Showing 15001 words to 18000 words out of 93605 words
Chapter 6 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
ya dogara idan aka koresa ya zaiyi da iyalansa, gara su keneth su gwamnati suke yiwa aiki koda za'a ɗau mataki sai dai a musu horo ba dai kora ba, da wannan damuwar Baba Idi ya zauna.
Suna shigowa bakin falon Mamma ta kwace hannunta tare da cewa.
" Dallah cikani!!! Dan ubanka, ke zainabu!!! Ke Zainabu!!! Zainabu!!!"
Momy da Khalil dake zaune suna hirar yaushe gamo ne ya sata saurin juyowa jin ana ƙwala mata kira tamkar za'a tashi sama, shima Khalil dubansa yakai wajen " Mamma!!" Ya furta yana miƙewa tsaye, Momy kuwa kusan suman tsaye tayi ganin Mamma a cikin gidan ta, shikenan ta shiga Uku, Mamma a cikin gidan ta!!! Dakyar cikin nauyin baki Momy ta amsa.
" Na'am Mamma kece tafe, lale marhaban sannu da hanya, kin kwaso rana, Bismillah Mamma ki ƙariso ki zauna."
Kallon sheƙeƙe Mamma ta yiwa Momy cikin masifa take kwaikwayon maganar Momy tace.
" sannu da zuwa Mamma kin kwaso rana, Bismillah ki ƙariso ki zauna!!! Riƙe sannun ki makira bana so, ina ruwanki da hanyar dana kwaso a kanki na taho da zaki min ƙirafi,. Koko ni makahuwa ce da bazan ga wajen zama ba sai kin gwada min, gidan kine kona ubanki ina dai gidan ɗana ne, ai dole na zauna ba tare da iso ba."
Shuru Momy tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa bata tankawa Mamma koda kalma ɗaya bace, Garko kuwa taɓe bakinsa yayi alamun kunfi kusa, shi kuwa khalil tamkar hadari haka ya haɗa fuskarsa a rayuwarsa ya tsani a ƙuntatawa Momy cike da masifa idanunsa sunyi jajur yace.
" Haba Mamma!!! Haba meye haka wannan ai cin mutumci ne, taya zaki samu mata tana zaune ki hauta ba tare da ta miki wani laifi ba, gaskiya wannan bai dac........"
Hanu Momy ta ɗaga masa tare da cewa
" Karna kuma jin muryarkae, baka da hankali ne, Mamman sa'ar kace, ina ruwanka da kai take" kallon Mamma tayi tace " kiyi hkr Mamma Allah ya huci zuciyarki."
" Ai da baki dakatar dashi ba, da kin barsa sai yazo ya dokeni, ya gani idan zai share dan ubansa, tambaɗaɗɗe marar mutunci, yo ni ina ma lissafi dakai a cikin jinina ne, kalilu, shege mai baƙar zuciya tunda ka shiga wannan tsinannan aikin ko zama cikakken Bayahude, to dan ubanka na dawo gidan nan da zama, sai ka shiryawa dukana wata rana tunda kace kai marar mutunci ne" tsagaitawa Mamma tayi da maganar sai kuma tasa kuka tana cewa " yanzu tsabar ba'a daukeni da mutunci ba, nan aka ajiye wasu ƙattin arna masu fuskar fir'auna, suka hanani shigowa gidan ɗana, wai harda bindiga aka ɗaura min saboda ba'a so nazo gara a haɗa baki dasu su kasheni, wai tsabar rainin wayo wai wannan ƙeƙashashen mai gadin ƙyauren naku ya kalleni ya kira ni mabaraciya, wallahi yau ɗin nan sai ya bar gidan nan Allah ya kawo Buba, zan nuna masa nice mai iko da gidan ba Buban ba."
Cike da takaici da haushi Khalil yake kallon Mamma gashi ba halin ya mata magana Momy ta hausa da faɗa, Garko kuwa dariya yasa tare da haurawa sama yana kiran " Mamma matsala" waje ta samu ta zauna tare da saka hanu a lalitar ta, ta ɗauko sigari da ashana, zata kunna, Khalil ya zaro ido tare da saurin ƙarisawa gabanta yana.
" Subahanallah!! Haba Mamma sigari kuma a cikin gidan nan, bazai yiwu ba, baki isa ba wallahi.!!!!"
