Showing 27001 words to 30000 words out of 93605 words

Chapter 10 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

mata ƙudurin ki akanta kiyi hkr ba laɓe na miki ba, naje aiken Aunty Zarah ne na jiki dan Allah Momy ki sauya hali ki daina ƙoƙarin cutar da Mamma, Momy Mamma tasha bani labarin yanda kuka wulaƙanta ta, lokacin Auren ki da Daddy har yanzu wannan abun yana cin zuciyar Mamma meyasa baza kiyi ƙoƙarin kyautatawa Mamma ba, domin kawo masalaha a tsakanin ku, ki goge laifin ki daga zuciyarta na tabbata Mamma zata manta da komai ku zauna lafiya."

Wani irin sanyi jikin Momy yayi, take gumi ya keto mata kunya duk ya lulluɓeta juyawa tayi ta kalli Jummo tare da zama baki kujera ta kalleta cike da tsana ta nunata da yatsa.

" Wato laɓe kike min, hmmm!!! Yau naji wata ƙaddara yarinya ke gida bana ubanki ba, bana dangin ubanki ba, bana dangin uwarki ba, babu dangi tsakanin mu dake amma ki shigo cikin gidan mu ki nemi hanamu sakat, to bari kiji muddun baki fita a harkata ba, na rantse da Allah sai na kawo ƙarshen ki a cikin gidan nan, shegiya mai kama da buzuwa, to bari kiji baki isa ki wargaza min shirina ba, YANDA na ɗauki alwashin ganin bayan Mamma a cikin gidan nan, wallahi sai na gani, dole sai kun barmin gidana ko koma can ƙauye kuje kuta fama da dawa da baƙar kuka mtss."

Momy tayi maganar tana juyawa tayi taku ɗaya taji muryar Jummo.

"Muddun ina numfashi bazan taɓa bari ƙudurinki ya cika akan Mamma ba, na rantse da Allah yanda Mamma ta shigo gidan babu wanda ya isa ya fidda ita a gidan ɗanta, tazo kenan, Momy ki dawo cikin hankalinki ki fahimci cewa kina kan kuskure ne, da Mamma munguwa ce mai bin doka irinki wallahi da ta juma da ganin bayanki koda bataxo birni ba, domin kuwa ƙauyenmu mun fiku matsafa, amma ita zuciyarta a tsarkake take bata iya mugunta ba, faɗan kawai ta iya dan haka ki kwana da sanin zan tseratar da Mamma daga duk wani sharrin ki, Sai dai ke ki fita kibar Mamma a cikin gidan nan wannan alƙawari na ɗauka."

Kunkumin ta Momy ta riƙe tana huci yayin da Aunty Zarah ta daskare tana kallon Jummo, bata taɓa zaton JUMMO tana da baki haka ba, Momy ɗauke Jummo tayi da mari tana nuna ta da yatsa tace.

" Ni kike kira munguwar, ehh lallai ɗan zaki ya girma, gaskiyar hausawa da suka ce idan ɗan ƙauye ya shigo Birni ya waye sai yafi ɗan Birnin iya shege, to bari kiji ni ba kanwar lasa bace, nafi ƙarfin ki, kuma ki sani nice ƙalubalenki."

Tana faɗin haka ta haura da sauri tana huci, Jummo dafe kuncinta tayi tare da kallon Aunty Zarah, zatayi Magana Aunty Zarah ta ɗaga mata hanu tare da cewa.

" Karki cemin komai, na fahimci komai, tabbas Momy bata kyauta ba, amma bai dace ki mata rashin kunya ba, komai tsiya dai Momy ta haifeki, na fahimci kinzo gidan nan ne domin ku fitar da Momy daga gidan ta, wannan kuskure ne, kuma bazan taɓa bari hakan ta faru ba, Farko ɗaukar mutumiyar kirki nake miki ashe ba haka kike ba, ashe munguwa ce mai fuska biyu kin bani mamaki Jummo."

A matuƙar firgice Jummo take kallon Aunty Zarah da ta mata munguwar fahimta cikin sauri Jummo tace.

