Showing 6001 words to 9000 words out of 93605 words

Chapter 3 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

saki faɗa yau ga wannan na taimaka miki badan halinki ba, kuma idan kika sha sigari da kuɗina ban yafe ba."

A'illo dariya tasa ganin dramar Mamma da Ya Garkuwa dama sun saba da wannan faɗan duk sanda yazo sai sun rikito suke dawowa dai-dai Mamma haɗe girar sama data ƙasa tayi tana ƙarewa kuɗin kallon wulaƙanci tace.

" Ka faɗawa ubanka Buba, domin kuwa har idanuna sunso sufi na ubanka girma , ubanka Buba shine mai ido kamar ƙwarƙwata kuma dan uwarka zainabu, da wannan kuɗin naka zan sayi sigari harsu ƙare, kai har aminiyata INNO sai na tsakura mata wannan kuɗin itama ta zuƙi koda kwali goma ne da kuɗin idan ma zunubin ne kaima sai ka samu naka tunda ka bamu gudumowa."

" Hmmm!!! Wannan tsohuwa INNO wannan INNOn ina mungun jin haushin ta, duk harda ita a cikin wanda suke daɗa kaiki ga hallaka, Allah dai ya shirya ku, amma dai mun haɗu da jarabawa tunda Allah ya haɗamu daku."

Fesar da hayaƙin sigarin Mamma tayi tace.

" Oho dai munfi ƙarfin ku, waima ya maganar Auren naka da Jummo, dan dai wallahi sai ka Aure ta."

Tsuka garkuwa yaja yare da haɗe rai yace.

" Har kina wallahi Saboda kece ubana, to idan kin isa kimin Auren dole, amma Allah ya isa tsakanina dake Mamma wannan jakar yarinyar kike dangantani da ita dan kawai ina wajenki mtsss."

yayi tsuka yana kallon A'illo yace.

"A'i muje ki shigo da wasu kayan idan naga yara a waje sai su tayaki ko."

Yayi Maganar yana ficewa ba tare da ya yiwa Mamma sallama ba, ya tsani koda sunan yarinyar a kira masa, ba ƙaunar ta ko kaɗan, A'illo bayan sa tabi tana murmushi, Mamma kuwa mita ta hau tana cewa.

" Kaji ɗan ƙwal Uba to dan ubanka idan ban haifeka ba, ai na haifi ubanka koma wallahi tunda kace sai na nuna maka na isa, baka da wata mata sai Jummo kaji min yaro dai mai baƙin halin tsiya, kai kullum cikin hali mtsss!!!"

Ta ƙarisa mitar tana fesar da hayaƙin sigarin, shi kuwa Garkuwa fitarsa ya samu yara a waje ya basa 5k suka shigo wa da Mamma kayan abinci, dubu goma ya bawa A'illo sannan yaja motar sa ya tafi ba tare daya haɗu da Jummo ba.

" Wayyo Allah na shiga Uku!!!! Wayyo na shiga Uku na lalace, wayyo Allah na!!!"

Jummo ce ta shigo gidan su da wannan ihun ta zauna a ƙasa sai rafkar kukan take, Sikayel da gudu ta fito tare da ƴar Jummo Boɗɗo a tsorace, INNO kuwa tana can banɗaki tana gudawa tunda Jummo ta mata zance mutuwa da rayuwar kabari take sintirin jawo, da sauri INNO ta fito daga bayin ko butar bata ɗauka ba, tana cewa.

" Wani shege tsinannan ne ya saki kuka, wani shegen ne?"

Tayi Maganar tana karisowa wajen Sikayel jikinta na ɓari take cewa.

" Menene ya sameki Jummo, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Kiyi magana mana Jummo keda waye."?

Ƙin yin magana tayi sai da taga INNO ta iso wajen ta fara cewa.

" Bazai aureni ba INNO yace baya sona, jikan Mamma na binni, wallahi shi nake so ɗan gaye ne, kuma kyakkyawa, ni dai na shiga Uku mutuwa zanyi INNO zan mutu idan bazai aureni ba."

Wani ƙuwƙuw cikin INNO ya yi jin Jummo na kiran zata mutu, cikin rawar jiki tace.

