Showing 1 words to 3000 words out of 93605 words
Chapter 1 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺
*GELLE ƁINGEL*
🏺🏺🏺🏺
*Story*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
*Littattafan marubuciya*
Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.
And now *GELLE ƁINGEL*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
➰➰ *1 to 2*
*Gombe State*
Garin gombe garine na fulani mai tarin albarka duk da kasancewarta garin Fulani, hakan bai hanata tara ƙabilu dabam dabam ba, kama daga tangale, kanuri, bolawa, wajawa, terawa, Daɗawa, Dadiyawa, da sauran su, haka ta tara ƙauyuka na fulani a cikin wannan jihar ta Gombe akwai local government wanda ake kira da *DUKKU* acikin wannan local government ɗin na dukku akwai wani ƙauye na fulani Usul ko hausa basa ji sosai, wanda ake kira da *TULDEN FULANI* Tulde ƙauye ne mai tarin albarka, kama daga kiwon dabbobi noma harma da ƴaƴan itatuwa, a cikin wannan ƙauyen suna zaune ne cike da farin ciki, da ƙaunar junansu kasancewar Fulani mutane ne masu haɗin kai, mutum biyu ne kawai matsalarsu wanda kullum suke jawo musu fitina wato *INNO* da jikarta *JUMMO* INNO ta kasance gagararriyar tsohuwa wacce kullum bata da aikin daya wuce hura sigari da gabzar goro rashin mutunci kuwa wajen INNO ya ta'azzara bata da tsoro bare shakka, INNO bata da mutunci ko kaɗan tamkar ba bafulatana ba, kowa shakkar ta yake cikin ƙauyen, wannan ɗabia ta INNO jikarta JUMMO ta biyo wasu daga ciki, sai dai koda wasa Jummo bata taɓa shawa'ar sigari ba, ita dai barta da rashin kunya gami da masifa bata tsoron kowa, mahaifiyarta Sikayel da kakanta Baffa suna mungun takaicin halin INNO da Jummo, domin kuwa toka ce ta haifi wuta, Sikayel macece mai sanyin hali da tarbiyya tana bawa Jummo duk wata tarbiyya daya dace, sai dai INNO sam bata bari ta ɗauka hakan yasa Sikayel dagewa da addu'ar Allah ya shirya mata Jummo, Jummo tafi dukkan ƴan matan ƙauyen kyau da diri duk inda ake neman cikakkiyar mace, Jummo ta tsaya a nan matsalarta ɗaya rashin tsafta, domin kuwa Jummo cikakkiyar ƙazama ce, wannan kenan.
Zaune take gaban INNO ta tanƙwashe ƙafafuwan ta, tare da saka hanu ta tallafi fuskarta tana kallon INNO dake famar hura sigari tana gugar goro kasancewar ta bata da haƙori, dole sai da guga, taɓe bakinta Jummo tayi cike da rashin mutunci tace wa INNO.
" Cap!!! Wallahi INNO kin shiga Uku, yanzu haka zaman da nake a gabanki hango masauƙin ki nake a cikin wutar jahannama!!! Yanzu ke INNO idan banda rashin tsoron Allah, Baffa ya tara almajirai a waje yana koya musu ƙur'ani, ke kuma kina nan zaune anan kina bitar sigari, Allah ka kashe INNO gobe ta shiga Uku a hanun walakiri!!!!''
Jummo tayi Maganar tana sheƙewa da dariya, INNO kuwa jikinta na ɓari ta bar gugan goron tare da ajiye tabar ta fuskanci Jummo, kanne ƙananan idanunta tayi, alamun rashin mutunci tace.
" Ubanki Jauro da uwarki Sikayel, masauƙin su kika hango!!! To dan kutumar ubanki, da kike kira min mutuwa, ni nan da kike gani bazan mutu yanzu ba, sai na gama ganin taku sai naga ta uwarki naga ta ubanki sannan naga taki, kuma duk da haka ina nan daram, shegiya mai kai kamar ƙoƙiya, kin faɗawa ubanki Jauro!!!'