" Baki fahimce ni ba Aunty Zarah, meye laifina dan Momy tayi kuskure zan gyara mata.?"

" Karya kike Jummo babu gyara a cikin lamarin ki, sai tsantsar munafurci idan ba munafurci ba, meyasa zaki sanar da Mamma Momy taje wajen boka, haka ake gyara, idan gyara zakiyi, kamata yayi ki nunawa Momy kinsan abinda take, ki nuna mata ta gyara cikin masalaha, ba wai ki kwashi magana gulma da munafurci ki kaiwa Mamma ba, wannan haɗa faɗa ne da ƙara rura wutar ƙiyayya a tsakanin su."

" Aunty Zarah wallahi ba nuf................"

" Karki cemin komai na riga na gama fahimtar waye ke, rogo nake yiwa kallon kitse........................."








*Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙi Naira 100 kacal zaki biya ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko ki turo hoton Mtn card na 100 ta wannan numbern 08147537180 sannan ki turo shaidar biya.*




*Kuyi haƙuri dan Allah yau kun sami readmore kadan abubuwa suka min yawa, amma dai hausawa sunce da babu gara ba daɗi, kuyi manage*





*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺

*GELLE ƁINGEL*

🏺🏺🏺🏺




*Story*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah)*





*Littattafan marubuciya*

Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.


And now *GELLE ƁINGEL*


*SADAUKARWA*


Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.


*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_________________________________*



*FREE PAGE*


➰➰ *27 to 28*


" Hmmm!!! A iya sanina gyara bai taɓa zama munafurci ba, na sanar da Mamma gaskiya ne domin tasan yanda zata kare kanta daga sharrin Momy, wai ma na tambayeki Aunty Zarah, wani daɗi Momy ta miki da har zaki shiga gabanta ki kareta, ki tsaya a gaban karya domin karya gwiwwar mai gaskiya yin hakan kuskure ne, kuma wallahi Aunty Zarah bazan taɓa sauyawa daga ƙudiri na ba, muddun ina tare da Mamma bazan taɓa bari burin Momy ya cika a kanta ba."

" Ai dama bazaki bari ba, Saboda kina da mungun niyyar raba uwa da ƴaƴanta miji kuma da mata, to niyyar bazai taɓa cika akan Momy ba, muddun nima ina cikin gidan nan, domin kuwa baki fini iya wayo ba, daga ƙauye kika fito ni kuma a cikin birnin kika shigo kika sameni dan haka dole na fiki waye wa, zan kare Momy kota halin yaya mugun nufinki bazaiyi tasiri a kanta ba."

Murmushi mai sauti Jummo tayi tare da matsowa gaban Zarah tace.

" Ina ta baki mutuncin ki amma naga alamar bakya son mutuncin da nake baki, kin min hallaci bazan so ɓata miki ba, shiyasa bana son kisan waye Jummo, ki tambayi A'illo labari na a ƙauye ba'a taɓa Nasara a kaina duk abinda na saka a gabana sai na cimma nasara, amm Aunty Zarah tabbas daga ƙauye na fito, amma zan nuna miki wayon ɗan ƙauye yafi na ɗan Birni mu buga wasan ƙarshen wasan shi zai bayyana mai Nasara, fatan Nasara Aunty na."

