Showing 9001 words to 12000 words out of 108372 words

Chapter 4 - NA CUCE TA (1 to End) Complete by Zuwairat Ummu Maryam .pdf

kanta kasa tayi Sannan tace
"yanzu.." Tafada tana murmushi,
"Jaira... Babu inda zamu yanzu ..saidai gobe..in bai yarda ba sai ki hakura..." Inji ammi,
"Nasan zai yarda...ai ba damuwa yayi da rayuwata ba...." Tafada cikin jindadi, hararanta ammi
tayi Sannan tace
"Je kiyi salla...nasan rabonki da salla tun NA zuhr..." Bata idaba dija tace
"Ai har yanzu ban gama ba..."
"Amma kaman kinyi salla da zuhr
" aa NA duba naga har lokacin bai tsaya ba balle inyi wanka..."$ ta amsa mata kaman ba ita
bace ke kwance kasa tana kuka kaman wata yar karama yarinya.
"Je ki kara dubawa..." ammi ta fada mata, da Sauri ta mike ta fita.

Yazid NA zaune kan gado babu kaya jikinshi kafafunshi cikin blanket waya ne hannun shi yana
magana kaman mai jin bacci idanuwanshi lumshe,
"Baby I can't wait..." Ya fada cikin whisper, daga Chan bangaren mufi dake kwance sanye da
kayan bacci ta danyi Dariya tare dacewa
"Can't wait for what?.." Ta tambayeshi, shima murmushi yayi yana kallon erection dinshi yace
"Nothing.. Kawai am eager to be with you.... Gani nake kaman 24 days din nan tamkar 24
months or year..." Idanuwa itama mufi ta lumshe saboda maganar shi ke yawo straight into her
system, mika tayi Sannan tace
"Nikam kaman gobe nake ganin 24 days..." Yazid Dan kwantawa yayi yana cewa
"Don baki damu dani kaman yanda NA damu da ke ba...amma ni I feel rike in tariyo time din..."
"Don't worry... Kaman gobe ne..." Ta fada mashi cikin sanyin murya,
"Hmmm alright... I have been patient for a while.. So 24 days won't matter..." Ya fada ahankali,
"That's my love... Shiyasa nake kara sonka....$" Dariya yayi
"Da gaske? Tell me why..." Yafada cikin whisper,
"Cos you are gentle..." Dariyan kasan makoshi yayi
"Hmmm baby am not that gentle... I don't want to disappoint you... On our first night..." Ya fada
kasa2 yanda ki NA kusa dashi bazaiji abinda yake cewa, kuka karya mufi ta farayi tana cewa
"Ka bar fadan hakan...kana tadamin hankali..." Dariya yayi
"Name...Kawai am telling you kar ki daukine gentle don I might be bad ass..."
"I know you are not..."
"To shikenan...I will try to be gentle as I look..." Yayi assuring dinta, hira suka cigaba dayi for
sometime Sannan sukayi sallama, Ahankali ya ajiye wayan, ana kallon joystick dinshi, tunani
yake wai haka maza ke ji in suna magana da mata ko matsala gareshi din mostly in har zasuyi
waya yana jin muryanta cikin kunnenshi sai ya samu erection, shidai gurinshi yayi aure ko ya
huta da wannan matsalan.
Ahankali ya mike ya shiga bathroom ya sakar wa kanshi ruwa Sannan ya dawo ya shiga blanket
ya rufe kanshi from head to toe.


The following day tun da wuri dija ta addabi ammi suka kama hanyan gidan kanin marigayin
babanta wato kawo nanu
Sallama sukayi ita da ammi suka shiga ba tare da an wani amsa masu ba don ana ganin
kaman roko ya kawo su kaman yanda suke zuwa wasu lokuttan in abubuwa suka kakare masu,
mutumin dake zaune yana wanke bakinshi da asuwaki ya kallesu
"lafiya tun dugudugu?..." Mutumin ya tambayesu, dija data nufi wurin shi tace
"lafiya lau...INA kwana..." Ta gaidashi tana durkusawa,
"Lafiya..." Ya amsa mata atakaice, ita ammi dakunan Matan gidan ta shiga tana gaidasu suna
amsa mata atakaice wata ma Bata amsa ba Sannan ta nufi inda dija ke tsaye gefen kawunta,
itama durkusawa tayi ta gaida nanu dake yi mata kallon wulakanci Kuma ba komai ya haddasa
hakan ba illa yaso ya aureta bayan mutuwan babansu dija amma taki sai ya tsaneta "Lafiya...wai me akayi ne?.." Ya tambayeta yana goge hakoranshi, ahankali ammi ta fara
fadamashi abinda ke tafe dasu, sai da ta kai karshe Sannan ya kalli dija dake tsaye tana
sauraron su