INNO tayi Maganar tana saka hanu ta ɗauki goronta ta cigaba da guga, Sikayel dake gefe tana surfa hatsin dawa ne ta girgiza kanta kasancewar tana sauraron dukkan hirar su, wai damma a haka ƴar ɗakinta JUMMO ne tayi Maganar, da wani ne yayi wannan maganar ba Jummo ba, mai shiga tsakanin su da INNO sai Allah, Jummo dariya tasa har tana sunkuyawa tace.
" INNO kice gadin duniya zakiyi kenan, to idan kowa ya mutu ya barki ke kinyi ta karshe waye zai miki sallah bare a rufeki a ramin ki?''
Ɗago kanta INNO tayi take ranta ya ɓaci ta haɗa fuska tamkar zata danna kuka, a duniya ta tsani a kira mata mutuwa, musamman a kira mata kabari sai taji tamkar ta zura da gudu, hantar cikin ta ya kaɗa, ranta na ɓace tace.
" Jummo kiyi hkr ki daina kira min mutuwa, banason sunan kabarin nan, Allah ni na yadda nayi ta ƙarshe a duniya, babu ruwana da wani mai min sallah, idan na mutu ai shikenan ni ina ruwana yama fimin dama bana son zaman wannan kabarin, kina gani rami ɗan karami za'a tona a saka mutum a cikin sa, a rufe ko ina tsabar mugun ta ko hujin da zakasha iska baza'a bari ba shikenan an raba ka da kowa iskar ma baza'a bari ka shaƙeta ba."
Dariya ce taso kwacewa Sikayel, sai ta danne dariyar gudun masifar INNO, ta cigaba da surfen ta, tana sauraron su, Jummo kuwa murmushi tayi tare da miƙewa tsaye, ta zari sandarta, gyara rigarta na fulani dake jikinta tayi, ta sunkuyo kan INNO daidai kunnenta ta raɗa mata.
" Ko zaki hallaka sai kin mutu an saki cikin wannan kabarin da bakya so, muddun baki daina shan wannan sigarin ba, da wani magulallen bakin ki, da babu haƙori."
Tana gama maganar ta zura da gudu tana dariya tace.
" Sikayel mi dilli sai mi warti (na tafi sai na dawo)"
Sikayel da kallo tabi Jummo tace.
" Garta jam (a dawo lafiya)"
Jummo bata ma ji Sikayel ba tuni ta fice, da gudu.
Ai kuwa INNO bala'i ta hau da mita.
" Sai naga uban da zai binne Ni, shegiya mai mungun fata, da ɗan iskan bakinki kamar murfin shadda, ina nan zaki dawo ki sameni."
Baffa dake zaune cikin tarin almajiransa ne ya kwalawa Jummo kira.
" Jummo!!!"
Cak ta tsaya tare da tura baki, tana ƙunƙuni, tasan bazai wuce zancen hadda Baffa zai mata ba, ita tun jiya da ta ajiye allonta bata kuma ɗauka ba, muryar Baffa taji yana cewa.
" Waro mana Jummo"
Ta kowa tayi gabansa tare da tsugunnawa cikin bagwariyar Hausar ta da bata nuna ba tace.
" Sannu da karatu Baffa."
Murmushi yayi yana kallon yanda ta haɗa rai, yasan wannan fushin da tayi duk dan karya mata zancen hadda ne, girgiza kansa yayi tare da cewa.
" Meyasa baki tafiya a nutse ne, Jummo kullum kina razane tamkar baki da hankali, ki dinga tafiya cikin nutsuwa wannan shine ɗabiar mace, kul na kuma ganinki kin fito da gudu."
Kanta ta ɗaga alamun to tare da ƙoƙarin miƙewa zata tafi Baffa ya dakatar da ita da cewa.
" Meya hanaki zuwa ki biye karantun ki, yau tun safe."
Ƙara haɗa ranta JUMMO tayi dama ta sani dole sai ya mata wannan tambayar, cuna baki gaba tayi sannan tace.
" Dama jiya dana koma zanyi karatu harna ɗauko allon, INNO ta aikeni shagon manu na saya mata karar sigari, dana dawo kuma dare yayi shine kawai na kwanta amma gobe zanzo na biya."
Girgiza kansa Baffa yayi cike da ƙyamar halin INNO yace.
" Tafi abinki Jummo!!"