" Ke dalla ki daina kirawo wannan mutuwar bazaki mutu ba, ehe, badai Garko bane to kwantar da hankalin ki, kamar kin aure shi, ai dai jikin Aminiya Mamma ne, karki damu zamu kitsa mu haɗa, karkaɗe jikin ki ki tashi kije ki sayo min sigari."

Wage yalon hakwaranta Jummo tayi tace.

" Da gaske zai Aure ni INNO ni dai wallahi shi nake so."

" Kwarai kuwa zai aureki."

Dariya Jummo tasa cike da murna ta miƙe tsaye tana cewa.

" Bani kuɗin sigarin na sayo miki, Allah ya barni dake INNO ta, ki daɗe kiyi ƙargo kiyi shekaru irin na dabino."

Sikayel cike da takaici da haushi tace.

" Amma Jummo baki da mutunci baki da kirki wallahi, yanzu tsabar ɗaukar alhaki akan wannan shirmen zaki shigo da ihu tamkar an kasheki ki tsinka mana zuciya, kekam wacce irin mutum ne Jummo wawiya marar lissafi."

INNO ce ta hau kan Sikayel da faɗa tana cewa.

" Kul kul ɗinki!!! Kiyayeni wallahi, karki kuskura ki ɓata mata rai ina ruwanki wani gulman ne yace ki fito, tayi ihun ai dai akan rayuwarta take ihun yau naji tsiya a daki mutum ace za'a hanasa kuka to baki isa ba wallahi baki isa kisa min jika a gaba ba."

Shuru Sikayel tayi idanunta suka ciko da hawaye tana mungun jin zafin Rayuwar da INNO take ɗaura Jummo akai, domin kuwa ita macece gidan wani zata idan har ta tafi a haka tabbas akwai matsala, juyawa tayi cike da ɗacin rai suka koma bukkar su, Jummo kuwa cuno baki tayi, INNO kuɗi ta ciro naira hamsin ta danƙawa Jummo tace.

" Rabu dasu jeki sayo min sigari ƴar kwali yanzu ki dawo muje gidan Mamman."

Ai kuwa da gudu Jummo ta fita sayowa INNO sigari.





*GOMBE LOCAL GOVT*


*NEW G R A*


wani makeken get Garkuwa ke dannawa Hom hom!!! Gaban gidan kansa abin kallo ne bare kuma idan an shiga ciki mai gadi ne ya wangale get ɗin danna hancin motar Garkuwa yayi cikin gidan wohoho kuzo kuga kyawu cikin gidan, kana kallon gidan zaka tabbatar da gidan attajirin mai kuɗi ne, parking space yayi parking a hankali ya fito daga cikin motar, ya nufi part ɗin mahaifiyar tasa, babban falo ne mai cike da kayan alatu wanda aka ƙawata sa da adon Black and White, sosai falon yayi kyau babu kowa cikin folon shuru, kansa ya ɗaga ya zubawa babban elagement ɗin dake manna a falon kallo, wani dattijo ne fari kyakkyawa gefen sa wata dattijiwar mace ce caculate color ita ba fara ba ita ba baƙa ba, sai a hanun damanta hoton wani kyakkyawan saurayi da kakin soja a jikinsa fari sol gefen Wannan dattijon kuma garkuwa ne, sai wata ƙaramar yarinya Black beauty a tsakiyarsu, a ƙasan hoton anyi rubutu da manyan harufa *ALHAJI ABUBAKAR BUBA TULDE FAMILY* murmushi Garkuwa yayi yana ƙarewa ahalin nasa, muryar Zarah yaji tana cewa.

" Bandirawo!! Yaushe ka tafi harka dawo"?

Murmushi Garkuwa yayi tare da komawa ɗaya daga cikin kujerun falon ya zauna yana cewa.

" Daman ai a yau zan dawo matar Babban yaya, ina Momy naji gidan shuru."?

" Momy tana bedroom ɗin ta da alamu ma wanka ta shiga, mutumiyar ka tazo Sadiya tun ɗazu take tambayar ka."

Murmushi Garkuwa ya saki cikin zuciyarsa ya furta, (Yau akwai holewa kenan, hmmm ita a nata tunanin zan aureta ne, daga ranar dana gama da jikinta daga ranar zan shafe babin rayuwarki.)

