Showing 21001 words to 24000 words out of 93605 words

Chapter 8 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

ɗan uwansa, uwar ta tsani ɗan shima ɗan ya tsani Uwar, su rabu kawai na huta."

" Wannan fa ƙaramin aiki ne a wajen wannan bokan dan haka karki damu duk abinda kike so zai iya miki muddun zaki sake masa kuɗi."

" Kinsan kuɗi ni ba matsala ta bace, muddun za'a rabani da Mamma wallahi zan kashe ko nawa ne."

" Shikenan ni bari na koma duk yanda kikayi naji kota waya ce."

Da to Momy ta amsa tare da tashi ta rako Asabe har compaunt ɗin gidan sannan ta dawo, cike da masifa take kwalawa Zarah kira, Zarah dake zaune ita da Jummo a bedroom ɗin Mamma ne ta jiyo muryar Momy na kiranta wani irin tsinkewa zuciyarta tayi, da sauri ta miƙe tana amsa kiran ta fito da sauri, da kallo Jummo tabi Zarah yanda taga ta gigice, Mamma kuwa dama baccin ta take sha, a falo ta sami Momyn tsaye, ta risina tace.

" Gani Momy."

" Uban kikeyi a cikin bedroom ɗin Mamma, uban waye zai miki ayyukan cikin gidan nan, naga alamar yanzu kin fara koyon munafurci ko, kega annamimiya uwar iya kissa, Saboda a soki ko, tunda mutanen nan suka dawo cikin gidan nan naga kin nane musu sai shiga jikin su kike, to bari kiji bazan kamu ci munafurci ba, daga yau babu ke babu sake zama a ɗakin Mamma iyakarki da ita ki shiga ki gaisheta ki fito, munafukar Banza, ki shige gacan wanki na sun taru kije ki wanke min, sannan yau tuwo zakiyi mana miyar ganye a cikin gidan nan shasha."

Sunkuyar da kanta ƙasa Zarah tayi duk masifar da Momy take babu wanda Zarah ta mayar mata harta bar wajen, numfashi Zarah ta sauƙe tare da nufar bayan momyn ta ɗauko wankin nata zuwa yanzu wahalar da take sha a gidan na aiki yabi jikinta sai dai cin mutunci da zagin da Momy ke mata shi kaɗai ne yake ci mata zuciyarta, a bayan gidan tayi wankin tas ta shanya su, bisa mamakin kafin ta gama wankin ta fito ta samu, Jummo ta gyara mata falon tas har wanke wanke sai da ta mata, dubanta ta kai da gas dake kunne, wajen ta nufa tare da dafa kafaɗar Jummo, targen semonvita ta samu jummo nayi, numfashi ta sauƙe tare da cewa.

" Jummo duk ke kikayi wannan aikin wa yace miki tuwo zanyi yau."

Murmushi Jummo tayi tana zuba semon ɗin cikin tukunyar tace.

" Aunty ina jin duk masifar da Momy take miki, hmmm!!! Aunty Momy bata da kirki wallahi dani take yiwa zagin da ta miki Allah saina rama, naga alamun Momy ta tsaneki, Aunty me kika mata kin taɓa mata wani laifi ne."

Numfashi zarah ta sauƙe tare da cewa.

" Jummo ban mata laifin komai ba, aikine na makara, kuma kinga dole tamin faɗa a matsayin ta na uwata, kinga mubar zancen nan, tunda kin kusa gama tuwon ni bari na tsinke ganyen."

Shuru Jummo tayi bata kuma cewa komai ba, har suka gama aikin Jummo ganin ta gama nata yasa ta fito falo Garkuwa ta gani zaune ya maida hankalin sa ga tv yana kallon BBC news, zama a kujera Jummo tayi tare da cewa.

" Ya Garkuwa, kai kullum kana gida, baka zuwa aikine sai zaman banza."

