Showing 3001 words to 6000 words out of 93605 words
Chapter 2 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
pm, yaushe zatayi tuwo har tayi miya, cikin raurau da murya tace.
" Momy tuwo kuma yanzu, bakwai da rabi fa, har yaushe zanyi tuwo nayi miya, dan Allah kiyi hkr Momy insha Allah zan kiyaye gaba bazan........"
Hanu Momy ta ɗaga mata tare da cewa.
" Bana son dogon turanci umarni na baki idan kuma baza kiyi ba fine."
Tana gama faɗin haka ta haura sama numfashi Garkuwa ya sauƙe tare da bin Momy da kallo harta haura, kallon sa ya mayar kan Aunty Zarah tare da cewa.
" Matar yaya, laifin kine, tunda kinsan bata son taliya ita a rayuwar ta, da sai ki kiyaye, idan ke kina son taliyar sai kiyi sannan ita kuma ki mata abinda take so, kiyi hkr kije ki ɗaura tuwon, Sadiya kije ki tayata kuyi bibbiyu."
Aunty Zarah tamkar zatayi kuka ta miƙe ita dai tana mungun takura a cikin gidan nan, uwar mijinta ta sata a gaba bata da kataɓus sai faɗa da iko, duk aikin gidan an jirge mata shi a kanta ita kaɗai ta hana a kawo mai aiki, bata da ikon ta dafa abinda take so a gidan mijinta sai abinda Momy ke so wannan wacce irin rayuwa ce, kitchen ɗin ta nufa ba tare da ta cewa Garkuwa komai ba, Sadiya tashi tayi zata bita Garkuwa ya saka hanunsa ya kamo hanun Sadiya tsayawa tayi ta zuba masa idanu cike da ƙauna tamkar zata haɗiye sa, murmushin yaudara ya sakar mata a hankali tamkar mai raɗa yace mata.
" 12:00pm ina jiranki kisan duk yanda zakiyi ki zo ki sameni zan barmiki ƙofa a buɗe, kinsan dai 2days nayi missing ɗinki."
Cike da shagwaɓa Sadiya tace.
" Babu wani missing ɗina da kayi da kayi missing ɗina, da kazo inda nake, amma tunda nabar gidan nan baka nemi inda nake ba, ko a waya ne idan ba na maka plashing ba bazaka kirani ba, a hakanne zakace kayi missing ɗina."
Murmushi ya saki yana murza tafin hannunta, tare da cewa.
" Oh my sweet girl, kin dai san ina sonki koh, rashin isasshen time yasa ban cika kiranki ba, amma kullum kina maƙale a ƙirjina, yanzu dai kije ki taya Aunty Zarah aikin sai na ganki."
Ya ƙarisa Maganar yana sake mata hannunta tare da kanne mata ido, murmushi Sadiya tayi tare da cewa.
" Okay baka da damuwa sweetie na insha zaka ganni."
Tayi Maganar tana shigewa cikin kitchen murmushi Garkuwa yayi tare da buɗe plast ɗin ya ɗebi Indomie ɗin a plet tare da tsiyayan fresh milk, a hankali yake cikin abincin cike da nutsuwa, harya gama, bedroom ɗin Momy ya shiga tana zaune bakin bed dinta tana duba littafin Azzakar ya zauna a gefenta.
" Garko ya kabar su Mamman.?"
" Duk lafiya na barsu, Momy wai meyasa Mamma bazata iya rabuwa da shan sigari bane, wallahi Momy bana jin daɗin ɗabiar Mamma ko kaɗan."
Numfashi Momy taja tare da ajiye littafin a gefe ta maida hankalinta ga garkuwa a hankali ta fara cewa.
" Garko Mamma mawiyacin abune ta daina shan sigari, da zata daina da tuni ta daina tun sanda Malam kakan ku yake raye malamin islamiyya ne,. Babba duk wani nasiha da wa'azi daya kamata a yiwa Mamma domin ta rabu da sigari yayi amma taƙi ɗauka harya mutu cikin wa'azi yake mata, bayan mutuwarsa mahaifinku ya ɗaura daga inda Malam ya tsaya amma Mamma taƙi ji, akwai aminiyarta INNO itace take ƙara kangarar da ita, domin kuwa INNO gagararriyar tsohuwa ce mai taurin kan masifa, duk wani wa'azi da zaka yiwa Mamma sai INNO ta koresa, domin kuwa dalilin INNO Mamma taƙi dawowa cikin gari, muddun ba INNO bace ta daina shan sigari ba, Mamma bazata daina shan sigari ba."
