Showing 1 words to 3000 words out of 62424 words
[5/4, 10:10 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
BARKAN KU DA SALLAH DA FATAN MUNYI SALLAH LAFIYA
*Yadda muka fara Allah yasa mu gama lafiya, kura-kuran da zamuyi a ciki Allah ka yafe mana, har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba Wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 1&2
Kishingid'a tayi kan kujera me mazaunin mutun uku, da ka ganta kaga halaman tana cikin farin ciki, saidai ga dukkan alamu tana dan jin barci, ji tayi an turo 'kofa hade da sallama cikin tattausar murya me dad'in sauraro.
Duk da ta ji dadin muryan amma kuma tuni farin cikin dake fuskarta ya kau, ta mi'ke cikin tsorata da ganin sa, murya na rawa ta ce "Sannu da zuwa Ya Umar"
Ba tare da ya amsa ba ya kauda kai dan irin yadda yake ji a jikin sa, baisan me yasa ba, a duk lokacin da yayi arba da yarinyar yana jin wani abu na masa yawo a jikinsa harma kwakwalwansa, shi yasa baya son ganin ta kwata-kwata, yanzu ma da yasan ita kad'ai zai Tarar a falon da ba abin da zaisa ya shigo. Kallonta yayi a karo na biyu yaga ta sunkuyar da kai, ya ce "Munafuka sai ka ce wata mutuniyar kirki, ina su Abubakar"
Da sauri ta ce "Sun fita"
Ya ce "Abba fa"
Ta ce "Bai dawo ba"
Ya ce "Keda waye a gidan"
Ta ce "Ni da Ummice Umma ma ta fita"
Ya ce "Yi min magana da Ummin"
Da sauri ta tashi tayi ciki cikin ranta kuwa sai tsine masa take, tana shiga ta samu Ummi a tana kishingid'e a gado, ta hau gadon ta ce "Ya Umar yana falo ya ce na miki magana"
Ta tashi ta zauna ta ce "Gani nan zuwa"
Ba 'bata lokaci Ummi ta fito yayin da ita kuma ta kwanta a gadon.
Yana ganin Ummi ya zame daga kan kujeran ya gaisheta cikin ladabi da biyayya sannan ya mi'ka mata wasu takardu ya ce "Gashi Baba ya ce Abawa Abba"
Ta amsa sannan ta ce " ya Baban naku da Maman naka"
Ya ce "Suna lafiya"
Ta ce " To ka gaishe su"
Ya ce "Insha Allahu zasu ji"
Zai fita kenan sai ga wata yarinyar ta shigo da uniform a jikinta tana goye da Jakarta a baya tana ganin sa ta ce " Ina yini Ya Umar"
Bata jira amsawarsa ba ta wuce don irin yunwar da take addabarta.
Kai tsaye tayi dakin Ummi tana daga kwance taji shigowan ta tuni ta diro daga kan gadon ta mike ta ce "Khadiyo wa ya dawo da ke"
Ta ce " Su Ya Abubakar ne"
Ay da gudu ta fito har tana bige Khadiyo, Khadiyo ta ce "Wallahi Aunty bana yin abin da kike yi haba kamar yarinya"
Bata jira cewarta ba ta fito ta samu suna tsaye da Umar bata damu ba ta d'ale bayan Usman da yake shi yake kusa da ita, shi kuma ya ce "Ohh BILKISU zaki karya ni"
Abubakar ya zuba mata dundu a baya ya ce "Khadiyo bata yin abin da kike sister"
Ta sauka a bayan Usman ta fara bubbuga kafa kamar karamar yarinya tana cewa "Ni wallahi tunda ka dake ni to bayanka zan hau"
Du'kawa yayi ya ce "To hau abinki ya isa"
Tsaki Umar yayi saboda haushinta ya wuce abin sa, duka suka kalle shi sannan suka kada kai suka shiga, sai da ya kaita falo sannan ya sauketa kan kujera ya ce "Kawo mana abinci"
Da sauri ta shiga kicin ta dauko musu tare da plate tana gama ajiyewa Khadiyo ta fito da alama ta watsa ruwa ne, ta zauna aka fara cin abincin da ita suna hiransu.