A zahiri kuma sai ya haɗe fuska gudun kar Aunty Zarah ta fahimci akwai wani abu a tsakanin su, domin kuwa a hankali yake takunsa yamutsa fuskarsa yayi tare da cewa.

" Ayya ta tafi kenan."

" No bata tafi ba, kasan sunyi hutu, anan zatayi nata hutun, nina roki mama tabar min ita muyi hutu a nan."

Da okey garkuwa ya amsa ya tashi ya haura bedroom ɗinsa, ita kuwa Aunty Zarah ko a zuciyarta bata kawo Garkuwa yana lalata da ƙanwarta ba, ɗauka kawai take shakuwace na zaman tare a tsakanin su.................



Wannan kenan muje zuwa mahaukaci ya hau kura yanzu aka fara labarin.



*Karku manta da wannan littafin na kuɗi ne*

*Wanda zaiyi TRANSFER to account number na 150 zai bada 0006064512 Rashida Usman jaiz bank.*


*Ga masu turo katin waya kuma zasu turo da 200 ta wannan numbern 08147537180*


*Sannan ku turo da shaidar biya ta wannan numbern 08147537180*


*Ga ƴan Niger kuma naji ƙorafin ku, karku damu kuma baza'a barku a baya ba, kumin magana ta wannan numbern 08147537180 zan faɗa muku yanda zaku biya kuɗin ku*


*Masoya naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin hanu biyu, dayawa daga cikin ku sun fara biyan kuɗin su, naji daɗi sosai Allah yabar ƙauna*



Vote
Share and comments.



*Alƙalamin Rasheedat Usman*



*Ummu Nasmah✍🏻*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺

*GELLE ƁINGEL*

🏺🏺🏺🏺




*Story*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah)*





*Littattafan marubuciya*

Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.


And now *GELLE ƁINGEL*


*SADAUKARWA*


Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_________________________________*



*Free page*

➰➰ *7 to 8*


Sake baki da hanci su INNO sukayi suna duban Jummo, takalmi Mamma ta ɗauka ta jefa mata tare da cewa.

" Eh lallai wuyanki ya isa yanka Jummo kin isa, to tashi ki bar bukkar nan kafin ki dake mu, tunda kin balaga ƙirjinki ya cika, kin fara zubda jini, dole ai ki zagemu."

"Zagi kuma Mamma, ni wallahi ban zageku ba, Amma kuyi haƙuri idan ranku ya ɓaci, haba dai Mamma ta, haba INNO ta, kune fa gata na, taya zan zageku, bakin nawa ne babu sakata duk sanda gaskiya tazo sai na faɗa, amma dai na tuba bazan sake ba, kinga Mamma ki rufa min asiri ki taimakeni ki taimaki rayuwata, ki zamo jagorata na auri Oda ta, ya Garkuwa na, idan na auri ya Garkuwa, Mamma katan katan zan dinga saya miki sigari, kuma babu shege ɗan iskan da zai raina min ke, kamar ƙwai haka zan dinga lallaɓa ki, ke kuma INNO duk shekara saina kaiki Makka, har Mamma ma sai ta koma duk da ta taɓa zuwa, dariya Jummo tasa tana kallon INNO tace, Cap wayaga INNO a Makka."

Ai kuwa take Mamma ta sauƙa tana wage baki tana dariya tace.

" Allahu Akbar ƴar albarka, kinji yarinyar kirki INNO, Oh kinji fa ƴar kirki, Makka zata dinga kaimu duk shekara, kuma fa wallahi akwai kuɗin da za'a kaimu Makka duk shekara a gidan Buba kuma kuɗin bazasu girgiza ba bare su san an ɗebe su, wannan tsinanniyar matar tasa zainabu ke hanasa min alkairi" sai kuma ta fashe da kuka tana mutstsuka idanunta ta cigaba da cewa " Sai gashi ƴar albarkatun jikata tana son ta auri jikina Garkuwa saboda kawai ta share min hawaye na, ko dan wannan niyyar taki ta alkairi, Jummo sai na tabbatar kin auri Garko kafin na mutu, ai dai da arziki a garin wasu gara a garin ku, a garin kuma a ɗakin ku, nayi miki alƙawari Jummo ko bayan raina sai Garko ya aureki ƴar albarka."

INNO ma fashewa tayi da kuka tana cewa Mamma.

