Showing 81001 words to 84000 words out of 108372 words

Chapter 28 - NA CUCE TA (1 to End) Complete by Zuwairat Ummu Maryam .pdf

have a peaceful home...ai kana ganin tunda kake baka
taba ganin ko jin hayaniyyan iyayenka mata ba...to that's the secret... Nasan at times zakaji
daya tafi kwanta maka ka daya amma never try to show it in public... Kawai ka nuna mata how
much you love her when you are alone... Kadaiji ko?..." Dad yafada yana rike kunneshi don ya
shaidawa yazid he's damn serious
"Yes dad...nagode... I will try any human in yi adalci a tsakaninsu..." Yafada kanshi kasa,
"That's very good...yanzu yaushe zaa daukota?..."
"I think Saturday..."
"OK...about the boy...inason a raineshi gidan inna...ko kanason Ku zauna tare?...." Dad ya
tambayeshi, da Sauri yazid ya girgiza kai yana mai jin dadin abun.
"Good...jiya mommies dinka sunce doc Zara zata dinga kula da yaron har ya fita daga neonate
stage..."
"Mahmud... Sunanshi Mahmud..." Yafada cikin sanyin murya.
"That's good...nice name...sai ka dauki rago biyu daga gona a yanka ranar asabar...."
"OK dad...nagode...." Yafada sounding very happy. Mikewa yayi ya fita daga wurin dad ya bi
bayanshi da kallo yana murmushi. Part din mom dinshi ya nufa wayanshi ya fara ringing, jin
ringing din yasa shi sanin cewa mufidace, murmushi yayi tare da picking call sannan ya
sanyanya voice dinshi tare dacewa. "My baby..."
"Yes babyna...baka iso bane?..."
"Na iso...yanzu na baro wajen dad..." Ya fada cikin sanyin murya
"Shine ko ka Karina ka fadamin kazo..."

"Sorry my love.... I wanted to surprise you ne..." Yafada muryan shi bai fita sosai,
"Baby wani abu?... muryanka kaman kayi kuka..." Murmushi yayi ya kara kashe murya
"Am OK...bari in wanka sai inzo in daukoki..." Yafada sounding very dull.
"Pls baby kana tada min hankali... Me dad ya fada maka?..." Tafada kaman zatyi kuka,
"Ki kwantar da hankalinki...in na daukoki ko me ke nan zakiji..." Ya shaida Mata,
"Me zan ajiye maka?...
" don't worry babyna....sai nazo... " tafada ahankali sannan ya katse wayan. Dariya yayi yana
cewa
"At least bazaki ga laifina sosai ba..." Fada yana bude kofan part din mom dinshi.
🧡����â¤
NA CUCE TA
����â¤í ¾í·¡
®Zuwairat (ummumpls am)
3⃣5⃣
_Follow me on:_
*Wattpad @ummumaryam29*
*Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com*
*IG: zuwairatummumaryam*
*Website:Www.ummumaryam.com*
*And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam
page.*
*Snapchat: ummumaryan29*
Bayan an gama aka saka mata shoes da suka hau da sky blue Arabian gown dake jikinta.
Perfumes matar ta fesa mata sannan ta tattara kayanta cikin bag tace
"Amarya kinyi kyau...." Tafada tana fiddo waya daga cikin pause dinta, pics tayi mata sannan ta
fita daga dakin, ita ai dija sai feeling so weird don gani take kaman an damkar mata buhun
cement a face dinta don nauyi taji fuskanta yayi mata.
