Showing 3001 words to 6000 words out of 108372 words

Chapter 2 - NA CUCE TA (1 to End) Complete by Zuwairat Ummu Maryam .pdf

Advertisement

karama ta haifi yusra da
Maryam Sannan Hajiya babba ta samu cikin Zainab, atakaice dai yaran Hajiya babba 4 yazid,
shahid, Zainab sai auta marzuq ita Kuma Hajiya karama nada 6, Sharif, yusra, Maryam,
mimata ihsan sai auta Ameera. Zaman su is very lovable saboda ko kadan alh bai basu room
din kishi ko wani abu makamancin wannan ba, he make all of them feel special don duk lokacin
da yake tare da daya yana mantar da ita wata kishiya, zai nuna maki babu kaman ki so
kowacce gani take yafison ta alhalin ba haka bane yana sonsu daidai amma fa bai wasa da
Hajiya babba saboda karamcinta.

Yau suna zaune falo Hajiya babba tare da Hajiya karama kowacce taci ado cikin expensive
swiss lace little brats of the house NA wasa cikin tsakiyan falo kaman yanda su Sharif ke kiran
marzuq ihsan da Ameera kenan,
Hajiya babba kam tamkar carbon copy NA yazid don komai nasu iri daya har red lips dinta.
Wata matace dauke da yar paper da pen hannun ta da alaman list take, Hajiya babba kallon
Hajiya karama tayi

"Ni iyakan abinda nakeson ayi kenan... Ki fada naki..." Tayi directing maganan ta to Hajiya
karama,
"Ni dai ayi dinner.. Ko Kuma party till dawn..." Tafada tana girgiza kirjinta, da ganinta irin civilised
women din nan ce, itama ta hadu ba kadan ba, dariya Hajiya babba tayi
"Kinsan Dan naki..Yana iya cewa bai attending..." Inji Hajiya babba,
"Kam har ya isa?.. AI bai isa ba...first wedding da zaayi a family din isa bala should be the talk
of the nation..." Hajiya karama ta fada, kallon Matan dake zaune tsakiyan su tayi Sannan tace
"Hajiya wedding planner...kiyi adding party till dawn...." Shuru tayi ta kalli kofan da aka bude,
shahid ne ya shigo ya zauna gefen Hajiya karama don mostly sunfi yi daita saboda Bata fiya
hanasu duk rashin jin da zasuyi ba, baki ta bude zatayi magana shima Sharif ya shigo ya zauna
dayan side din Hajiya karama, Hajiya babba kallon su tayi ta saki murmushi tare da girgiza kai,
Hajiya karama tacigaba dacewa
"As I was saying before my angels interrupt me...kiyi planning big till dawn party..." Wannan irin
shewa Sharif da shahid sukayi tare da manna mata kiss a both cheek dinta
"That's why I love you little mom..." Inji shahid don haka suke kiranta da little mom, dariya tayi
tana lumshe idanuwa don jindadi,
"Wallahi haka ya kamata ayi Kawai..." Inji Sharif, Hajiya babba dariya tayi tana cewa
"Ai kunsan da Kyar Zai yarda...kun San halin yayan naku..." Daure fuska sukayi shahid yace
"Big mom..Kawai ki fada mashi yayi zaman shi Chan abuja in yaso in an gama bikin sai ni da
Sharif mu saka matar a mota mu kai mashi..." Yafada babu wasa,
"Ai hakan Kawai zaayi...zuwan shi ma bai da amfani..." Inji Sharif,
"Kunci gidanku... First son dina kuke cewa hakan?... Zanci ubanku wallahi kunsan halina
sarai..." Hajiya karama ta daka masu tsawa, shuru sukayi din sun San tana Iya birkice masu
yanzu, Hajiya babba dai kallon su Kawai take with adoration, tana tunanin lokacin da akace
zaayi mata kishiya komai nata tsayawa yayi saboda bakin ciki amma yanzu kam kullum cikin
hamdala take da Allah ya hadata Dana gari,
"Kuma ki hada mana get together NA mothers Kawai..." Inji Hajiya karama, matar da aka kira da
Hajiya wedding planner sai rubuce2 kawai take, duk abinda aka fada sai ta rubuta, sai da aka
gama fada mata komai da zaa bukata sannan tace
"To zanyi listing komai Sannan in aiko maku da bill..." Inji Matan
"Wannan babu case..." Inji Hajiya karama dake magana tamkar danta zaayiwa biki, matar
mikewa tayi Hajiya babba da Hajiya karama suka bi bayanta, har bakin motan Matan suka
rakatq Sannan suka komo cikin part din Hajiya babba don most of the time nan suke zama suci
susha, har yan yaran ma basu zama a dakin wasansu sunfi son su kwaso kayan wasansu su
dawo part dinta Kuma bata hanasu tunda da akwai masu aiki da zasu gyara waje ko sun Bata.
Falo suka dawo suka zauna suna listing wayanda zasu gayyata din kar lokacin ya kara
matsowa su rikice, Hajiya babba NA fadan sunayen mutanen itakuma Hajiya karama NA
rubutawa cikin iPad dake hannun.



