Showing 69001 words to 72000 words out of 93605 words

Chapter 24 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

mutu a cikin rayuwarsa, bazan taɓa yadda Garkuwa yasan ina raye ba, nasani har gobe ina zuciyarsa, fahimtar ina raye zai tono abubuwa masu yawa ciki harda barazana ga ɗana Abdul, dan haka na kashe Garkuwa a zuciyata bazan taɓa yadda mu haɗu ba."

" Safreena karkiyi haka dama ce yanzu a gareki na Garkuwa yasan kina raye, domin kuwa hakan shine zai fitar dake daga zargin ɗanki ma'ana dai ina nufin Garkuwa ya kamata ki aura domin rufin asirin ɗanki, ya kamata kiyi tunani akan maganata."

Murmushi safreena tayi tare da miƙewa tsaye tace.

" Bana buƙatar tunani akan wannan maganar taki babu ni babu Garkuwa har abada bazamu taɓa haɗuwa dashi ba ki ajiye wannan a ranki Aure tsakanina dashi abinda bazai taɓa yiwa bane."

" Amma Safreena ya kamata ki duba maganata kiyi tunani akan rayuwar ɗanki da kuma hanyar da kuka sameshi hakan zaisa ki fahimci gaskiya nake nuna miki."

" Zee bani da tunani akan Abdul muddun Baba yana raye na tabbata zai zamo gatansa bazai bari yayi kuka ba a rayuwarsa."

Dafe kanta Zee tayi ganin duk yadda taso Safreena ta fahimce ta abun yaci tura, har ga Allah ita tsakaninta da Allah take faɗawa Safreena gaskiya, duk gatan da Baba zai bawa Abdul koda kuwa kullum goyasa zai dinga yi, Wallahi wata rana sai tambayi waye ubansa da Safreena zata gane Garkuwa ya kamata ta aura tun Abdul yana yaro bai san komai ba ya taso a hanunsa hakan zai kauda hankalinsa ga tunanin shiba ɗan sunnah bane amma ta kasa fahimta, hmmm.

Zee taja numfashi tare da miƙewa tsaye tana cewa.

" Kinsan dai bazaki tabbata a rayuwarki babu Aure ba Safreena muddun kuwa Baba yana numfashi, idan mijin yazo me zaki ce masa kina da ɗan da kika haifa ba tare da aure ba, ko zaki ɓoye masa, ki sani koda kin ɓoye masa Baba bazai ɓoye ba domin kuwa anayin Aure ne bisa turbar gaskiya mai ɗaurewa dole ne a sanar dashi abinda ke faruwa domin samun ingantaccen aure mai ɗaurewa, a yayin da shima Abdul zai bincike ki waye mahaifinsa, domin kuwa akwai wannan ranar zata zota muddun baki ɗauki shawarata ba, kiyi tunanin wacce irin amsa zaki bayar a lokacin da aka miki wannan tambayar."?

Tana gama faɗin haka Zee ta fice daga ROOM tabar Safreena tsaye bakinta buɗe cikin nazari duban Abdul dake wasa tayi kyakkyawan yaro son kowa ƙin wanda ya rasa sai dai ƙaddara ta yiwa rayuwarsa mungun tabo shuru tayi tana nazarin maganganun Zee numfashi ta sauƙe ita kaɗai tasan hukuncin da ta yankewa kanta miƙewa tayi itama ta fita tare da ɗaukar Abdul sukayi ROOM ɗin Mama.



Ƙarfe biyu dai-dai na rana suka shiga cikin Tulde robon Daddy da garin tabbas ya juma da kallo yake bin garin abubuwa da yawa sun sauya kasancewar ya juma sosai rabonsa da wajen Ya khalil shine ya musu jagora har gidan su Jummo, a ƙofar gida suka samu Baffa yana cikin almajiransa, har abada Baffa bazai taɓa manta fuskar Garba ba, murmushi Baffa yayi tare da musu sannu tabirmar karamno aka kawo musu suka zauna Baffa da kansa ya shiga ya kawo musu ruwa bayan sunsha ne sukayi musabaha cike da mutunta juna, Baffa ne yayi murmushi tare da cewa.

" Garba kaine tafe garin namu, lallai anyi shekaru rabon da mu ganka, har mun fidda tsammanin zakazo, sannu ya Mamman take da INNO, da kuma iyalan naka, wannan kamar kalilu, ya jikin Mamman da ita Jummo."?