"To ki tashi mu tafi...." Wata yar uwan ammi ta fada mata, jiki ba kwari ta mike idanuwanta cike
da kwalla amma basu zubo ba, wurin grandparent dinta aka kaita suka karayi mata adua sai
wajen amminta nan dija ta dinga kuka kaman ranta zai fita, tana kuka tana dafa maranta. Saida
ammi ta daka mata tsawa sannan tayi shuru "Kuma wallahi kar ki bari inji ance kiyiwa mijinki laifi...duk abinda yace kiyi kiyi kina jina?"..." Da
Sauri ta daga mata kai
"Allah ya kaddara saduwanmu...tashi ki tafi Allah ya yi maki albarka ya yafe maki
kurakurenki...." Jiki na rawa dija ta mike mata na biye daita, suna fita waje mata na tsaye cike
da waje wasu sunyi ready zasu bi ta don kashe qarkwatan idanuwansu. Bayan an nunawa dija
motan Salem ta shiga baya sai kuka take, sai yau Salem yaga dija, duk da kanta na kasa jikinta
ya nuna karamar yarinya ce, murmushi yayi ya kauda kanshi gefe cikin ranshi yana cewa
"Shege yazid...." Salem lekawa yayi a mirror yaga yanda mata ke rige2 shiga mota
"Allah yasa kar su lalata masu mota. Bai Ankara ba wasu mata kusan su uku suna kikarin shiga
gidan gaban motanshi, sai ture juna suke kaman wasu awakai, kaman yayi magana sai kuma
yayi shuru
"Ki bari ni na kamata in bita ba ke ba..." Inji daya daga cikin su,

"Lallai ma..." Daya ta fada, matar datayiwa dija makeup dake zaune baya kusa da dija ta tabe
baki sannan tace
"Haba kubi ahankali mana...ko so kuke Ku lalata masu mota..." Tafada cikin tsiwa da Sauri suka
ja baya daya ta shiga. Salem ya fixgi motan suka bar wajen, duk sauran cars na dauke a
mutane 8 biyar baya sai biyu gaba da driver. Salem kam yayi deciding bai maidosu saidai ya
samo bus da zai maidosu, babu abind ke tashi cikin motan sai sheshekan dija. Bayan sun gama sukayi wanka tare mufida ta zauna gaban mirror yazid ya goge mata gashi da
karami towel sannan ya shafa mai hair cream tare da combing kan, kawai yanayi yana kallon ta
tacikin mirror yana aduan Allah yasa this is not a trap don ko kadan babu wata damuwa tattare
daita hes wondering how comes don lokacin daya shaidawa mufida halinda ake ciki tamkar zaa
kwantar daita hospital, hannunta data dora kan hannunshi ya maidoshi hayyacinshi, murmushi
ya sakar mata yana cewa
"Baby I love you... Kinsan wannan shine abinda kikayimin daya fi komai burgeni...thank you.. "
murmushi tayi dukda maganar shi ta bata mata rai wato duk kokarin da take wajen biya Mashi
bukatan shi bata burgeshi kaman wannan ba, amma ko kadan bata nuna Mashi hakan ba
saboda advice da mom dinta ta bata. "Baby na zauna nayi tunanin babu komai duniya...sannan banason rabonda ke tsakaninka daita
ya aikadani lahira...so kawai Allah ya bamu zaman lafiya...kuma pls promise me you will love
and cherished me all the days of my life...." Tafada Mashi cikin natsuwa, hannuwanshi yayi
rounding waist dinta daga inda take zaune yayi hugging bayanta, "Baby I will love you for ever...I wish dukkan mata zasuyi yadda kikayi...su San cewa what will
be will always be nor matter what...." Yafada yana kissing bayan wuyanta
"Baby I love you too..." Tafada tana shafa face dinshi dake bayanta.
"Yanzu baby tell me abinda kikeso inyi maki...." Shuru tayi kaman tana tunani for a while sannan
tace
"Why not mu bari muje umrah tare...." Dadi yazid ya karaji ya kara rungume yana jin wani irin
sonta da kaunarta har cikin system dinshi.
"That sounds perfect my Queen... Yanzu yaushe su Aisha zasuzo?..."
"Zuwa later..."
"OK muyi sallah...kafin ki shirya kafin su zo...and pls my Queen kar ki biyewa duk abinda
zasuce....I know them too well...." Murmushi mufida tayi tace
"Baby don't worry... I won't let anyone lead me astray..." Tayi assuring dinshi
Murmushin jin dadi yayi bude closet ya saka jallabiya ya fita sallan asr. Itama doguwar riga tasa
tayi sallah.