ASALINSU
Garin Bauchi garine me tarin Albarka, da yawa mutanen garin basa zaman banza, mazansu da matansu suna neman na kansu, saidai kalilan me a ciki wanda basu damu su nema ba, akwai yan kasuwa akwai kuma masu aikin gomnati saidai yan aikin gomnatin sunfi yawa akan yan kasuwan.
Malam Hamza yana daya daga cikin yan kasuwan da suke garin Bauchi yana da Yara biyu, Ibrahim shine Babba sai kuma 'kaninsa Jafar Malam Hamza bai bar yaransa haka ba, ya sasu makarantar boko da ta Allo sannan kuma suna bin Mahaifin nasu kasu idan kuma sun dawo suna taya Mahaifiyarsu Hauwa aikin gida.
Koda suka yi karatu suka gama Ibrahim ya ce shi kasuwanci zai ci gaba da yi, shiko jafar fannin dabbobi ya karanta, yana da sha'awan zama likitan dabbobi.
Alhamdulillah duk kansu burinsu ya cika a nan ne kuma Inna Hauwa ta fara masa maganan aure, Ibrahim yana da wacce yake so mai suna Aisha, Jafar ne ko nena ma baya yi, amma da Mahaifiyar tasu ta bukata sai ya samu wata yarinya Sauda tana kawo 'kwai asibitinsu na dabbobi wato inda yake aiki,
Sauda ta fito daga gidan arziki gidan tarbiyya saidai kuma tarbiyan da gidan su suka bata ta watsar dashi, Sauda bada damu da ibada ba, saidai idan taji ankira Sallah idan da mutane a kusa zata yi Sallah a nutse kamar muminan gaske, idan ko ba kowa zatayi zaman ta idan ta wuce ta wuce kenan baza ta yi ta ba, ko kuma Idan tayi alwala a gaban mutane sai ta shige daki tasa hijabi tayi zaman ta.
Aisha kuwa ta fito daga gidan tarbiyya kuma tarbiyyan da aka bata bata watsar dashi ba.
Malam Hamza yayi bincike sosai sannan ya yadda da auren inda aka daura auren Ibrahim da Aisha sai Jafar da Sauda watansu biyu ko wannen su suka biya wa matansu da su kansu saudiyya a lokacin kuma suna da 'kananan ciki koda suka je sukayi ta rokon Allah ya basu zuri'a ta gari yayin da Sauda kuwa gaba daya kasar ne ma ta ishe ta tana Allah-Allah su koma kasar su, dan ba wani ibadan take ba, Aisha bata lura da hakan ba saboda ita tata ibadan tasa a a gaba.
Haka suka dawo gida da tsaraba niki-niki
Haka suka ci gaba da rayuwa Jafar ya fara gane Sauda bata damuwa da ibada dan wanda take ma na ganin ido ne don haka ya yi mata nasiha tare da tsoratarwa da fada mata irin azabar da zata shiga ranan gobe 'kiyama, ta tsorata matuka, ya lura harda rashin ilimi ke damunta dan haka yaringa koya mata karatu da yadda zata gudanar da ibadan ta.
Alhamdulillah yanzu tana damuwa da ibadan kuma tana yi hakan yasa Jafar yayi farin ciki, cikin haka ne cikin su ya Tsufa Aisha ta fara Haihuwan d'a namiji sai bayan kwana biyu kuma Sauda ta haihu itama namiji, Duk da Malam Hamza baida lafiya amma yayi tarnan ganin jikoki har guda biyu, har gida aka kawo su ya fara daukan Babban wato dan Ibrahim ya masa huduba da suna ABUBAKAR SADIQ sannan dan Jafar ya saka masa UMAR FARUQ.