" Hmmm!!! Lallai kuwa naga alama domin kuwa ko yau dana bata kuɗi cewa tayi sai ta tsakurawa INNO wani abu a ciki tasha sigari, yama kamata fa mu tambayoyi malamai game da bawa Mamma kuɗi kinga dai sigari take sha dashi, kar muje ta dinga ɗiban zunubi da kuɗin mu tana yaɓa mana, amma dai wannan INNOn Allah ya kasheta mu huta."
Murmushi Momy tayi tare da cewa.
" A'a karka kuma kira mata mutuwa ka mata fatan Allah ya shiryesu duka, ya kamata kaje kayi wannan tambayar domin kuwa nima yana cimin tuwo a ƙwarya."
" Shikenan Momy insha Allah zanje, kunyi waya da Khalil kuwa."
" Eh ya kiran da safe yace ya nemi layinka baya tafiya."
" Network ɗin Tulde gaskiya ba kyau ba lallai bane ya sameni, amma zan kirasa anjuma."
Da to Momy ta amsa kafin Garkuwa ya tashi ya fice daga bedroom ɗin yayi nasa.
Aunty Zarah cikin awa biyu ta gama girkin 9:00pm dai-dai, dake Sadiya ta tayata da miya, a daining ɗin suka jera sannan Zarah taje ta sanar da Momy ta gama da to Momy ta amsa sannan Aunty Zarah ta shige nata bedroom ɗin tsabar takaici da haushi da take ji yasa bazata iya cin abincin ba, haka ta kwanta da yunwa.
Da misalin tara da rabi dai-dai Daddy ya shigo cikin gidan a gajiye sannu da zuwa Momy ta masa sannan ta kai masa ruwan wanka sai da yayi wanka sannan ya sauƙo falo, a tsakiyar falo aka shimfida masa darduma kasancewar baya cin abinci a daining, abinci Momy ta ɗauka ta kawo darduman ta ajiye, malmalar tuwo biyu ta saka masa da miyar ɗanyar kuɓewa, kasancewar Daddy mutum mai son tuwo ko dan ya tashi a ƙauye ne, cike da nutsuwa Daddy yake cin abincin Momy na gefen sa harya gama ruwa yasha sannan ya wanke hanunsa, idanunsa ya dago ya kalli Momy tare da cewa.
" Zainab Garko ya dawo kuwa."
" Eh ya dawo tun ɗazu yana bedroom ɗinsa."
" Jeki kira min shi.?"
Da to Momy ta amsa tare da tashi ta haura tare suka dawo da Garkuwa kusa da Daddy ya zauna tare da cewa.
" Sannu da dawowa Daddy"
"Yauwa sannu Garko ya ka samu Mamman tana lafiya dai ko.?"
" Tana lafiya Daddy sai dai hali ne har yanzu bata fasa ba, ya kamata ka dawo da Mamma gidan nan idan akayi dace sai ta daina shan wannan sigarin."
Girgiza kansa Daddy yayi tare da cewa.
" Mamma bazata yadda ta dawo ba, ni na sani ka rabu da ita kawai mu cigaba ba da mata addu'a idan da rabon zata gyara ko a ina take zata gyara, gobe da safe ka tuna min zan aikeka kasuwa bakin Cross zakaje min shagon Alhaji yawale akwai saƙon da zaka amso min."
" To shikenan Daddy Allah ya kaimu."
Da ameen Daddy ya amsa yana miƙewa tsaye yace.
" Bari naje na kwanta na gaji sosai."
Kansa Garkuwa ya ɗaga sannan Daddy da Momy suka haura.
Ko da misalin 12 na dare Sadiya bata tsallake umarnin Garkuwa ba, sanda ta tabbatar ƙafa ta ɗauke babu kowa ta faɗa bedroom ɗinsa, itace bata fito ba sai wajen 2 na dare, bedroom ɗin da take sauƙa idan tazo ta faɗa, tare da shigewa tolet, wankan tsarki tayi, sannan ta dawo bed dinta ta kwanta sai kuma ta fashe da kuka mai cin rai, a hankali cikin shashsheƙar kukan take cewa.
