Showing 69001 words to 72000 words out of 108372 words
Chapter 24 - NA CUCE TA (1 to End) Complete by Zuwairat Ummu Maryam .pdf
abinci...." Inji mom din sultan, sultan
bin wata hanya yayi bayan ya umarci yazid daya biyoshi.
Nan suka shiga wani part mai dauke da falo da dakunan bacci biyu.
"Uztaz kayi amfani da wannan dakin.. " ya nuna mashi left hand side room,
"OK..thanks... Amma yanzu zanje inda na fada maka.... In na dawo da yamma zanci
sbuncin...pls help me explain it to mom kar tayi fushi...." Tsaya kallon shi sultan yayi
"Amma why not ka watsa ruwa nima in watsa ruwa sai muje tare?.." Da sauri yazid ya girgiza
Mashi kai kaman Mara gaskiya,
"No...I will find my way back...." Amsa mashi
"Hmmm you are just unbelievable.... To bari driver ya kaika tunda ba garin kasani ba sosai..."
"OK.. " yazid ya amsa mashi amma ba don ya so ba
Sultan fita yayi ya fadawa mom dinshi yanda sukayi da yazid, Sam bataji dadi ba amma daya
fada mata nan gidan zai kwana sai ta saki ranta. Wurin driver yaje ya sanar dashi ya shirya zai
fita da abokinshi.
Part din shi ya koma ya tarda yazid daya rafka tagumj, nan ya fada mashi motar is ready da
sauri ya mike kaman wanda ke zaune kan allura. Bayanshi sultan yabi da kallo yana mamakin
how boring yazid have become. Yazid na fita ya tarda driver dake zaune cikin motan yana
jiranshi da sauri ya jefa kanshi gaban motan yanda zai samu view din gari da kyau, "Ka kaini supermarket..." Ya fadawa driver don sayawa su ammi foodstuffs kaman yanda ya
saba saye duk sanda zaije kauyensu. Daya daga cikin supermarket driver ya kaishi. Fita yayi ya
shiga yana kalle2. Bayan kaman minti ashirin aka biyoshi da kayan abinci kala2. Daga nan suka
kama hanyan kauyensu ammi.
Ita kuma dija data tashi yau taji duk jikinta babu dadi, haka nan take samun weird feelings,
kawai cewa cikinta tayi batajin dadi, ta fita tana yawonta amma she walking tana bude legs
sabida yanda batajin dadin tafiyan. She feels so uncomfortable. Inda take cin abinci Safiya taje
ta gaida matar "Dija an tashi?..." Matar ta tambayeta,
"Eh...." Ta fada tana zama dan nesa daita don tana ganin the look on people's face duk sanda
ta zauna kusa dasu hakan yasa take zama dan nesa dasu. Tafi minti goma zaune bata ce kala
ba, juyowa mai kosan tayi
"Yau dija baki sayen kosai ne?... Ko sai ta kare?...." Matar ta tambayeta,
"Zan saya...." Ta amsa mata cikin sanyin murya, shuru ya an biyo baya sannan tace
"Dan Allah....inyi wanka.....gidanki?...." Ta tambayi matar muryan ta na rawa,
"Eh...babu matsala...amma ki jira in gama sai muje tare tunda da nisa kadan..." Matar ta amsa
mata, wani irin dadi taji don tunda aka gano she's on the street bata kara samun wurin wanka
ba, da tana wasta ruwa cikin bathroom din hospital amma yanzu angano she's not a patient aka
hanata wanka wurin. Yanzu ta manta rabonda ta sakawa jikinta ruwa. Kosai ta saya na hamsin
ta zauna nan ta ci tana jiran matar ta gama su tafi.
Sai wajen 10:30 matar ta gama ta tattara kayanta dija tabi bayan ta suka tafi gidanta
Suna isa ta nuna mata kewayenta
"Bissimillah...." Matar ta fada mata,
"To...na...gode..." Dija ta fada ta nufi tiny toilet din, tana shiga taga empty bucket, daukowa tayi,
"Ina...ruwa...da sabulu?..." Ta tambayi matar da ke kaikaye gidanta saboda yanda yara suka
hargitsa mata gida.