🧡����â¤
NA CUCE TA
����â¤í ¾í·¡
®Zuwairat (ummummaryam)
3⃣6⃣
_Follow me on:_
*Wattpad @ummumaryam29*
*Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com*
*IG: zuwairatummumaryam*

*Website:Www.ummumaryam.com*
*And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam
page.*
*Snapchat: ummumaryan29*
*Wishing all my beautiful people happy sallah, Allah yasa dukkan ibadun mu* *karbabbune,
Ameen*
Ahankali ya bude kofan yana aduan Allah yasa Matan da suka rakota sunyi bacci, yana shiga
falon luckily mata biyar ya gani kwance kasan tiles suna bacci, kaman barawo ya taka yana
aduan Allah yasa tana inda she's suppose to be, yana bude kofan bedroom daya fi dukkan
sauran haduwa ya ganta kwance kasa sannan babu kowa, da Sauri ya shiga kaman Mara
gaskiya ya maida kofan ya rufe, ya yazo ya zauna gabanta bata san ya shiga ba, zama yayi
yana kallon yanda take sauke ajiyan zuciya kaman wacce tayi 360 race.
Kawai sai ya saki murmushi yana lumshe eyes kaman Wanda aka yiwa albishir da aljanna.
Kallon yanda take shessheka kawai yake don ya san ba karamin kuka tasha ba, kallon
hannunta dake kan maranta yayi., ahankali ya mike bayan ya ajiye drugs da abinci daya shigo
dasu. Cikin saddo ya bude kofa ya fita yana tafiya ahankali har ya isa kitchen, kara kallon
kitchen din yayi yana tunanin ya gan dija tana amfani da kayan kitchen din don ko shi da kanshi
bai san amfanin wasu kayan ba don he's not use to kitchen. Wani cup ya. Dauka cikin kayan da
aka jera ya kai sink ya wanke sannan ya dauki plate shima ya wanke sannan ya fito. Kara shiga
dakin still tana kwance yanda take. Zama yayi ya cika cup da milk sannan ya fiddo ragolis water
ya ajiye gefen milk din, plate ya dauka ya zuba roasted meat, hannu ya daga kaman ya tadata
amma baisan abinda zai tada mata hankali, yafi minti biyar yana daga hannu amma yana rasa
courage, amma ganin wankin hula zai kaishi dare yasa yayi karfin halin dan taba kafanta, aikam
a firgice ta farka tana mazurai, kallon Wanda ya tadata tayi da kyau ta tabbatar yazid ne, nan
take ta fara ja da baya tana yarfe hannunta at the same time tana fashewa da kuka
Cikin kuka ta fara cewa
"Wayyo Allah na....wayyo ammi na shiga uku..." Tafda sounding very tired and fed up, sai ka
take da baya while shikuma yayi kuri ya kura mata ido babu abinda yake sai kallon ta. Dija najin
ta kai bango ta kara volume din kukanta. Yazid ji yayi kaman ya rikota amma yasan it will only
make it worst. Gyara zamanshi yayi tare dayin ganmo da legs dinshi duk eyes dinshi kan ta, " tashi ki shiga bathroom ki wanko bakinki..." Ya fada sounding formal, da sauri ta girgiza kai
batare datace Kala ba, kuka tacigaba dayi
"Nace ki shiga bathroom ki wanko bakinki..." Yafada da karfi, aikam da sauri ta mike tashiga
bathroom, tana shiga ya fara dariya yana girgiza kai, ya gano one of her weakness, which is
tsoro, yasan tamkar monster yake wajenta and he's going to use it to his advantage, dija na
shiga ta dafa bathtub tana kuka, tana mamakin duniya bayan duk abinda yayi mata amma sun
hadata aure dashi, cikin kuka ta fara cewa
"Don sunga bani d baba....don Abba ya mutu...shiyasa sukayi min haka..." Tafada cikin kuka, ji
tayi muryan yazid nacewa
"Ina jiranki...." Da sauri ta dubi toothpaste rack and dispenser ta dauki brush ta zaro toothpaste
ta zuba jikinta sai rawa kawai yake, cikin sauri ta wanke bakin ta fito face dinta sharkaf da
hawaye, daga kai yayi babu faraa sosai kuma fuskanshi ba daure yake ba, tsaye tayi bata da
niyyan zama

"Ki zauna mana...." Yafada mata, da sauri ta saki jikinta ta zauna sai kuma ta rike maranta,
mikewa yayi ya dauki milk da plate ya ajiye gabanta.