" Ke dai bari Mamma nine da kuka ba ke ba, Allah sarki ƴar albarka, kaf cikin haulata babu wanda ya taɓa maganar zai kaini Makka sai Jummo ƴar albarka, Allah sarki yarinyar kirki, Allah dai ya nuna min wannan Auren, shiyasa nake sonki kaf cikin haulata, idan kin ɓatawa Mutum rai kinsan yanda zaki faranta masa Allah karka kasheni da wuri."

Dariya ce ta ƙwacewa Jummo ganin daga ambaton zata kaisu Makka har sun manta tsiyar da ta shuka musu ita kuwa INNO Uwar rashin so mutuwa, harda roƙon karta mutu da wuri, cikin ranta take cewa (Ko Gombe bazaku bari ba, bare Makka, ina ma zaku ƙara ganina ina Aure ya Garkuwa na, yasin ban sanku ba, ni wannan rugar ma ba sake zuwanta zanyi ba) a fili kuma dariya tayi tana kuma tsarasu tace.

" To kuma idan ban kaiku Makka ba, waye zan kai, kune fa gatana Mamma nifa da zaki dage ayi wannan Auren nan da sati ɗaya, da nai miki alƙawarin sai na kori Wannan zainabun da ta dameki daga gidan duka har abada bazata dawo ba, kuma dai kinsan zan iya"

Zaro idanunta INNO tayi ta cewa Jummo.

" Ke Jummo kanki ɗaya kuwa, surikar taki kike cewa zaki kora, eh lallai baki da hankali."

Mamma ce tace.

" Wannan ma shine hankali yarinya za tayi abun arziki kike ƙoƙarin dakatar da, ita, Jummo daga yau na ɗaura ɗamarar aura miki Garkuwa muddun zaki yayanki yaƙin tumɓuke Zainabu."

Tsalle Jummo tasa tare da furta.

" Za kuwa aga tsiya yasin na rantse da Allah muddun kika aura min ya garkuwa sai na fidda miki da Zainabun."

Ta ƙarisa Maganar tana ficewa da gudu cike da farin ciki, INNO ce ta kalli Mamma tace.

" Kinsan me kike cewa kuwa, kina nunawa yarinya hanyar tsiya ta kori matar da ta, shekara talatin a gidan mijinta, to wai ma ina ruwanki da matar nan ne, tana gidan ta, kina gidan ku, garin ku ma ba ɗaya ba, amma kinbi kin ɗaga hankalinki a kanta."

Murmushi Mamma tayi tana kallon INNO tace.

" Haba kema kinsan abinda Zainabu ta tare min, kuma kin san alƙawari na ɗauka kafin na mutu sai murƙushe Auren Zainabu da ɗana Buba, kuma na samu wannan damar yanzu da nayi shekara talatin ban samu ba, zanyi amfani da soyayyar da Jummo take yiwa Garko na kawo ƙarshen Zainabu kuma nasan Jummo zata iya, kin sani INNO mugayen laifukan da Zainabu da danginta suka min, dole na ɗauki fansa ta hanyar raba Zainabu da farin cikin ta, kin san a rayuwar mace babu abinda za'a mata taji haushi ta shiga cikin damuwa da tashin hankali, irin a raba ta da gidan Auren ta, da yaranta wannan yafi komai ciwo, INNO harta yaranta sai nasa sun tsaneta, ki saka ido kiyi kallo kawai."

Numfashi INNO ta sauƙe tare da cewa.

" Mamma meyasa ke baki da yafiya ne, meyasa bazaki manta abinda ya faru shekara talatin baya ba, nasan ba a kyauta miki ba, kuma an tozarta ki, an nuna miki iko da fin ƙarfi amma dan Allah Mamma ki manta kiyi hkr tunda har anyi shekaru ya wuce haka."

" Hmmm!!! Sai dai idan kene zaki nuna min iko akan jikarki, ki hanata tayani ɗaukar fansa, amma idan ba haka ba, baki da ikon hanani ɗaukar fansa."

" Ko ɗaya bazan nuna miki iko akan Jummo ba, yanda take jika a wajena haka take a wajen ki."

" To ki samin ido kawai."

Numfashi INNO ta sauƙe tare da ɗauko wani zancen daban suka ɗaura a kai.