Da yake kan iyayen a hade ne, tare yaran suka girma kamar 'yan biyu ko yaushe kayansu iri daya, saidai ita Sauda bata kaunan hakan a cewar ta kowa ya rike nasa, dan ita kan tunda ta samu Umar ma ta daina haihuwa dan bata son ta tsufa mijinta yace zai auri wata, kullun cikin masa kwalliya take don kada ya kyalla ya gano wata shiko ma ba abin da ya dame shi ba kenan, ganin ta samu abin da take so yasa, taje aka juya mata mahaifa ta ci gaba da abin da take yi.
Shekaran Abubakar Biyu Aisha ta kuma samun wani cikin murna gurin dangin ba'a magana, Jafar yaso ace Matar sa ma ta samu dan su haihu tare, saidai yana tunanin kila kafin ta haihu ita ma ta samu.
Cikin yana kaiwa haihuwa ta haifi d'anta namiji, wannan karan ma Malam Hamza da kansa ya rad'a masa suna USMAN, A sannan ne kuma Mahaifiyar su take jinyan ajali, tare sukayi ta jinyar ta Usman yana wata shi da ta ce ga garin ku, sunyi bakin cikin rashin mahaifiyarsu saidai ba yadda suna iya tunda ubangijin da ya halicceta ya fisu sonta. Tun lokacin Malam Hamza yaki yayi wani auren yana cike da damuwa ga hawan jini dad'i da ya samu jikin girma.
Haka suka ci gaba da rayuwa Aisha tun daga haihuwan Usman bata kuma na sake wani haihuwan ba, ta fara nuna damuwarta saidai mijin ta ya nuna mata illar yin haka.
Alhaji Ibrahim ba me ra'ayin zama da mace daya bane dan haka ya samu Aisha da lallashi da kalamai masu kwantar da hankali kan cewa zaiyi aure, taji damuwa a ranta amma da yake ita din bata da tashin hankali yasa tayi murmushi ta ce "Allah ya sanya Alheri Alhaji nidai roko na gare ka ka zama me adalci a tsakanin mu"
Murmushi yayi ya ce "Na gode kuma ki taya ni da Addu'a Allah yasa na zamo me yin adalcin "
Ta ce "Amin"
Tana cikin damuwa sosai dan haka ta dukufa Addu'a ta haka taji zuciyarta tayi wasai sannan ma ta ji tana son wannan aure da mijinta zaiyi.
Sauda kuwa tana jin labarin karin auren da Alhaji Ibrahim zaiyi ta shiga damuwa sosai a ganin ta ita ma mijinta zaice zaiyi dan haka ta garzaya taje ta samu Aisha bayan sun gaisa ta ce "Umman Yara naji Wai Alhaji zaiyi aure"
Aisha tayi murmushi ta ce "Kiyi hakuri laifina ne da ban fada miki ba, amma naso naje har gida na same ki da maganar "
Sauda ta ce "Haba Umman yara za'a miki kishiya amma ko ki nuna damuwa, kinsan wacece kishiya kuwa?"
Mrs Aliyu ce🥰
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad'e вa'aje вa.✍🏻
[5/14, 6:59 PM] Mim😘: 🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer'ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com
loadιng...........✍🏻
🌐BILKISU
Labari da rubutawa
MAIMUNA ISAH MUSA
(Mrs Aliyu)
Marubuciyar:-
INA DANGINA
IZZAR MULKI
JININA
YAK'I A SOYAYYA
AMANATA
FAHIMTA FUSKA
MAIMUNATU
MAHAUKACINA
and now
BILKISU
*Har yanzu kofa a bude take ga masu sharhi ko gyara 09034313679*
_Ban yadda wani ya juya min labari ba da izini na ba, wanda yayi hakan shi da mahaliccinsa_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Page 3&4
Aisha kan kallon mamaki tayi ta mata har ta dire sannan ta ce "Amma Maman Yara kin bani mamaki, Dan Alhaji zaiyi aure sai in tada hankalina akan me, nima fa auto ni yayi, A'a ni gaskiya kada ki kara kawo min irin wannan maganan ina farin ciki da auren da zaiyi ay karuwa ce"
Shiru Sauda tayi ganin bata samu nasara ba ta ce "Kiyi hakuri insha Allah bazan kara zuwa miki da irin wannan magana ba Allah ya baku zaman lafiya"
Aisha ta ce "Amin"
Koda bikin yazo da ita akayi komai ita kanta Aishan taji dadi da taga Saudan tana shiga da fita ita ko Sauda karfin hali ne kawai take a tunanin ta Mijinta zaice zaiyi auren shima tunda d'an uwansa tayi.
