Showing 6001 words to 9000 words out of 108372 words

Chapter 3 - NA CUCE TA (1 to End) Complete by Zuwairat Ummu Maryam .pdf

bari insa a samo min wata kilan tayi learning daga
gareta don NA lura su ma yaran suna son sakarcinta especially Ameera..."
"Yo daman yara haka suke...sunfi son naughty people..." Inji Hajiya babba, Hajiya karama Bata
kara cewa komai ba ta dauki wayanta tana cewa
"Bari in kira yayan katsina muji ko zan samu mai aikin...." Ta fada tana dailing number elder sis
dinta dake aure a katsina
馃挌馃挋馃挏馃枻鉂ゐ煉�
NA CUCE TA
鉂ゐ煉欚煉涴煐ゐ煉滒煉�



庐zuwairat(ummu Maryam)

4鈨�





_Three days later_



Dija ce dauke da roban furan ta tana yawo tana shiga manyan gidaje don ita gani take yan
kananan gidan basu da kudin siyan fura
"Duk daya muke daku..." Take fada duk sanda taga yar karamar gida. Tana cikin tafiya ta shiga
cikin wani beautiful house, daga tsakar gidan ta hangi wata mata zaune kan carpet tana waya,
daman ta taba shiga gidan Kuma an saye dukan furanta, hakan yasa ta tsaya Bata tafiba ta
tsaya tana sauraron abinda matar ke cewa "Eh wallahi Hajiya ce tace kanwata na son yar aiki Kuma duk Wanda NA samu sai suce Kano
yayi masu nisa..." Ta fada ahankali tana sauraron abinda ake fada mata, bayan few seconds ta
kara da cewa
"Ni ma ko kadan banason ace wasu su kai mata yar aikin ba muba saboda cewa tayi yayarta
matar isa bala ce..kinga da akwai samu...." Ta fada Sannan shuru ya kara biyo baya tana
sauraron abinda ake fada mata,
"To shikenan.. Dan Allah ki bincika.. Nima zan cigaba da nema amma fa ance wacce zata Iya
aikin komai..." Matar ta fada, dija kam duk tana jin abinda matar ke cewa, shuru tayi tana
tunanin inama a dauketa, bayan kaman minti biyu matar ta kashe wayan ta Sannan ta daga
kanta ta kalli dija, da Sauri dija tace "Kuna sayen fura?..." Ta fada ahankali, matar murmushi tayi Sannan tace
"Ki kawo in gani..." Ta fada mata fuskan Hajiyan dauke da murmushi da ganinta kasan irin yan
duniyan nan ce don da gani tana shan taba, ahankali dija ta karasa ta sauke furan gaban Matan
ta yaye ledan furan don matar ta samu daman ganin furan da kyau,
"Kece kika kawo min fura kwana kin baya?..." $ matar ta tambayeta, da Sauri dija ta gyada mata
kai tare dacewa
"Eh nice..." Ta fada har lokacin Bata daina tunanin abinda taji matar NA cewa ba,
"To ki bani NA dari biyu in saka a fridge...don naji dadin furan kwanakin baya..." Da Sauri dija ta
dauko Leda daga gefen roban ta ta fara zuba furan cikin natsuwa kaman ba ita ba, sai da ta
gama ta ta dauko biyu ta kalli matar tana cewa.
"Ga gyara..." Ta fadawa matar, murmushi matar tayi Sannan tace
"Nagode..." Ta fada tana daukan purse dinta, budewa tayi ta dauko dariya biyu ta Bata, dija ta
amsa tare dacewa
"Nagode..." Rufe furan tayi da ledan Sannan ta mike tana son yiwa matar magana amma ta