" Meyasa na kasance mai saɓon Allah meyasa bana iya kaucewa umarninsa, na kasan cikin mutanen da Ubangiji yake fushi dasu, ina ji ina gani na maida kaina karuwa innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Meyasa na kamu da matsananciyar soyayyar Garkuwa, duk halin dana shiga sonka shine ya jamin, meyasa meyasa dole sai kayi zina dani, innalillahi!!!"
Ta ƙarisa Maganar tana kuma sakin kuka, sosai take kukan idanunta suka bushe, har sai da aka yi sallar asuba sannan ta samu bacci ya dauketa, ko da gari ya waye da jikinta a sanyaye ta fito falon, Daddy ta fara gaishewa cike da sakin fuska ya amsa yana ce mata.
" Halima kinzo mana hutu kenan, ya gidan naku, kika baro su.?"
" Duk suna lafiya Daddy, suna gaishe ku"
Momy ce tace.
" Sadiya meya sameki idanunki suka kumbura, kuka kikayi ne."
Ras zuciyarta ya buga, ɗan murmushi tayi tace.
" Ciwo idanun suka kwana suna min shiyasa suka kumbura"
Ta ƙarisa Maganar tana kallon gefe da gefe ko Garkuwa yana wajen wayam babu shi a wajen, numfashi ta sauƙe tare da zama aka cigaba da breakfast da ita, itama Aunty Zarah yau bata zauna anyi da ita ba da alamu fushin jiya ne bata huce ba.
Bayan sun gama breakfast ɗin ne Sadiya ta haura bedroom ɗin Aunty Zarah tana zaune tayi shiru kusa da ita Sadiya ta zauna tare da cewa.
" Good morning Aunty"
'' morning Sadiya, Sadiya, jiya ƙarfe biyu na dare nagan ki bakin bedroom dinki zaki shiga, ina kika fita kikaje"
Zuciyar Sadiya ne ya tsinke cike da tsoro muryar ta na rawa tace.
" Ina kuma naje Aunty, daga ina kika ga na fito."?
Tsurawa Sadiya ido Aunty Zarah tayi tare da cewa.
" Banga inda kika fito ba, amma dai na ganki sanda kike ƙoƙarin shiga bedroom dinki, ina kikaje."
Numfashi Sadiya ta sauƙe cikin zuciyarta tana godewa Allah da Aunty Zarah bata ga fitowar ta da bedroom ɗin Garkuwa ba, cike da waskewa tace.
" Kitchen naje na dan ɗibi abinci naci yunwa ce ta tashe ni."
" Okay,am dan Allah Sadiya kije ki gyara min falo da bedroom ɗin Momy kafin tazo ta fara min mita."
Dariya Sadiya tayi tana miƙewa tace.
" Kai Aunty Momyn ce mai mitar."
" Eh mana!! Ayi mata kullum cikin takura mutum ita jikinta bazai taɓu ba, sai jikin wani, Allah dai ya dawo da khalil lafiya, dole ne fitar dani daga wannan gidan na gaji wallahi."
Dariya kawai Sadiya tayi tare da ficewa taje ta hau aikin da Aunty Zarah ta sakata.
*TULDEN FULANI*
"INNO da Mamma zaune a cikin gidan Mamma gefen su Jummo ce, dukkan su hanunsu riƙe da sigari sai busawa suke, tagumi Jummo tayi tana kallon su, yanda suke busa sigari suna tauna goro, kamar ba Fulani ba, Jummo kasa shuru tayi tace musu.
" Ikon Allah, duk wanda Allah ya shiryar shine shiryayye, umhm!!! Wasu dai wallahi su jira mutuwar su, muddun suka yadda suka mutu a haka babu abinda zai hana Allah babbaka mutum, ku zauna kuna haƙar sigari kuna tauna goro tamkar ƴan bariki, ya Allah kasa INNO da Mamma su................."
Saurin yunƙura Mamma tayi tana bige bakin Jummo tace.
