Showing 60001 words to 63000 words out of 93605 words

Chapter 21 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

dogon tunanin da ta tafi kallon ta, ta kai ga wayar Maman Abdul abinda ta gani a rubuce murmushi Jummo tayi tare da ɗaga kiran tana sallama.

Daga can Safreena ta amsa sallamar tana murmushi tace.

" Ƙawata kwana biyu shuru kin manta dani Allah dai yasa ba laifi na miki ba."?

Murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Ni kuwa laifin me zaki min Mmn Abdul, kawai dai naga kamar bakya buƙatata cikin rayuwarki ne shiyasa na ƙyaleki badan kin min laifi ba."

" Bana buƙatar ki cikin rayuwata kuma, meyasa kikace haka?"

" Mmn Abdul kenan!!! Ai alamun hakan sune suka nuna baki damu dani ba, domin kuwa baki taɓa kirana ko da sau ɗaya bane, ko yaushe Ni ne kawai nake kiranki, sannan nazo nayi kwana da kwanaki bana kiranki, amma baki damu da meyasa bana kiranki ba, bakiyi tunanin anya lafiya kuwa bana kiranki ba, shiyasa kawai na daina kiranki amma kullum ina tunawa dake a cikin raina."

Numfashi Safreena ta sauƙe cike da jin kunyar abinda ta yiwa Jummo tace.

" Ko kaɗan ba haka bane, domin kuwa ina buƙatar ki a rayuwata tun haɗuwata dake nake jin alkairi ne, ji nake tamkar akwai wani abu nawa mai mahimmanci a rayuwata a jikinki, tabbas nayi maki laifi domin kuwa ban kyauta ba, ya kamata ace koda ba kullum ba na dinga kiranki sai dai Allah bai nufi hakan ba, kimin afuwa insha Allah zan gyara laifuka na."

" Ba komai ya wuce, ina ɗana Abdul?"

" Abdul yana bacci bai farka ba, ya kk ya gida dasu Mama."?

" Ayya Abdul sarkin bacci shi dai a rayuwarsa yana son bacci, kowa yana lafiya, Ya Baban Abdul yake."?

Wani ras zuciyar Safreena tayi, jin tambayar Jummo, Allah sarki ita tayi zaton ni matar aurece bata san ban taɓa Aure ba, batasan na samu Abdul ne ta hanyar banza hanyar da bata dace ba, numfashi Safreena ta sauƙe tare da cewa.

" Ammm!!! Yi hakuri Jummo bara nazo zan sake kiranki ana kirana sai anjuma ki gaishe da Mama"

" Na gode"

Katse kiran Safreena tayi tare da sakin numfashi zuciyarta a jagule, dama ta sani komai jumawa dole ne za'a binciki Asalin Abdul, wanda take kunyar sanar da hanyar da aka samesa shin me zata faɗawa duniya game da yacce ta samu Abdul, guntun hawaye ne ya zubo daga idanunta tare da saka hanu ta share cikin zuciyarta tana furta ( A rayuwata nayi kuskuren da bazan taɓa daina danasani ba a rayuwata tabbas Zina abin kunya ce da bazata taɓa bibiyar wanda ya aikata ba har tsufansa, kai harma da bayan rayuwarsa dole ne wata rana sai an yiwa zuri'ar ka gori) kanta ta saka ta fice ba tare da tacewa Zee komai ba, itama Zee bata tankata ba domin raji dukkan hirarsu."


✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Jin an dafata yasa Jummo juyowa, Aunty Zarah ne tsaye a bayanta ɗan murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Aunty kece.?"

" Ni ce Jummo, me kikeyi a gindin taga lafiya kuwa naga kamar ma kina cikin damuwa.?"

Ɗan murmushi Jummo tayi tare da juyowa ta fuskanci Aunty Zarah ta ce.

" Babu komai kawai ina hango giftawar ababen hawa ne, meyake faruwa ne kika shigo room ɗin mu."?

" Babu komai kawai nazo na baki hkr ne bisa rashin fahimtar ki da nayi a baya, na so na jefa kaina cikin hallaka sanadin Momy sai na rantse miki da Allah babu hanuna cikin rashin lafiyar Mamma."

Murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Menene kuma na rantsuwa, ai tunda kin gane gaskiya komai ya wuce Aunty dama ni ban riƙeki a zuciyata ba, Mamma kuwa alhamdulillah tunda ta samu lafiya."

" Zuciyarki mai kyau ce Jummo, a fuska gaki kamar zakiyi faɗa amma a zahiri sam ba haka kike ba na gode da fahimta ya kamata idan har kin yafe min ki biyoni zuwa kitchen mu cigaba da girki tare kamar yadda muka saba ƙanwata."

Murmushi Jummo tayi tare da kama hanun Aunty Zarah tace.

" Faɗan ma ina dashi muddun aka kaini bango, muje Aunty komai ya wuce."

Dariya Aunty Zarah tayi tare suka jera har kitchen, Momy kuwa tunda ta shiga bedroom ɗin ta take tunanin ta wacce hanyar ce zata raba tsakanin Jummo da ɗan ta, tana cikin wannan tunanin Ya Garkuwa ya shigo fuskarsa a ɗaure, gefe da ita ya zauna dubansa Momy tayi tare da cewa.

" Baka da hankali ne zaka shigo min room babu sallama, ka taho sai famar haɗa fuska kake tamkar zaka dakeni akan wannan shegiyar Yarinyar."

" Tabbas hankalin nawa ya fara tafiya saura kaɗan yabar jikina na zamo tantirin mahaukacin zaki wanda idanunsa zasu kulle ya bi duk wata hanyar da yasan zai samu abinda yake farauta, domin kuwa kece Uwar da take shirin haukata ɗanta da kanta take neman kaisa ƙasa ba tare daya shirya ba, ko wacce Uwa burinta farin cikin ɗanta, amma ni tawa uwar baƙin ciki na shine abinda take muradin ta gani buri take ta ganni cikin ciwo, ki faɗa min wani zunubin na aikata miki da kike min wannan azabar a matsayinki ta Uwar da ta haifeni ba yadikko ba, wani laifi na miki, shin biyayya ne bana miki ko kuma kyautatawa ce bana miki, menene na rageki dashi na haƙƙinki wanda yake kaina da kike ƙoƙarin ganin baƙin ciki na, ki faɗa min Momy menene aibun Jummo da kika tsaneta, karuwace ko shegiya ce, ko kuma Tarbiyya ne bata dashi, tana da rashin kunya ne, ko ta taɓa zaginki ne, shin tana da mugun ciwon da zai dakatar da Aure a tsakanin mune, shin iyayenta mutanen banza ne, ko ilimi ne bata dashi, ki faɗa min wanne ta rasa!!!"?

Yayi Maganar a harzuƙe tamkar mahaukaci, yana kallon Momy, cike da tsoro Momy ta bisa duk da tasan halin Garkuwa mutum ne shi mai zuciyar gaske wanda baya taɓa ɓoye fushin sa, a duk sanda ransa ke ɓace sosai to fa fusace yanayinsa yake kasancewa duk da sanin halin sa baisa Momy ta saurara masa ba, sai ma hawansa da tayi da masifa.

" Ai yanzu ma a haukace kake Garko, sai kaje kabi hanyar da kake gani idan zaka sameta, yau nine kake yiwa Magana cikin faɗa Garko, muryarka harta yi sama da tawa saboda Mace, hakan yana nuna min kenan da zarar ka sameta zakayi watsi dani ka maida hankalinka gareta, kuma bazan bari hakan ta faru ba, badai sai ka aureta ba Kafin ka juya min baya to sai naga ta yadda za'ayi wannan Auren, ina kyautatawa anan Garko ka shigo kaina kana min ihu a matsayinka na ɗana, ina tarbiyya wajen ka tunda na baka umarni kaƙi bi, shin ashe Garkuwa bani da darajar da zan hanaka abu ka rabu dashi komai girman son da kake yiwa abun, shin ko wuta na haɗa nace ka faɗa ashe bazaka min wannan karar ba, karka manta da cewa nice UWAR dana ɗauki cikin ka tsawon wata tare cike da laulayi, da wahala na haifeka ban huta ba, nine wankan ka rainon ka, goyonka , wanke kashin ka da fitsarin ka, kamin amai a jiki da kashi fitsari duk na wanke ban taɓa gajiyawa da ɗawainiya da kai ba har girmanka, amma yau duk ka mance da wannan kazo ina faɗa kana mayar min akan mace, har tambayoyi kake min akanta saboda ka ƙureni, to bazan baka amsa ba Garko ka shaƙe ni koka dakeni Idan naji wahala sai na amsa maka."