Zaro idonsa Garkuwa yayi yana juyo da kansa ya kalleta wani irin bugawa zuciyarsa tayi, take yawunsa ya tsinke, ganin Jummo cikin ƙananan kaya riga da wando wanda ta ɗan kama mata jiki, ga dukiyar fulaninta sun cika rigar tam, shi kansa wandon ya ɗan kamata, gashi tayi fresh tayi kyau, ( wai dama haka take da kyau, hmmm!!! Lallai wannan akwai kayan daɗi a jikinta, Allah ya kai damo ga harawa ko bai ci ba yayi ɓarna) leɓensa ya cije tare da fasa yin masifar da yayi niyyar mata kau da kansa yayi tamkar baiji ta ba, Aunty Zarah dake tsaye bakin kitchen tana jin maganar da Jummo ta faɗawa Garkuwa ya sata yin dariya tace.

" Waya faɗa miki Garkuwa baya aiki, yana aiki a babban Companyn *A,A ASAD INTERNATIONAL AIRPORT* matuƙin jirgin sama ne, hutu ya ɗauka shiyasa kike ganinsa kullum a gida."

Taɓe bakinta Jummo tayi tare da miƙewa tsaye tace.

" Ummm!!!! Aunty wai fa sonsa Nak..................."


" Assalamualaikum."

Sallamar Sadiya cikin gidan shiya hana Jummo ƙarisa Maganar da tayi niyya, da kallon waye wannan Jummo tabi Sadiya, Sadiya ranta a matuƙar haɗe tana jefawa Garkuwa wani irin kallo mai wuyar fassarawa Garkuwa ɗago kansa yayi ya zubawa Sadiya ido tare da kau da kansa gefe, sai kuma ya saki murmushin gefen baki, wanda shi kaɗai yasan me yake nufi miƙewa yayi ya shige bedroom ɗin Mamma, numfashi ta sauke Sadiya tare da ƙarisowa ta zauna tana kallon Aunty Zarah.

" Sadiya lafiyar ki kuwa kika shigo ranki a haɗe, meya sameki."?

" Umhmmm!!! Ba komai Aunty yanayin nature ne, amm Aunty ina ya khalil ashe ya dawo.?"

" Eh ya dawo ya fita, sai anjuma zai dawo, zamu kwana ne ko zaki koma gida yau."

Kanta ta ɗaga ta kalli Jummo tare da cewa.

" Na dawo bani da Ranar tafiya akwati na yana wajen mai gadi yanzu zai shigo min dashi, wacece wannan Aunty."?


" Jummo ƴar uwar su................"

Dakatar da Aunty Zarah tayi ta furta.

" Jummo Jummo Jummo!!! (A zuciyarta tace Oh ko dai itace wacce Garkuwa yake bani labarin ta wacce take sonsa a ƙauyensu, to amma ya akayi har ta waye haka, bura'uba heee lallai banga ta zama ba, domin kuwa wannan nayi wasa wallahi sai ƙwace Garko daga hanuna.) Numfashi ta sauƙe tace.







*Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira 100 kacal zaki biya kuɗin ki ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko hoton mtn card ta wannan numbern 08147537180 sannan ku turo shaidar biya.*





*Ku HANZARTA ku biya Free page yazo ƙarshe Naira ɗari ce ba yawa da zarar Free page ya kare BOOK ɗin ya tashi daga Naira 100 ya koma 300 ku HANZARTA maza kar wannan damar ta shige ku.*



*Sorry for typing error banyi editing ba.*





*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🏺 *GELLE ƁINGEL* 🧺



*(Garinsu yarinyar)*




*Na marubuciyar*


Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Akan ƴar Uwata
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu
Doctor Hassan
Ƙauyemu


And Now *GELLE ƁINGEL*



Sadaukarwa ga ƙawata Zarah Abdul Momyn Ahlan.




*Dan Allah ina roƙon namiji karya shiga group ɗin nan dan Allah*

*Wannan littafin na kuɗine idan kin san ba saya zakiyi ba kema dan Allah karki shiga, haka idan kinsan baza kiyi comments ba nan ma karki shiga Naira 100 ne kaɗai kuɗin littafin ban tsawalla ba in dai kina da niyyar saya, iya Free page kawai zaki samu a cikin gidan nan*



https://chat.whatsapp.com/LTWeFGmoKqTDbMbsU37088




✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨




*FREE PAGE*


➰➰ *17 to 18*



" Dakata dan Allah Sadiya!!! Wannan maganar taki ta fara toshe min kunne ta fara wuce gona da iri, dama akwai alkawarin Aure tsakanina dake ne yanzu koko nace miki zanyi Aure nan kusa, da zaki sawa zuciyarki nutsuwa ki kwantar da hankalinki idan Aure kike buƙata ki nemi wanda yake da niyyar yi kiyi Auren ki zai fiki alkairi, domin kuwa babu Aure a gabana ke ni aure nan da shekara biyar ma albarka, amma idan har na taɓa miki alƙawarin Aure sai ki tuna min, dan haka kiyi hkr kawai Sadiya Allah ya haɗa kowa da rabonsa."