"Ga ruwa cikin wannan drum..." Ta fada tana nuna mata drum dake tsaye
"Sannan da akwai sabulu bakin window..." Ta nuna mata inda soap yake, jiki na rawa ta debo
ruwa, bata diba da yawa ba ta dauka ta kai toilet sannan ta dawo ta dauki sabulun.
Tana rufe kofa ta fara rage maranta sannan ta cire kayan jikinta, tana yi tana dan cije labe ko
ina ke mata zafi oho, tana gama cirewa ta ratayesu, tsayawa tana shafa cikin ta,
"Yau zamuyi wanka...." Ta fada cikin whisper, hannunta biyu rike da tummy dinta ta jingina da
bango, sai tayi saurin dagowa tare da Dan sakin kara, hannu ta dan zagaya bayanta tana tabo
inda keyi mata zafi, still inda ammi ta doketa da itacene, tana tabawa taji kaman wajen na ruwa.
Kurawa cikinta ido tayi kaman baa gobe, tana shafawa tana murmushi, "Ko ta ina zaka fito?...." Ta tambayi cikin, ahankali ta duka ta fara watsawa jikinta ruwa sannan
ta dauki soap da soso dake rataye ta fara wanke jikinta kaman wacce bata taba wanka ba, the
more tana wanke jikinta the more tana jin relief especially her private part, wani irin sakayau taji,
bag dinta dake gefe daya ta bude ta dauki wata riga amma ba neat one ba, saka kayan tayi ta
maida wanda ta cire sannan ta fito. Adua take Allah yasa matar tace ta zauna ko da na minti
ashirin ne,
"Na...gama...." Ta fadawa matar, juyowa matar tayi da murmushi fuskanta
"To dija...." Ta amsa mata
"Nagode...." Dija ta fada mata ahankali,
"Babu damuwa...." Ta amsa mata. Ahankali dija ta juya ta bar gidan.
Wankan datayi yasa taji kaman ta samu wuri ta kwanta, still tana jin yunwa cos kosan bai
isheta ba, tana tafiya cikinta na crumbling,
"Yi hakuri....kudin mu ya kusa karewa....dole muyi maleji...." Ta fadawa cikinta tana tafiya.
Wani waje Mara yawan mutane ta samu ta zauna nan kasa tare da mike legs dinta ta harde
hands dinta kan cikinta ta zauna tana kallon masu wucewa.
A kano kam ba karamin shagali ake ba, family house dinsu yazid ya cika tatul da mutane. Da
mufida tazo ranar Friday tambayan yazid hajuya karama tayi ta sanar da ita zai zo yau asabar,
mom dinshi kam haushi da takaici ya cikata da bata ga yazid ba, amma data tambayi Hajiya
karama ko tayi waya da yazid sai ta shaida mata mufida tace zai zo yau. Hakan yasa ta dan
kwantar da hankalinta.
Yau tun ten suke saka ido don ganin yazid amma babu shi, number shi mufida ta kira taji switch
off. Mom dinshi fada ta dinga yi dataga har karfe 1 babu yazid kuma karfe biyu ake daurin
auren. Itama kira tayi taji kashe
"Wannan yaron na naiman raina ni ko?... Zai ci ubanshi ne..." Inji mom dinshi dake tsaye kusa
da Hajiya karama cikin wata karamar daki wanda babu kowa,
"It's not late...kilan ya iso kafin daurin auren..."
"I doubt that... Gashi wayanshi bai zuwa?... Wallahi in bai zo ba to he better remain in abuja...
Don ranshi zaiyi mugun baci in har ya taka Gidan nan...."
Inji Hajiya babba dake huci
"Kiyi hakuri anty..kinsan yazid ya chanza...nidai Allah yasa yaga dija ko hankalin kowa ya
kwanta...." Inji hajia karama in a calming tune. Hajiya babba bata kara cewa komai ba ta fice
daga wurin, Hajiya karama daukan wayanta tayi ta sake trying number yazid amma shuru.