" A'a Momy ba ihu nake miki ba, zuciyata ne ta kasa ɗaukar hukuncin da kika yanke, Momy bazan taɓa fifita Mace ba sama dake, domin kuwa kinmin ɗawainiyar da bazan taɓa iya saka miki ba, dai-dai da second ɗaya, Momy da ace kin rabani da Jummo gara ace wutar kika bani umarnin na faɗa domin kuwa sai tafi min sanyi fiye da tsanani da azabar da zuciyata zata shiga idan na rasa Jummo ƙarshe ma na iya mutuwa, Momy kin sani a yanzu zuciyata ba cikakkiya bace domin kuwa a cikin ciwo take abu kaɗan kan iya Tarwatsa min ita, ki rufa min asiri Momy ki taimakeni kimin rai a matsayinki na mahaifiyata ki barni da zaɓi na dan Allah Momy badan ni ba, domin samun salamar rayuwata, Momy ki daina ambaton na dakeki, Allah karya nuna min ranar da zan saka hanu a jikinki, da ganin wannan Ranar Gara ace na rasa hanuna ko na mutu."

Tsuka Momy taja tana harararsa tare da nuna masa ƙofa.

" Fice min daga room karka kuma tunkarata da zancen wannan shashar Yarinyar idan kuma ka sake to zan ja maka Allah ya isa ko kuma ka biyani nono na da ka sha domin kuwa baka cancanci na kiraka da sunan ɗa ba, fice min a gabana."

A razane Garkuwa ya ɗago yana kallon Momy cike da matuƙar tashin hankali marar misaltawa, goshinsa duk ya feso da zufa yace.

" Momy.............."

" Shittttttt!!!! Fice min bana buƙatar kuma jin muryar ka yanzu get out of my room, get out!!!!"






*UMMU NASMAH CE*
[4/29, 9:44 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*



➰➰ *53 to 54*


Ficewa Ya Garkuwa yayi zuciyarsa na tafasa izuwa yanzu ya fara zargin tabbas akwai wani mummunan al'amari daya faru tsakanin Momy da Jummo tabbas akwai abinda Jummo ta yiwa Momy na rashin kyautawa, ƙiyayyar tayi yawa dole akwai wani abu domin kuwa bazata tsaneta haka kawai ba, tunda ya fito yake ƙwalawa Jummo kira tamkar zararre, bedroom ɗinsu ya buɗe bata ciki ƙasa ya sauƙo still dai kiran yake mata, jin motsi cikin kitchen ya sashi faɗawa ciki yana kiran.

" Jummo!! Jummo!!! Jummo!!!"

Jummo da Aunty Zarah dake famar aiki ne suka juyo tare a tsorace Aunty Zarah ce tace.

" Garko lafiya kake mata wannan kiran haka, ni wallahi harka razana ni."?

Ya Garkuwa da idanunsa suka kaɗa sukayi jajur ne ya fisgo hanun Jummo tare da jawota zai fita da ita daga kitchen ɗin, Aunty Zarah ta tare gabansa tare da cewa.

" Wai meye hakane Garko, ina maka Magana kayi banza dani zaka jata ka fita da ita, meyake faruwa ka sanar dani mana."?

Idanunsa Ya ɗago da suka gama rinewa har jijiyoyin kansa suna tashi yace.

" Ba abinda ya shafeki bane, dan haka babu buƙatar dole sai kinji, kauce min a hanya na shige."

Wangale baki Aunty Zarah tayi tare da cewa.

" Amma ai Garko ya kam.............."

" Ya Isa dan Allah Aunty Zarah, karki matsamin akan abinda bazan faɗa miki ba."

Numfashi Aunty Zarah ta sauƙe tare da kaucewa suka shigo, tamkar wawiya haka yake jan Jummo tana binsa, dariya Aunty Zarah ta sheƙe DASHI tare da furta.

" Maganin shegen biri karen maguzawa, ita nan tunani take gaskiya na gane harna tuba, bata san tsabar iya taku bane, gaskiya kika faɗa min Momy dole zata amince dani idan na biyo mata a haka, muje zuwa Jummo insha Allah sai mun ga bayanki, burin Momy shine zai cika a cikin gidan nan."

