governor!
A wannan lokacin ne Allah yayi wa sarki abbas rasuwa!
Sarauta da mulki ya dawo kan sarki attahiru modibbo !
Mai martaba sarki Ya cigaba da gudanar mulkinsa cikin aminci da adalci,domin su kansu
al'ummar yankin na 'yabo' sun san cewa masarautar modibbo ta samu chanji da cigaba ba
kad'an ba,domin ko ta fannin ginin masarautar an samu chanji,domin duk bayan shekara uku
mai martaba yake sawa a canja komai na cikin masarautar izuwa tsari na zamani! Sai da yarima hashim ya shekara 5 ,sannan fulani ta samu juna biyu!
Bayan wata goma ta haifo santalelen d'anta ,ranar suna ya ci sunan sarki abbas,amma da
[SULTAN] ake kiransa!
¤¤¤¤¤BAYAN SHEKARU ASHIRIN [20] ¤¤¤¤¤!
Written by:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/14, 6:42 PM] ‪+234 810 476 6513‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE
~7~
Ba'kar Mota 'kirar pathfinder akayi parking a
harabar gidan ! Cike da hanzari royal chaffeur
[direba] ya fito daga gidan gaba ya zo ya bud'e
kofar gidan baya !
Saurayi,matashi ,maji 'karfi,mai kwarjini da kyawun
fuska gami da kyawun sura ,wanda shekarunsa
basu wuce ashirin da biyar[25] ba ya fito daga
gidan bayan,yana sanye da uniform na sojoji
wanda suka masa d'as a jikinsa!
Wannan matashi ba kowa bane face
'CAPT.YARIMA HASHIM ATTAHIRU MODIBBO!
A 'kasaice ya d'aga kansa ya dubi masarautar
modibbo fuskarsa d'auke da murmushi,yana mai
yaba tsarin palace d'in ,domin ko a 'kasashen
larabawa sai haka!
Cike da takun 'kasaita ya nufi hanyar cikin gida!
Royal guards sai zubewa suke suna kwasar
gaisuwa ,hannu kawai yake d'aga masu!
Har ya iso 'kofar da zata sadashi da cikin palace
d'in!
A gaban 'kofar! ,Fulani ce tsaye tare da hadimai
,fuskarta d'auke da murmushi,ganin yarima hashim
yasa ta ware hannayenta tana cewa 'come to me
my prince charming,the soldier of the nation!
The pride of the of the modibbo's palace!
my soul dear,welcome home'
Fad'awa yayi jikinta yana cewa 'my gorgeous
umma! i miss you so much,dafatan na sameku
lafiya' 'lafiya lau my souldear' fulani ta bashi amsa
tare da jan hannunsa suka shige ciki,hadimai na
biye dasu ,suna yiwa yarima hashim kirari,basu
tsaya a ko ina ba sai a tsakiyar palace parlour
wanda aka 'kawata da purple velvet royal chairs na
zamani da curtains masu kyau!
Fulani ta dubi hadiman tare da cewa 'kuje ku
tabbatar da komai da yarima zai bu'kata a
d'akinsa an tanada' ,'angama ranki ya dad'e'
hadiman suka fad'i tare da wucewa domin cika
umarnin fulani!
Fulani takai dubanta ga hashim tana cewa 'my
souldear yanzu ka je ka gaida ummun ku
[naja'atu],bayan kun gaisa ,sai kaje da'kinka and
freshen up,sannan kaje turaka ka gaida
mahaifinku,after that kazo dinning ka ci dad'ad'an
abinci dana dafa maka da hannuna' ,hashim yayi
murmushi yace 'angama your majesty,your wish is
my command' ,sannan ya wuce ya nufi hanyar da
zai sadashi da bangaren mahaifiyarsa!
Sultan ne ya tareshi yana cewa 'd'an gatan umma
kenan,tun d'azu nake jiran isowarka,amma umma
sai da ta rigani ganinka ' hashim yayi murmushi
yana cewa 'naughty bro,ba dole ta rigaka,duk fad'in
gidannan umma ta fi kowa 'kaunata ' ,sultan ya
cafke da cewa 'ba sai an fad'a ba,by the
way,welcome home big bro ,ya aiki da kuma fama
da zaman daji' ,'alhamdulillah' hashim ya bashi
amsa tare da cewa 'yaushe ka dawo daga
malaysia?' 'shekaran jiya na dawo for good ,cause
i'm done with my degree programme,yanzu haka
service zan tafi in the next 2weeks domin har an
aiko min da posting letter' ,hashim yace 'congrats
bro,yanzu ka zama bigboy fah,ina sukayi posting
d'inka?' ,'enugu!' sultan ya bashi amsa , hashim
yace 'enugu kam is a nice place to be,zaka ji
dad'in garin sosai' ,sannan ya ri'ke hannun sultan
yana cewa 'muje ka rakani gun ummu in
gaisheta!',hannunsu ri'ke da juna suka wuce part
d'in ummu [naja'atu]!