Tayi Maganar tana murmushi tare da barin wajen ta nufi bedroom ɗinsu, Aunty Zarah dafe kanta tayi ta nemi waje ta zauna cike da tsantsar damuwa, bata taɓa zaton wayon Jummo ya kai haka ba, (duk da babu shiri tsakanina da Momy komai tsiya ai ta zamo uwata tunda ina Auren ɗanta ya zamo dole na kareta daga sharrin Mamma da Jummo, domin barin Momy cikin gidan nan yana nufin rugujewar farin cikin mijinta ita kuwa bazata jure ganin mijinta cikin damuwa ba, farin cikin sa shi take buƙata, zatayi wannan yaƙin ne domin farin cikin mijinta) numfashi ta sauƙe mai nauyi tare da miƙewa ta shige kitchen, itama Jummo bakin gado ta zauna tana ji a cikin ranta bata kyautawa Aunty Zarah ba da ta mayar mata Magana ko yayane Aunty Zarah ta nuna mata ƙauna da duk wata wayewa, "amma ya zamo dole ta kare mutuncin Mamma a da Soyayyar Garkuwa ne ya kawota gidan nan, sai dai a yanzu komai ya juye ta fuskanci matsalar Mamma da ciwo a raba uwa da ɗanta sai gashi Momy ta raba Mamma da ɗanta na tsawon shekaru, ta daɗe Mamma CIKIN ciwon rashin ɗanta a kusa da ita, sai yanzu ta samu damar zama kusa dashi ace za'a koreta sam bazan bari hakan ta faru ba, zan ajiye Soyayyar Garkuwa a gefe domin kare Mamma ta zauna da farin cikin ta Buba, ya zamo dole na zamo ƙalubalen Momy koda hakan yana nufin ƴaƴanta zasu tsaneni na rasa Soyayyar Garkuwa, na yadda na kare Mamma."

Bakinta ta cije tare da Kwanciya ta runtse idanunta, A'illo da kallo ta bita tare da saka hanunta cikin na Jummo tace.

" Mamma itace ta goyeni tun ƙaramar yarinya ta bani tarbiyya ta mantar dani maraicin iyayena komai tana min babu mugunta, ada ina jin zafin ki, sai kuma gashi a yanzu ina jin ƙaunar ki, kin san meyasa Saboda kin ɗauko hanyar dawowa Mamma na da farin cikin ta, sanda muke ƙauye a ko wani dare sai Mamma tayi kuka tana cewa, Buba ya gujeni baya zuwa wajena ɗansa kawai ki ziyartana sai dai ya min aike nakan fi shekara banga Buba, nafi buƙatar ganin Buba a kusa dani fiye da kuɗi da kayan abinci da yake aiko min A'illo matar Buba ta rabani dashi dama sunyi wannan alwashin ita da iyayenta cewa da zarar Buba ya tafi da Zainabu Birni bazan kuma ganinsa, kinga kuma maganar su ta tabbata tunda buba ya tafi binni bai kuma zuwa wajena ba sai aike kawai da yake min, sai yaushe zan zauna inuwa ɗaya da Buba sai yaushe A'illo" numfashi A'illo ta sauƙe tare da duban Jummo ta cigaba da cewa " Sai gashi ta sanadiyyar ki domin nemo miki Soyayyar ki Mamma tace mu taho Birni neman gidan Buban ta, ƙaddarar ki itace ta dawo da Mamma cikin gidan ɗanta, dan Allah Jummo karki bari Mamma ta koma ƙauye na tabbata idan Mamma ta koma ƙauye baƙin ciki ne zai kashe ta, shikenan ni kuma na rasa gatana na rasa me kula dani."

Miƙewa Jummo tayi ta zauna tare da ƙara danƙe hanun A'illo ta fara magana cike da rawar murya.

" Yanda ƙaddarata ta dawo da Mamma gidan ɗanta insha Allah haka ƙaddarata zata zaunar da Mamma gidan ɗanta har abada, insha Allah burika na zasu cika ina ji a jikina komai daren daɗewa zan mallaki yaya GARKUWA, sai dai nasan akwai tarin matsaloli a gabana, bani ƙarfi sai na Ubangiji ƙarfin hali kawai nake a wannan yaƙin, addu'a zaki tayani A'illo Allah ya bani Nasara a kansu, Allah yasa kar su suyi Nasara a kanmu, zanyi Magana da yaya khalil maybe shi zai fahimce ni."

Kanta A'illo ta girgiza tare da cewa.

"A'a Jummo karkiyi Magana da Yaya khalil domin kuwa baya son laifin Momy shi duk abinda tayi akan dai-dai take, gara ma yaya Garko shi mutum mai fidda gaskiya a duk sanda tazo koda akansa ko akan Momy ko Daddy baya tsoron ya faɗawa mutum gaskiya, gara shi kiyi Magana dashi akan yaya khalil."