Ƙara sheƙewa tayi da dariya tare da juyawa ta cigaba da aikinta.

Shi kuwa Ya Garkuwa har garden yayi da Jummo tare da sakar mata hanu yana huci,. Sai yanzu Jummo ta iya buɗe baki da ƙyar tace.

" Wai meye kake haka, kazo ka jawoni ina aiki, ka kawo ni nan kana huci tamkar mayunwacin zaki."

Cike da tsawa ya Garkuwa yace.

" Ai har gara mayunwacin zaki fiye dani, domin kuwa shi zaki idan ya fita farauta zai samu abinda yake so, ni fa koda na fita farautar ba samu zanyi ba domin kuwa duk hanyar da zanbi bi take tana tarewa, kaina ya fara kullewa tunani yamin yawa kuna neman haukata min ƙwaƙwalwa, wai bakwa tausayi na ne, kun san ba cikakkiyar lafiya bane dani why why!!!"?

Jummo cike da rashin fahimtar maganganun Ya Garkuwa tace.

" Me kake faɗa ne wai haka ban gane ba, kamin magana yanda zan gane kasan ni ba bahaushiya bace, ka min yanda zan gane.?"

" Jummo ki faɗa min gaskiya karki ɓoye min komai, meye tsakanin ki da Momy shin kin taɓa mata rashin kunya ne, ko akwai wani saɓani tsakanin ku, ƙiyayyar da take nuna miki tayi yawa, haka kawai bazata miki wannan tsanar ba dole akwai wani abu."?

Sai yanzu Jummo ta fahimci inda Ya Garkuwa ya dosa gefe ta samu ta zauna tare da ɗaga kai taa kalli Ya Garkuwa ta fara Magana cikin raunin muryar.

" Ko ɗaya Farin ciki na babu abinda ya taɓa shiga tsakanina da Momy, ban taɓa yiwa wani ma rashin kunya ba, bare kuma ita, ni kaina idan na zauna nakan yawaita tunanin me na yiwa Momy ta tsaneni haka, amma nafi zaton zuciyarta ce kawai bata ƙaunata ko kuma na fito da ƙauye ne, ko kuma saboda iyayena basu dashi ne, shiyasa bata ƙaunar ɗanta dani, amma shawarar da zan baka, shine kabi umarnin mahaifiyarka wataƙi babu alkairi ne tsakanin mu shiyasa taƙi Auren abinda babba ya hango yaro ko ya hau tsauni bazai taɓa hangowa ba, uwace ita biyayya a gareta ya zama dole muddun kana neman albarka, Allah da kansa sai da ya ambaci Uwa sau Uku kafin ya ambaci Uba, sanda Ubangiji yace ku bini, sai kuma yace daga ni sai Uwa, hakan yana nuna mana girman mahaifiya, a duniya babu wanda yafi Uwa son ɗanta saboda tafi uba sanin zafin sa, Ya Garkuwa ina sonka ina kallon ka a matsayin hasken rayuwata, rayuwa babu kai a gareni tamkar mutuwa tace sai ita ƙaddara tana zuwa ne ba tare da tambaya ba ko shawari wata ƙil babu rabon Aure ne a tsakan.............."

Saurin saka hanu Ya Garkuwa yayi ya toshewa Jummo baki yana girgiza mata kai tare da cewa.

" Karki ce haka babu abinda zai rabamu sai dai mutuwa ina ji a jikina kece Uwar ƴaƴana, insha Allah sai munyi Aure Jummo, nasan ta inda zan fitowa Momy, tashi kije ki kwantar da hankalin ki karki ɗaga min hankalinki komai zaizo mana cikin sauƙi."

Tashi Jummo tayi tare da kallon Ya Garkuwa tace.

" Ya Garkuwa, bana son Momy tayi fushi dakai ta dalilina, a kaf faɗin duniya baka da wacce ta fita, kabi komai a sannu karka yadda ka ɓata mata rai idan harta turje ka bi umarnin ta hakan shine cikar ɗa na gari."