Anyi biki an watse amarya Suwaiba ta tare a dakin ta, zaman lafiya sosai ya wakana a gidan ita take yiwa su Abubakar komai dan ma Umman su tana hanawa takance "Haba kina Amarya kina wahalar da kanki a kan yaran nan"
Takance "Ay nima yarana ne kinga ko ay baza ki iya raba ni da su ba"
Hakan akayi karshe sai su Abubakar din suka koma gurin ta, idan Umar ma yazo a can yake tarewa tayi ta koya musu karatu.
Ba haka Sauda ta so ba, taso Mama Suwaiba ta kasance yar ba'kin hali irin saboda su hadewa Umma, saidai bata samu wannan ba, taso ta hana Umar zuwa gidan saidai kuma Babansa da kansa yake kai shi, ba yadda zata yi dole ta hakura.
Shekara biyar kenan da auren Mama Suwaiba amma ko batan wata batayi ba, sunje asibiti lafiyanta kalau Umma ma shiru ba labari, ita kan ma Mama Suwaiba bata damu ba tunda ta samu su Usman. Alhajin ne dai yaso su kara haihuwa tunda shi yana bukatar yara da yawa.
Tafiya yake a mota a hanyar dawowan sa daga Kumo ta jihar gombe, dan yin ta'aziyyar wani abokinsa da matarsa ta rasu, yana sauraron karatun Al-qur'ani mai girma ganin yariya yayi da kayan Fulani da kwaryan Nono a kan ta kafin ya Ankara ya bugeta Nonon ya kwaranye a titi ita kuma ta fadi kasa warwas, Alhaji ya duba yaga ba kowa a gurin ya dubeta yarinya ce karama bata wuce shekara sha hudu ba, ya dauke ta, daukanta yayi ya sata a mota ya karasa cikin gombe da ita ya kaita Asibiti, saida ya gama biya kudin komai tukun sannan ya ce su kula da ita bari yaje ya duba 'yan uwanta, yana zuwa gurin yaga wata mace ita ma baffulata ce tana kuka da fasheshen kwaryan a hannunta cikin muryanta na Fulani tana cewa "Sikenan Na rasa 'yarnan yanzu Halin ma an tafi da ita,"
Gefenta akwai namijin sai ya matsa kusa da na mijin ya ce "Assalamu Alaikum, ka fada mata ta daina damuwa yarta tana nan ba tafiya da ita aka yi ba"
Da Sauri ta juyo ta ce "Alhaji ina take"
Ya ce "Ta samu hatsari ne an samu kuskure ne na bugeta a mota"
Sake fashewa tayi da kuka tana cewa "Sikenan ta mutu Ko Baffa mun rasa Hali ma"
Baffa ya daga sandan zai bugawa Alhaji sai kuma ya sauke ya ce "Kayi sa'a naji wa'azi da na karka"
Alhaji ya ce "Ay hakuri dai muje in kaika inda take"
Duka suka duri motar shi dama Baffa yana shiga mota idan zaije cin kasuwa, ita ce dai bata taba shiga ba shi yasa ta kasance a tsorace.
Suna zuwa suka samu ta farfado tana ganin iyayenta ta fara cewa Inna kiyi hakuri bansam mato na zuwa ba gashi Nonon duka ya zube,"
Baffa ya ce "Ay ko sai ya biyà"
Hali ta ce "Ayya Baffa bafa laifin sa bane nice naje ketare titin zan nemi motan gombe ban ji karan motar sa ba"
Inna ta ce "Dama laifin ki ne", taje ta fara dukanta
Alhaji da ya tsaya yana ganin ikon Allah yaje ya ce " Kiyi hakuri Inna zan biya kudin bari ta samu lafiya"
Kawar da kai tayi ta koma gefe, alamun kunya, haka yayi ta lallashin su har ya gama biyan komai ya tafi da niyyar zai dawo washe gari ya sake duba su.