"Ke haka ne?..." Ya tambayeta
"Eh kawu..." Ta amsa mashi cikin sanyin murya
"To shikenan.. Allah ya bada saa..." Ya fadawa dija don ko kadan bayason magana da ammi,
"Yauwa kawu Ameen...mun gode.,.." Ta fada cikin murna sosai Wanda ko kadan Bata Iya
boyewa,
"Ammi mu tafi..." Ta fada tana barin wurin da Sauri, itama ammi ta bi bayanta tana tafiya
ahankali kawu nanu ya bi bayanta da kallo yana cewa
"Ga mace har mace amma ta bar dukiyanta suna wulakanta babu mai kula dasu...yanzu da ina
nan ina morewa amma ta yi min bakin ciki..." Ya fada tare da Jan tsoki, ammi fita tayi Bata kar
bin ta kan Matan gidan ba don su har yanzu kishi sukeji suna ganin kaman tana iya amincewa
mijin su ya aureta don ta fisu komai da komai, Dija NA tsaye waje tana jiran fitowan ammi tana fitowa dija tayi saurin cewa.
"Ammi ki bani kudin abun hawa in tafi daura in fada mata kun amince..." Hararanta ammi tayi ta
wuceta Bata tanka mata ba, har suka kai.gida dija Bata bar fada mata ta Bata kudi ta tafi daura
ba, saida ammi taga zata sha mata kai Sannan ta fada mata Hajiya Aisha zata dawo anjuma,
sai lokacin dija ta sake ta fita ta fara gayawa kawayenta zata birni, da sun tambayeta katsina
zata? Sai tace
"Kambu ni na wuce katsina.. Kano zani..." Duk saida tabi kusan dukkan gidajen kauyen su ta
fada masu zata birni
Ammi kam tunanin yanda dija Bata damu dasu ba Kawai take don ko kadan ta nuna bazatyi
missing dinsu ba, sai kuma ta tuna da yarinta ke damunta. Dija wanke faded clothes dinta tayi
ta shanya su ko abinci bataci ba, ammi kallonta tayi
"Ke baki ma tunanin halin da zamu shiga in kin tafi...kinsan bamu da komai gidan nan..Kuma da
tallan nan muke ci, gashi zaki tafi..." Dija Dan Bata rai tayi Sannan tace
"ammi ki bawa binto ta saida mana..." Hararanta ammi tayi
"Amma baki da hankali... Wannan yarinyan zan bawa tallan fura?..."
"Yo ammi ni ai ban kai ta ba NA fara tallan awara..to ki yi mata awara ta dinga kaiwa tasha...."
Ta fada in I don't care manner, ji take kaman ta kira Hajiyan ta zo ta dauketa.
Sai bayan sallan asar Hajiya Aisha tazo, alokacin kam dija har ta fidda ranta zatazo ita Kuma
ammi tana ta aduan Allah yasa kar tazo sai gata da sallama ta shiga cikin gidan da gudu dija ta
rungume ta tana cewa
"Sun yarda..sun yarda..." Ta dinga fada tana rike da Matan, itama Hajiyan riketa tayi tana cewa
"Da gaske?..." Kai akwai dija ke ta daga mata cikin jindadi, Hajiya kam tamkar Tasan halin da
suke ciki, kallon ammi dake zaune tana murmushi tana aduan Allah yasa aso yarta tamkar
yanda Hajiya Aisha ke son dija.
"Kisa yara su biyoni..." Ta fada mata tana fita, da Sauri su dija da sauran yan gidan suka bi
bayanta, bayan motanta ta bude sai ga shinkafa da mai da magi sai su taliya katon da
macaroni. Ihu su dija suka fara Sannan suka fara shigowa da kayan da Sauri ammi ta mike
tsaye tana kallon su. Nan ta zube kasa tana godewa Hajiya Aisha. Bayan sun zauna ammi take shaida mata sun yarda ta tafi da dija
"don Allah kisa a kula daita...Dan Allah kisa su dauketa tamkar su suka haifeta..." Inji ammi
dake hawaye, kafadarta Hajiya ta dafa Sannan tace
" ki kwantar da hankalin ki...yaran da na kai gidan aikatau sunfi su ashirin Kuma baa taba samu