"Bissimillah....." Yafada mata tare da nuna abubuwan dake gabanta, da sauri ta girgiza kai tana
kuka,
"Kinason ranki ya baci?..." Ya tambayeta, da sauri ta sake girgiza kai,
"To ki cinye yanzu nan...." Bai idaba ta fara cin naman tana kuka, duk cin da zatayi sai tears
dinta ya diga, har ta koshi amma tana tsoro daina ci, gani yayi tana Neman cinye kaza daya
kuma da alaman ta koshi amma bata Iya dainawa
Kallon yanda take tauna nama kaman paper yayi, kauda kai gefe yayi ya saki murmushi cos
he's enjoying the moment don yasan Yana daga cikin abinda zai dinga zolayanta dashi in future,
dauke plate din naman yayi ya maidata gefe sannan ya dauki cup of milk ya ajiye gabanta,
"Bissimillah..." Ya sake fada mata, tana shesssheka ta dauki cup din tana sha tana kuka at the
same time tana tunanin halin d zata fada yau don tasan bazai fasa yi mata abinda yayi mata da
ba, har yanzu bata bar tunanin dalilim dayasa ammi ta yarda aka hadata da irin wannan mutum
ba, ajiye empty cup din tayi tare da goge bakinta da bayan hannunta, yazid daukan ledan drugs
din yayi ya bude ya ballo wayanda zatasha ya mika mata, ganin yayi bata amsa ba, hannu yasa
ya kama right hand dinta Wanda yasa dija kara volume din kukanta, murmushi ya kara saki
enjoying the tenderness and warmth of her skin, ajiye drugs din yayi cikin hannunta ya dauko
ruwa daga cikin ledan daya shigo daita ya bude ya mika mata, jikinta na rawa ta amsa ta juye
dukkan Maganin cikin bakinta ta zuba ruwa ta rumtse ido ta hadiye, mikewa yazid yayi ya shiga
bathroom ya hada mata ruwan wanka ya fito,
"Ki tashi kije kiyi wanka...." Ya fada sounding so commanding, da sauri ta mike kaman Kazan
Da aka tsoma cikin ruwa ta shiga bathroom, tana kuka tana cire kayan jikinta, kallon kofan tayi
don gani take kaman zai shigo, bathtub ta shiga don already tasan amfani shi tun sanda tayi aiki
gidansu yazid. Jikinta na rawa ta gama ta fito ko goge jikinta batayiba ta maida kayanta ta fito
kanta kasa sai hawaye ke diga, "Ko pump albarka...." Yazid ya fada yana kallon yanda tears ke fita daga eyes dinta. Yazid
mikewa yayi daga inda yake zaune ya je bakin gadon ya yaye duvet dake rufe da gadon sai
wata bedsheets ya bayyana daga kasa
"Zo ki kwanta...." Ya umarceta, nan jikinta ya fara shaking to the extent yana ganin yanda duk
jikinta ke rawa, yasan he has ruin her life and he promise himself to make things right again, he
will do anything to make her trust and rely on him, duk tafiyan da zatayi sai jikinta yayi rawa,
ajiye duvet din yayi ya nufeta, bata ankaraba ya dauketa, wani irin kuka ya kufceta mata "Wayyo na shiga uku....ammi...." Tafada cikin matsanacin kuka, kasa tafiya yayi ya tsaya rike
data kaman babu komai hannunshi, kurawa swollen and tired eyes dinta ido yayi yana kallon
yanda tears ke rolling,
"Dan Allah..... Ciwona....ciwo gareni....kayi hakuri....." Tafada sounding so tired and afraid,
idanuwanshi ne suka ciko da tears, ahankali ya fara girgiza mata kai,
"Khadija.... Kiyi hakuri...." Bai idaba tayi saurin daga Mashi kai tana kuka
"Abinda ya faru tsakanina dake kaddara ne....dan Allah ki yafe min....nayi maki alkawarin bazan
cutar dake ba....bazan karayi maki abinda baki raayiba....duk abinda kikeso zanyi maki...." Duk
maganar dayake babu abinda take sai daga Mashi kai cike da tsoronshi with her eyes closed,
ahankali ya taka zuwa bakin gadon ya kwantar daita, bargon ya dauko ya rufa mata, zama yayi

bakin gadon yana yana kallon ta, bayan kaman minti five ya mike yayi pecking goshinta sannan
rage wutan dakin ya fita feeling so happy, cikin motanshi ya koma ya dauko dayan ledan ya
kulle motan ya nufi part din mufida.