kasa, daukan furan tayi har ta kai bakin gate ta juyo ta kalli Matan dake latse2 wayanta,
tsayawa tayi bakin gate din Wanda yasa matar kallon ta,
"Lafiya dai ko?..." Matar ta tambayeta, da Sauri tace
"Eh...daman...." Sai tayi shuru, matar tsaya kallon ta tayi don sauraron abinda zatace, jin tayi
shuru Kuma Bata tafi ba yasa ta cewa
"Daman me?..." Inji matar cikin natsuwa, dija kasa cewa komai tayi Kawai tayi tsaya kikam
dauke da robanta akanta,
"Dawo inji..." Matar ta fada mata, ahankali dija ta dawo , gefen ta matar ta nuna mata
"Sit..." Matar ta fada mata, dukda dija batajin turanci ta gane abinda matar ta fada mata,
ahankali ta sauke roban kanta ta zauna gefen Matan.
"Ki fada min...me kike son fada min..." Matar ta tambayeta, dija dai shuru tayi tana wasa da
yatsunta,
"Ke nake sauraro..." Matar ta sake fada mata, ahankali ta fara cewa
"Daman....naji...kina...cewa....kinason... Mai..aiki...shine..." Sai tayi shuru saboda yanda
gabanta ke faduwa, Matar ta gane inda ta dosa dukda muryanta NA cracking
"Ina jinki..." inji matar,
"Nace..in..babu...damuwa....zan....yi..." ta kai.karshen maganar da kyar, murmushi matar tayi
tana cewa
"Da kaman bazaki ida maganar ba...kina Iya aikin ne?..." Da Sauri dija ta gyada mata kai tana
cewa
"Eh.." Yanda tayi maganan yasa matar dariya tana cewa
"In iyayenki basu yarda ba fa?..." Da Sauri tace
"Babanmu ya rasu..nasan ammi zata yarda...in kin je ..kin fada mata ..." Ta fada muryanta na
cracking, matar kura mata ido tayi tana kallon beautiful and innocent face dinta Kuma tana
tunanin wane irin dalili ne zaisa yarinya ta so zuwa gidan aiki Kuma da kanta ba wai forcing
dinta akayi ba, amma tana kallon how faded her hijab and wear looks sai ta gane she will
definitely needs some income Kuma Tasan ta cancanci irin gidan da ake magana.
"In Bata amince ba fa?.." ta sake tambayan ta, muryan NA rawa tace
"Nasan zata yarda..." Ta Bata assurance dukda tana ganin da kyar hakan zai yiwu don Tasan
stand din ammi kan barin ta tafi wani wuri aiki amma gaskiya ta gaji da wannan wahalan tallan
Kuma tayi deciding zatayi anything necessary don ammi ta amince NA wannan zancen
"Wane wuri kike?..." Ta tambayeta, nan dija ta fada mata sunan kauyensu, baki matar ta bude
"Yanzu daga Chan kuke zuwa nan cikin garin?.." Kai dija ta gyada mata
"Lallai kam..amma ina ganin da nisa Kuma aikin ba a garin katsina zaayi ta..Kano ake bukatan
mai aiki..." Da Sauri dija ta katseta dacewa
"Ai ba komai... Tunda baa kasa zanje ba..." Dariya matar tayi
"To..yanzu tunda an fadamin ana bukatan mai aikin da wuri bari in kaiki garin naku sai muyi
magana da amminki..." Wani irin dadi dija taji amma sai cewa tayi
"Ai ban gama saida furan ba..." Dariya matar tayi tana cewa
"Ki kirge min sauran..." da Sauri dija tayi counting sauran cikin Leda ta mika mata
"NA nawane?..." Matar ta tambayeta
" sauran na dari uku da sabain..." Dari biyar matar ta dauko ta Bata,
"Ki jirani nan..." Inji matar Sannan ta shiga cikin falonta, Bata yi wasting time ba ta fito da gyale

tare da car keys dinta, sai adua take Allah yasa a amince don Tasan ba karamin samu bane in
kayi hulda da family isa bala, dija sai mar mar da idanuwa Kawai take, mota matar ta fidda
daga parking lot dija ta shiga ciki duka kama hanyan garinsu.

