Showing 33001 words to 36000 words out of 93605 words

Chapter 12 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

ba tsoron Momy ba."

Shuru Aunty Zarah tayi tana kawar da kanta gefe tace.

" Na sani Momy bata da gaskiya, amma ke yanda kika ɗauko naki salon gaskiyar ne baiyi ba yazo da rashin kunya da neman tarwatsa farin cikin gidan nan.?"

" Hmmm!!! Aunty Zarah kenan meye ribata idan na tarwatsa muku farin ciki? Amma Aunty Zarah na tambaye ki, baki son a rusawa Momy farin cikin ta ko a rabata da ƴaƴanta? To meyasa ita kuma Momy take son ta raba Mamma da ɗanta bakiyi yunƙurin hanata ba, Saboda ita Mamma bata da gata ko bata buƙatar farin ciki ko, Momy kawai itace mai gata meyasa Aunty Zarah."?

Shuru Aunty Zarah tayi jikinta yayi sanyi tabbas duk maganganun Jummo ta fita gaskiya, shuru tayi bata amsawa Jummo ba, murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Na sani zakiji kunyar amsa min wannan tambayar domin kuwa amsar bazata wuce son Zuciya ba, da neman gindin zama a wajen Momy, Aunty Zarah kema fa Momyn nan bakiji daɗin ta ba, da kike bin bayanta ke kanki bata ƙi ace yau ta koreki kinbar gidan nan ba, komai cikin ƙiyayya take miki shi a cikin gidan nan baki da ƴancin kanki a gidan mijinki sai abinda Momy taga dama kullum cikin zaginki take da aibata ki, amma yau ita kike bi kike ƙoƙarin ture gaskiya, ki sani duk hanyar da zaki bi idan ba ta gaskiya bane bazaki taɓa ganin dai-dai ba, kiyi tunani akan maganata ba rashin kunya ko gori na miki ba, na tuna miki abubuwan da kika manta ne."

Jummo tana gama faɗin haka ta juya ta fice daga kitchen ɗin, Aunty Zarah sosai jikinta yayi sanyi jinginuwa tayi jikin bango tana tunani akan maganganun Jummo, tabbas gaskiya ta faɗa mata numfashi ta sauƙe tare da cigaba da aikinta.


Ita kuwa Jummo bedroom ɗin Mamma ta nufa ta sameta zaune sai busa sigari take, haɗa fuska Jummo tayi tana tuno maganganun yaya khalil, zama tayi tare da cewa.

" Mamma dan girman Allah ki yiwa Allah ki rage shan wannan sigarin, ki daina shanta kamar ruwa, ki dinga sha sau ɗaya a rana, babu kyau fa Mamma kuma kin sani, sannan tana lalatawa mutum kayan cikin sa."

Kallonta Mamma tayi tare da cewa.

" Eyyye!!!! Sannu malama Jummo yaushe kuma kika fara karatu, to bazan daina ba, bari kiji da sigari tana haifar da matsala da tuni ta kasheni tunda tun kafin a haifi ubanki nake sha, ba fa zan daina shanta ba, babu uban da ya isa ya hanani, ya lalata min kayan cikin mana ina ruwanki."

" Mamma da ruwana mana idan kika shiga cikin wani hali ai nima na shiga Uku."

Hararar Jummo Mamma tayi tare da cewa.

" To ki zubar da ruwan naki kinga shikenan mun rabu, ni fa kin isheni."

" Mamma dan girman iyayenki ki ajiye sigarin nan haka."

Kashe sigarin Mamma tayi tare da cewa.

" To mayya na ajiye karki cinye ni dan Allah."

Murmushi Jummo tayi tace.

" Yanda namanki yake da ɗaci Mamma ai bazan iya cinye ki ba."


A hankali yake sauƙowa daga step ɗin jikinsa a mungun sanyaye tamkar wanda aka yiwa mungun duka, daining ya nufa ya zauna tare da cewa Momy da Daddy dake zaune.

" Good morning."

Daddy ne ya amsa da

" Morning My son, lafiya na ganka cikin sanyin jiki haka."

Momy tace.

" Ai kuwa nima tambayar da zan masa kenan."

Murmushin yaƙe Garkuwa yayi tare da cewa.

" Bana jin daɗi ne Daddy kaina ke ciwo."

" Subahanallah!!! Kasha magani."? Cewar Daddy.

Kansa Garkuwa ya ɗaga alamun eh, ya khalil ne ya sauƙo shima ya zauna yana gaishe da su Daddy hanu ya miƙawa GARKUWA yana cewa.

" Bro wai yaushe zaka koma kan aikinka ne, naga yau satina biyu da dawowa cikin gidan nan har zan koma jibi banga kana da niyar komawa ba."

Numfashi Garkuwa ya saki tare da cewa.

" Bros sai next week zan koma, amm Bros yaushe ne kam zaka dawo min da wannan kuftar da ka tafi da ita."

Murmushi khalil yayi tare da cewa.