Yazid dai nan zuwa gidansu ammi driver ya fito ya fara shiga da kayan da yazid ya sayo. Ammi
ta koma rai da kashi don babu sauran flesh jikinta, duk wanda ya ganta sai yayi tunanin bazata
kai hour daya da rai ba, yazid yayi sallama ya shiga bayan an gama shiga da kayan, an gidan
ya fara gaidawa suna amsa mashi, da suna fushi dashi kan abinda yayiwa jikansu amma yanzu
sun gane haka Allah ya kaddara, ji yayi binto nacewa
"Har yanzu bamu ga adda ba...." Ta fada mashi don tasan saboda ita yake zuwa. Nan take
yazid yaji legs dinshi sunyi sanyi, amma daman he wasn't expecting su ganta. Inda ammi ke
kwance ya nufa, gabanta ya durkusa ya gaidata, ko bude ido batayi ba balle ta amsa mashi, sai
nishi kawai take "Dan Allah ki bari in kaiki asabiti....dan Allah ki rufamin asiri kar hakkinku yayi min yawa...." Inji
yazid dake magana kaman zaiyi kuka, still ammi bata ce kala ba, yafi minti goma nan durkushe
amma ko eyes bata bude ba balle ta tanka mashi, ahankali ya mike ya je wajen tsohon gidan.
Request ya nema kan a fadawa ammi ko zata yarda ya kai ta hospital, tsohon mikewa yayi ya
tarda ammi inda take kwance ya dinga sauke mata zafafan words wanda yasa ammi fashewa
da kuka
"Zanje...." Naji ta fadawa tsohon,
"Maza tashi ki shirya...in banda abinki ai wannan yaron nada tsoron Allah...ji yanda yake
wahalan zuwa nan....INA tabbatar maki in wasu ne ko tunawa basuyi....maza tashi ..." Ya daka
mata tsawa, ahankali ta mike jikinta sai rawa kawai yake Kaman 100 years old woman. Da
taimakon binto ta shirya, yazid na waje yana jiran fitowanta, few minutes later ta fito binto rike
da hannunta, sai wata mata dake biye dasu. Da sauri yazid ya bude mata bayan motan ta shiga
da binto sai yaruwan ammi.
Shima yazid shiga yayi,
"Ka kaimu asiti...." Yazid ya fada ma driver,
"Wanne?..." Driver ya tambayi yazid,
"Nima ban sani ba....amma ka kaimu mai kyau..." Yazid ya amsa mashi, tada motan driver yayi
yana cewa
"Ko in kaiku general hospital?..." Da sauri yazid yace
"Aa...nasan da akwai cikowa..."
"Zanyi masu bayani tunda momin abokinka babbace a asibitin... Na tabbatar basu bata maka
lokaci..." Inji driver,
"In ka tabbatar da hakan mujeto..." Ya fada ba don yaso ba don shi anything general ba so yake
ba.
Around three suka kama hanyan cikin gari, ammi ta jingina idanuwanta lumshe,binto sai kalle2
kawai take, adaidai lokacin da suka kusa isa gate da zai sadasu da hospital ita kuma dija ta
taho zata cin abinci rana don tun wannan kosai bata kara cin komai ba duk don tayi manejin yan
kudinta da baifi 1k ba, binto ta fara ganinta daga nesa amma bata yarda cewa itace ba, shima
yazid ya ganta kuma kallo daya yayi mata ya kauda kanshi gefe, da sauri ya kara maida kanshi
yana kallon ta while motan na shiga hospital, da sauri binto tace
"Laaaaa....wannan kaman.. Adda dija...." Tafada da sauri, da sauri ammi ta bude ido, yazid ji
yayi gabanshi yayi mugun faduwa,
"Stop the car!!!!!....." Ya fada cikin muryan da shi kanshi baisan yana dashi ba,
"Adda!!!!...." Binto ta kwalawa dija dake wucewa gefensu, dija daga kai tayi sukayi ido hudu da
binto, tsayawa tayi tana kallon binto then ammi data fashe da kuka ganin yanda dijarta ta koma
kaman almajira ga kuma ciki, yazid dai mutuwar zaune yayi yana kallon dija at the same time
hawaye na bin juna, dija na tabbatar amminta da binto ta gani ta saki bag dinta ta fara bin
motan nake Neman wajen parking da gudu tana kira ammi on top of her voice, motan na
tsayawa ta karasa wajen tarufe Marfin motan ta bude, nan take ta fada jikin ammi tana kuka,