Karfe biyar da minti ashirin suka iso kofar gidansu dija, da Sauri dija ta fita ta shiga gida matar
ta fito tana kallon kauyen tana mamakin
Ya akayi suke rayuwa a irin wannan wuri don tamkar bayan duniya suke saboda karanta
kauyen, dukda ba cikin gari take ba amma Sam batasan daura yayi extending zuwa haka ba.
Dija na shiga gidan ta fara kwala ammi kira
"Ammi!!...ammi!!!..." Ta dinga fada tun.zaure, ammi dake kada miyan kuka ta mike da Sauri
saboda yanda gabanta ya fadi don kiran dija har cikin zuciyanta saboda yanda take kwala mata
kira on top of her voice, da Sauri ta ta taro dija dake shigowa, kallon ta tsaya yi hannun ta dafe
da kirjinta, "Dija lafiya?..." Ta tambayeta cikin tashin hankali, dija kallon ta tayi da gwala2 idanuwanta tana
murmushi
"Ke lafiya?..." Ammi ta sake tambayeta tana kallon ta from head to toe,
"Lafiya lau..wata Hajiya ce ta zo wurin ki..." Ta amsa mata tana ajiye roban furan ta, kallon
mamaki ammi tayi mata,
"Wacce Hajiya?..." Ta tambayeta,
"Gata nan..." Dija ta fada tana nuna matar data shigo cikin gidan da sallama, da Sauri ammi ta
amsa tana kallon ta,
"Barka da zuwa...shigo mana..." Ammi ta fada jikinta NA rawa don batasan abinda dija tayi ba
da aka biyota, da Sauri ammi ta shiga cikin dakin matar ta bi bayanta tare da daga labulensu da
ya kasu kusa kashi takwas saboda yanda ya yage, ta kasan wusiya matar ta dinga kallon dakin
tana mamakin how living creature can sleep in such an awful place, ammi kakkabe tabarma
dake kasa tayi jikinta sai rawa yake Kuma zuciyanta tamkar ya fito ta bakinta saboda fargaba.
Dija kam gefe daya ta tsaya tana aduan Allah yasa a samu nasara, Da Sauri ammi ta debo
ruwa cikin randa ta mika wa matar tana cewa
"Maraba..maraba..." Cikin faraa matar ta amshi ruwan amma tasan ko da wasa bazatyi gigin kai
kofin bakinta ba, rike cup din tayi tana kallon dija dake ragube jikin bango tana kallon su,
murmushi ta sakar mata itama dija tayi karfin halin maida mata martani, ammi durkusawa tayi
kasa kneels dinta biyu kasa sai tafin hannun ta biyu suma kasa "Ina yininmu..." Ammi ta gaidata, cikin faraa matar ta amsa da
"Lafiya lau..ya gida ya yara?...."
"Lafiya kalau suke...." Ammi ta fada Sannan tayi shuru tana sauraron abinda ke tafe da matar,
ahankali matar ta ajiye cup din Sannan ta fara cewa
"Sunana Hajiya Aisha...ina zaune a cikin garin daura...ina Sana'a kala2 cikin su har da kai yara
gidan gidan manyan mutane don suyi masu aiki don gyara rayuwan yaran..." Ta Dan yi shuru ita
Kuma ammi dai tana nan durkushe tana sauraron ta, Hajiya Aisha ta cigaba dacewa
"To da akwai wata kanwar aminiyata dake son mai aiki karama daidai kaman yarki dija...shine ta
shaidamin..." Da Sauri dija ta dan buga kafa kasa wai ita mai wayau don kar ta fadi ita tace tana
son aikin, Kuma Hajiya ta gane sai tayi shuru ta chanza maganan zuwa
" shine naga yarki nace bari in biyo in tambaya ko zaki amince in kaita..." Ammi da kanta ke