Tashi tayi cikin sauri tabar wajen jugum Baffa yayi yana nazarin mummunan ɗabiar matar tasa, ya rasa ya zaiyi da ita dukkan ta inda ya ɓullo mata dashi, sai tabi ta toshe, wannan wacce irin munguwar rayuwa INNO ke fama dashi, numfashi yace ( " Allah ka shirya INNO" ) ya cigaba da biyawa almajiransa karatu.
" Ni Jummo Jummo jummala!!! Jummo me nake bukata faɗi muji jummala🎸🎸 ni dai taliyar turawa nake bukata jummala, wai shin ina zana samu jummo ce, taliyar turawa akwa.............''
Katse waƙar tayi ganin Gaɗɗo tsaye a gabanta sai haki take da alamu gudu tasha, cikin tashin hankali take cewa Jummo.
" JUMMO rumfar Ja'e Sumaye!!! Yako zai kasheta!! Zai kasheta ki taimaka min Jummo!"
Gyara tsayuwarta Jummo tayi tana dariya domin kuwa yau ta samu, murmushi ta saki take yalon hakwaranta suka bayyana tacewa gaɗɗo.
" Ta faɗi ƙasa gasassa dama kuwa aradu goma nake nema, biyani Naira goma naje na sayi faɗan''
Tayi Maganar tana riƙe kunkumi harda jijjiga tare da miƙawa Gaɗɗo hanu alamun ta bata, gaɗɗo babu musu ta danƙawa Jummo murtala ɗaya kuɗin da innar ta, ta aiketa sayo dunƙule, karɓa Jummo tayi ta ɗaure a bakin zaninta tare da tattare zaninta, ta kwasa a guje ta doshi shagon Ja'e, Gaɗɗo ma rufa mata baya tayi basu tsaya ko ina ba sai rumfar Ja'e, tsakiyar Sumaye da Yako Jummo ta tsaya tare da riƙe kunkumi ta haɗa fuska tamau, sunkuyawa ƙasa tayi ta ciko tafin hannayenta da ƙasa ta miƙawa Yako.
" Na sayi faɗan ganaa masifa gana bala'i zaɓi wanne zamuyi a ciki"
Dariya Yako yasa dama kuwa ya juma yana jiran wannan ranar, ranar da zaici uban Jummo domin kuwa mungun haushin ta yake tun sanda ta yiwa ƙanƙara Jaɓɓo duka, na bala'in ya buge, ai kuwa Jummo bata jira mai zaice ba, tayi wani irin zillewa ta sunkuya ƙasa kafin Yako ya ankara ta kwashi ƙafafuwan sa, ji kake tim!!! Yako ya faɗi ƙasa, kafin ya yunkura ta doka masa sandar ta a ƙafafuwan sa, wani irin ƙarar azaba Yako ya danna, kansa Jummo ta ɗale tare da shaƙo wuyansa, Sumaye ta kalla tace mata.
" Ɗebo ƙasa ki cikawa shege a baki."
Ai kuwa sumaye ba musu ta ɗebo ƙasar Jummo ta matse bakin Yako suka ɗura masa sai famar muƙurƙusu yake ya gagara kwacewa jinsa duk yayi tsami, ada gani yake duka ɗaya zai yiwa Jummo sai ruwa amma yanzu ya fahimci tabbas yarinyar aljana ce, Ja'e daya fito daga bayi ne, ya karaso wajen da sauri yasa hanu yana janye Jummo daga jikin Yako, da ƙyar ya ɓanɓareta, yana haki Yako kuwa idanunsa yayi jajur sai famar furzar da ƙasan bakinsa yake, da ƙyar ya tashi ya zauna Ja'e ne yace.
" Haba Jummo, meyasa zaki masa haka Yako fa ba sa'an ki bane sa'an yayanki Sauru ne, ki shige ki tafi a nan ke sam baki jin magana kowa faɗin fitinarki yake cikin rugar nan."
" Karma ta tafi dan ubanta!!" muryarsa ta doki dodon kunnen ta wani irin lumshe idanunta tayi tare da saka hannunta ta dafe ƙirjinta *Mai oda* yaushe yazo cikin garin nan? Ta jefawa kanta tambayar, juyowa tayi ta taho da gudu zata rungumesa tana.
" Oyoyo my oda ta!! Oyoyo yaya *GARKUWA* kifiyar sonka ta soke ni aradun Allah ina sonka."