Sai daf da sallan ishai su dija suka dawo daga tallan daman kusan kullum haka suke dawowa
saboda sai bayan sallan asar suke tafiya, agajiye ta shigo gidan ba ko sallama ta shiga dakin ta

tarda ammi zaune su binto suna bacci kan tabarma, ajiye ruban tallan tayi da karfi ta zauna
kasa gaban ammi
"Sannu da dawowa..."
Ammi ta fada mata tana cire gammo daga kanta,
"Yauwa..." Ta fada tana kallon su binto dake bacci,
"Har sunyi bacci?.." Ta fada har lokacin Bata bar kallon su ba,
"Yan rigima sunyi bacci...ya kasuwa?..."
"Lafiya lau..." Ta amsa mata tana kwanciya kasan inda take,
"Madalla..."
"Ga kayan da kikace in sayo nan cikin roban,...." Ta fada tana nuna Roban data ajiye
"Yauwa yar albarka..." Ammi ta fada tana jawo roban gabanta tana kallon abubuwan da dija ta
sayo, dija gyara kwanciya ta tayi yanda zata Iya dauko kudin dake daure a haban zaninta, daga
kwance ta fara kunce daurin ta dauko kudin
"Ga sauran...dari biyar ne da ashirin.. NA sayi awara ta talatin cikin kudin..." Ta fada tana
mikawa ammi kudin
"To dijata...nagode kinji...dafatan babu Wanda yayi maki zancen banza yau?..." Daga kwance ta
girgizawa ammi kai
"Yau ban shiga garejin ba...cikin garin dauran na shiga kuma na saida duka...."
"To alhamdulillah...." Ammi ta fada tana jin dadi, ammi mikewa tayi ta dauki roban ta ajiye shi
gefe
"Ammi gobe Dan Allah a kai gero injin... Wallahi marata ke ciwo...." Tafada tana Dan dafa
maranta, ammi ajiye roban tayi ta dawo ta zauna
"To sai a kai injin din..amma ki kokarta muyi surfe mu wanke don mu bawa awaki su sha..." Dija
turo baki tayi tana cewa
"Ammi ni marata ke ciwo...irin ciwon da yayi min wancan lokacin yake yi min..."
"To kilan bakon watanne zai zo..." Sai lokacin dija ta tuna da watan da ya gabata ta fara ganin
jini Wanda ammi ta shaida mata cewa alaman girma ne.
"Wai ammi duk wata sai nayi wannan abun?..ni wallahi banason shi...." Tafada hannun ta biyu
kan maranta,
"Ai lalura ne Kuma Allah ne ya dorawa mata Kuma ba din bayason mu ba...wasu ma sai sun
nema amma basuyi...don haka ki bar cewa bakison shi...."
"To ammi..."
"Tunda bai kaiga zuwa ba kije kiyi sallan ishai...." Dija ta fi minti biyar kwance Sannan ta mike ta
fita ta dauki buga ta shiga kewayen su da aka zagaye da buhu. Few minutes later ta Fito tana
cewa
"Ammi yazo..." Tafada da karfi, ammi murmushi Kawai tayi Bata amsa mata ba.
[3:12PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 馃挏馃挍鉂ゐ煐ゐ煉欚煉�
NA CUCE TA
鉂ゐ煉滒煉涴煐ゐ煉氿煉�


庐zuwairat(ummu Maryam)

