Showing 87001 words to 90000 words out of 93605 words
Chapter 30 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
kashesu sai dai bata san yaushe bane, tabbas Safreena tayi danasanin zarginka tayi ƙoƙarin zuwa gidanku ta dakatar dakai daga tafiya da wannan motar amma ina kun tafi, tun daga nan ta daina zarginka ta fita daga rayuwarka, Safreena bata cikin rayuwarka yanzu na tabbatar da bata sonka bata son tunawa da kai, rayuwarta ɗanta shine kawai a ranta, ta ina zata inganta rayuwar sa shine burinta, dan Allah karka lalata mata mafarkinta akan ɗanta ka bani Abdul na tafi."
Tunda Zee ta fara Maganar idanun Ya Garkuwa yayi jajur ji yake tamkar wuƙa take daɓa masa, cike da ɓacin rai ya furta.
" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Hmmm!!! Kusan shekara ɗaya da rabi ina cikin zargi koda a cikin baccina ban taɓa mafarkin na kashe koda ƙuda bane bare kuma ɗan adam tabbas baki shike yanka wuya na shiga ban ɗauka ba kuma bata fidda ɓarawo, ban taɓa tunanin Safreena zatayi tunanin zanyi kisan kai ba, domin kuwa tasan waye ni, sai dai na godewa Ubangiji daya tseratar dani daga sharrin da kuka wurga min ya kuma wanke Ni, sai dai abinda nake son na sani ina Safreena take."
" Tana Egypt"
Yaji an amsa masa daga bayansa cikin rawar murya mai alamun kuka, da sauri ya juya yana kallon Jummo numfashi ya saki tare da miƙewa yaje gabanta ya sunkuya.
" Ban ɓoye miki komai game da rayuwata ba, na sanar da ke dukkan zunuban dana aikata da kanki kika yarda zaki zauna kiyi rayuwa dani a yadda nake, na sanar dake wacece SAFREENA da cikin dake jikinta a gareni ban munafurce kiba, sai dai a yanda nake kallon ƙwayar idanunki ina hango tsana da haushi na a cikin su, Jummo.........."
Hanu ta ɗaga masa tare da girgiza kanta ta tashi da sauri tabar wajen, numfashi ya sauƙe Yana maida hankalin sa ga Zee yace.
" Meya kai Safreena Egypt ki faɗa min, bazan iya baki Abdul ba har sai nayi magana da Safreena ki sanar da ita cewa idan tana son amsar ɗanta ta nemeni."
Yayi Maganar yana shigewa bedroom ɗinsa riƙe da Abdul runtse idanunta Zee tayi cike da ɓacin rai ta juya itama tabar gidan.
Sosai hankalin Jummo ya tashi, tabbas bai ɓoye mata komai ga me da Safreena ba, sai dai zuciyarta yana mata zafi ace tana zaune da ɗan shege mijinta na da ɗan layi wannan wacce irin masifa ce, numfashi ta sauƙe tare da ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Ta juma zaune cikin wannan tashin hankalin kafin ta yunƙura cikin sanyin jiki tayi tollet.
Zizah da SALLAMA ta shigo cikin gidan shuru babu kowa, bedroom ɗin Jummo ta nufa kanta tsaye da SALLAMA nan ma shuru taji, tsakiyar ROOM ɗin ta tsaya tana ba kowa ne, gyaran muryar Jummo da taji a tollet yasa ta fahimtar Jummo tana tollet, murmushin mugunta ta saki cikin sauri ta buɗe jakarta laya biyu da wata ƙaramar kwalba mai cike da wani ruwa, tayi gaggawar ɗaga katifar Jummo ta ajiye layar, murmushi ta kuma sakewa tare da sunkuyawa ta ajiye kwalbar tare da ɗayar layar a ƙarƙashin gadon Jummo, cikin sauri ta fice daga ROOM ɗin ganin har yanzu babu kowa cikin falon ya sata ficewa maa daga gidan gabaki ɗaya cike da farin ciki.