" To fa ubana!!! Bazai yiwu ba kace, to danne ni ka ƙwace, kai ko ubanka fa bai Isa hanani shanta ba, bare kai, waima dakata, kalilu bala'i kake nema dani ne, sai famar shige min hanci kake, to wallahi zan facoka, ka fice daga idanuna na rufe yau naga tsiya, meye haɗin ka kaska da garahumi, nace na cireka cikin zuriata to meye ruwanka dani."
Tsuka Khalil yaja tare da saka hanunsa ya murɗe hanun Mamma ba tare da yayi magana ba, sigarin ya ƙwace da ƙarfi yana miƙewa tsaye yace.
" Na danne ki na ƙwace!!! Mamma sai kiyi abinda zakiyi, wallahi muddun zaki zauna a cikin gidan nan, to wallahi bazaki sha sigari ba, kuma na isa na dakatar dake, a ƙauyen ne zaki sha sigari ki zauna lafiya amma ba'a cikin gidan nan ba, ni ki daina zaro min idanu, ba tsoro zai bani ba!!!"
Yayi Maganar yana zarowa Mamma itama ido tare da ciro bindiga yace.
" Kuma kina magana zan ɗauke kanki da wannan bindigar kiyi kuma ki gani." Tsawa ya dakawa A'illo da Jummo yace " ku kuma bazaku nemi waje ku zauna bane kuka tsaya akan mutane kamar mashi."
Tura bakinta Jummo tayi tare da zama kusa da Mamma tace.
" Kiyi hkr Mamma Allah zai saka miki, wannan ai zalunci ne, wai kema Mamma dama kinsan wannan gidan na azzalumai ne shine kika taho dani, to wallahi ni bazan yadda da zalunci ba, kuma bazan yadda a zalunce ki ba, babu wani ƙato ko ƙatuwar da zai bani tsoro, har wani ciro bindiga ake, to wa yake tsoron mutuwa mtss............................"
😆😆😆😆😆 *GIDAN CAKWAKIYA KENAN, WACCE IRIN RAYUWA ZA'AYI NE A WANNAN GIDAN, KU BIYO NI DA GUDU DOMIN JIN INDA WANNAN CAKWAKIYA ZATA TSAYA*
*NAIRA 100 KACAL ZAKU TURO TA WANNAN ACCOUNT NUMBERN 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK, KO HOTON MTN CARD NA 100 TA WANNAN NUMBERN 08147537180 SANNAN KIYI SCREEN SHORT KI TURO SHAIDAR BIYA*
*PLEASE DAN ALLAH MASU VTU KU DAINA, BANDA VTU BANA SO, PLEASE KU DAINA*
🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️ *KUYI SAURI KU BIYA FREE PAGE YA KUSA ƘAREWA, ARAHA TAFI BASHI 100 NE KAWAI BABU YAWA INA ALFAHARI DAKU MASOYANA*
*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:20 PM] UMMU NASMAH❤️: 🧺🧺🧺🧺
*GELLE ƁINGEL*
🏺🏺🏺🏺
*Story*
*Rasheedat Usman*
*(Ummu Nasmah)*
*Littattafan marubuciya*
Sauyin Rayuwa
Nasmah Ko Nasirah
Sara Da Sassaqa
Indo A Birni
So Bai San Jini Ba
Akan ƴar uwata.
Hatsabibiya Saude
Ruɗanin Zuciya Biyu.
Doctor Hassan.
Ƙauyenmu.
And now *GELLE ƁINGEL*
*SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafin daga farkonsa har ƙarshen sa ga ƙawata *ZARAH ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
*FREE PAGE*
➰➰ *15 to 16*
Zaro idonsa Khalil yayi yana ƙarewa Jummo kallo, nuna ta da yatsa yayi yana zaro mata ido ciki tsawa yace.
" Keeee!!!! Dan ubanki waye ƙaton ko ƙatuwar, dawa kike, kai!!! Momy kina jin abinda wannan ajabon yarinyar take faɗa mai kama da Aljana."