3鈨�




Da Sauri ta dawo cikin dakin tana cewa
"Ammi NA ganshi..." Tafada cikin jindadi
"Naji...wai in tambayeki...murnan me kike?...." Ammi ta tambayeta tana kallon ta,
"Babu komai..." Ta fada ahankali,
"Hmmm NA gane Kawai don bakison yin sallah ne...to kiji tsoron Allah... Maza ki tashi ki tafi
makaranta....nasan an zauna tunda anyi sallan ishai...." Ammi ta fada mata, nan ta kara Bata rai
tana cewa
"Ammi NA gaji..." Bata idaba ammi tayi mata dakuwa
"Kinci mai garinku...maza ki tashi ki tafi..." Ammi ta umarceta, bata fuska tayi kaman zatayi kuka
ta fara cewa.
"Ammi gasu binto basu je ba?...ni ki bari sai gobe.. " ta fada kaman zatayi kuka, baki ammi ta
bude tana kallon ikon Allah, tana mamakin yanda komai sai dija ta hada kanta da kanwarta,
komai Bata yarda itace babba sai tace su binto kasa da kasa
"Wai ke in tambayeki... Ke da binto waye babba?..." Ammi ta tambayeta tana kallon yanda
idanuwanta suka chanza kaman zatayi kuka
"Ni..." Ta amsa mata ahankali,
"To meyasa komai sai kin hada kanki da binto?... Baki San kome kika shi su ma Zasuyi ba?...
Ke ce babba son haka ki dinga daukan girma..." Ammi ta fada mata cikin lallashin,
"To ammi..." Ta fada rana turo baki don ko kadan Bata gamsu da maganar ammi ba, kullum
komai ita, shiyasa kullum tana aduan Allah yasa a dauketa, har wani lokacin adua take tana
cewa
"Allah kasa a saceni a kaini katon gida ko shara da wanke2 in dingayi..." Take fada duk lokacin
da take tallan fura ba kaman in ta zama frustrated.
"Maza tashi kar a fara ba dake ba..." Ammi ta fada mata,
"To..ammi amma ki bani ashirin din in kashe in naje chan..."
"Ban baki ashirin... Amma ga goma..." Ammi ta fada mata tana bata naira goma daga cikin
kudin data kawo, amsan kudin tayi Ta bude wata old Ghana must go ta dauko wata old and
faded pant tare da kyalle ta cire pant dake jikinta ta saka Wanda ta dauko tare da tura kyallen
data dauko, ta gyara daurin dankwalinta tana fita daga gidan babu hijab, tana tafiya tana kallon
yara dake wasa cikin hasken wata har ta kai kusa da wani mai nama, karasawa tayi kusa da
inda mutum yake
"Danmusa inayini..." Ta gaida shi tana kallon naman dake maiko a gabanshi
"Khadija ya kike?..." Inji saurayin Wanda bazai wuce shekara 18 to 20 ba
"Lafiya lau..." Ta amsa mashi ko blinking batayi saboda yanda take kallon naman, murmushi
yayi

"Har kun dawo kenan?..."
"Eh..." Ta amsa mashi atakaice, har lokacin tana kallon naman tana aduan Allah yasa ya
yanmata kaman yanda ya saba,
"Makaranta zaki je?.." Ya tambayeta
"Eh...", dariya saurayin yayi yana kallon yanda take lashe baki, yanka uku ya debo ya zuba cikin
takarda ya mika mata, kaman zakin daya shekara bai ci abinci ba ta miko hannu zata amsa sai
saurayin ya maida hannun shi yana kallon ta Sannan yace
" yaushe zaki bani amsa ta?..." Ya tambayeta ahankali, Dan turo baki tayi tana cewa
"Gobe..." Dariya saurayin yayi
Hmm dija sarkin wayau..kullum sai kice min gobe...to yaushe goben zai iso?..." Da Sauri tace
"Allah gobe zan baka amsa..."
"Allah ya kaimu goben... Amma in baki bani amsa ba bazan kara baki nama ba...kin amince?.."
Da Sauri ta gyada mashi kai tana cewa
"NA amince..." Sai lokacin ya mika mata naman, tana amsa ta bar wajen da Sauri tana bude
takarda naman, tana tafiya tana yaga kadan2 wai don kar ya kare. Haka tana zaune makaranta
tana cin namanta ahankali daman she's use to it.Har aka tashi karfe goma dija bata gama cinye
naman ba saboda yanda take yagan daman ahankali. Ana tashi ta tafi gida tana hamma,
daman Tasan kafin ta iso duk sunyi bacci don haka tana shiga gidan taja kaurensu da baida
sakata taje ta kwanta tana tunanin yanda gobe zai kasance mata.