����🧡
NA CUCE TA
����🧡
®zuwairat( ummumaryam)
3⃣7⃣
_Follow me on_
Wattpad *@ummumaryam29*
Email : *Zuwairat.nuhu@gmail.com*
IG: *zuwairatummumaryam*
Website : *www.ummumaryam.com*
*And you can also join my new facebook group:
_zuwairat ummumaryam_ and _zuwairat ummumaryam page_ to get updates on my novels.*
Ajiyan zuciya ya saki
"Pls ya Allah let it be like this for ever.... " ya fada yana kallon yanda mufida ya manna dija kan
chest dinta tana shafa bayanta, mufida daga Kan dija tayi tana kallon how weak, fragile and
innocent she looks, ahankali tadaga hannunta ta goge mata face tana cewa
"ko daina kuka kinji?" ahankali dija ta daga mata Kai, mufida mamaki take da bata jinhaushin
dija for a bit instead tafi him haushin yazid.
"kinci abinci?.." ta tambayeta cikin sanyin murya, Kai dija ta girgiza mata,
" to muje kici abinci.... " mufida tafada tana rike da hannunta while going into dijas apartment,
Dan tirjewa dija tayi sannan tace
" nakoshi.... Gida... Nakeso... Su tafi... Dani.... " ta fada tana kallon bus daya fita daga cikin
gidan,
"ai yanzu nan ne gidanki.... " da sauri dija ta girgiza mata Kai tana cewa
" banso... " tafada tana fashewa da sabon kuka,
"hmm ai dole kice bakiso... Don I understand what you went through in his hands...ni naji jiki
balle ke? ". Mufida tafada cikin ranta,
" bakison zama Dani? " mufida ta tambayeta tana murmushi, cikin kuka dija ta ce
"inaso... "
"to kiyi hakuri mu zauna tare kinjiko? " da sauri dija ta gyada mata kai,
"to muje kici abinci... " inji mufida, dija bata Kara cewa komai ba tabi bayanta hannunsu rike
dajuna. Mufida Kara kallon Falon tayi for the second time tasan yazid ko family dinshi sukayi
mata kayan.
" kizauna in je in dauko maki abinci... " inji mufida tafada tana zaunar daita kan kujera,
"da akwai abinci Chan dakin... Bari in dauko wannan... " dija ta fada tana mikewa,
Ahankali ta taka ta shiga bedroom dinta mufida tabi bayanta da kallo tana cewa
"maza basu da imani.... " ta fada kasan breath dinta. Dija dauko abinci da aka bata Dazun tayi
ta fito dashi kanta kasa,
"gashi... " dija ta fada tana nuna mata abincin, amsa mufida tayi ta bude taga it's rice and stew
da few slices of plantain,

"ki ajiye wannan... Bari in dauko maki wani... " mufida dake maida murfin takeaway din. Amsa
dija tayi while itakuma mufida ta Mike tafita daga cikin part din, ajiye abincin dija tayi ta koma
tazauna kasa kamar ba matar gidan ba.
Mufida na shiga part dinta ta tarda yazid zaune yana ganinta yayi saurin mikewa ya rungumeta,
harara ta watsawa bayanshi tana cewa
"Wai meye? " Dariya yayi yana cewa
"baby you're the best.... "
"wato don na nunawa matarka so shine kake jin dadi ko?.. That shows that you care for her
happiness more than mine.... " bata idaba ya tari numfashinta yana cewa
"you know ba haka bane...kawai am happy that the love you have for me bai rufe maki ido ba....
I love you so much babyna...."
"naji... " ta fada tana tureshi gefe daya, sakinta yayi ta shiga kitchen yabi bayanta wanting to
know what she's up-to, gani yayi tanazuba sauran pepper soup da sukayi breakfast dashi cikin
food warmer,
"baby ina zaki Kai wannan Kuma? " ya tambayeta dukda yasan it's for dija, banza mufida tayi
dashi ta hada tea cikin mug ta ajiye kan tray, ta juyo ta kalleshi,
"ka kaiwa matarka.... " ta fada mashi atakaice, murmushi yayi
"why not a kirata nan taci... Basai kin Kai mata ba.... " inji yazid,
" alright then... " mufida ta fada tana fito da abincin daga kitchen zuwa dining table, kaman
walkiya yazid ya fita daga part din mufida ya shiga part din dija dasallama ya shiga Wanda yasa
dija muguwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login