Washe gari yana komawa ya samu dakin ba kowa ya sake dubawa basa nan, ya wuce office din likita, saida ya zauna ya ce "Likita ina maras lafiyan nan da na kawo jiya"
Likita ya ce "Alhaji wallahi sunƙi zama sun tafi rigar su, nayi nayi da su wai su basu yadda da mu ba, ay an fada musu duk wani likita dan mafiya ne"
Alhaji ya ce "To yaya jikin yarinyar to"
Ya ce "Alhamdulillah ta samu sauki "
Ya ce "To yanzu kasan inda suke kuwa"
Likita ya ce "Ban sani ba amma kaje can inda kuka samu hatsarin ka bincika ko zaka same su"
Godiya ya masa ya masa sallama ya wuce, yana zuwa dai-dai gurin kuwa ya ci karo da shanu a gefen hanya suna kiwo yana dube-dube can ya hango Baffa a karkashin saniya da kwarya a hannunsa yana tatsan nono, daga nesa ya yayi sallama Baffa ya ɗago yana kallon sa ya taso da kwaryan yana washe baki ya iso gurin ya ce "Hannu Alhaji, kai amma kai mutumin kirki ne tunda har ka iya biyo mu, dama haka mashu mota shuke, Ay ni nayi tunanin duk baku da imani "
Alhaji Ibrahim ya ce "Ay ba duka aka taru aka zama daya ba"
Baffa ya mika masa ƙwaryan nonon ya ce "Gashi Alhaji shanye du"
Alhaji ya amsa ya kurba ya mika masa ya ce "Ya isa haka"
Ya ce "A'a Alhaji shanye du, du zaka shanye"
Alhaji ya sake kurɓa ya ce "Ay ban iya shan danye bane "
Ya ce "To muje can gida dama akwai wanda Hali ta tatsa ka tafi gida da shi"
Alhaji Ya ce "Nagode dama nazo in duba jikin Halin ne sannan na bada kudin Nonon da tsautsayi ya fada kansa"
Baffa ya ce "Kada ka damu Alhaji ay nikan ma sa riga na samawa Hali Mijin aure"
Alhaji ya ce "Masha Alhaji sai a fada mana ranan sai muzo a daura auren dani kaga na kawo iyalaina ma ayi miki da su"
Baffa ya ce "Ay kaine mijin Alhaji yanzu za'a daura ku tafi da ita"
Tsayawa yayi Ya kasa tafiya, Baffa ya juyo ya ce "yarana sun jima ba suyi aure ba, har mutanen rigagen da muka zauna suna cewa hala tsafi zanyi dasu, to ni kuma ina son zaɓa musu mijin da zai rike su tsakani da Allah ne, nayi niyya a raina koda yara na zasu tsufa ne bazan aura musu mungun miji ba, to Alhamdulillah na aurar da Bilki a wani mutumi me kirki har ta haifi yaro ma kuma tana zuwa gun mu, saura ita Hali, ita ma yanzu na gano mata miji, Alhaji Sadaki kawai zaka kawo a daura, dan baza kabar rigar nan ba saida Matarka Hali.
Alhaji ya ce "Mata na biyu kuma ay Hali tayi ƙarama a aurar da ita”
Tab to idan da na aurar da ita lokacin auren ay da yanzu tana da yara.
Ya ce "Mubar wannan maganan muje in ganta kawai"
Suka tafi cikin rigar duk inda suka ratsa yaran rugan suna kallon Alhaji har sukaje ƴar bukkan su Buba Inna tana ganinsa ta shege daki da sauri ta dauko tabarmar kaba ta shimfida masa tana masa sannu da zuwa, Hali ya hango can gefe itako tana ganin sa tazo ta durkusa ta gaishe shi kanta a kasa sannan ta shiga cikin bukka ta dauko masa madara ta mika masa Inna kuma ta kawo masa ruwa, yasha ruwan kadan, sannan ya ce "Inna ya kuka bar asibiti kuma