Ɗan murmushi Daddy yayi tare da cewa.

" Gaskiya na juma to ya muka iya abubuwa ne suka riƙemu bamu da isasshen lokaci, kuma kasan komai sai Allah ya nufa, Mamma jiki yayi sauƙi har Jummo, Ina Jauro yana nan kuwa da Garbati abokin faɗa, Baffa amma Jummo ƴar Garbati ne ko."?

Murmushi Baffa yayi tare da furta.

" Hakane komai sai Allah ya nufa amma idan aka saka niyya sai kuma Allah ya dafa, A'a ba ƴar Garbati bane ƴar Jauro ne, Garbati yana nan hayen tsallake shida matar sa da yaransa shi nasa yaran ai duka maza ne su Shida."

" Allah Sarki, Masha Allah, to Baffa so muke zamu koma gida da wuri, Kuma munzo wajenka ne da magana mai mahimmanci."

" Ayya to ina sauraronku."

Nisawa ALHAJI Ahmad yayi tare da sanar da Baffa abinda ke tafe dasu Daddy ya ɗaura da cewa.

" Allah yasa zaka bamu Auren Jummo, domin kuwa abun alfahari ne da farin ciki haɗa zuri'a daku idan akayi duba da tarbiyya da ilimin addini da kuke dashi."

Nisawa Baffa yayi yana hango tarbiyyar gidan su Momy da shi kansa Daddyn da yake shakku akan tasa tarbiyyar domin kuwa yayi watsi da mahaifiyarsa ya bi mace bai kuma wauwaice ta ba sai Itace ta nemesa Wannan ma babbar illace da zata hana a basu Aure a duba ta mahangar hankali, domin ana Auren mutum ma saboda nasabarsa, nasabar gidan su Momy ta tsubbu ce da suka maidashi SANA'AR da zasu ci su sha da ita, suka ɗauke ta ɗabiar jini da suke gada daga wajen iyayensu duk wanda yake zaune cikin ƙauyen Tulde yasan wannan asirin nasu, wanda suke gina kansu da haram, ga kuma fitsara da rashin kunya da suka ɗauke ta ɗabia, da hukuncin sa zai yanke tabbas bazai basu Aure ba, sai dai Idan ya hango Mamma baiwar Allah sai yaji bai cancanta ya bata kunya ba ta guje jininta saboda kuskuren ɗanta, numfashi ya sauƙe tare da cewa.

" Duk da ina da iko akan Jummo amma mahaifinta shine yake da haƙƙin ya bada Auren ƴarsa, da zaku min hkr ku ɗan dakata kaɗan sai na aika ayi kiransa a jeji muji ta bakinsa, amma bazan ɓoye maka ba Garba kaida matarka baku da hali na ƙwarai da za'a ɗauki yarinya a baku, saboda baku kyautawa rayuwarku ba, ka yi watsi da mahaifiyarka wanda a duniya baka da wanda zaka kyautatawa bayan ita ka samu albarka, domin kuwa uwa itace jigon rayuwar ɗa zata iya sadaukar da komai nata na rayuwa domin inganta rayuwar ɗanta ciki kuwa harda bada rayuwarta, a yayin da ko wani ɗa na ƙwarai yake kusantowa kusa da mahaifiyarsa domin samun albarka, kai kuma lokacin kake nisanta kanka da ita taya albarka da zaman lafiya zasu zamo mafakarka bayan ka juyawa wacce zaka samu albarka a wajenta ba, a yanzu kana da damar da zaka gyara kuskuren ka domin kuwa Mamma tana kusa da kai, kana da sauran lokaci har yanzu, ita kuma matarka kowa yasan asalin gidan su a wannan ƙauyen namu ba Mutane na kirki duk da ban sani ba ko ita zainabun Allah ya shiryeta ta gyara halinta."

Gabaki ɗayan su shuru sukayi cike da sanyin jiki suna sauraron Baffa yayin da jikin Daddy YAFI na kowa sanyi, idanunsa ne suka cika da hawaye tabbas ya sani gaskiya Baffa yake faɗa, hanu yasa ya share guntun hawayen yana ɗago kansa ya kalli Baffa tare da cewa.