babu abinda take cewa sai
"Ammi....ammi...kiyi hakuri....ban...karawa....ammi waje nake...kwana.....ammi kalli
cikina....ammi Dane cikin cikina...ammi yana motsi..ammi...ki maidani gida....ammi kar ki barni
nan...ammi ban kara yi maki gardama....ammi dan Allah ki maidani gida in barjin sanyi
daddare....." Yanda take magana sai ka rantse Mara hankali ce, babu abinda yazid yake sai
kuka, yana hawaye hannunshi biyu kan bakinshi. Dija kara rike ammi tayi tana kuka tana
magana, binto kuka likewise sis din ammi, shima driver dake zaune kusa da yazid juyawa yayi
yana kallon yar yarinyan dake irin wannan maganar shima saida hawaye ya tarar mashi, ammi
tallabo face dinta tayi
"Dijata...." Tafada cikin kuka, dija na kuka jikinta na rawa ta kama hannun ammi
"Ammi ki taba kiji....yana motsi...." Ta fada cikin matsanacin kuka, tun yazid na hawaye kawai
sai kukan taci karfinshi, jin kukan mutum yasa dija daka kai ta dan leka gaba, nan suka hada ido
da red and tearful eyes din yazid, da sauri ta mike tana
"Ammi shine....ammi wallahi shine...." Tana maganar tana ja da baya, ganin mota ya taho ita
kuna na ja da baya2 yasa yazid saurin fita daga cikin motan, aikam tana ganin ya fito kuma su
ammi basu hanashiba yasa ta juya da gudu wanda yayi daidai da zuwan motan. Before driver
Motan ya taka break it was late, wani irin karo dija tayi da motan yayi sama daita.
Hannu yazid ya dafa ga kai tare da saki wani irin razanannen ihu.
í ¾í·¡â¤
NA CUCE TA
â¤í ¾í·¡
®Zuwairat (ummumaryam)
2⃣9⃣
_Follow me on:_
*Wattpad @ummumaryam29*
*Email:Zuwairat.nuhu@gmail.com*
*IG: zuwairatummumaryam*
*Website:Www.ummumaryam.com*
*And also join my new Facebook group: Zuwairat ummumaryam and Zuwairat ummumaryam
page.*
*Snapchat: ummumaryan29*
Ammin data dade batayi tafiyan kirkiba sai gata ta fito daga cikin mota da gudu, haka zalika su
binto da driver dake cikin mota, yazid bai San sanda ya karasa inda dija ke wance ba, shima
doc daya bugeta fitowa yayi cikin tashin hankali,
"Khadija!!!....." Yazid ya dinga kiranta yana rike daita nan kasa, hannu ammi ta dora bisa kai
tana kuka,
"Khadija dan...Allah... Wake up...." Yafada yana girgiza ta da karfi amma ko motsi batayi,
mutane taruwa sukayi suna kallon su, doc daya bugeta ya rike yazid don ya samu daman duba
dija amma wani naushi yazid ya kai Mashi Wanda ya tsorata shi yayi saurin ja da baya,
"Khadija... Pls....don't do this to me....I will be miserable for the rest of my life...." Yafada yana
dorata kan kafanshi at the same time yana kuka kaman ranshi zai fita, duk mutanen dake tsaye
babu Wanda yayi kokarin taimakawa, doc daya bugeta nason taimakawa amma yana tsoro kar
yazid ya kara naushinshi, yazid tsaya kallon yanda cikinta ke motsi yayi ya daga kai yana kallon
faces din mutane yana cewa
"Dan Allah Ku taimaka min....pls help....." Da sauri doc din nan ya zo ya rike wrist dinta for a
while sannan yace
"Ka dauketa muje...." Inji doc cikin sauri, da sauri yazid ya mike ya dauketa, ammi da dasu binto
babu abinda suke sai kuka, bin bayan yazid sukayi shi kuma yazid na biye da doc, sai sauri
yake amma ko gabanshi bai kallo sai dija, yana tunanin yanda ta koma kaman baitaba
"Me zanyi maki in biyaki for all this pain...." Yafada yan kuka, kallon yanda cikinta ke ta motsi
kawai yake, bai ankaraba yaji zaa amsheta daga hannunshi, sai lokacin yaga nurses da gadon
da ake tura mutum, baisan ya akayi sukazo ba, babu musu ya dorata kan gadon aka fara turata
amma yana rike da hannunta, goshinta daya kumbura ya kalla. Motsin dan cikinta looks so visible da ko daga nesa kana Iya hangen yanda cikin ke motsi
