Showing 93001 words to 93605 words out of 93605 words
Chapter 32 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
koda taje gidan Mamma haka yake an gyara sa sosai, Mamma Sosai taji daɗin ganin Jummo tayi kyau tayi jajur abinta ita da yaronta, Jummo a wajen Mamma take jin wai ashe rana ɗaya za'a haɗa Auren A'illo da Zizah inda Ashe ALH Auwal ne zai aureta malamin Makarantar su, sosai Jummo taji daɗin hakan.
Satin Jummo ɗaya suka tattaro suka dawo tare da su Mamma, inda a kuwa satin akayi auren Zizah da A'illo duk abinda Daddy ya yiwa Zizah haka ya yiwa A'illo sosai Mamma taji daɗin hakan, Mamma da Momy tamkar basu taɓa faɗa ba, kowa ya yafewa kowa sosai Mamma ta tausayawa halin da Momy take ciki na mutuwar ɓarin jiki.
Allah sarki abun tausayi ɗan Adam yaji tsoron duniya, koda aka kai Zizah kano sosai suka sha mamaki ashe mijin ƙarya ya musu dashi mai kuɗi ne, bashi da komai asalinsa ma clener ne a wani ƙaramin asibiti dake jihar Kano a gidan haya ya ajiye ta irin gidan nan mai ɗakuna jere ban ɗaki ɗaya kitchen ɗaya, Zizah sosai hankalinta yayi mungun tashi, fir tace bazata zauna a gidan ba, sai da aka kira Daddy ya mata ba daɗi dole yasa Zizah ta hkr ta zauna cikin takaici da ɓacin rai ga ɗaki ɗaya, kujarar ta guda biyu ne kawai suka shiga, sauran kaya duk juyowa dashi akayi.
Bayan wata ɗaya da auren su Zizah Jummo suka wuce aikin hajji, a wajen Aunty Zarah tabar Ahmad ta masa yayen dole, suka tafi sauƙe farali..
✨✨✨✨✨✨✨✨
Bayan shekaru Bakwai
Zaune take ita da Ahmad tana masa assignment da gudu Afnan ta shigo tana.
" Ammi Ammi!!! Kinga Shahid ya ɗauka min teddy na ko."
Murmushi Jummo tayi tare da miƙewa tana cewa Ahmad.
" Ka ƙarisa assignment Ahmad bara naje na samu Shahid."
Kama hanun Afnan tayi tare da cewa.
" Zo muje na baki wata mamana ki rabu da Shahid."
Dariya Afnan tasa suka shiga room ɗin yaran, kayan wasa ne da yawa a ciki, kama kunnen Shahid Jummo tayi tare da cewa.
" Ina dai kai baka jin Magana ko Shahed, to zan bata wata ka kuma ɗauke mata sai na yanke maka hanu."
Bakinsa Shahid ya tura, yaƙi kula Jummo, kasancewar sa miskilan gaske, wata Jummo ta ɗauka ta bawa Afnan ta fita tana murmushi tare da addu'ar Allah ya shiryi Shahid.
Bedroom ɗin Ya Garkuwa ta shiga yana zaune da system a gabansa, murmushi ta sa tare da rungumosa ta baya tace.
" Ina can yaranka na ƙoƙarin saka min ciwon kai kai kuma kanan zaune hankali kwance."
Dariya yasa tare da jawo ta ta dawo ta gabansa murmushi ya saka ya ture system ɗin gefe tare da cewa.
" Farin ciki na, kina nan ai bani da matsala da yara, ina sonki matata."
Murmushi Jummo tayi tare da kai masa kiss a hanunsa tace.
" Ina sonka rayuwata, kallonka na yaye min baƙin ciki, kaine jigona a rayuwa."
" Kin zamo hasken gidana Jummo, har abada bazan taɓa daina ganin hasken ki ba."
Dariya Jummo tasa tare da ƙanƙamesa cikin farin ciki domin kuwa Rayuwa ta mata daɗi.
Tamat bilhamdulillah.
Duka duka anan na kawo ƙarshen wannan littafin, abinda na faɗa dai-dai Allah ya bani ladansa abunda kuma na kuskure Allah ya yafe min.
Ina roƙon gareku ƴan PAYMENT GROUP, da idan akwai abinda na muku a zaman mu ku yafe min domin rayuwa ta gaji haka zaka zauna da mutum ka ɓata masa baka sani ba.
Sai ku biyoni a cikin sabon NOVEL ɗina mai taken AMINAINA KO ITA?
Bissallam
*UMMU NASMAH CE*