kasa sai ta fara girgiza kai alaman AA, dija dake tsaye tana kallon su nan take taji kwaiwanta
yayi sanyi don Kawai so take ta je.
"Gaskiya Hajiya kiyi hakuri... Yarana marayune...nice uwarsu nice ubansu tunda yawancin yan
uwan ubansu basu damu da suna raye ko suna mace ba...nasan muna cikin hali amma gaskiya
nafison in wayi gari in gan dukkan yarana kusa dani...ko kadan banason abinda zai taba masu
mutuncinsu saboda nasan yanda ake wulakanta marasa karfi cikin birni..." ta fada ahankali cikin
natsuwa da sanyin murya Kuma har lokacin bata mike daga inda take ba, ahankali matar ta
daga kai ta kalli dija da idanuwanta suka ciko da kwallan bakin ciki, murmushi Hajiya ta saki
Sannan tace
"Babu komai...amma yar uwa inason in shaida maki cewa babu inda mutuncin ya mace ke
saurin zubewa kaman talla saboda yanda duniya ta lalace... Da akwai maza azzalumai Wanda
suke gurin lalata rayuwan yaran mata mussanman wayanda ke yawo kan titi...." Ahankali ammi
tace "Allah NA tsarewa ai...ni kaina don babu yanda zanyi ne amma ko kadan yata Bata talla" Ta
fada cikin sanyin murya, ahankali Hajiya Aisha tace
"ga dama nan...NA daya yarki Bata zuwa koina tana cikin gida..Kawai ta kula da bangaren uwar
dakinta Kuma ba ita kadai bace...Sannan duk wata zaa aiko da albashinta Wanda INA tabbatar
maki yafi talla saboda ita Bata wahala ba ke baki wahala ba....Kuma wannan gidan da nake
fada maki suna kuka da masu aikinsu tamkar yaran da suka Haifa don har boko da islamiyya
suke saka su sai na karshe ina tabbatar maki dacewa zaa kare maki mutunci yarki...don haka
ina baki shawaran da zan bawa kaina...ki gwada ki gani in hakan baiyi maki ba kina iya bukatan
a maido maki ita...." Hajiya Aisha ta karasa maganar ta tana kallon dija dake hawaye, ammi dai
shuru tayi har saida Hajiya ta kai aya Sannan tace
"Ni gaskiya nafison in tashi in ga yarana kusa dani...Sam hankali na bazai kwanta ba duk
lokacin Dana tuna yata tana wani wajen Kuma basan irin halin da take ciki ba..." Ta fada kanta
kasa, da Sauri dija ta fita daga dakin tayi waje ta fara kuka sosai kaman an doketa
"To shikenan... Allah ya shige mana gaba..amma zan dawo gobe koda kin chanza shawara.. Ba
don komai yasa na fadi hakan ba sai don dija ta shiga raina...haka nan naji ina sonta tamkar
nawa..." Itadai ammi shuru tayi Bata kara cewa komai ba, Ahankali Hajiya ta mike tare da dauka
handbag dinta, itama ammi mikewa tayi tana cewa "Don Allah ki tsaya kici turo..." Dariya Hajiya Aisha tayi
"Aa ..nagode kwarai..." Itama ammi Dariya tayi tana cewa
"Ai Baku Iya cin irin abincin mu dake lami..."
"Sam ba haka bane...Kawai na koshi ne..." Ta fada tana fitowa waje ammi na biye daita har
waje, ta wutsiyar ido ta kalli kukan dake tafasa tsanwa shar babu alaman kayan miya ciki.
Kallon yaran ukun dake zaune tayi ta bude bag dinta ta Ciro Dari biyar ta mikawa babban cikin
su wato binto, durkusawa tayi ta amsa tana cewa "Mun gode..."
"Haba Hajiya...har da wata hidima...mun gode kwarai Allah ya saka da alkhairi..." Tafada tana
raka ta zaure,
"Babu komai... NA gode nima...sai goben..." Hajiya tafada tana fita waje, sai ihun dija ke tashi
duk ammi najinta amma tayi banza daita dukda Tasan halin yarta da kwallafa amma saidai ta
mutu. Hajiya kallon dija data Dora hannu bisa kai tayi tana Dariya

"Haba dija...ki bar wannan kukan mana...in Bata amince ba to Allah bai kaddara zaki ba..kiyi
shuru kinji..." Ta fada tana kallon yanda take Bata baki tana kuka kaman anyi mata mutuwa,
kara volume din kukanta tayi dataga Hajiya ta shiga cikin motanta. Da gudu ta shiga cikin gida
ta kwanta kasa tana cewa "Wallahi... Ban kara zuwa talla..."
[3:12PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 鉂ゐ煉滒煉涴煐ゐ煉氿煉�
NA CUCE TA
馃挏馃挍馃挌馃枻馃挋鉂�



庐zuwairat( ummu Maryam)



5鈨�





Tafada cikin matsanacin kuka tare da kwantawa kasa tana rolling kaman wacce akayi wa
albishir da mutuwa, babu Wanda ya tanka mata su binto tsayawa sukayi kanta suna kallon
yanda take birgima kasa, ko kallon ta ammi batayi ba har tagama zuba wa su binto miya kan
tuwon dake cikin kwano Sannan ta shiga ciki, har lokacin dija NA kwance kasa yaran neighbors
sai lekota suke don ba karamin ihu take ba tana cewa
"Ban kara zuwa talla...ban kara zuwa talla...saidai yunwa ta kashe mu gidan nan...." Ta fada
cikin kuka, ammi na shiga cikin dakin ta nufi inda take ajiyan bulala ta yo waje, dija dake
kwance na ganin ammi da bulala ta tashi tayi waje da gudu tana kuka,
"Shegiya da kin tsaya yar banza...." Ammi ta fada tana maida bulalan. Har bayan sallan magrib
dija Bata dawo gida ba tana nan labe gefe daya tana kuka gashi har lokacin Bata bar fargaban
abinda ammi zatayi mata ba.