Saurin kaucewa Garkuwa yayi gudun karta taɓa sa da wannan dattin, ransa ya haɗa fuskarsa a ɗaure dama can shi ba ma'abocin dariya bane a hankali tamkar baya son magana ya nuna ta da yatsa.
" Ke kam wacce irin jaka ce, dabba ce ke, wawiya jakar ƙauye, mahaukaciya, idan kika kuskura koda wasa hanunki ya taɓa koda gefen rigata ne, wallahi sai na kwantar dake mtsss!!! Nonsense mtsss!"
Yayi Maganar yana buɗe motarsa fara sol mai kyawun gaske ya shige, idanu Jummo tabi sa dashi a duniya tana mungun son Garkuwa soyayya ta zahiri, motar ta nufa da gudu tana cewa.
" Wallahi ina sonka my oda ta, my hanta ta, kai kayan ciki nane ma kai, kuma wallahi sai ka soni, zaka aureni ya garkuwa."
Girgiza kansa garkuwa yayi tare da figar motar da ƙarfi ya buleta da ƙura, tsayawa Jummo tayi shuru sai kuma ta kwasa da gudu tamkar mahaukaciya tabi bayan motar, tama manta da su Sumaye a wajen, Gaɗɗo ganin Jummo tabar wajen ya sata kama hanun Sumaye suma suka gudu, gudun kar Yako ya tashi su shiga Uku.
Yako kuwa idan banda huci babu abinda yake, ji yake cikin ransa wallahi bazai bar Jummo ba, ƙara zai kaita wajen Lamiɗo, bazai yadda da cin mutunci ba.
Ja'e kuwa babu abinda yake sai yiwa Yako sannu domin dai yaji jiki.
Tsakanin ta da Allah Jummo take gudu tana bin motar, ƙofar gidan kakansa garkuwa yayi parking, a hankali ya fito daga motar kina ganinsa kinga cikakken bafulatani kasancewar sa fari sol siriri kyakkyawa, sai dai mutum ne mai izza da iko gami da jin kai, tamkar aljana ya ganta tsaye a gabansa.
" Allahumma ajirni fil musibati, Allah ya haɗa ni da mayya, wai meyasa kika addabeni kika damu rayuwata ne, dole ne sai kin shiga sabgata yau naga mayya ayi mutum shi bashi zuciya tamkar kare."
Bakinta ta tura tana murguɗa bakin tace.
" Ni dai sonka nake ka Aure ni."
Zaro idonsa garkuwa yayi yana nuna kansa da yatsa yace.
" Ni kike so na aureki, lallai ya tabbata ke mahaukaciya ce, Allah ya tsari gatari noma kauce ki bani waje mahaukaciya ƙazama"
Ƙara turo bakinta tayi tace.
" Ni dai ba mahaukaciya bace!!! Ehem sai dai idan kaine mahaukaciyan ko Mamma Amma dai bani ba, kuma wallahi Allah sai ka aureni.
Zaro idonsa yayi ya furta.
" Ni da Mamma mune mahaukatan?'''
" Eh kune ba niba"
Wani irin mahaukacin mari Garkuwa ya ɗauke ta dashi yana nuna ta da yatsa yace.
" Na tsaneki tamkar na kasheki haka nake ji, na tsaneki na tsaneki, kinga daga yau idan na shigo wannan ƙauyen kika kuma tareni sai naci ubanki!!!"
Yayi Maganar da ƙarfi yana hankaɗata da hanunsa ta faɗi ƙasa, shigewa cikin gidan kakan nasa yayi yana tsuka, ita kuwa Jummo kuka ta saki mai cin rai, tashi tayi da gudu ta nufi gidan su tana danna ihu tamkar wacce za'a kashe.
Da sallama ya shiga cikin gidan, Kakarsa Mamma na zaune tana ƙoƙarin dafa dambu ya shigo, kanta ta ɗaga tana murmushi tace.
" Ameen wa'alaiku mussalam, Garko kaine tafe da rana tsaka, lale maraba sannu da zuwa."
Ranshi na ɓace ya amsa mata da yauwa sannu, yana jawo kujera ƴar tsugunno kallon sa Mamma tayi ransa a yana haɗe cike da tsokana tace.