Almajirai ne cike ƙofar gidan, kowane riƙe da Allo suna ta karatu, Baffa dake zaune a gefe ne ya miƙe ya shiga cikin gidan, Sikayel na zaune tana tankaɗen garin dawa, Baffa ya shigo, zama yayi gefen Sikayel tare da cewa.

" Ina Jummo!!! Yau satin ta ɗaya bata zo ta biye karantun ta ba, ido na zuba mata amma naga alamar bata jin zuru yau idan na riƙe Jummo sai ranta ya ɓaci na fara gajiya da munanan halinta......."

Baffa bai rufe bakinsa ba, almajiransa ya shigo da sallama sunkuyawa yayi tare da cewa.

" Malam Yanzu Lamiɗo yayi aika, wai kaxo fada yanzu yana neman ka."

Cike da mamaki Baffa yace.

" Lamiɗo Kuma to Allah yasa lafiya, Sikayel bari naje kiran lamiɗo."

Da a dawo lafiya Sikayel ta amsa Baffa ya fice darect fadar lamiɗo ya nufa.

A gefe ya zauna yana gaishe da lamiɗo cike da girmamawa gefen sa ya kalla Yako da innar sa ne zaune sai dogari, lamiɗo gyaran murya yaya tare da cewa Baffa.

" Malam Yaya kaji na aika ayi kiranka ko.?"

Ɗaga kansa Baffa yayi alamun eh, lamiɗo ɗaurawa yayi da cewa.

" To ganan Yako shine ya kawo min ƙarar jikarka Jummo" yanda Yako ya faɗawa lamiɗo haka ya mayarwa Baffa yanda akayi, shuru Baffa yayi babu musu duk abinda akace Jummo tayi zata aikata duban yako Baffa yayi tare da cewa.

" Dan Allah Yako kuyi haƙuri na sani Jummo zata aikata fiye da abinda ka faɗa ina mai baka hkr insha Allah kuma zan mata faɗa bazata kuma ba, Inna kiyi hkr kiyi hkr."

Darajar Baffa yasa innar Yako jin jikinta yayi sanyi, cike da girmama Baffa innar Yako tasa Yako ya yafe maganar lamiɗo sosai ya yiwa Baffa ƙorafi akan Jummo, shi dai Baffa hkr kawai yake bayarwa cike da ɓacin rai Baffa ya koma gida, cikin dace kuwa ya samu jummo ta dawo ai kuwa cike da faɗa Baffa ya ke yiwa Jummo magana.

" Wato Jummo baki da hankali ko, ke kam sai yaushe zaki nutsu ki zamo cikakkiyar Mutum kullum kina nan tamkar marar hankali, wallahi ki nutsu ki fahimci rayuwa, idan bakiyi hankali da duniya ba, wallahi wata rana sai kinyi kuka da idanunki domin muddun akace baka da nutsuwa da tunani wata rana sai kinyi danasanin halayyar ki, yanzu ki faɗa min kwanan ki nawa rabonki da kizo ki biya karatun ki, yau sati guda, saboda rashin hankali da nutsuwa, kiyi hankali da rayuwa, karatun Alkur'ani shine gatan bawa, wawiya kawai dubeki kin girma har yanzu baki san kin girma ba, kin haɗa hankalinki da tuwo kin cinye, idan banda ke wawiya ce waye yake faɗa da namiji, mema zai haɗaki da Yako, to wallahi daga yau karna kuma jin kinyi faɗa da wani namiji idan kuma naji wallahi sai na bata miki rai shashs."

Tunda Baffa yake wannan faɗar Jummo ta cuno baki sai ƙunƙuni take sanda Baffa yayi shuru sannan Jummo ta hau.

" Haba dai Baffa shikenan dan lamiɗo ya kiraka ya gaya maka ƙarya da gaskiya sai ka yarda, ni dai wallahi wannan lamiɗon na tsanesa munafiki ne ga............"

Bige bakin ta Baffa yayi bata ƙarisa Maganar ba yace.

" Shi lamiɗon ne munafiki, kinga rashin hankalin naki ko, Allah ya shirye ki Jummo Allah ya kimtsa miki bakinki, shige ki bani waje."

Juyawa tayi tana cuna baki ta shige bukkar INNO.



*ABUJA CITY*


Da sauri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login