Written by
[10/14, 6:43 PM] ‪+234 810 476 6513‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE
~8~
Zaune akan darduma suka riski ummu tana
karatun al'qur'ani,neman waje sukayi suka
zauna,har sai da ta idar,sannan tayi addu'a suka
shafa tare,a sanyaye ta rufe al'qur'ani tare da kai
dubanta ga sultan tana cewa 'd'ana kazo a dai dai
kuwa,d'azunnan dama maka fura,duba fridge d'in
can ka d'auko' ,sultan baki a washe ya nufi fridge
d'in ya d'auko robar damammiyar furar ya dawo ya
zauna yana mai cewa 'ummu you are the best
mom on earth' ,murmushi kawai tayi !
Hashim ne yayi gyaran murya tare da cewa 'ummu
ina wuni,dafatan na sameku lafia' ,'lafia lau,an
dawo?' ummu ta fad'a ba tare da ta dubeshi ba
,'eh shigowata kenan ummu!' ,'toh madallah'
abinda ta fad'i kenan sannan ta cigaba da jan
sultan da hira,inda sabo hashim ya riga ya saba
da halin ko in kula da ummu take nuna masa
kasancewarsa d'an fari,domin tafi sakarwa sultan
fuska tare da jansa ajiki,shi kuwa yafi samun
kulawa a gun fulani!
A haka ya fice ya bar ummu da sultan suna
hira,sultan na shan fura!
Da'kinsa ya nufa,yana shiga ya rage kayan
jikinsa,ya fad'a bathroom yayi wanka tare da yin
alwala,ya fito ya shirya cikin wata ba'kar jallabiya
mai taushi,ya kuma gabatar da sallar zuhr,sannan
ya fice ya nufi palace parlour!
A kan dinning ya hango mai martaba,fulani,ummu
da sultan suna cin abinci!
Dinning Table d'in ya nufa ya zauna ba tare da
yayi wa kowa magana ba,kasancewar idan suna
cin abinci basa magana,jakadiya mara'kisiya ce
tayi wa hadimar dake serving abinci nuni da ido
datayi serving d'in yarima,da hanzari ta zuba masa
abinci a plate kamar yadda ta zubawa kowa d'azu
,sannan taja gefe ta 'kame ,kamar yadda jakadiya
ta 'kame a gun ita ma!
Bayan sun ci sunyi nak ,sai suka d'unguma suka
dawo restroom,inda yawanci suke zama suyi hira a
tsakaninsu,bayan sun zazzauna,sai hashim ya
russuna ya gaida mai martaba,mai martaba ya
amsa masa da fara'a yana mai shafa masa kai
yace 'd'azu ummanka take sanar dani
dawowarka,dafatan babu matsala a can inda aka
turaku kwantar da tarzomar' ,'alhamdulillah babu
matsala' ,'toh Allah yayi maku albarka' ,fulani tayi
caraf tace 'amin!',
sultan yayi 'kwafa yace 'kaji su umma masu
d'a' ,fulani ta harareshi tace 'fad'i ka 'kara fad'a
da babban murya',ummu tayi murmushi ta shafa
kan sultan tana cewa 'rabu dasu d'ana,kaima Allah
yayi maka albarka' ,'amin ummu na' ,sultan ya
fad'i tare da kwantar da kansa akan cinyarta ,yana
mai yiwa hashim gwalo!