" Koda baka bamu Auren Jummo ba, bazanji haushin ka ba Baffa, domin kuwa duk wanda ya sanni yasan abinda ka sani a kaina dole zai gujeni da haɗa zuri'a, na sani ban kyautatawa Mamma ba, tabbas nayi kuskure, amma a yanzu na gane kuskurena tun kafin na taho nan harma na nemi yafiyar Mamma kuma ta yafe min, na sani Allah ya na sona da shirya shiyasa yabar min Mamma har yanzu a raye domin na gyara laifuka na gareta, kuma a shirye nake ga hakan, zamu jiraka aje a kiran jauron."

Murmushi mai sauti Baffa yayi tare da furta.

" Masha Allah!!! Haka ake so Idan Mutum yayi laifi ya fahimci yayi kuma ya gyara, Allah ya muku albarka." Baffa yayi Maganar yana yana ƙwalawa Junguɗo kira almajirinsa, tare da basa umarnin yaje ya kirawo masa Jauro su taho dashi tare yanzu, da to Junguɗo Ya amsa tare da tafiya aiken Baffa, Ya khalil sosai hankalinsa ya tashi jin yanda babu mai faɗin alkairin iyayensa a cikin rugar musamman momy, numfashi ya sauƙe yana maida kansa ƙasa, basu wani juma ba kuwa Jauro suka taho tare da Junguɗo, cikin mutunci suka gaisa dasu Daddy, Baffa da kansa ya gabatarwa Jauro abinda Garba ke tafe dashi bayan doguwar tattaunawa a ƙarshe dai Jauro ya bawa Daddy Auren Jummo, harma suka saka rana cewa Auren bazai wuce nan da sati Uku ba, Alh Ahmad da kansa ya bawa Baffa sadakin Jummo Naira dubu hamsin 50k tare da sanar dasu cewa insha Allah a cikin satin da za'a shiga zasu aiko da kayan lefe, cikin mutunci da girmamawa suka rabu yayin da kafin Daddy yabar ƙauyen sai da ya bi ya zaga ƴan uwa, kowa sosai yayi mamakin ganin Daddy sai dai ya masu alkairi marar misaltawa har fadar lamiɗo sai da yaje, sannan suka bar ƙauyen, a cikin lokaci kaɗan labarin Auren Jummo da ɗan gidan Garban Mamma ya zagaye ƙauyen kowa yana mata son barka wasu kuwa suna cece kucen mai zaisa Baffa ya yarda ya haɗa iri da gidan su Zainabu, to dama dai shi Aure ya gaji haka duk sanda ya taso sai kaji ƙorafin kowa da mai faɗan alkairi da kuma mai faɗin sharri koma dai me sai dai muce Allah ya sanya alkairi.

A can kuwa Birni hankalin Momy yafi na kowa tashi jin da gaske Auren ya tabbata, gashi a yanzu bata da ikon yiwa Jummo asiri saboda tsoron INNO, Zizah kuwa sosai tasa Jummo a gaba da cakala da neman fitina, sai dai ina Jummo bata kulata mahaukaciya take maida ta har tayi ta gama Aunty Zarah kuwa murnar Auren taji domin kuwa hankalin Momy zai bar gareta zata daina takura mata ta maida hankalinta ga Jummo, shi kuwa Ya Garkuwa yayi farin ciki sosai sai dai hankalinsa yana tashi a duk sanda ya tuno cewa Momy bata son Wannan Auren sai dai babu yanda ya iya dole zaici gaba da hkr harta huce, ko Kayan Auren da Daddy yayi umarnin a haɗa Momy kin sauraran zancen tayi sai Aunty Zarah Daddy ya bawa kuɗi ta haɗa babu laifi ta saka mata kaya masa kyau zannuwa guda arba'in ta saka banda dogayen riguna da sleeping dress, kayan makeup turaruka masu tsada duk ta saka, akwati shida ta saya, koda ta kawo kayan Momy dai taƙi koda zuwa ta kallesu domin kuwa ji take tamkar makara suka kawo mata na kaita kabari, haka taƙi ta sanar da ƙawayenta da abokan mutunci zuwa makwafta suzo suga kayan, itama Aunty Zarah gudun fitina yasa bata faɗawa kowa ba, ko gidan su domin kuwa tasan muddun ta kira wani yazo yaga Kayan ta shiga Uku Wajen Momy, Wajen Mamma ta kai kayan sosai suka sawa kayan albarka hatta Jummo sai da aka kirata ta gani tare da ƙawarta Meenat shima Daddy ya shigo yaga kayan kuma ƙwarai ya yabawa siyayyar AUNTY Zarah, koda Daddy yaga kayan bai saurari Momy ba ya sanar da Hajiya Rabi matar abokinsa suzo su kai kayan ita da Zarah haka kuwa akayi washe gari da safe suka kama hanyar Tulde suka kai kayan cikin daraja da mutuntawa, wannan kenan.