Tamkar sauƙar aradu Sadiya taji Maganar tasa wani gumin azaba ne ya keto mata, take taji ɗakin na juya mata dafe kanta dake sara mata tayi, cikin nauyin baki tace.

" Please Ya Garkuwa ka daina min irin wannan wasan bana so yana tsinka min zuciyata, dan Allah ka daina."

" Wasa kuma Sadiya na taɓa irin wannan wasan dake, ba wasa nake miki ba Sadiya, wallahi babu Maganar soyayya yanzu tsakanina dake Saboda baki dace da ki zamo Uwar ƴaƴana ba Sadiya idan har namiji kike buƙata, ai naga ina ɗauke miki sha'awar ki idan kuɗi kike buƙata ina baki, meye a cikin Auren ina dai shine to wannene bana miki, idan har zaki iya mu'amala dani a haka babu zancen Aure ƙofata a buɗe take, Aure kam nida shi ba yanzu ba."

Runtse idanunta Sadiya tayi hawaye ne mai zafin gaske ya siraro daga idanunta, tabbas namiji ba ɗan goyo da zani ba ne, ta bawa Garkuwa rayuwarta harda mutuncin ta, amma yaci amanar ta koda a cikin mafarki bata taɓa tunanin garkuwa zai juya mata baya ba, ashe burinsa kenan akanta ya ta lalata da ita ƙarshe ya gujeta " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Tabbas soyayyar Ya Garkuwa ta zamo min masifa" hawayen ta goge tare da cewa.

" Dan Allah ya Garkuwa ka rufa min asiri karka juyawa soyayyata baya, kai kaɗai zuciyata take so, bata da wani farin ciki idan ba naka ba ya Garkuwa, wallahi ina sonka, rasa ka gareni tamkar barazana ce ga rayuwata, karka yaudareni ya Garkuwa dan Allah ka Aure ni Wallahi kai kaɗai nake so meye aibuna da bazaka soni ba?."

Shuru Garkuwa yayi yana sauraron ta, sanda ta gama maganar ta cikin sannan Garkuwa ya sauƙe numfashi tare da cewa.

" Duk wani Maganar da zan miki ki fahimta, Sadiya nayi amma naga alamar kina da taurin kan tsiya, bazaki fahimta ba, dan haka ina mai gargaɗinki Sadiya karki kuma kiran wayata, idan kuma zaki kira wayata to ki tabbatar cewa kin amince ne mu cigaba da alaƙar mu kamar da, amma karki kuma min Maganar Aure this is the last warning."

Yana ƙarisa Maganar ya kashe wayar gabaki ɗaya, yana jan tsuka tare da jin haushin Zarah me take nufi da ƙoƙarin rabasa da Sadiya yasan bata san alaƙar saduwa dake tsakanin sa da Sadiya ba, to meye dalilin ta, na cewa Sadiya ta rabu dashi, harga Allah shi da zuciya ɗaya yake zaune da ita, sai gashi tana cin dunduniyar sa, tsuka yaja tare da ɗaga kafaɗarsa yana Kwanciya ya furta.

" Wannan damuwarki ne, dama can ni ba Auren ƴar uwarki zanyi ba, asali ma itace ta liƙemin tamkar cungam domin kuwa babu ta yadda zan yarda na auri mazinaciya,. Uwa ta gari ya dace na samawa yarana ba mace Irin Sadiya ba."

Numfashi ya sauƙe tare da lumshe idanunsa yana kallon slim.


Ita kuwa Aunty Zarah tuni ta manta da Jummo dake jiranta ta Lula rayuwar Auren ta, bacci ne mai nauyin gaske ya ɗauketa a ƙirjin Khalil, itace bata farka ba sai da taji ana kiran sallar magaruba a hankali ta buɗe idanunta akan fuskar khalil dake baccin sa hankali kwance.