Mai martaba yayi dariya yace 'ku da 'ya'yan naku
baku da dama wallahi' ,sannan yayi gyaran murya
yace 'hashim yaushe zaka koma? ' ,'on monday
zan koma kaduna inyi reporting' 'jibi kenan?'mai
martaba ya tambaya,'insha Allahu' hashim ya
amsa,mai martaba yace' Allah ya kaimu ' sannan
ya dubi sultan yace 'ranar talata ka shirya zamuje
osun state,zan dubo company,MD yayi min waya
akan cewa ma'aikatan company sun tafi yajin
aiki,so zanje da kaina in ji dalili,in kuma kwantar
masu da hankali ,in kuma shawo kan
matsalar'',sultan yace 'toh Allah ya kaimu
abba' ,fulani ta yamutsa fuska tace 'kaji tsiyar
yarbawan kenan,duk garuruwan hausawan dake
fad'in nigeria ,basu isheka bud'e company ba ,sai
can garin su oduduwa da sango ka idanunka suka
hango,i ga irin ta nan,da zaka bi shawarata da ka
rufe kamfanin wallahi,ka dawo ko nan cikin sokoto
ne ka bud'e wani' ,mai martaba yayi murmushi
yace 'fulani kenan ban san meye had'aki da
yarbawa ba,mutanennan na zauna dasu kuma naji
dadin zama dasu a lokacin danayi bautar 'kasa a
can ,hakan yasa na yanke shawarar bud'e kamfani
acan yankin erin dake jihar osun,domin taimakawa
talakawa mazauna wannan yankin samun aiki a
kamfanin,saboda su sami abinda zasu ciyar da
iyalansu,kuma naga inada kamfanin purewater da
tumatir a kaduna,da kuma kano' ,fulani tasan in ta
tsaya jin kalaman bakin mai martaba yanzunnan
ranta ne zai 6aci ,zuciyarta ta buga a banza,domin
akan posting d'in sultan da akayi zuwa garin enugu
,ta so yayi redeploying ya dawo nan arewa, amma
mai martaba ya hana,domin shi zuciyarsa babu
wannan 'kabilancin sam !
Numfashi ta sauke tace 'hmm Allah ya
taimaka,amma su kansu YARE babu yaren dasuka
tsana sama da hausa'
ummu tayi murmushi tare da cewa 'haba yaya,ki
daina fad'in haka ,dukkanmu d'aya muke a gun
Allah'
a haka suka cigaba da hira har lokacin sallar asr
yayi,suka tashi domin suje su gabatar da sallah!
[10/14, 6:45 PM] ‪+234 810 476 6513‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE
~9~
MODIBBO & SONS .CO kamfani ne da yayi fice a
nigeria kasancewar suna da branches{reshe}a
garuruwa daban daban a 'kasar nigeria MODIBBO
& SONS .CO kamfani ne da yayi fice a nigeria
kasancewar suna da branches{reshe}a garuruwa
daban daban a 'kasar nigeria!
Suna da kamfanin pure water a kano,kamfanin
tumatir a kaduna,kamfanin auduga a katsina da
sauransu!
Duka kamfanonin mallakin masauratar modibbo ce
'kar'kashin jagoranci da mallakar sarki attahiru
modibbo!
Shekaru 10 da suka wuce ,mai martaba da kanshi
yaje jihar osun ,yankin erin ,ya shaci fegi aka siyar
masa ,ya bada kwangilar gina babban kamfanin
manja
[RED OIL COMPANY]!
Bayan an gama gina wannan kamfanin!,a kamfanin
an kwashi ma'aikata da dama tunda ga kan
manyan ma'aikata masu takardu har izuwa
'kananun ma'aikata irinsu leburori da masu gadi
musamman mazauna wannan yankin!
Abdulrazak adebayo wanda aka fi sani da baba
leji, ya kasance lebura a wannan kamfanin!
Yana zaune da iyalansa a wannan yankin erin
,yana da matar aure guda d'aya mai suna
riskatu,sai 'ya'yansa guda biyu mace da namiji!
Namijin sunansa bamidele ,macen kuma sunanta
BOLAJI!
Wanda a yanzu haka shekarar bamidele 23 ,yayin
da bolaji take da shekara goma sha takwas!
Bamidele yana aji uku a secondary ya bar
makarantar wato yayi dropping out ,sanadiyar babu
da suke fama da ita,ya kama harkar sai da
bunburutu wanda maami [riskatu] ta bashi jari!
d'an abinda yake samowa a cinikin bunburutun,da
shi suke samu su siyi abinci,albashin babalaji ba
wani afki gareshi ba ,domin Allah ya had'asu da
azzalumin shugaba a kamfanin,wanda sai ayi wata
5 ko 6 ,bai biya 'kananun ma'aikata ba!
BOLAJI yarinya mai 'ko'kari da haza'ka,tanada
garin jiki,ba'ka ce,amma tanada kyawun fuska da
kyawun sura ,domin ko a yankin erin kafin a sami
mace ba'ka mai irin kyawunta sai an tona!
Ta kasance yarinya mafad'aciya idan an
ta6ota,tana da zafi,kuma tana da sanyi a wasu
lokutan,gata bata da tsoro ko kad'an,ta kasance
ruwa mai sa 'kwai yayi tauri ,haka zalika mai sa
dankali yayi laushi,tana tafiyar da mutum ne ta
yadda ya tafiyar da ita!