Yayi Maganar yana ɗauke Jummo da mari, saurin dafe kuncinta tayi ganin wasu taurari masu bala'in haske sun shige ta gabanta, bai sauƙe hanunsa ba, itama Jummo ta ɗaukesa da mari, daga Mamma Momy har su A'illo a razane suka miƙe suna kallon Jummo, duk da Jummo ba yau ta saba dakuwa da maza ba amma wannan marin da tayiwa Khalil sanda ya razana kowa a cikin falon cike da tsantsar mamaki , khalil yake kallon ta, ji yayi tamkar ya ɗauketa da bindigar da take hanunsa, sai kuma yaji hanunsa ya masa nauyi, idan harma yace zai daki wannan yarinyar mai zai samu a jikinta ai sai dai ya ɓallata, amma tabbas wannan babu hankali a jikinta, haka kuma ya tausaya wa rayuwarta domin kuwa duk mace mai ɗabi'ar Jummo abun tausayi ce, tabbas akwai ƙauyanci da jahilci yana yawo a jikinta shi kuwa jahili babu abinda bazai iya aikatawa ba lallai wannan yarinyar tana buƙatar tarbiyya shikaɗai yake zancen zucin yayin da ya juya cikin ɓacin rai, Momy kan Jummo ta hau da masifa tamkar zata daketa cike kuma da ƙyamar ta, Mamma ta dakatar da ita.
" Kul kul!!! Kika saka hanu jikinta Zainabu, shi wanda ta mara ɗin ganin mutunci manya yake ai gara itama marinsa kawai tayi, shifa yanzu yaso kasheni Allah ya tsererar dani, waini dama Zainabu haka ake rayuwa a cikin gidan ki babu tarbiyya da kwaɓa eh lallai dole na samu zama a cikin gidan nan duk na gyara muku zama."
Momy cike da takaici tana hararar Jummo ta haura sama Zarah ta kwaɗawa kira, da sauri Zarah ta fito tana amsawa a bakin kofa ta samu Momy tsaye tace.
" Gani Momy."
" Kije ƙasa ki kaiwa Mamma ruwa da abinci, tana can tana mita ni bazan iya zan shiga ɗaki na kwanta."
Da to Zarah ta amsa Momy ta shige bedroom ɗinta, Zarah bakinta ta taɓe tana cewa.
" Har kin fara jin haushi kenan, hmmm!! Abinda kike min kema shi ake miki, ba gara Mamma bama DUK tsiyar da zata shuka miki, bazata azabtar da mutum da bauta ba, mtss ai naji daɗin zuwan Mamma gidan nan."
Ta ƙarisa Maganar tana sauƙa ƙasa, fuskarta cike da murmushi, jikin Mamma ta faɗa tana dariya tare da cewa.
" Oyoyo Mamman mu, oh tsohuwar nan, sai yau kika ga damar kawo mana ziyara munyi kewarki har mun gaji."
Itama dariya tayi tana riƙo hanun Zarah tace.
" Ke dai zara'u bari, gajiya nayi da zaman ƙauyen nace bari na dawo binni na ɗan sha jar miyya, yauwa ƴar albarka zara'u ba ƴar soyayyiyar kaza ne, a kawo mana mu ɗan goge bakin tunda wannan shegen mijin naki mai baƙin ran tsiya ya ƙwace sigarin."
Dariya Zarah tasa tare da cewa.
" Kai Mamma gidan son da daɗi, ai kuwa ba'a taɓa rasa nono a ruga, bari naje na kawo kaza kici harta isheki."
Wangale baki Mamma tayi tace.
" Ke dai sannu ƴar albarka, ai duk rugar da aka rasa nono bata amsa sunan ta ruga ba."
Dariya Zarah tayi ta cewa A'illo.
" A'a harda Hajiya A'illo ne, lallai zuri'a ta haɗu, wannan fa waye ce Mamma ban Santa ba."
Ta nuna Jummo, murmushi Mamma tayi tace.
" Au wannan Jummo kenan, jummon INNO da Mamma, tare muka zo jikar aminiyata ne, INNO, tare zamu zauna na aurar da abina a gidan nan."
Murmushi Zarah tayi bata fahimci Maganar Mamma na ta aurar da Jummo a gidan ba, ta matsa kusa da Jummo tare da cewa.
" Sannu da zuwa Jummo, kin min kyau."
Dariya Jummo tayi haka kawai taji Zarah ta shiga ranta, tana dariyar tace
" Nima kin min kyau, zaki koya min irin gayunki, ina son nima nake irin wannan kwalliyar taki.?"
Dariya Zarah tayi tace.
" Ai daga yau kin dawo ƙawata, zan koya miki, bari ma kiga naje na kawo muku abinci idan kunci sai na rakaki kiyi wanka na miki kwalliyar."