matsala ba...kullum iyayensu cikin gode min suke saboda yanda rayuwan yaransu ya
chanza...don haka ki kwantar da hankalin ki..." Kai ammi ta gyada mata. Sannan suka tashi
tafiya dija ta dauko old Ghana most go dinta, Dariya Hajiya tayi tana cewa
"Ki bude wannan bag din in gani..." Dan dija ta baje kayanta, banda Dariya babu abinda Hajiya
takeyi,
"Kawai ki bar wayan nan..in munje daura sai in Dan samo maki.kaya kafin in kaiki..." Tsalle
Kawai tayi ta fita ta tsaya jikin motan tana kallon yan kauyen su da suka taru jikin motan suna
kallon ta, Hajiya fitowa tayi ta bude motan dija ta shiga Sannan suka tafi.
[3:14PM, 3/20/2018] 鈥�+234 806 125 0020鈥�: 鉂ゐ煉氿煉滒煐ゐ煉欚煉�
NA CUCE TA
馃挏馃挋馃挍馃枻馃挌鉂�




庐zuwairat(ummu Maryam





6鈨�





Dija ko kallon mutanen batayiba balle ta daga masu hannu kaman yanda suke daga mata
hannu, ammi dake kuka Kawai take kallo tana tausaya mata amma in ta tuna yanzu basu da
matsalan abinci sai ta samu nutsuwa, har suka iso cikin garin daura Bata ce uffan ba, Hajiya
kallon ta tayi taga yanda tayi sanyi farat daya ta saki murmushi tare dacewa "Lafiya dai ko?..." Ta tambayeta cikin muryan dake kwantar da hankalin mai sauraro, dija daga
idanuwa tayi ta kalleta
"Babu komai..." Ta fada muryan ta NA rawa, tunanin yanda komai zai kasance Kawai take,
tunda take Bata taba kwana wani wajen ba sai in sun je kauyen ammi.dake bauchi shima tare
suke zuwa Kuma su dawo tare, Kawai sai taji Kuma batason tafiyan. Ana kiran magrib suka
shiga gidan Hajiya tayi parking motanta suka fito daidai lokacin da wasu yanmata biyu suka fito
daga falonta, daya babba ce sai daya kaman dija, dukkan su sanye da kaya ta alfarma, dija
kallon su tayi ta fara tunanin ya akayi ita bata tura yaranta aikatau ba sai ta tuna Ashe su masu
kudi ne Kuma ita talakace, gaidasu tayi suka shiga cikin falon. Jikinta sai rawa yake don she
feels so out of place, yanmatan sai kallon ta kawai suke, Hajiya zama tayi ta dauki wayanta ta
kira number yayan Hajiya karama ta shaida mata ta samu yar aikin da suke bukata Kuma ta
fada mata zata shigo mata daita gobe.