kaman zai fito
Doc kallon ta yayi for ya moment sannan yace
"Take her to the labour room..." Hankalin yazid ne ka Kara tashi, baisan lokacin dayace
"Its just seven months....", doc dai baice komai ba amma deep down yana tunanin wanne
relationship ke tsakaninshi da ita don they look so different, babu alaman dangantaka
tsakaninsu don duk Wanda yagansu yasan they are from two different part of class and level
amma yanda yake nuna damuwanshi is questionable to him Inda dija ta kwana for some days aka shiga daita only she was unconscious, tsaye yazid yayi
aka shiga ciki daita, ammi dai kuka yaki tsayawa, yazid goge face dinshi yayi ya fiddo wayanshi
dake cikin aljihunshi Wanda ya kashe tun 12am na jiya kuma bai kara kunnawa ba saboda kar
mufida ta tisashi gaba. Kunnata yayi sannan yayi dailing number Salem, after like ringing biyu
zuwa uku yayi picking yana cewa
"Wai me yayi zafi da zaayi bikin lil brothers dinka amma baka zo ba?.... Gaskiya baka kyauta
ba... Dazun saida dad dinku yayi min magana bayan daurin auren... Karya nayi Mashi nace
kuna port...." Duk maganar da yake yana fada cikin annoyance ne amma gurin yazid shine ya
kai aya sannan ya fada Mashi abinda yake son cewa, yana jin shuru yafara cewa "Na ganta!..." Ya fada in one word,
"Wa?..."
"Khadija..." Ya amsa Mashi cikin sanyin murya , dasauri Salem ya saki ajiyan zuciya tare
dacewa
"Ina?..."
"A jos...."
"Da akwai cikin?..." Ya tambayeshi full of excitement,
"Yes....amma she have an accident while running away from me...." Yazid ya fada muryanshi na
rawa,
"Subhanallah!!....how is she?..."
"Yanzu anshiga daita ciki....salem... Na cuceta....you need to see her....ta koma kaman
baitaba....I don't know what made me do it...." Yafada yana kokarin sake kuka saboda yanda
heart dinshi keyi Mashi zafi,
"Rabo...kaddara...destiny...." Salem ya amsa Mashi in a calmly manner
"Yanzu me doc yace?... Hope it's not serious?..."
"Bata motsi....amma naga cikin na motsi...ka tayani adua...I don't want to loose anyone of
them.... Inason in biya Khadija for the pain and agony I caused her....kuma inason abinda zata
Haifa....nasan ana iya stigmatizing dan ko yan...amma ba laifin shi ko ita bane....it's all my
fault... The child deserve to live...." Yafada in a regretting manner at the same time hawaye na
gagarowa daga idonshi,
"Insha Allah the child will live...babu abinda zai samu both of them.... Ka kusa zama dad ko..."
Salem ya karasa maganar da zolaya, yazid zai bude baki yayi magana yaji call ya shiga,
dubawa yyi yaga small mom,
"Bari zan sake kira...mom is calling..."
"OK..pls give me updates about her..." Inji Salem
"OK..." Kawai ya fada yayi picking call dinta, itama balbaleshi ta farayi kan meyasa baizo daurin
auren su Sharif ba, saida ta kai aya sannan ya fada mata ya gan dija
"Kai alhamdulillah...." Ta fada with excitement kaman baita ke fada few seconds ago ba, dan
murmushi yayi sannan ya fada mata halin da ake ciki,
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!....hope it's not bad?..." Fada mata komai yayi
"OK...ka kula daita...zan yiwa anty magana don she's so angry..." Ta fada Mashi,
"OK nagode...." Ya fada yana juyawa don gani Wanda ke tahowa, ganin doctor ne yasa yayi
saurin katse wayan tare da nufanshi
"Doctor... Ta tashi?..." Ya tambayeshi,
"Yes...pls waye mijinta?..." Shine tambayan da doctor yayiwa yazid Wanda har su ammi sunji
Sadda kai ammi da family dinta sukayi while yazid ya kasa replying question din doc,
"Pls ya jikinta..hope