Dariya Jummo tasa tace.
" To meye sunanki?"
" Sunana Zarah amma ki kirani da AUNTY, tashi muje kitchen ɗin ki tayani kawo abincin."
Da to Jummo ta amsa tare da tashi suka shiga kitchen ɗin tare, murmushi Mamma tayi tare da jin Zarah ta ƙara kwanciya a ranta, cikin minti goma Zarah da Jummo suka fito da abinci tare da kazar da Mamma ke so, sosai suka gyara zama suka kwashi abincin, sai Jummo bata wani ci sosai ba, kasancewar ta wanda bata da yawan cin abinci bare kwaɗayi, bayan sun gama ne Zarah ta kama hanun Jummo suka haura bedroom ɗin da Sadiya ke sauƙa idan tazo, fallen zani Zarah ta bawa Jummo tace ta cire kayanta ta ɗaura babu musu kuwa Jummo ta cire tolet suka shiga, gashin kan Jummo dake naɗe timili guda, Zarah ta sunce take gashin ya zubo bayan, gashi ne mai tsayin gaske baƙiƙƙirin sai datti dake danƙare a cikin sa, shanfo ta ɗauka ta fara wankewa Jummo gashin sosai ta wanke gashin ya fita tas, sannan ta matsa mata makilin a sabon brush ta bata tace ta wanke bakin, tana tsaye take gwada mata yanda zata wanke, tsabar yalon da hakwaran Jummo sukayi sai da yayi jini wajen wankewa, alhamdulillah kuma haƙorin ya fara fita ba laifi, sannan ne fa Zarah ta fita tabar Jummo tayi wanka, bedroom ɗin ta ta koma da niyyar ɗaukowa Jummo kaya a cikin nata ta saka, a zaune ta samu khalil ya haɗa tagumi yayi shiru, kusa dashi ta zauna cike da nutsuwa tace.
" Ya khalil, meya sameka haka kayi tagumi cike da tunanin, madadin wannan tagumin ai gara ka dinga ambaton innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Sai Allah ya sanyaya maka zuciyarka, ya yaye maka damuwarka, tunda kaga dai ba kyau tagumi waima tukunna meya faru haka wannan tagumi Bana son ganinka cikin tunani mijina Please tell me."?
( Haka ake son mace ta kasance mai yawan nuna damuwarta ga mijinta idan ta ganshi cikin wani hali, tambayesa damuwarsa cikin hikima da iya zance, ina tabbatar miki, zai sanar dake matsalarsa.)
Numfashi Khalil ya sauƙe tare da kwantar da kansa a kafaɗar Zarah.
" My dear!! Tarin matsala zasu ƙaru a cikin gidan nan sakamakon zuwan Mamma ina gudun faruwar abubuwa da yawa nan gaba, bata ƙaunar Momy na tabbatar zaman Mamma cikin gidan nan matsalace ga Momy ko nace tashin hankalin ta, Mamma fitinanniyar tsohuwa ce wacce sam bata da fahimta, bansan taya zan fara fitar da Mamma daga cikin gidan nan ba, ta koma ƙauye, gashi tazo da wata tantiriyar yarinya marar kunya, kinsan yarinyar nan har marina tayi, amma na mata uzuri da alamu akwai jahilci a jikinta, domin baƙauyen mutum zai iya aikata ko wani irin aikin rashin hankali, shiyasa idan kika cewa balaraben mutum ɗan ƙauye, to kin gama masa zagin duniya tana buƙatar mai bata tarbiyya yarinyar."
" Hmmm!!! Ya khalil wace irin matsala kuma a tunanina babu wata matsala da Mamma tazo gidan ɗanta, ita dai Momy dole itace zatayi haƙuri da Mamma, Maganar ka maida Mamma ƙauye bai taso ba, Daddy ma ba yadda zaiyi ba, Ya khalil ka ɗauki komai da sauƙi sai yazo maka da sauƙi, yayin da kuma ka ɗauki abu da zafi, to da zafin zai tafi maka, ko yaushe kaine kake bani baki kana nuna min nayi haƙuri da Momy, to meyasa ita Momyn bazaka nuna mata tayi haƙuri da Mamma ba, haba ya khalil karka zamo mutum mai son kai mana, kaso mahaifiyarka fiye da mahaifiyar wani, wannan sam ba adalci bane, kayi tunani akan haka, ya khalil Maganar marin da Jummo ta maka kuma, dan Allah kayi hkr, bazance yarinta ke damunta ba, amma zance maka jahilci ke damunta kamar yadda ka faɗa, to ya khalil meyasa bazaka taimaka mata ba, wajen ganin ka inganta rayuwar ta, domin da alamu Jummo tana da basira idan Allah ya taimaka sai ta amfani al'umma da yawa, ka tallafa mata nima kuma ina da niyyar bata gudumowa."