Shi kuwa Ya Garkuwa yana nan riƙe da Abdul cike da tunani iri iri a zuciyarsa, taya zai fara sanar da iyayensa wannan mungun abu daya aikata ta ina zai fara gabatar musu da Abdul a matsayin ɗansa, lallai ya tafka kuskure a rayuwarsa ya Daddy da Momy zasuji wannan maganar shin zasu karɓi Abdul da zuciya ɗaya, numfashi ya sauƙe cike da tsoro sai harga zuciyarsa yana jin Abdul a ransa yana ƙaunarsa tamkar yadda zai ƙaunaci ɗan sunnah, ya yadda zai jure zagi da cin mutunci akan Abdul, lallai ya zamo dole Safreena ta dawo rayuwarsa, yana buƙatar domin samun farin ciki mai ɗaurewa, yana so a yanzu suyi rayuwa a ƙarƙashin inuwar Aure ɗaya rayuwa kuma mai tsafta, tabbas yana da tabbacin Jummo bazata gujesa ba, zata karɓi kaddarar sa da hanu yana da tabbacin haka, miƙewa yayi tare da Abdul suka nufi ROOM ɗin Jummo.
Ita kuwa Jummo ko da ta fito daga room ɗin ta duba mai sallama ta hau yi, wayam ROOM ɗin ba kowa, bakinta ta taɓe tana jin wataƙil kunnen ta ne basuji dai-dai ba, bakin bed ɗin ta ta zauna, tana runtse idanunta, zamanta keda wuya kanta yayi wani irin mungun sarawa, saurin dafe kan tayi tana runtse idanunta, zuciyarta ta kuma tsinkewa da ƙarfi take wani haushi da takaici gami da tsanar gidan ya dira a zuciyarta miƙewa da sauri ta fito falo tare da nufar ƙofa zata fice daga gidan a fusace kiciɓus sukayi da Ya Garkuwa, cike da mamakin ganinta a fusace yace.
" Ke Jummo lafiya kika fito a fusace haka."?
Wani mungun kallo Jummo ta jefa masa tare da cewa.
"Gidan mu zan tafi ka sakeni bazan kuma zama a gidanka na tsaneka na tsani gidan ka, ka bani takarda ta."
Wani irin tsinkewa zuciyar Ya Garkuwa tayi cike da tashin hankali yace.
" Jummo kina da hankali kuwa kin san abinda kike faɗa kuwa, nine fa ya garkuwanki kike kiran na sakeki, haba Jummo karki juya min baya akan matsalar Safreena bani da laifi na sanar da komai kafin Auren mu, ban rufe miki KOMAI ba, meyasa zaki karya alƙawarin da kika min dan Allah Jummo ki tausaya min karki barni bazan iya Rayuwa babu ke ba."?
" nima bazan iya rayuwa kaga ka matsa min na tafi idan yaso sai ka biyoni da takarda ta daga baya."
Tayi Maganar tana ƙoƙarin turesa ta shige ganin kamar Jummo bata cikin hankalinta ya sashi saurin turata ROOM ɗin ta tare da jawowa da sauri ya saka key a kofar Abdul ya ɗauka tare da ficewa daga gidan da sauri ya shiga mota rasa ina zaije yayi tsabar ya gigice, sosai hankalinsa yake tashe, Momy ya kamata yaje ya samu da Maganar sai dai bazai yiwu naje wajen Momy ba, tabbas ina cikin tashin hankali, Shetima ne ya faɗo masa a ransa, wayarsa yayi saurin ɗauka ya kira numbern Shetima, bayan ya ɗaga ne cike da tashin hankali Ya Garkuwa yace.
" Shetima kana ina?"
" Lafiya Garkuwa meke faruwa naji muryarka cikin tashin hankali."
" Bana cikin kwanciyar hankali, ina cikin tashin hankali Shetima kana ina ina buƙatar ganinka yanzu pls."
Numfashi Shetima ya saki tare da cewa.
" Ina gidan mu, kazo ka sameni."
Katse wayar Ya Garkuwa yayi tare da jan motar cikin tashin hankali mai gadi ya buɗe masa ya fice.
Ita kuwa Jummo sai buga ƙofar take cike da tashin hankali da ɓacin rai ga kanta dake mungun sara mata ji take idan ba ta bar gidan ba, bazata taɓa samun nutsuwa ba, tamkar mahaukaciya haka take dukar ƙofar, a birkice ta juya ta fara neman key a cikin ROOM ɗin ta buɗe kanta, komai na ROOM ɗin bincikarsa take tana watsarwa, idanunta ne suka sauƙa akan wani key dake cikin bedside drower da sauri ta kai hanu ta ɗauki key ɗin ta nufo ƙofar..........