" Bismillahil lazi ahayana ba'ada ma amatana wa ilaihinnushur!!! Subahanallah subahanallah subahanallah!!!! Wala hamdulillah Wala hamdulillah Wala hamdulillah!!! Wala ilaha'illallah wallahu akbar."

Wannan shine ya zamewa Aunty Zarah ɗabia a rayuwarta duk sanda ta farka daga bacci sai ta yi wannan addu'ar da ake so ko wanni musulmi ya jimance sa yayin tashi daga bacci, a hankali ta saka yatsanta a kunnen Khalil na sosa masa, domin ya farka, cike kuwa da nutsuwa ya buɗe idon yana kallon ta lumshe su yayi ya kuma sake buɗewa murmushi ya sakar mata tare da furta.

" Oh My dear wani irin bacci haka mukayi ba tsarki a jikin mu, kamar sallah ma naji ana kira ko.?"

" Sallah ake kira ya kamata ka tashi ka HANZARTA kayi wanka Kafin a shiga Masallaci."

Miƙewa tayi daga jikin sa tana jawo bargon ta ƙara rufe jikinta hanunta ta saka ta jawo towel dake jikin gadon ta miƙawa Khalil karɓa yayi ya miƙe tare da ɗorawa a ƙugunsa ya shige tolet, ita kuwa Zarah jingina tayi jikin gadon tana lumshe idanunta, Jummo ce ta faɗo mata a rai, saurin ware idanunta tayi tare da furta.

" Subahanallah!!! Oh My god, tana can sai zaman jirana take."

Sauƙowa tayi daga bed ɗin tare da jawo zani ta ɗaura a ƙirjinta, ta buɗe wadrop ɗin ta ta ɗaukowa Jummo baƙar doguwar riga mai ratsin golden a jiki, hijab ta saka ta fita da sauri bedroom ta shiga, a yashe ta samu jummo a ƙasan tayels sai bacci take murmushi Aunty Zarah tayi tare da furta.

" Allah Sarki ta gaji da jirana har bacci ya ɗauketa" sunkuyawa Aunty Zarah tayi a hankali ta dinga tashin Jummo harta buɗe idanunta.

" Haba Jummo ganan gado me zai kwantar dake a ƙasan tayels wannan sanyin ai sai ya cutar dake, karki kuma Kwanciya a wajen baki ga A'illo tazo ta ajiye kayanta a gadon ba, nan shine ɗakin ku keda ita akwai ƙanwata da take zuwa ita ma a nan take sauƙa, Kiyi na barki kina ta jirana ko, Ya khalil ya sani aiki, yanzu kin san me za'ayi jekiyi alwala tunda kinji ana kiran sallah idan kinyi alwalar sai na miki kwalliyar sai kiyi sallar ki hankalinki kwance."

Ta ƙarisa Maganar tana zama bakin bed ɗin, Jummo da to ta amsa tana shigewa tolet ɗin, alwala ta ɗauro sannan ta fito, Aunty Zarah ta tsara mata kwalliya sosai Jummo tayi kyau bana wasa ba, doguwar rigar ta zauna a jikinta kasancewar Jummo ba dai dukiyar fulani ba, dariya Zarah tayi tare da cewa.

" Wow hajiya Jummo kinga kuwa yanda kikayi kyau anya kuwa bazan yiwa mijina kamu ba, kalli madubi kiga."

Madubin Jummo ta kalla tana dariya tace.

" Aradu nayi kyau Aunty, to Aunty zaki dinga min kwalliyar kullum."

Dariya Aunty Zarah tayi tare jan kumatun Jummo tace.

" Me zai hana, miki kai insha Allah ma tunda kina son kwalliya zan kaiki shagon makeup ki koya yanda zaki dinga yi da kanki ba sai na miki ba, yanzu dai je kiyi Sallah an shiga Masallaci, nima bari naje nayi sai na fito na shiga kitchen ko"

Da to Jummo ta amsa tana dariya ta ɗauki darduma ta hau Sallah, ita kuma Aunty Zarah ta fice nata bedroom ɗin.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Can kuwa masallaci khalil tare sukayi Sallah da Daddy kasancewar ya dawo ana kiran sallah parking kawai yayi ya shiga Masallaci, bayan an idar da Sallah ne khalil ya yiwa Daddy sannu da dawowa, fuskar Daddy cike da murmushi ya amsa yana kallon Garko dake tsaye ya zuba hanu a aljihunsa, murmushi Daddy yayi yace.