"To shikenan.. Allah ya kaimu.." Inji yayar Hajiya karama. Sallama sukayi Sannan Hajiya Aisha
ta kalli yarta dake zaune kusa daita tana kallon dija
"BaBy zaki aramin kayanki biyu...zuba uku..." Yarinya Bata rai tayi
"Mom me zakiyi da kayana Kuma?..."
"Zan Bata ne....I promise zan saya maki replacement..." Sai alokacin yarinya ta saki fuskarta,
kallon dija data sadda kai kasa tayi Sannan ta kwalawa nata mai aikin kira, nan wata babban
budurwa ta fito, dija kallon ta tayi
"Tabdin...wallahi bai kaiwa kaman wannan, ina yar aiki..." Ta fada cikin ranta, y
Mai aikin durkusawa tayi ta gaida Hajiya ta amsa Sannan Hajiya tace
"Ki kaita dakinki..ki Bata abinci taci ta koshi Sannan Dan Allah ki duba kanta in yana bukanta
gyara ki wanke mata kisata ta wanke bakinta ta wanke koina NA jikinta zan kawo kaya
yanzu....." Hajiya ta fadawa mai aikinta,
"To ..." Kawai yarinya tace Sannan tayiwa dija alaman tazo, da Sauri ta mike ta nufi wajen
yarinyan sukayi dakinta, dija bude bakinta tayi tana kallon dakin mai aikin,
"Kam Allah kasa nima a bani kaman quartan wannan dakin Dana haye..." Ta fada cikin ranta.
"Ki zauna..." Yarinyan ta fada mata tare da nuna mata katifan dake kasa, da Sauri dija ta zauna
ita Kuma ta fita daga dakin, few minutes later ta dawo da jelof din taliya dayasha kayan miya,
"Wow dadi...Allah yasa inda zaa kaini su dinga cin irin wannan..." Ta saki fada cikin ranta tana
aman abun daga hannun ta, nan dija ta apkawa abincin ta cinye tas ta tside kwano Sannan ta
ajiye, yarinyan dauke kwanon tayi ta kai kitchen Sannan ta dawo,
"Bude kanki in gani..." Yarinyan ta fadawa dija, da Sauri dija ta bude kanta, kitson kanta yafi
wata daya dayi Sannan kanta dilindilin,
"Kambu..da akwai aiki..." Inji mai aikin Hajiya Aisha,
Da Sauri ta fita daga dakin ta fadawa Hajiya Aisha status din kan dija,
"Kina da sauran relaxer?..." Hajiya ta tambayeta,
"Eh ..."
"To ki shafa mata kan..don gaskiya bazan kaita a haka ba tunda manyan mutane ne..." Ta fada,
nan mai aikin ta koma ta bawa dija tsinke ta shigar daita bathroom dinta
"Ki tsaya nan ki kwance kanki..in kin gama kiyi min magana..." Ta fada mata Sannan ta fita ta
barta nan tsaye, dija kam tsaya kallon bathroom din tayi tana gani ya ninka dakin su kyau sau
goma, dukda babu wasu kayan wanka cikin bathroom din amma tiles din wurin Kawai ya isheta
kallo, da Sauri ta kwance kanta dake gari bisa jikinta daman Zane ne guda six amma ki
tsaganta baka ganin saboda tsufa. Lekawa tayi ta kalli mai aikin
"NA gama..." Ta fada mata, budurwa mikewa tayi ta dauki sauran relaxer ta shiga bathroom din,
nan ta umarceta data durkusa Sannan ta fara shafa mata, tana shafa wa tana mamakin irin
gashin dija, don Bata San dunkule yake ba saida ta fara shafa man, tafi minti talatin tana shafa
mata, "Lallai.. Kina da tsawon gashi..." Ta fada, dija dake neman kuka saboda zafin relaxer tace
"Yanke min ammi take saboda tsawo..." Ta amsa mata muryan ta na rawa, few minutes da
gamawa dija ta fara yarfe hannuwanta tana cewa
"Ki cireshi haka nan...wallahi zafi nake ji..." Yanda tayi maganan yasa ta Dariya, nan ta wanke
mata kai tas taga yanda kanta ke silky saboda baki da tsawo,.
"Hmm daman mu yan kauye munfi yan birni komai.. Amma wahala bai sa a gane hakan..." Yar