*UMMU NASMAH CE*
[5/31, 12:40 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*
➰➰ *76 to 77*
Ƙarfe Uku dai-dai agogon Nigeria jirgin ya Garkuwa ya sauƙa a Birnin Egypt sanda fasinjan duk suka sauƙa ya yi settling ɗin jirgin kasancewar a ranar zai juyo, bayan ya samu hutu yaci abinci sannan ne ya kira numbern Safreena kusan ringin shida bata ɗaga wayar ba, dole tasa ya dakata da kiran, kafin zuwa can ya kuma kira, ai kuwa cikin Sa'a ta ɗaga wayar, numfashi ya sauƙe tare da sakin murmushi yace.
" Ina kika bar wayar ina ta kiranki shuru baki ɗaga ba, ina Egypt so nake mu haɗu da gaggawa domin jirgina zai tashi nan da awa Uku."
Shuru Safreena tayi zuciyarta sam bata ƙaunar haɗuwa da Garkuwa sai dai ta masa alƙawari kuma tasan girman alƙawari, cikin daƙilalliyar murya ta masa kwatancen inda take babu ɓata lokaci kuwa ya hau taxi a inda ta masa kwatancen ya tsaya tare da kiranta babu jumawa kuwa ta fito jikinta sanye da Kayan sanyi ta yane kanta da jan mayafi, sosai shigar ta mata kyau gefe dashi ta tsaya ba tare da ta kallesa ba tace.
" Ina jinka nima sauri nake ina da aiki."
Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.
" Ko gaisuwar bazan samu ba, okay hakanma na gode, yanzu dai kafin mu shiga cikin maganar mu kai tsaye, ya labarin abinda ya kawoki ƙasar nan, kina samun Nasara kuwa akan Ibrahim ɗin."
Safreena cikin ƙunar rai tace.
" Har yanzu babu wata Nasara dana hango game da shirina akan kawu IBRAHIM, na ma kasa samun damar ganinsa, da alamu yayi ƙarfi sosai anan, hakanne ma yasa na yanke shawarar jibi zan dawo Nigeria na sake shiri kafin na komo."
Hanunsa ya Garkuwa ya zuba a aljihun sa tare da cewa.
" Dama ni na sani cutar da Ibrahim a wannan ƙasar zaiyi wahala, domin kuwa ganin sa ma zaki shekara baki gansa ba saboda done ne shi anan yayi ƙarfi yana kuma tare da manyan ƙasar nan, ni anawa shawaran naji labarin zaizo hutun ƙarshen shekara Nigeria, a Nigeria kuma na Tabbata zaki samu ganinsa cikin sauƙi mai zai hana bazaki hakura ba ki jira dawowarsa Nigeria, sai kiyi Amfani da wannan damar wajen cikar muradinki."
Kanta Safreena ta ɗaga cike da gamsuwa da Maganar Ya Garkuwa tace.
" Wannan shawarar tamin, ina ga nima hakan zaisa na samu sauƙin aikin, na gode da shawara, tell me meke tafe da kai."
Numfashi Ya Garkuwa ya saki tare da cewa.
" Harna fidda rai da samunki a rayuwata KULLUM ina miki addu'ar mamaci fatana dai Allah ya kai haske cikin kabarinki, dake KULLUM nake kwana nake tashi duk da ina ɗaukarki a matsayin matacciya, tunda na rabu dake ban kuma samun macen da zata maye mini gurbinki ba, sai Jummo, itace kaɗai nake kallo a matsayin ki, Safreena bazan ɓoye miki ba, ina son Jummo matuƙar so jigo ce ita a rayuwata, sai dai duk soyayyar da nake yiwa Jummo bata saka na manta dake a rayuwata ba, duk ke maƙiyi kika ɗaukeni ta fuskar zarginki, Safreena mahaifina ya amince na karɓi Abdul a matsayin ɗana, ya kuma umurceni dana aureki Saboda Rayuwar Abdul, kuma nima hakan take a zuciyata, ina sonki har gobe farin cikin rayuwata zai cika ya tumbatsa idan kika kasance dani, Safreena ina son muyi Aure."
Tunda ya soma Maganar Safreena take binsa da kallon mahaukaci, kafin ta dubesa ido cikin ido tace.