" To uban ƴan bakin rai, me kuma aka maka kake yamutsa fuska kamar kwanannen lawashi, ni tsiya ta da kai baƙin hali."
Harara garkuwa ya daka wa Mamma yace.
" Anyi baƙin halin, ba yamutsatsiyar lawashi ba Allah yasa yamutsatsiyar Albasa, nifa Mamma Daddy na shiga haƙƙina da yake turoni wannan ƙauyen, ayi ƙauye duk sheɗanu, Allah na kusa daina zuwa wannan ƙauyen idan baki shiga tsakanina da wannan shegiyar aljanar yarinyar ba, joma take jumma."
Dariya Mamma tayi, tare da cewa.
" To uban ƴan baƙar magana, ubanka ma sheɗanin ne kenan tunda shima nan aka haifesa, wai meye laifin Jummo ne kam da bazaka sota ba, kyakkyawar yarinya, ni dai banga laifin ta ba"
Mamma tayi Maganar tana ɗauko sigari ta saka a bakinta, ashana ta ɗauka zata kunna, Garkuwa ya ƙwace ashanar yana haɗe rai cike da ɓacin rai yace..............
Wannan labarin yana ɗauke da abubuwan al'ajabi iri iri labari ne mai ɗauke da tsantsar tausayi, bariki ga kuma ban dariya, ku dai ku biyoni sannu a hankali domin jin inda zaren
labarin zai kai mu.
*Na faɗa muku wannan book ɗin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙi 150 kacal masu TRANSFER to account number na 0006064512 Rashida Usman jaiz bank ga masu turo kati kuma MTN card zasu turo na 200 ta wannan numbern 08147537180 banda VTU*
Vote
Share and comments
08147537180
Alƙalamin Rasheedat Usman.
UMMU NASMAH✍🏻
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺
*GELLE ƁINGEL*
🏺🏺🏺🏺
*Story*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
*Littattafan marubuciya*
Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.
And now *GELLE ƁINGEL*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
*😆😆😆😆😆 Sai TAMBAYATA akeyi menene ma'anar sunan BOOK ɗin nan wasu suce da wani yare ne wasu kuma suce sunan ya musu tsauri sun kasa faɗa akwai wacce tace min sunan kamar da indian ci😆😆 to bari na faɗa muku ma'anar book ɗin, da farko dai da harshen fullanci na bada sunan BOOK ɗin GELLE ƁINGEL da Hausa yana nufin (GARIN SU YARINYAR) ga dai shi na fassara muku, sai ku barni nasha iska*
*WAƊANDA SUKA BIYA KUƊIN SU ZASU GA NAYI ADDING ƊINSU A PAYMENT GROUP BAZAN IYA BINKU ƊAYA BAYAN ƊAYA NA GAYA MUKU BA, ZAKU GANKU CIKIN PAYMENT GROUP*
➰➰ *5 to 6*
7:25pm
A hankali take sauƙowa daga step ɗin cikin taƙama da iko, fuskarta sam babu annuri cike da gadara ta sauƙo daining table ta nufa tare da zama ta jawo ɗaya daga cikin plast ɗin dake jere a daining ɗin da alamu dener zasu yi, bata juma da zama ba, Aunty Zarah ta sauƙo itama ta zauna, can sai ga Sadiya ƙanwar Aunty Zarah, shi kuwa gogan, shine yayi ƙarshen zuwa, Momy plast ɗin ta buɗe, yamutsa fuska tayi tana kallon abincin dake cikin plast ɗin, Indomie ce tasha kayan haɗi, Momy cike da iko ta turawa Aunty Zarah plast ɗin tare da cewa.
" Meye wannan kika dafa, Indomie kike nufin zamuci da daren nan, baki da hankali ne Zarah, kullum sai na gargaɗeki akan dafa mana taliya da daddare, amma kunnen ki baya ji, yanzu kina nufin daddyn ku shima wannan abun zaici idan ya dawo Saboda baki da hankali, mtsss!!! Ki tashi kije ki ɗaura tuwo da miya yanzun nan, tunda ke kince bakya jin magana"
Momy ta ƙarisa Maganar tana tashi daga daining ɗin alamun bazata ci Indomie ba, Aunty Zarah kamar zatayi kuka ta kalli agogon hannunta, 7:30