Yazid bai shiga apartment dinshi ba sai bayan sallan ishai daman mostly sai bayan sallan ishai
yake shiga gida don quarters din is very lonely Kuma shi bayason hayaniya most especially
Kuma ba yanayin halinsu daya da sauran guys din ba don mostly su da yan mata suke wining
time dinsu shikuma da calling iyayenshi ko Kuma karatun alquran sai kuma kiran mufida Wanda
wani lokacin da wayan yake kwantawa a kunnenshi saboda ita.

Yana shiga apartment dinshi Wanda ta hadu daga company don komai is made abroad, ko
zama baiyi falo ba ya shiga daya daga cikin four bedrooms din ya cire kayan jikinshi yayi folding
dinsu tamkar mace ya ajiye su cikin closet ya shiga wanka ta fito bai wani shafa mai ba ya saka
jallabiya Sannan ya dauki wayanshi yayi dailing number Hajiya babba Alokacin duk suna babban falon alhaji suna fira yara suna wasa sai sai yanmatan na chatting
da wayansu ga katon naman akuya roasted suna ci ana hira, Hajiya dauka wayan tayi yan yara
suka taho wurin ta da gudu don sun san shine cos mostly lokacin yake kiran su, sallama Hajiya
babba tayi ya amsa yana cewa "My mommy good evening..."
"Evening sweetie... Ya aiki?..."
"Alhamdulillah... Ya gida da yara?..." Ya tambayeta a nutse, da Sauri yaran sukace
"Yaya ga mu...." Suka fada a chorus, Dariya yayi, Hajiya babba ta ajiye masu wayan bayan ta
sashi hands free, nan suka fara labari ko wa NA bashi labarin abubuwa kala saida suka gama
Sannan Hajiya babba ta dauki wayan suka fara hira tana cewa
"Son ga junior mom tana hada maka party till dawn..." Dariya yayi yace
"Small mom...nasan kina jina...banason party till dawn..." Ya fada yana Dariya,

Itama dariya tayi Sannan tace
"Kayi kadan..." Tafada cikin high voice, yanda zai jita da kyau, dariya ya karayi yana cewa
"Nidai ko kun hada ban zuwa...sai dai kuyi abunku Ku kadai..." Yafada cikin raha yana jiran
amsan small mom don yasan ta da tirjewa kan abu,
"Ai kayi kadan yaro...party kam an hada an gama..." Ta fada again da karfi, alhaji kam ko kallon
su baiyi sai cin naman yake yana korawa da juice while suma yan yaran suna ci suna wasa.
"Wai yaushe zaka dawo?..." Hajiya babba ta tambayeshi,
"Sai nan da sati biyu..." Ya amsa mata
"Kai yaro maza ka dawo...nan da sati biyu is too far..." Inji Hajiya karama,
"Sai lokacin hutuna zai fara..."
"Nidai ka dawo nan da sati daya..." Hajiya karama ta umarceshi,
"To momcy..." Ya amsa mata in a funny way.
"Ina twins?..." Ya tambaya, don haka yake kiran Sharif da shahid,
"Basu dawo ba..." Hajiya babba ta amsa mashi
"Aikensu akayi ko yawon ne Mara amfani?..." Ya sake tambaya, dariya Hajiya karama tayi tana
cewa
"Suna waje suna shan iska...."
"Ai ba zafi ke da akwai cikin gidan ba...bari in kira su..." Ya fada Sannan sukayi sallama, kashe
wayan yayi Sannan yayi dailing number shahid, alokacin Sharif na tukin mota shi Kuma shahid
na zaune, yana chatting, yana ganin kiran yazid ya kalli Sharif yace
"Guy ga vigilanty NA kira..." Yafada yana dariya, shima Sharif dariya yayi
"Kar kayi picking.. Kilan ya kira gida an fada mashi muna waje.." Kin picking sukayi har wayan
ya gama ringing, yazid dai girgiza kanshi yayi yana murmushi
"Sheggu..." Ya fada yana dailing number mufida. Sai da suka kusa hour biyu suna waya Sannan
sukayi sallama ya kwanta yana imagining nan da sati four yana da aure.