" Kiinci kutumar ubanki, kaji min shegiyar yarinya dan ubanki sai kizo ki fara kona mu, Kafin Allah ya kona mu, shegiya mai bakin tsiya baki iya gani kiyi shuru, a hakan zan baki jikan nawa ki aura shegiya mai kai kamar ƙoƙiya."
INNO ce tayi carap ta karɓa.
" Barni da ita shegiya mai shegen baki, ke dai Jummo kin shiga Uku da bakinki bazai gani yayi shuru ba, to shan sigari yanzu muka ɗaura ɗamara sai muga shegen da ya isa ya hanamu a CIKIN garin nan, ko a ɗakin uwarki muke Shane, kaji min jaraba da nacin tsiya kekam Jummo da mayya ce wallahi sai kin cinye mutum ko kashin shi bazaki bari ba."
Turo baki gaba Jummo tayi cike da jin haushi tayi tsalle ta dire tace.
" Sai kuta zagina kuta zagina saboda kawai na faɗa muku gaskiya, kuma wallahi ko zaku kasheni bazan fasa faɗa ba, idan yaso ku tsire Ni, kuji Mamman nan dai har wani cewa kike (a haka zan baki jikan nawa ki shegiya mai kai kamar ƙoƙiya) tayi Maganar tana kwaikwayon Mamman ta ɗaura da cewa, da wani magulallen bakin ki, a wajen da ba hakwaran kirki, yo nida ke ɗin waye mai kai kamar koƙiyar, ai gara kaina ma da naki, ke naki kuma ai sai dai ace kamar ƙwallon goruba, ko kina so bakya so, ko zaki mutu karshen baƙin ciki sai na auri yaya garkuwa, ke kuma INNO na juyo kanki, mai ƙunnen ƙashi, idan aka barni dake ɗin me kika iya dani, dan Allah idan kuna so randa kuka mutu ma, a kunna muku sigarin a asa muku a bakinku ku je kabarin ku dashi ni ina ruwana waye Allah zai babbaka walakiri ya jibgi banza, ni ina nan duniya ina gaɗa da nanaye mun rage iri.........................."
*Karku manta da wannan littafin na kuɗi ne ku HANZARTA ku biya domin kuwa kuɗin babu tsada*
*Ga masu TRANSFER to account number na zasu turo 150 kacal ta wannan account ɗin 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank*
*Ga masu turo katin waya kuma zasu turo mtn card na 200 saboda idan an sai dashi yana rage farashi ta wannan numbern 08147537180*
*Da zaran kin tura sai ki yi screen short ki turo shaidar biya ta wannan numbern 08147537180*
Vote
Like
Share and comments
*Alƙalamin Rasheedat Usman*
*Ummu Nasmah✍🏻*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺
*GELLE ƁINGEL*
🏺🏺🏺🏺
*Story*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
*Littattafan marubuciya*
Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.
And now *GELLE ƁINGEL*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata ƙawar sirri ƙawar amana *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
https://chat.whatsapp.com/E72lrz6syKr4CNvD9usiuA
*Ga waɗanda suka min magana kan cewa wancan group ɗin ya cika sunyi joining yaƙi to ga wani amma fa ki sani iya Free page kawai zaki samu a ciki idan kina da ra'ayi biya kudinki kawai ki wuce wajen*
*Dan Allah kar namiji ya shiga mata ne zallah, dan Allah karku shiga wannan gidan*
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
Free page.
➰➰ *3 to 4*
" Haba Mamma wai yaushe zaki gane Annabi ya faku ne wannan ba mutuncin ki bane wallahi shan sigari, da mutuncin ki, wallahi wannan da'a cikin gari ne da sai kin jawo mana abun gori, ya kamata kinsan kin girma, kusan 86 kike da shekaru yanzu amma ace har yanzu baki daina saɓon Allah ba, haba ya kamata ki daina shan wannan sigarin haka ki duba kiga yanda bakinki yayi baƙi tafin hannunki taɓin ƙafarki kaf ya rine ya koma baƙi saboda shan sigari shiyasa Khalil baya zuwa wajenki saboda ya tsani yazo ya ganki a wannan halin, wallahi idan kika mutu a haka wuta zaki shiga gara tun w......."