" Bazan aureka ba kuma bazan baka Abdul ba, ka sani rayuwata da ta ɗana zata inganta ko babu kowa a tare dani, ka sani babu Aure a gabana yanzu, kuma koda ina da niyyar Auren ma wallahi bazan aureka ba, zaifi maka sauƙi ka fita a rayuwata dani da ɗana, kaje ka riƙe matarka ta isheka rayuwa, sai kuma ka godewa Allah da bai jarrabeka da fitinanniyar mace ba, na zunuban daka aikata, matarka macece ta gari mai kima da mutunci mai Alkunya gami da kawaici samun irinta a yanzu yana matuƙar wahala koni nan ban Kaita ba, kawai kaje ka riƙe matarka ni ka rabu dani, ko sauraranka da nayi yanzu saboda alƙawarin dana ɗaukar maka ne, da ko inuwata bazan yarda mu haɗa ba, na barka lafiya."
Tayi Maganar tana barin wajen cikin sauri domin kuwa har cikin zuciyarta take jin bazata iya auren Garkuwa ba, shuru yayi cikin damuwa yana kallon ta, har sai da ta ɓace masa, idanunsa ya runtse yana jin insha Allah sai ya shawo kan Safreena ta amince dashi, juyawa ya bar wajen, ya koma airport ɗin, ƙarfe takwas na dare agogon Nigeria jirgin nasa ya tashi zuwa Nigeria.
Jummo ce zaune gaban Momy tana goge mata ƙafafunta tare da ɗan matsa mata, Momy sai bin Jummo take da kallo ba tare da tayi Magana ba, cikin zuciyarta ta fara jin son Jummo bata taɓa tsammanin wacce ta tsana a rayuwarta ba, zata jinyace ta, harta wanke mata kashi da fitsari, abinda ko ɗan uwanka ba kowa bane zai maka wannan aikin, Lallai duk yanda kaga Mutum karka rainasa a rayuwa domin kuwa baka san wacce irin rana zai maka ba a rayuwa zai yiwu shine wanda zai taimakeka a lokacin da kake neman mai taimako, lallai ta tafka kuskure na ƙin Jummo a rayuwarta, gashi ƴarta da ta haifa bata tsaya ta kula da rayuwarta ba harkokin gabanta kawai ta saka a gabanta amma ita Jummo gata da ciki ma amma haka take ɗawainiya da ita, numfashi ta sauƙe tare ɗago hanunta mai amfani da ƙyar ta ɗaura akan Jummo, Jummo ɗago kanta tayi ta kalli Momy, murmushi Momy ta mata, a hankali ta furta.
" Na gode Allah ya miki albarka"
Murmushi Jummo tayi cike da farin ciki tunda Momy ta kwanta jinya yaune kawai tayi Magana, Ya khalil ne ya shigo da Sallama, a gefen Momy ya zauna cikin sanyin jiki yace.
" Momy dan Allah kiyi hkr ki yafewa Garko ki cire damuwa a ranki Garko kuskure yayi ya kuma tuba, nasan bazai kuma ba Momy, Momy ubangiji ma fa muna masa laifi ya yafe mana, bare kuma mu ƴan adam, kiyi hkr Momy dan Allah lafiyarki muke nema yanzu."
Jummo ce ta ɗaura da cewa.
" Momy duk da nasan ba ƙaunata kike ba, amma zan nemi alfarma a gareki, ki yafe masa ke uwace fushinki garesa zai iya jawo masa wata masifar a rayuwa, Momy ya Garkuwa ya sanar dani dukkan abinda ya faru da rayuwarsa tun kafin ya Aure ni, harta wannan cikin da ya yiwa Safreena ya sanar dani cikin nadama kuma ya tuba tun tuni, wallahi Momy Ya Garkuwa mutumin kirki ne yanzu ƙaddara ce ta faɗa masa ki yafe masa dan Allah."
Momy hawayene ya zubo mata daga idanunta cikin ƙasa da murya irin na majinyaci tace.
" A irin tarin zunubai na, ai dole ubangiji ya jarrabeni, ni ba mutumiyar kirki bace, shiyasa rayuwa ta juya min baya, ku duba kuga yadda Allah ya mayar min da halitta ta lokaci ɗaya wai nice komai sai anmin, haka Rayuwa take muddun ba alkairi kake ƙullawa ba, to ka jira ranar tozartar ka, domin kuwa Allah bazai taɓa ƙyaleka ba, nayi sihiri iri iri a rayuwata, na raba tsakanin Uwa da ɗanta, Mamma tana cike da tsanata a zuciyarta, bana da kirki, to meyasa ma zanji haushin Garko saboda ya aikata wannan mungun aikin, me yiwuwa nubina ne ya biyo ta kansa, na yafe masa duniya da lahira, kema Jummo ki yafe min."