Tana gama faɗin haka ta bar wajen da sauri tana kuka, Ya Garkuwa kansa ya dafe komai ya kulle masa a yanzu bashi da mafitar daya wuce ya je ya sami Daddy shine kaɗai zai dakatar da Momy daga wannan mungun ƙudirin nata, numfashi ya sauƙe tare fitowa daga garden ɗin, parking space ya nufa tare da shiga cikin motarsa yaja, darect *I D D BARAU NIG LTD* ya nufa kusan tare suka shigo da Safreena da take cikin keke napep, a tsakiyar Companyn aka sauƙeta, ta biyasa tare da nufar cikin Companyn, tayi nisa da tafiya shi kuma Ya Garkuwa ya fito, shima ya doshi ciki, Safreena a kujerun dake zagaye a harabar ta zauna wajen da ake kiran masu interview tana jira, yayin da Ya Garkuwa ya shigo kansa tsaye, Ya saka kai sai yaji wayarsa tayi ringin ɗaga wayar yayi ya kara a kunnen sa yana amsa kiran yayin da ya tsaya gefenta sam bai kula da ita ba, hankalinsa ya tafi ga wayar da yake, Safreena jin ƙamshin turarensa ya tabbatar mata da Garkuwa ne domin kuwa hancinta bazai taɓa manta ƙamshinsa ba, a hankali ta ɗago idanunta ta zuba masa, wani irin bugawa zuciyarta keyi tana jin zuciyarta ta tokare, har yanzu tana jin Soyayyar sa, sai dai ina ya manta da ita a rayuwar sa shi ɗaukar matacciya ma yake mata, numfashi ta sauƙe tare da dafe ƙirjinta sam bata gajiya da kallonsa kanta ta sunkuyar ƙasa sai kuma hawaye ya zubo mata, duk wannan abinda take Ya Garkuwa bai lura da ita ba, katse kiran yayi dai-dai wani farin bafulatanin mutum yazo fuskarsa ɗauke da annuri ya miƙawa GARKUWA hanu yana cewa.

" Ehh lallai yau ka cika alƙawari, muje office ɗina."

Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Anya kuwa bazamuje mota muyi magana ba, sauri nake, ina da uzuri zanje office."

" Kai Abokina wani sauri kuma dan Allah muje office muyi magana, Shetima ma yana office ɗin."

" Kaji Shetima ɗan iska, wato dai gulma ce ta kawosa, muje to."

Yayi Maganar tare da juyowa saitin da Safreena ke zaune, wanda ta sunkuyar da kanta tare da rufe fuskarta da gyalenta yadda babu mai ganeta, Ganin yatsun ƙafar Safreena yasa zuciyar Garkuwa tsinkewa ya zubawa yatsun idanu ji yake tamkar yasan mai wannan yatsun, gangar jikinta yabi da kallo fuskarta rufe hakan yasa bai gane ta ba, numfashi ya sauƙe tare da taɓe bakinsa yabi bayan Kabir Safreena dake kallonsa ta cikin gyalenta ne ta sauƙe numfashi tare da buɗe fuskarta tana bin bayan sa da kallo, harya shige office din.

" Abdul kamarka daidai take da ta mahaifinka, Naso ace ƙaddarar samunka ta hanyar aure yasa muka sameka, da tabbas ka samu gatan uba, sai dai ƙaddara tazo maka a murɗe mun sameka ta hanyar Haram, baka da wani gatan uba sai nawa, ina tausayin ka Abdul dolene na ɓata rayuwata wajen baka cikakkiyar gata."

Goge hawayen tayi tare da jingina jikin kujerar, tafi awa ɗaya kafin aka kira sunanta ta shige Office din interview, har wannan lokacin Ya Garkuwa bai fito ba, kuma dama haka taso, bata so ya fito ya sameta.

" Kabir kaji halin da nake ciki, na rasa meyasa Momy take son rabani da Jummo menene ya kamata nayi dan wallahi ƙwaƙwalwata ta toshe na ma rasa wani irin tunani zanyi."?

Shuru Kabir yayi domin kuwa maganar ta ɗaure masa kai, Shetima ne yace.

" Kabir a rayuwata ban taɓa tunanin cewa Garkuwa zai so wata mace ba sama da Safreena, da ace kasan Soyayyar su da kasha mamaki, na so ace sunyi Aure sai dai Allah yayi ikonsa Safreena ba mai tsawon rayuwa bace, tana da hankali gami da nutsuwa ga sanin mutumcin ɗan Adam, hakan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login