Yanzu haka tana ss3 a G.S.S ERIN ,suna zana
jarabawar w.a.e.c wanda kud'in w.a.e.c da 'kyar
aka had'a aka biya mata,domin tana 'kaunar
karatu,bata san ta kasance kamar d'an uwanta
bamidele!
¤¤¤¤
Da sallama ta shigo gidan hannunta ri'ke da
qur'ani! Ta dubi maami dake faman sa'ka ashoke
[sana'ar ta kenan] tace 'bawoni!' tana mai cire
hijabinta ,maami ta dubeta tace 'ahh bolaji are you
back ,welcome' ,'thank you oh maami,how your
body' ,'i thank oluwa oh ' maami ta bata amsa,
bolaji ta ja kujera ta zauna kusa da maami tana
cewa 'maami mi! This your pregnancy eh,i wish
make you born twins,boy and girl ,so that i will
back one and hold one' ,maami tayi murmushi tace
'bolaji ahh ,you no dey shame,since the time wey
you dey small i no get bele,na now wey you don
grow finish,i com dey get another bele' ,bolaji ta
dubi turtsetsen cikin da ke jikin mahaifiyarta
haihuwar yau ko gobe,tayi murmushi tace 'na so
God dey take do his miracle oh,me i just dey pray
sey make you deliver safely'
'amin oh my daughter ,go kitchen carry your food
chop oh' maami ta fad'i cike da kulawa ! Bolaji ta
tashi taje ta d'auko abincin ta,sannan ta d'auko
littafin jarabawar da zasuyi gobe tana ci tana
karatu!
Written by : Abdulaziz ililee isma'il
Like · 2 · Reply · Report · Yesterday at 10:08am
Aminatu Yusuf Sokoto
=YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE
~10~
Tana gama cin abinci,ta ajje littafin,ta nufi kitchen
ta kwamfaci ruwa ta sha ,sannan ta had'a kan
kwanuka ta fito ta wankesu tas ,sannan ta dawo ta
zauna tana cigaba da duba littafinta ,maami tana
mata sannu ta hanyar cewa 'ekhuse' ,bolaji ta
amsa da 'eshe'!
Babalaji ya shigo da sallama,gaba d'aya suka
amsa ,bolaji taje ta amshi ledar hannunsa tana ce
masa 'ekabo' ,babalaji ya amsa 'my daughter
eshe',maami ta tashi da 'kyar tana gyara d'aurin
zanin nata,tabarma ta shimfid'a masa,tana mai
cewa babalaji 'ekabo' ,bayan ya zauna yana sauke
ajiyar zuciya yace 'iya bolaji[maman bolaji] eshe
oh,how body' ,'we thank God oh,my husband,how's
your day,hope it went well' ,bolaji ta iso da ruwa a
cikin kofin silva,ta russuna ta mi'kawa babanta,ya
amsa ya shanye tas,bayan ya shanye ya dubi bolaji
yana cewa 'thank you my daughter,may the
almighty oluwa bless you' 'amin oh' bolaji da
maami suka amsa!
Babalaji ya dawo da dubansa ga maami yana mai
cewa 'hmm,i'm tired oh,we the labourers have been
standing at the company's entrance for the past
4hours waiting for our 7month salary to be paid to
us,before we get back to work and call of the
strike,but the payment did'nt take place,instead the
manager told us to excersise patient,and we should
come back on tuesday cause the owner of the
company will come and tackle the
problems!' ,maami ta dubi mijinta cike da tausayi
tace 'this is wickedness,i don't know what this
country is becoming,but no wahala,oluwa dey ,he
dey watch and he's in control' ,babalaji ya amsa
mata da 'na so oh,let's wait for the tuesday,we
shall see' ,maami ta tashi ta d'auko masa abinci ta
kawo masa,yana ci ,tana masa firfita tare da jan sa
da hira!
¤¤¤¤
Ranar litinin misalin 7:30am hashim ya gama
shiryawa,yayi sallama da iyayensa,direba ya
saukeshi a airport,inda palace pilot ke jiransa,ya
shiga private jet d'insu,suka d'aga kaduna!
Misalin 'karfe 10 na dare ,mai martaba na zaune
kishingid'e a d'akin fulani,kasancewar ranar
girkinta ne!