" A'illo ni kuma bazan yi magana da Garkuwa ba, saboda a halin yanzu yana ɗaukata ne a matsayin jahila mahaukaciya wacce bata san abinda take yiba, a haka yake ɗaukata, dan haka bana buƙatar Magana dashi, shima KHALIL ɗin na barsa."

" Shikenan to Allah ya mana jagora."

Da ameen Jummo ta amsa tana maida kanta ta kwanta.

Momy kuwa tunda ta shiga bedroom ɗinta ƙirjinta ke suwa wani irin tsana da haushin Jummo take ji, tunda take a rayuwarta bata taɓa jin tsanar mutum bilhaƙƙi da gaske ba sai Jummo, wani irin mataki ya kamata ta ɗauka akan wannan agolar Yarinyar, ita wannan yarinyar take neman ta tonawa asiri, numfashi Momy ta sauƙe tare da furta.

" Hmmm!!! Lallai akwai Babban ƙalubale a gabana dole sai na fara kawo karshen Yarinyar a cikin gidan nan kafin na juyo kan Mamma wannan wani irin masifa ce, kai kaji yarinya da ƙwaƙkwafin tsiya wato ma turo ta Mamma take tamin laɓe, ai kuwa zanci ubanta zan nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane, zan nuna mata na haife ta, bata isa nuna min wayo ba."

Zama tayi ta dafe kanta ta furta.

" Wannan wacce irin masifa ce take tunkaro Ni, dubu hamsin na bawa wannan malamin yamin wannan aikin sannan kuma ace nayi asaran kuɗina, ina Wallahi bazai yiwu ba!!! Dole ne sai Mamma taci wannan maganin" shuru tayi tana tunanin sai can zuciyarta ta ayyana mata mai zai hana tayi amfani da Zarah wajen kalallameta ta samu ta sakawa Mamma wannan maganin "taya zan fara" zuciyarta ce tace mata " ta hanyar nunawa Zarah kulawa da nuna mata cewa Mamma tana neman rayuwarta tun ba yau ba tabbas kika je mata cikin kuka dole zuciyarta zai karaya taji tausayinki ta baki haɗin kai, idan har kika samu nasarar jawo Zarah jikinki tabbas aikinki zaiyi kyau." Murmushi Momy ta saki tare da miƙewa tsaye tana cewa " tabbas haka zanyi" ta ƙarisa Maganar tana shigewa cikin tollet.


Jikinsa ta mirgino tana sakin murmushi tare da riƙo yatsar hanunsa ta saka a bakinta, lumshe idanunsa yayi yana jin wata nutsuwa na sauƙa masa a hankali ya furta.

" Sadiya kina da ni'ima tamkar Sweet haka kike zaƙinki yayi yawa, hmmm!!!"

Murmushi Sadiya tayi ta cire yatsar daga bakinta tace.

" Duk daɗi na ban kai kaba kai na musamman ne, shiyasa nake fatar na kasance mata a gareka, dan Allah ka aureni yaya Garkuwa, wallahi da kai kaɗai zan iya rayuwa kaine zabin zuciyata."

Gashin kanta ya shafa tare da cewa.

" Sadiya tun yaushe nake ce miki ki daina min zancen Aure, ban miki alƙawari ba Sadiya, amma shi Aure mukaddari ne, Allah shi kaɗai yasan matata, dan haka ki dage da addu'a idan Allah yasa kece fine."

Shuru Sadiya tayi tana duba agogo 6:30pm duban sa tayi tare da miƙewa daga jikinsa ta ma nufar tollet wankan tsarki tayi tare da fitowa ɗaure da towel kayanta ta mayar tana furta masa cewa.

" Lokacin komawa na gida yayi, ni zanje na hau adaidaita."