Yau ta kama ranar asabar babu makaranta Jummo na zaune a harabar gidan cikin fararen kujerun roba tayi shuru, Garkuwa daya shigo da motar sa ne yayi parking ya nufo ta tare da zama a ɗaya daga cikin kujerun yana kallon ta harya zauna bata san ya zauna ba tana tunani, hanunsa ya tafa a fuskarta, da hanzari ta dawo daga duniyar tunanin da ta lula tana sakin ajiyar zuciya ganin Ya Garkuwa a gabanta, idanu ya zuba mata cike da tuhuma yace.

" Zaƙin Zuciyata, tunanin me kike haka.?"

Numfashi Jummo ta saki tare da maida hankalin ta ga Ya Garkuwa zuciyarta sam babu daɗi tace.

" Ina tunanin rayuwa ne My HeartBeat, Duniyar tana bani tsoro idan na dubi abubuwan da suke cikinta, hmmm!!! Momy bata sona bansan mena mata ba ta tsaneni haka, naso ace Momy ta ɗaukeni tamkar yar da ta haifa a cikin ta, ni kuma na mata biyayya kamar yadda zaka mata, sai dai ina hakan sam bai yiwu ba, taƙi ta sawa Auren mu albarka, meyasa Momy bazata amince da Auren mu ba muyi rayuwa cikin farin ciki, gashi jibi zamu koma Tulde da INNO tace lallai acan zaayi bikin."

Shima numfashi Ya Garkuwa ya sauƙe tare da cewa.

" Bani da amsar tambayar ki nima Jummo bansan wani dalili yasa Momy ƙinki ba, sai dai na san insha Allah komai yayi farko zaiyi ƙarshe, da yardar Allah ina ji a jikina wata rana Momy zata sauƙo ta soki tamkar yadda take sona ki daina ɗaga hankalinki akan wannan ke dai ki dage da addu'a Allah ya nuna mana ƙarshen wannan masifar, ga can Invitation card an buga, adress ɗin da aka saka can TULDEN ne tunda Baffa yace anan za'a ɗaura Auren, insha Allah gobe da safe zamuje ki buɗe account zan saka miki kuɗaɗen da zaki buƙata, ina ga yau saura 7 days ko, sai dai fa ni babu wani bidia da zanyi su dener su wani party ni duk bazanyi ba, walima kawai za'ayi kin gane."

Kanta Jummo ta ɗaga alamun eh, sun ɗan juma suna hira har akayi kiran sallah sannan suka tashi a wajen.


Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a juma baaje ba, yau ta kama ranar Alhamis kuma itace ranar da Jummo zata koma Tulde, can harma sun fara hidimar bikin su tun kafin zuwan su Jummo, a yayin da cikin gidan su Ya Garkuwa kuwa babu wani bikin da aka fara domin kuwa babu wanda Momy ta bari yasan ana Aure a cikin gidan, INNO Mamma Jummo sai MeenatSune zasu kama hanyar Tulde, sam Jummo ta manta bata sanar da Safreena Auren nata ba sakamakon abubuwa da suka mata yawa ga kuma Auren sam babu armashi sakamakon rashin sakewar Momy, INNO da kanta ta bawa Jummo umarnin taje tayi sallama da Momy babu musu Jummo ta amsa tare da nufar room ɗin Momy, a rufe yake ta ciki, nocking tayi tare da tsayuwa tana jiran a buɗe ƙofar tafi minti goma tana tsaye kafin Zizah tazo ta buɗe ƙofar turus ta tsaya tana duban Jummo cike da mamakin me kuma ya kawo ta, wani irin kallon banza Zizah ta watsa mata tare da sakin tsaki tace.

" Mtsss!!! Ashema shara ce ke nocking ai ni nayi zaton mutane masu amfani ne suka zo, ashe Kuma jikar mayu ce mtss, marar zuciya."