Dakatar da Garkuwa Mamma tayi itama tana sauya fuska tace.
" Dalla rufe min baki dan ubanka, shan sigari ne saɓon Allah, to ai mutuncin nawa ya juma da zubewa idan shan sigari shine rashin mutunci tunda tun kafin na haifi ubanka nake sha banga kuma shegen da zai hanani shanta ba, idan na shiga wutar ina ruwanka kabarin mu ɗaya ne da kai da zaka damu, dan ubansa shi kalilun Allah yasa kar yazo har abada ina ruwana dashi, ni mantawa ma nake dashi jikana ne a duniya, dan haka ka kiyaye i ko ubanka Buba bai isa ya hanani shan sigari ba, ni da sigari mutu ka raba takalmin kaza, dalla!!! Bani ashanata ai ba ubanka bane ya sai min ita, gacar wanda zakaje ka yiwa faɗa wacce bata da mutunci bata ƙaunar dangin mijinta bata ƙaunar wani ya raɓesa yaji sanyi Uwar ka, Zainabu nake faɗa ita zaka je ka yiwa wannan wa'azin ba niba da na gama da iyayen mijina lafiya."
Ta ƙarisa Maganar tana wafce ashanar ta daga hanunsa ta kunna sigarin tana zuƙa, tare da wulla masa harara, sosai garkuwa yaji zafin maganganun Mamma akan mahaifiyarsa ya rasa menene tsakanin ta da Momy, basa shiri, haɗiye ɓacin ransa yayi tare da miƙewa tsaye yana kwalawa A'illo kira, A'illo dake cikin bukkar Mamma taji kiran Yaya Garkuwa ai kuwa da gudu ta fito tana.
" Oyoyo Bandirawo!! Yaushe kazo ɗazu nake cewa, Ya Jalo yaushe zaka zo yace min bai sani ba sannu da zuwa."
Murmushi Garkuwa yayi tare da cewa.
" Yanzu shigowata Ai ina Jalon yake zai shigowa da Mamma kaya a cikin mota ni zan koma ne yanzu."
Ɗan murmushi tayi, harga Allah bataji daɗin tafiyar da Garkuwa zaiyi ba da wuri haka, kallon sa yana kwantar mata da hankali, duk da tasan ya garkuwa yafi ƙarfin ta, amma zuciyarta na mungun ƙaunarsa, cewa tayi.
" Ya Jalo yanzu ya fice kasuwa, amma dai banji daɗin tafiyar da zakayi ba, yanzu fa kazo meyasa bazaka kwana ba."
Mamma ce tayi carap tace.
" Saboda naci ubansa na faɗa masa gaskiya, shi kuma ga ɗan masu ido da kwalli wanda ba'a masa faɗa idan kaga dama ka dawo tsuntsu sai ka bar garin da wuri, kai ga isasshe malakakke baza'a faɗi lefin uwarka ba, to ka buɗe waɗannan fala falan kunnuwan naka masu kama da ƙosai kaji, Uwarka bata kirki bata da mutunci ubanka kuma ya zama hotiho, idan kaje ka faɗawa gagararriyar Uwar taka cewa nice na faɗa har kana wani haɗa min rai dama ya fuskar taka take kullum a haɗe tamkar hadari, kaga fice min daga gida ka koma inda ka fito."
Dariya ce ta ƙwacewa Garkuwa har haƙwaransa suka bayyana dimple ɗinsa ya loɓa yace.
" Dan Allah dubeki ko kunya bakya ji, kinsa surikar ki a gaba tamkar zaki kasheta itako bata ma san kinayi ba, waima ke da kinyi zaton wannan ɓaɓatun da kike shi zaisa na tafi, to bashi bane dama can banzo da niyar kwana ba, a yau zan juya, kuma wallahi bazan fasa faɗa miki shan sigari haramun bane kuma zai kaiki ga wuta idan baki daina ba aljanna sai dai kiga muna shiga, kin wani tsareni da mitsimitsin idanunki tamkar ƙwarƙwata wai ke ga masifaffiyar tsohuwa, ki gyara ko ki shiga Uku."
Ya ƙarisa Maganar yana zaro dubu talatin a cikin aljihunsa ya ajiye mata yana cewa.
" Da alamu talauci ke