Ammi na ganin Bata dawo ba tasa binto ta nemota, sanin inda take zama in tana kuka yasa
binto bata sha wahalan gano ta ba,
"Kizo inji ammi..." Ta fada mata, hararanta dija tayi da red eyes dinta tana cewa
"Ki wuce ki bani wuri..."
"Ammi tace kizo ..." Binto.ta sake fada mata, aikam sai ta rarumi takalminta binto NA ganin
hakan ta bar wajen da gudu taje ta fadawa ammi yanda sukayi daita,
"Ta shigo Dan kanta..." Ammi ta fada tana shiga cikin daki, har bayan sallan ishai dija da zaune
inda take tana kukan bakin ciki, gani take gwara Kawai ta amince tana son dan Musa suyi aure
kamar yanda yake yawan fada mata dukda batasan burouban da akeyi cikin aure ba amma ko
kadan batason ta kara talla, tana nan zaune Bata ankaraba taji an damketa da Sauri ta daga kai

taga ammi, baki ta bude zatayi kuka ammi ta dora yatsanta daya kan bakinta tana cewa
"Wallahi kika sake naji bakinki sai NA lahira ya fiki jin dadi...maza tashi ki shige min gaba..."
Amma ta fada tana rike daita don tasan dija da kafan gudu kaman taci kare, da Sauri dija ta
mike ra shiga gaban ammi suka taho gida sai shessheka Kawai take saboda yanda tayi kuka,
daki ra shiga ta rabe jikin bango tana sauraron abinda ammi zatayi mata, ammi ce ta shigo rike
da kwanon tuwo ta ajiye gaban dija
"Maza ki zauna ki cinye kafin ki ci ubanki...." Ammi ta umarceta, babu musu ra zauna ko hannu
Bata wanke ba ta fara cin tuwon, ko kai Bata dagaba har saida ra cinye tas saboda sanin halin
ammi, tana kamawa ta daga kai ta kalli ammi dake kallon ta, ahankali ammi ta fara cewa
"Yanzu dija kin fi son gidan wasu kan gidan mu?... Kinfi son zama da wasu kan zama damu?..."
Ta tambayeta cikin natsuwa, dija shuru tayi batace kala ba, ammi ta cigaba dacewa
"Yanzu kinfison inda zakije a maidaki kaman baiwa?...baki da gatan komai sai yanda akayi
dake?... Dija njasan bani da ko sisi amma ban barin wani ko wata ta wulankanta Mani
Ku....yanzu tambaya daya nakeson yi maki...kin fison zama dxa wasu kanmu?...." Da Sauri dija
ta girgiza mata kai, "To wane dalili ne yasa kike kuka don NA hanaki zuwa aikatau?..." Ammi ta sake tambayan ta,
tana shessheka ta fara cewa
"Ammi....Kawai inason mu dinga samu kaman yanda su hase ke samu..."
"Kinsan halin da take ciki?..." Bata idaba dija ta katseta dacewa
"Ammi babu halin da take ciki..kalli yanda ta koma ranar da ta dawo...Kuma tace min har boko
take zuwa...nidai ammi ki bari in je...in babu dadi zan dawo..." Tafada da gaske, ammi.zama tayi
tana kallon ta cike da mamakin yanda take magana babu alaman tsoro, kara fashewa tayi da
kuka tana cewa "Dan Allah ammi ki bari inje...in da akwai matsala zan dawo...Kuma ni wallahi inason boko..." Ta
fada cikin kuka,
Ammi tsaya kallon ta kawai tayi saida tayi kukan mai isanta Sannan ammi tace
"Amma kinsan cewa ba ni kadai ke da iko da Ku ba ko?.... Dukda yan uwan ubanku basu damu
da Ku ba nasan da zaran wani abu ya faru zasu samu bakin magana..." Da Sauri dija tace
"Ai duk suna birni...kawu nanu Kawai ne nan...ammi muje mu fada mashi...." Ta fada har jikinta
NA rawa,
"Badai yanzu kike nufi bako?..." Ammi ta tambayeta, sadda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login