The following day ya shirya as usual ya tafi office daman a chan ake kawo mashi breakfast.

Dija kam sai data gama surfe geron ta wanke ta shanya Sannan ta shiga wanka, acikin karamin
toilet din Wanda babu cement ta tsaya tana kallon tsaraicin ta, daman tunda alamun girma suka
fara fito jikinta ta maida kanta tamkar madubi ba kaman in ta shiga kewaye, yau ma haka ta
tsaya tan kallon white skin dinta dake fari tas compared to her face don jikinta ya fi fuskan ta
haske nesa ba kusa ba, kallon yan boobs dinta tayi ta kurawa dark nipple dinta ido tana
mamakin yanda akayi Bata lura da sanda suka fara fitowa ba don ita kaman farat daya ta fara
ganin su,Dan juya baya tayi tana kokarin kallon ass dinta amma Bata gani kaman yanda ta
bukata, tafi minti talatin tana kallon kanta don ko kadan Bata gajiya da kallon kanta
"Wai ubanme kike in kika shiga kewaye?..." Ammi ta fada da karfi, da Sauri tace
"Ammi kashi nake..."
"Ke kullum sai in kin shiga wanka kike kashi?... Dalla maza ki fito kafin in sameki..." Ammi ta
daka mata tsawa
"To.." Ta amsa mata Sannan ta fara wanka. Ko.minti biyar batayi ba ta fito da daurin kirji ta shiga
daki ta shafa Vaseline ta saka wata faded but neat atamfa Sannan ta fito lokacin ammi NA jifan
Dan wake cikin tukunya

"Ke dauki yaji ki daka.." Ammi ta fada mata, turo baki ta karayi don one thing about khadija ko
kadan batason aiki ko sai goma zaa aiketa sai ta nuna bacin ranta dukda zatayi amma ba don
ta soba
Haka ta daka yaji tana turo baki har ta gama, bayan kaman minti arbain aka sauke danwake
sukaci Sannan ta tafi injin din. Da wuri ammi ta gama mulmula mata furan amma still sai bayan
sallan asar suka tafi tallan.


Hajiya karama ce zaune kusa da Hajiya babba a falon Hajiya babba tana cewa
"Gaskiya yaya nidai NA gaji da halin wannan yarinyan... Kokadan Bata daukan darasi...ka
barnatar da kaya..gaskiya wata yar aiki zan sake..." Inji Hajiya karama, Hajiya babba shuru tayi
for a while kaman mai tunani Sannan tace
"To me zai hana a karo maki wata batare da ki kori ita zulan ba?.." Hajiya babba ta fada mata,
da Sauri Hajiya karama ta girgiza kai
"Gaskiya ni ko kadan banason zama da wannan yarinyan yanzu..Kawai wata zansa antyn
katsina ta samo min..." Dariya Hajiya babba tayi tana cewa
"Har katsina Neman yar aiki?..."
"Yo yaya ya zanyi ?.. Ai gara katsina tunda yawancin yan Matan birnin nan sun fiya
wayewa...amma in aka samu cikin kauyen kayayau basu daukan abu for granted,..." Inji Hajiya
karama
"To shikenan amma Dan Allah karki sallami zulai...kinsan babu kyau hana mutum hanyan
samun abinci.. Kawai a nemo maki wata ki hada su biyu..." Inji Hajiya babba,
"To shikenan...amma yarinyan nan taci arzikinki wallahi.. Don da nayi niyyan da an kawo min
sabuwa zan sallami shegiya ta je Chan gidansu ta bar na tar masu da abinci kaman yanda take
nan..." Yanda tayi maganar yasa Hajiya babba dariya
"Wallahi kin Iya bada dariya..." Inji Hajiya babba, itama Hajiya karama dariya tayi
"Ai yarinyan ce da ban dariya...sai ta kusa karar da dettol daya wajen wankin toilet...jiya daga
nace ta hadawa Ameera tayi tayi fulling jug da tea ta mika mata..." Hajiya dariya ta karayi,
"Funny Wallahi.. Sakarcinta is written all over her..." Inji Hajiya babba,
"Aikam am feed up with her wallahi... Amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login