" My dear, na sani nan gidan ɗan Mamma ne, ban miki musu akan haka ba, amma nina san abinda ke baki sani ba, wallahi ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba, ba zuwan Allah da Annabi Mamma tayi ba, tazo ne kawai domin ta tadawa da Momy hankali akan wata hujjar ta marar ma'ana wanda dalilin rashin jituwar Momy da Mamma yasa bana shiri da Mamma, ko shaƙuwa ta tsakanin kaka da jika babu tsakanina da Mamma saboda bana taɓa bari Mamma ta ciwa Momy mutunci muddun ina kusa, bazan juri ganin Momy cikin tashin hankali ba, dole ne Mamma ta koma ƙauye, da kike Maganar na taimakawa wannan yarinyar, ta wacce hanyar kike tunanin zan taimaka mata, ni da nake neman yadda zanyi su koma inda suka fito."
Numfashi mai nauyi Zarah ta sauƙe tare da ɗaura hanunta a cinyar khalil tace.
" Kayi hkr insha Allah babu wata matsala da zata faru a cikin gidan nan, idan ma kuma akwai ta, to na ɗauki alƙawarin dakatar da ita, ina tabbatar maka babu abinda zai faru, idan kuma har abinda kake gudu ya faru, to ka ɗaura laifin komai a kaina, zan dakatar da gabar dake tsakanin Momy da Mamma, na sanya soyayya da shaƙuwa tsakanin su, na ɗauki wannan alƙawarin, Maganar Jummo kuwa, ma yita wata rana, amma dai yanzu kamin alfarma ka yafewa Jummo marin da ta maka, sannan kuma ka saki ranki naga farin ciki da annashuwa a gareka, domin farin cikin ka ya fimin komai daɗi a duniya."
Ta ƙarisa Maganar tana murmushi tare da ɗan jawo gemun khalil alamun rarrashi, murmushi Khalil yayi tare da kwanciya yana jawo Zarah ta faɗo jikinsa rungumota yayi yana dariya tare da cewa.
" Tabbas samun mace ta gari irinki a wannan zamanin yana matuƙar wahala, a duk sanda na shiga damuwa kinsan yanda zaki sanya ni farin ciki, ke ta dabance a cikin mata."
Itama Zarah dariya tayi tare da haɗe bakin ta da nasa, a hankali ta lalumo harshen sa wani irin tsotsa take masa mai fitar da tunani, lumshe idanunsa khalil yayi yana jin wani munguwar feeling yana tsarga masa daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa, a hankali ya saka hanunsa ya tallafo kanta tare da aika mata nasa salon, tuni Zarah ta manta da Jummo na jiranta, ta Lula duniyar ma'aurata.
Jummo tafi awa ɗaya tana jiran Aunty Zarah shuru babu alamunta, tun tana zaune a ƙasan tayels ɗin sanyin ac na kaɗata, har bacci ya fara kwasarta tun tana gyangyaɗi harta silale ta kwanta, bacci ne mai nauyi ya dauketa sakamakon ac dake kaɗata dama kuwa Jummo gwanar son sanyi ne.
Mamma kuwa tana hakince cikin falon zaune tace bazata bar wajen ba har sai Daddy ya dawo ta kurawa tv idanu, tana kallon wasan kwaikwayo na Arewa24 Daɗin kowa, sai dariya take ita ɗaya tana Magana.
Garko dake zaune bakin bed ɗinsa yana buga game a wayarsa ne yaji wayar tayi ringin " *SADIYA* " haka ya gani rubuce, numfashi yaja yana yamutsa fuska ya ɗaga kiran tare da yin shuru daga can Sadiya ta fara magana cike da muryar kuka.
" Ya Garkuwa, wai kana nufin kace baka ga text ɗina bane, kayi shuru baka kiran ba, baka kuma min refly ba, ya kamata kazo mu san mafita."
" Idan naga