" Kai Garko ina sakon dana aikeka wajen Alhaji Isma'il?"

" Daddy naje ban samesa ba, still na dawo kasuwa wajenka Sadiq yace min ka fita."

" Okay mu ƙarisa cikin gidan."

Tare suka shiga cikin gidan da Daddy, da sallama suka shiga falon, muryar Mamma itace ta fara amsawa Daddy, sallama, shi kuwa khalil idanunsa ne suka sauƙa akan Jummo da tayi bala'in kyau tamkar ba wannan ƴar ƙauyen da suka zo da Mamma ba, wani bugawa zuciyarsa tayi, yayi saurin dafe ƙirjinsa tare da runtse idanunsa, shikam Garko baima lura da Jummo sam hankalinsa baizo wajen ba, waya ma yake da abokinsa Hashim, daddy waro ido yayi cike da farin cikin ganin Mamma ya ƙariso gabanta ya zauna a ƙasa gefen kujerar da take zaune.

" Mamma kece yau a gidan nan, sannu da zuwa, sannu da hanya, wa ya kawo ki Mamma."

Fashewa Mamma tayi da kuka tare da kaikaicewa ta fara masifa tana kuka.

" Buba ɗazu Tasiu ya kawoni nace ya dawo dani gidan ka na ƙarisa rayuwata anan nida jikokina, amma tsabar walaƙanci tun daga bakin ma shigar gidan ka ake wulaƙantani ana cemin wai ni mabaraciya ne nazo bara wajenka, Buba har bindiga suka samin zasu kasheni, dana tsallake wannan siraɗin wannan ɗan albarka Garko ya shigo dani, sai na kuma samun wata masifar a cikin gidan nan, ina shigowa wannan shegiyar matar taka tana ganina sai ta haɗa fuska tamkar hadari ranta ya ɓaci tamkar taga masifa, na taƙaice maka da ita da wannan ja'irin ɗan naka mai baƙin hali suka zageni tas, ko abinci Zainabu bata bani ba, shi kuwa kalilu bindiga ya ɗaura min yace na kuskura na faɗa maka sai ya kasheni, tunda nazo matarka da ta haura sama ta barni a yashe a nan har yanzu bata fito ba, bare na samu darajar ta bani ruwa sai wannan ƴar kirkin zara'u itace ta ciyar dani ta shayar dani gata kuma tazo muna hira, dan haka yanzun nan ba sai anjuma ba, Buba tashi ka maidani ƙauye tunda ana neman rayuwata a nan, bazan zauna ba."

Ta ƙarisa Maganar fuskarta shakaf da hawaye harda shashsheƙar kuka, khalil zaro idonsa yayi yana mamakin Mamma yanda ta ƙarawa yanda akayi gishiri, Garkuwa ma zaro idonsa yayi yana sauraron Mamma, duk da yasan halin Mamma zatayi sharrin da yafi wannan ma, idanun suka haɗa da Jummo, wani ras yaji zuciyarsa ta tsinke, "wannan kamar Jummo" ya furta cike da mamaki tare da taɓe baki ya kawar da kansa gefe, Daddy wani irin ɓacin rai yaji idanunsa sukayi jajur, " taya za a ci mutuncin mahaifiyarsa a cikin gidan sa, ina Wallahi bazai yiwu ba, dole yau sai ran kowa ya ɓaci a cikin gidan nan idan ana son zaman lafiya dole ne abi umarnin mahaifiyar sa............."





*Biya Naira 100 ki ƴar uwa ki cigaba da karatu cikin nutsuwa, ki gaggauta biya domin kuwa akwai kwanakin dana ɗebawa wannan BOOK ƊIN da zarar kwanakin ya cika LITTAFIN zai tashi daga 100 ya koma 300 gara ki biya da wuri kafin wannan damar ta wuce ki biya ta wannan hanyar👇🏻*


*0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko hoton mtn card ta Wannan numbern 08147537180 sannan kiyi screen short ki turo shaidar biya*






*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺

*GELLE ƁINGEL*

🏺🏺🏺🏺




*Story*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah)*





*Littattafan marubuciya*

Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login