Tayi Maganar tana taɓe bakinta tare da cigaba da zubawa Jummo mungun kallo, wani irin zafin maganganun Zizah Jummo tayi, sai dai a wannan lokacin tana buƙatar ta sarrafa zuciyarta saboda Ya Garkuwa, numfashi ta sauke tare da kauda kanta gefe tace.

" Naji na gode, Momy nake nema ba keba Zizah kina iya bani waje na shige."

Murmushi Zizah ta saki tare da furta.

" Heeee!!!! Na!wa!wo! Oh kaji wata banzar Magana a wajen wannan Yarinyar, to sai naga dama kiga Momyn, ko bokanki ne ya baki wani ƙullin ki sawa Momy, to kinyi ƙarya domin kuwa Momy tafi ƙarfin tuggunki kinji ballagaza.!"

Runtse idanunta Jummo tayi ranta na mungun ɓace tace.

" Ya isheki haka cin zarafin Zizah, da alamu kin rantse sai nayi faɗa dake, naso ace sanda nake jummon ƙauye ce na tabbata da sai nayi maganinki yanda gaba koda sunana aka kira sai kin tsorota, sai dai kinyi matuƙar Sa'a Jummo ta dawo ta ƙwarai ta barwa karnuka irinku faɗa,da zaki kwana dubu kina nemana da faɗa bazan taɓa biye miki muyi ba domin da alama ke jahilar karatun addini ne, dan Allah a koma makaranta ko za'a samu a zamo na ƙwarai, ni kuwa inama ni ina faɗa da karen Tailan karnukan hauka, ki matsa na shige ko ƙarfina yasa na shige."

Wani irin munduƙun baƙin ciki Zizah taji, Momy dake tsaye ta harɗe hanunta ne a ƙirji tana sauraron duk maganganun su sosai Momy taji zafin abinda Jummo ta yiwa Zizah a matuƙar hasale Momy ta nufar ƙofar idanunta na rufewa tsabar baƙin ciki, wallahi yau babu abinda zai hana bata yiwa Jummo shegen dukan da babu mai gane fuskarta.






*UMMU NASMAH CE*
[5/19, 12:33 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*





➰➰ *60 to 61*



Tas!!! Tas!!! Tas!!! Momy ta ɗauke Jummo da mari har Uku tana nuna mata hanya.

" Get out!!! I say get out!!!!"

Tayi Maganar cikin tsawa mai firgitarwa, cike da tsoro Jummo ta matsa baya tana riƙe fuskarta da tayi ja, shatin yatsun Momy ya bayyana a fuskar, runtse idanunta Jummo tayi tare da juyawa cike da ƙuncin Zuciya, tsuka Momy taja tare da cewa Zizah.

" Meyasa bazaki mata shegen duka ba, ki kwantar min da shegiya a sume, sai ki tsaya kina cacar baki da ita, na tsani wannan Yarinyar ta rusa min duk wani shirina harta tsarin tarbiyya ta cewa take ba dai-dai bane, bana son koda kallon fuskarta ne, abun baƙin ciki wacce na tsana a rayuwata wai itace take shirin zama surukata, tirrr tirrr!! Zan kalli wannan ƙaddara a matsayin baƙar ƙaddara "

Numfashi Zizah ta sauƙe tana zama bakin gadon Momy tare da taɓe bakinta tace.

" Momy ina ni ina saka hanu jikin wannan ƴar ƙauyen wacce taci tuwo ta ƙoshi ƙarfinmu ma ai bazai zo ɗaya ba, wallahi Momy baki kaini tsanarta ba, tunda ta mallake min room na fara jin tsanarta tazo kuma ta saki a gaba, hmmm!!! MOMY babu faɗan hanu tsakanina da ita amma wallahi Momy ko anyi wannan auren nine zan kashe wannan Auren bazan taɓa bari auren nan yayi lasting ba, da makirci da kirsa wallahi sai na kashe mata aure, naci wannan alwashin kuma sai na cika da, ki kwantar da hankalinki Momy zanyi maganinta dani take zancen."

Murmushi Momy tayi tare da cewa.

" Idan har kika min haka tabbas zan tabbatar da cewa ke photocopy ɗina ce, zan kuma yi farin ciki, na baki wuƙa da nama Zizah kiyi duk abinda kikaga ya dace."

" Ai kuwa Momy zaki tabbatar da ni ɗin harma na zartaki, na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login