Fulani ta dubi mai martaba tare da cewa 'gobe ne
tafiyar taku ko?' ,'insha Allah' mai martaba ya bata
amsa,fulani ta gyara zama tana cewa 'abban
hashim baka ganin cewa daraja da arzikin wannan
masarauta ya wuce ace ka bud'e kamfani[compani
es/factories] a garuruwa,ni a ganina sarauta da
mulkin ka sun girmi hakan, ,musamman kamfanin
pure water da aka bud'e a kano ,da kuma na
manja da aka bud'e a garinsu oduduwa,bai kamaci
wannan masarautar ba,da kuma kai kanka da ka
kasance tsohon gwamna' ,mai martaba yayi
murmushi wanda ya 'karawa fuskarsa kwarjini
,yace 'fulani kenan,ni ba kowa bane face d'an
adam kamar kowa,wad'annan kamfanonin ba'a
bud'e su domin samun kud'i ba ,an bud'esu ne
saboda talakawa mazauna yankin da aka bud'e
kamfanonin, su samu hanyar da zasu nemi halas
da guminsu ta hanyar samun aiki a
kamfanonin,kuma kinga a yanayin da 'kasar tamu
take ciki,aiki yana yi wa matasa wuyar samu duk
da kwalin degree d'insu,,kinga kenan samun aikin
matasa a kamfanonina zai sa a rage samun
matasa masu zaman banza da kashe wando
[jobless youths],kuma da kike cewa masarautar
nan ta girmi hakan,ta ina masarautar nan ta girmi
haka,me kike d'au sarauta a duniyar nan ne?,mu
da mutanen gari,musamman talakawa ,duk d'aya
muke a gun Allah!
sarauta da mulki sai sarautar ALLAH s.w.t 'malikul
mulk',mabuwayi,gagara misali,wanda dukkan mu
gaba d'ayan mu a 'karkashin ikonsa da mulkinsa
muke! kuma kamfani yanzu na fara 'bud'ewa ,in
akwai abinda yafi purewater 'kas'kanci idan har na
samu dama sai na bud'e kamfaninsa,in har hakan
zai zamo alkhairi ga al'ummar annabi muhammad
[s.a.w],musamman talakawa!
masarauta bata girmi yin ko wacce irin
halastaciyyar sana'a ba,ko da kuwa wannan
masarautar tana da daraja da arziki' ,jiki a
sanyaye fulani tace 'ALLAH ya bada lada,ya kuma
'kara arziki,na fahimci manufarka,kuma ina fatan
sauran sarakuna irinka zasu koyi da kai' ,mai
martaba yace 'amin fulani,addu'arku kawai nake
bu'kata a kullum,' ,haka suka cigaba hira na
farantawa juna rai ,har izuwa lokacin da bacci ya
riskesu!
[10/14, 6:49 PM] ‪+234 810 476 6513‬: =YARE BIYU=
{2tribes}
na ILILEE
~2~
Tsawa fulani ta dakawa sultan tana mai cewa ' kar
ka kuskura ka cire wandonka!' ,a tsorace sultan ya
mi'ke tsaye jikinsa na rawa ya dubi fulani yana mai
d'aure tazugensa a kunyace.
Fulani ta zabga masa harara,sannan ta dubi bolaji
dake kwance a yashe a sume,a fusace ta watsawa
sultan tambayar 'meye sameta?' ,sultan ya hau
inda inda yana sosa 'keya ya labarta mata abinda
ya faru!
Dogon tsa'ki fulani taja tana mai cewa 'toh
jarababbe,ayu,duk matan hausa/fulani dake cikin
fad'in garin nan basu isheka dannewa ba,sai
wannan YAREN,yaren ma bayarabiya,ni na rasa
meya ke rud'arku a tattare da ita da har hakan zai
ja hankalinku gareta,wallahi ina ba'kin ciki in wayi
gari inga wannan bayarabiyar yarinyar a
gidannan,yayanka yaje ya kwasota a matsayin
matar aurensa,kai kuma yau kazo zaka hai'ke
mata ko?,wallahi ina daf da tsine maka
albarka,domin bana fatan in had'a tsatso da
YAREN da ba hausa/fulani ba,kuma naga kaima
kana shirin bin sawun yayanka,tunda har ka fara
kokarin yiwa wannan bayarabiya fyad'e,toh nan
gaba ma ,bayarabiyar zaka auro d'ungurungum
kaima' ,sultan baki na rawa yace 'umma ki yi
ha'kuri,ita ma wannan tsautsayi ne ya kawo ni
wajenta,kuma tunda ban aikata ba,shikenan bazan
'kara ba!'
Tsaki fulani ta ja tana cewa 'ni ban hanaka neman
matanka ba,amma bana son kayi mu'amala da
YARE,ga yan mata kyawawa ,tsala tsala hausa/
fulani,ka nemesu mana,kuma wannan jinin
oduduwar wallahi tallahi sai