Cike da farin ciki Ya khalil da Jummo suke murmushi, wannan shine burin Jummo a rayuwarta, Momy ta gane gaskiya karta mutu cikin saɓon Ubangiji, cike da farin ciki Jummo ta sanar da Ya Garkuwa cewa Momy fa ta yafe masa sosai shima yayi farin ciki a ranar ya zo wajen Momy cikin farin ciki.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Rayuwa tana tafiya yayin da jikin Momy zaace alhamdulillah sai dai har yanzu ɓarin jikinta babu wani canji bakinta kam ya dawo dai-dai sai ɓarin jikinta har yanzu babu wani canji a yayin da cikin Jummo ke da wata bakwai ganin tayi nauyi yasa Ya khalil neman TRANSFER ya dawo Gombe shida Zarah, Jummo kuma ta koma gidanta Aunty Zarah ta cigaba da kula da Momy.
Suna zaune a falo suna hira Jummo ta dubi Ya Garkuwa tace.
" My love, gaskiya nifa idan na haihu Tulde zan koma wanka."
Zaro idanunsa yayi tare da tsuke fuska yace.
" Ban miki alƙawari ba, anan zakiyi wanka, karma ki saka a ranki."
Jummo zatayi Magana sukaji Bbc news na sanar da cewa jirgin daya taso daga Egypt zuwa Nigeria yayi hatsari ya faɗi, a yayin da jirgin ya ƙone ƙurmus, Ya Garkuwa a matuƙar razane ya miƙe tsaye wani irin gumi na keto masa hankalinsa yayi mungun tashi, Jummo miƙewa tayi tare da dafa kafaɗar sa tace.
" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Safreena fa tana cikin jirgin nan innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!!!"
*UMMU NASMAH CE*
[6/2, 4:40 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*
➰➰ *78 to 79*
"Ta mutu kenan Ya Garkuwa.?"
"Jummo Safreena tana cikin jirgin nan domin kuwa Zee ta tabbatar min cewa Safreena ta taso yau, kenan tana cikin jirgin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allahumma ajirni fil musibati wa'akfilni kairan minha!!!! Bara nayi gaggawar zuwa airport ɗin mu, nasan suna can sashin bincike zan kuma nemi Zee naji ya ake ciki"
"Dan Allah idan kaje duk abinda ake ciki ka sanar dani dan hankalina bazai kwanta ba har sai naji halin da Safreena take ciki."
"Karki damu insha Allah zamuji alkairi."
Ya mata Maganar cikin sigar rarrashi domin kuwa ya tabbatar da cewa muddun Safreena tana cikin wannan jirgin sunanta gawa, saboda jirgi baya taɓa faɗuwa ƙasa wani ya rayu duk wanda suke ciki sai sun mutu, kanta Jummo ta ɗaga masa alamun to jikinta sai famar rawa yake.
Cike da tashin hankali shima yaje airport ɗin nasu sashen bincike ya nufa kusan dukkan ma'aikatan suna cikin wajen, a kusa da Shetima ya tsaya tare da cewa
"a wani ƙasa jirgin ya faɗi.?"
" Afghanistan anan jirgin ya faɗi kuma an tabbatar da cewa mutum 40 a ciki duka sun mutu harda Samuel drevern jirgin shima ya mutu."
Idanunsa ya Garkuwa ya runtse tare da zaro wayarsa ya kira numbern Zee ringin ɗaya kuwa ta ɗaga tana sakin kuka mai sauti, idanunsa ya kuma runtsewa kukan Zee ya tabbatar masa da cewa Safreena tana cikin jirgin kuma ta mutu, cikin raunin murya yace.
" Safreena tana ciki ko? Safreena ta mutu innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allahumma ajirni fil musibati!!! Kiyi haƙuri Zee mutuwa rigar kowace kowa dole sai ya saka wannan rigar babu wanda mutuwa zata bari, Ubangijin daya ɗauki Safreena ya fimu sonta, ita da ta tafi batayi sauri ba, mu kuma da muke raye ba muyi jinkiri ba, komai daren daɗewa sai munje mu tadda ta."
Ya ƙarisa Maganar hawaye na gudu a saman fuskarsa, Lallai yayi babban rashi, ya tsarawa rayuwa da farin ciki biyu Jummo da Safreena, hmmm sai dai ina Allah ya ƙaddara Safreena ba matarsa bane, katse