aikin Hajiya Aisha ta fada cikin ranta, saida ta gama ta hada mata ruwan wanka mai dumi, dija
kam jinta take kaman princess,
"Ni ake hadawa ruwan wanka mai dumi..." gari su kam duk sanyi sai dai kayi wank da ruwan
sanyi din baka samun ruwan.
"Ki wanke jkinki sau biyar kafin ki fito...kinji?..." Da Sauri dija ta gyada mata kai. Tana fita dija ta
cire wet clothes dinta ta fara dirje jikinta kaman mai dilka da sabulu mai kamshi don ita dadin
sabulun Kawai take ji, sai adua take Allah yasa da akwai irin wannan hutun inda zaa kaita.
Wanke jikinta tayi sosai har in ta saka ruwa jikinta bai zama saboda yanda ta wanke kanta.
tsayawa tayi tana kallon kanta kaman yanda ta saba, tafi hour tsaye har saida taji an Dan buga
kofan bathroom din Sannan tayi saurin cewa
" na gama....kayanane suka jike..." Ta fada da karfi,
"Ki daura wannan tawul ki fito..." Ta fada mata, dija tsaya kalle2 tayi tana mamakin meye tawul,
jin shuru yasa mai aikin cewa
"Wannan farun kyallen zaki daura...." Sai lokacin dija ta gane ta dauko towel ta daura amma sai
ta kasa fitowa saboda yanda bai da tsawo,
"Na daura...." Ta fada, kanta kasa sai gasjinta baje kan shoulder ta, budewa mai aikin tayi ta
shigo ta zuba mata makilin a brush ta bata ta nuna mata yanda zatayi dashi.
Atakaice nan take dija ta fito kal kaman ba itaba, Hajiya ta shigo mata da wata doguwar Riga
yarta ta Bata, ita kanta hajiya sai da ta tsaya tana kallon gashin dija don ba karamin mamaki
tayi ba.
Kallon mai aikinta tayi Sannan tace
"Dan Allah ki Bata shawaran da kike bawa sauran in an kawosu kafin In akaisu gidan aikin su..."
Inji Hajiya Aisha,
"to..." Ta amsa mata, fita Hajiya tayi dija ta zumbula rigan da aka bata, nan mai aikin Hajiya
Aisha ta fara cewa
"Kina jina?..." da Sauri dija ta gyada mata kai,
"NA farko inda zaa kaiki ba gidan Ku bane...gidan aikinki ne...ki tabbatar kina girmama koda
akuyan gidan..." Da Sauri dija ta kalleta, itama kallon ta tayi
"Eh din...dole ki girmama su...babu ruwan ki da abinda baa saki ba...duk abinda akace kiyi
kiyi...in ance ki bari ki Bari...banda kwadayi...banda zuwa inda baa ce kije ba...banda
shisshigi...banda yayata sirrin uwar dakinki ko na wata...babu ruwanki...banda sata..." Again dija
kara kallon ta tayi "Yo kina mamaki ne?.... To da akwai wata yarinya da Hajiya ta kai saida aka maidota wai tana
dauk2....don haka ko kudin su zai dinga yawo kasa babu ruwanki don wani lokacin gwadaki
suke...kar kiga babu mai kallonki kiyi abinda baace kiyiba...kiji tsoron Allah a duk inda
kike...Kuma kar zaman birni yayi maki dadi ki mance inda kika fito...kinji ko?..." Da Sauri dija ta
daga mata kai,
"Sannan babu mai son yar aiki kazama...kiyi wankan ki kafin ki fara aikin gida....don haka ki
tabbatar kina mikewa da wuri...ki kula da kanki...Kuma in kina da wata matsala ki fadawa uwar
dakinki... Mussanman irin matsalan mu na mata...da fatan kinji abinda nake fada maki...." Da
Sauri dija ta kara daga mata kai "Ke ki bar daga kai.kaman wata kadangaruwa...ki dinga amsawa..."
"To ..." Dija ta fada, wasu advice ta Kara Bata sosai kan yanda zata zauna da su batare data

samu wata matsala ba, dija taji dadi sosai don sai gata tana cewa
"Nagode..." Labari suka cigaba dayi har bacci ya dauki yar aikin Hajiya Aisha ita kam dija yanda
ta ga rana haka ta ga dare. Tun da asuba mai aikin Aisha ta tashi tayi wanka itama dija tayi
wanka ta maida kayan ta bi bayanta suka fara aiki tana nuna mata abubuwan daya kamata
mutum yayi, "Ai Kwara wannan da dakan fura..." Ta fada cikin ranta,. Kafin bakwai da rabi sun gama komai
har mai aikin Aisha ta kusa ida breakfast. Sai karfe takwas Hajiya ta fito ta sha tea da bread su
Kuma yaranta sukaci abincin, mai aikinta ta debo abinci ta kai dakinta sukaci da dija Sannan
Hajiya Aisha ta kirata ta fito, wata karamar jaka ta bata "Gashi da akwai kaya kala uku cikin shi...ki kula dasu kafin su kara maki wasu..." Da Sauri dija
ta amsa Sannan suka kama hanyan katsina. Gidan yayar Hajiya karama suka isa, nan ma dija
baki ta bude don kyau da girman gidan, matar dake kaman daya da Hajiya karama ta kallesu
fuskan ta dauke da murmushi tana cewa "Wannan yarinyan tana da kyau.. Ina kika sameta?..." Ta tambayi Hajiya Aisha, Dariya Hajiya
Aisha tayi ta labarta mata yanda akayi ta samu dija,
"To alhamdulillah... Yanzu bari in baki address dinsu dukda gidansu ba boyayye bane a garin
Kano..." Nan ta rubuta mata address, ta mika mata, Sannan tace
"Bari in dauko maki NA mai..." ta fada tana hayewa upstairs, dija

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login