Da to ya amsa yana miƙewa shima, ya ciro 70k ya miƙa mata, hanu tasa ta karɓa tare da ɗaukar bag ɗin ta ta fice tana ce masa sai ya dawo, tollet ɗin shima ya shiga yayi wankan tsarkin tare da ɗauro alwala kayansa shima ya mayar tare da kwasar wayoyinsa da key ɗin motar sa, ko kaɗan bai lura da camera dake maƙale jikin window dake saitin su ba, ya fice, yana fita ma'aikacin ya shiga ya ɗauki camera tare da seving ɗin videon, ya fito yana sakin murmushi, Zee ya kira tare da faɗa mata aiki ya kammala zata iya shigowa ta karɓa, sannan ya katse wayar.

Wajen bakwai dai-dai Sadiya ta shigo gidan, babu kowa cikin falon zata haura sama taji muryar Aunty Zarah tana cewa.

" Sai yanzu kika ga damar dawowa, amma ba ce miki nayi 5 zaki dawo ba shine kika je kika kai har 7."

Juyowa Sadiya tayi tana murmushi tace.

" Oh Aunty na faɗa miki gidan su zarina naje, kasuwa na rakata shiyasa mukayi dare."

" Kyaji dashi dai" Aunty Zarah ta furta tana shigewa kitchen, murmushi Sadiya tayi ta shige bedroom ɗinsu Jummo ta samu zaune tana lazimi, baƙin ta Sadiya ta taɓe tare da furta.

" Wai dama su ƴan ƙauye har sun iya karatun Sallah ne."?

Murmushi Jummo tayi domin kuwa taji sarai abinda Sadiya ta faɗa kuma tasan da ita take, ta rasa meyasa Sadiya take jin zafin ta alhakin babu wani saɓanin daya shiga tsakaninsu, ko meyasa take mata haka, ita dai Jummo bata tanka mata ba.





✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨



" Lallai Rayuwarki tana daf da ƙarewa muddun wannan azzalumin shine wanda zaki iya rayuwa dashi."

Safreena tayi Maganar idanunta na kan videon da Sadiya da Garkuwa suke tsirara haihuwar uwarsu tana lalata, murmushi safreena tayi tare da ɗago Abdul dake calla kuka ta rungume sa tare da cewa Zee.

" Zee Wannan Yarinyar bata da hankali fa, kina ji darect yake sanar da ita bazai aureta ba, amma dake ƙaramar ƙwaƙwalwa ke gareta ta kasa fahimta, da ace Garkuwa ya furta min shigen kalaman gaskiya da yake nunawa wannan Yarinyar wallahi da ban sakankance dashi ba, yanzu meye abun yi."

Murmushi Zee tayi tare da amsar camerar ta cire memory ɗin, wata waya Android dake gefe ta ɗauka ta saka memory ɗin, tare da cewa.

" Ita wannan yarinya duk inda ta fito jaka ce marar basira dan haka rabu da ita kawai muyi abinda ke gaban mu, kinga wannan wayar na saka mata sabon layin da akayi registration ɗinsa ba hoto, address kuma ba nan garin na saka ba, Bauchi na saka, sannan sunan da nayi amfani dashi wajen registration ɗin shine *D N G* dashi zamuyi amfani wajen tsorata Garkuwa, yanzu zamu tura masa wannan video ɗin ta WhatsApp ɗinsa."

Murmushi safreena tayi tare da furta *D N G S* meaning *DANGEROUS* murmushi ta saki tare da karɓar wayar ta tura masa saƙon tana sakin murmushi.

Yana tafiya ta kashe datar tare da duban Zee tace.

" *Wasan ya fara daga yanzu* .........................."







*Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi Naira 100 kacal ki daure ki biya sai ki cigaba da karatu cikin nutsuwa Free page daga 30 ya ƙare zaki cigaba da samun wannan littafin ne idan kin biya ɗarin ki.*



*Ki biya ta wannan hanyar 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko mtn card wannan numbern 08147537180 sannan kiyi screenshot ki turo shaidar biya 100 ce kaɗai babu yawa.*








*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺

*GELLE ƁINGEL*

🏺🏺🏺🏺




*Story*

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah)*





*Littattafan marubuciya*

Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.


And now *GELLE ƁINGEL*


*SADAUKARWA*


Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login