" Oh Bro kai dai baka mantuwa insha Allah zan dawo maka dashi next time idan zan dawo hutu, wai ina Zarah tazo ta haɗa mana abincin nan mana so fa nake na fita da wuri."

Bai rufe bakinsa ba sai ga Zarah seving ɗin kowa tayi sannan ta saka nataa, har sun fara cin abincin sannan Jummo da Mamma suka zo, Jummo Daddy ta gaishe CIKIN ladabi amsawa yayi fuskarsa a sake yana cewa.

" Jummon INNO, INNO dai tayi kewarki sosai gaskiya nayi mamaki ma da ta iya bawa Mamma kyautarki."

Dariya Mamma tayi tare da cewa.

" Yo kaji min buba da wani zancen, ai kasan INNO babu abinda bazata iya mallaka min ba, ko ka manta tsakanin mune."

Dariya Daddy yayi tare da girgiza kansa yace.

" Ina kuwa zan manta Mamma, Mamma ya dai yanayin gidan da fatan dai kina jin daɗin zaman gidan."?

Murmushi Mamma tayi tace.

" Babu komai Buba gida alhamdulillah ina jin daɗi ba laifi amma dai a fita a hanci na idan ba haka ba zan yiwa matarka tsiya."

Khalil ne ya ɗago kansa ya kalli Mamma numfashi ya sauƙe tare da kawar da kansa shi kuwa Garkuwa baima kula sha'aninsu ba, damuwarsa ne kawai a gabansa, Momy cike da baƙin ciki ta kalli Mamma ta rasa me yasa Mamma ta dami rayuwarta, kanta ta mayar ta cigaba da cin abincin ta, murmushi Jummo tayi tare da cewa Momy.

" Ina kwana Momy?"

Wani irin mungun kallo Momy ta wurga mata tare da cin abincin ta bata amsawa Jummo gaisuwar ba, Daddy cewa Mamma yayi.

" Kiyi hakuri Mamma insha Allah za'a gyara."

Khalil shine ya fara tashi daga daining ɗin yana cewa Jummo.

" Jummo bari idan na dawo sai na gwada miki yanda zakiyi Amfani da wayar ko."

Da to Jummo ta amsa tare da adawo lafiya, shima Daddy a dawo lafiya ya masa sannan ya fita, Zarah tabi bayan sa, Garkuwa yana zaune ya kasa cin abincin yaji ƙarar shigowar text ɗago wayar yayi tare da buɗe saƙon.


*_ALBISHIR MALAM GARKUWA A YANZU HAKA INA NAN TSAYE ƘOFAR SHAGON UBANKA ALHAJI BUBA GARKO DA WANNAN VIDEO SHINE MUTUM NA FARKO DAYA DACE YA FARA GANI_*

Wani irin zabura Garkuwa yayi gumi na keto masa ya furta.


" *Whatttt* ................"










Wannan littafin na kuɗi ne karki karanta min littafi ba tare da kin biya ba 08147537180







*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *Wannan littafin na kuɗi ne bisa amana idan kin san baki saya ba karki karanta min littafi kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba 08147537180*.




*Payment group Only*



➰➰ *33 to 34*



Ɗaga idanun su Daddy sukayi suna kallon sa cike da tsoro, Momy ne ta furta.

" What kuma!!! Meya faru waye ya mutu."?

Cike da gigita Garkuwa ya sharce gumin sa, zuciyarsa na cinkewa cike da matsanancin tsoro, muryar sa na rawa yace.

" Ba... Ba... Ba... Bakomai Ibrahim ne ya kirani wai Asiya bata da lafiya suna medical center tana cikin mungun yanayi."

Ya ƙarisa Maganar yana runtse idanunsa zuciyarsa na harbawa, numfashi Daddy ya saki tare da furta.

" Subahanallah!!! Lallai Asiya tana cikin jarabawa Ubangiji Allah ya bata lafiya, ni bara na fita kasuwa."

Saurin dakatar da Daddy Garkuwa yayi yana cewa.

" A'a Daddy am karka fita ya kamata yau ka zauna da Mamma kuyi hira tunda Mamma ta dawo gidan baku sami zama kun gana kunyi hira sosai ba, ya kamata yau ka zauna, idan yaso ni zan fita kasuwar."

Kallon sa Daddy yayi cike da mamaki yace.

" What!!!! Na zauna a gida kace, yaushe ka fara son fita kasuwa Garkuwa kai da ka tsani kasuwa yau kuma kake cemin na zauna kaika fita, no bazan zauna ba fita zanyi saboda ko da na barka ka je kasuwa bazaka min abinda nake so ba, so na riga na ware ranar da zan samu zama da Mamma ranar Friday, ka bari kawai zan fita."

Dafe goshin sa Garkuwa yayi cike da tsantsar tashin hankali, idan har ya sake Daddy ya fita kasuwa yau ya shiga Uku kashin sa zai bushe asirinsa ya tonu, " ina bazai yiwu na bar Daddy yaje kasuwa ba" saurin kallon Mamma yayi yace.

" Am Mamma ki yiwa Daddy magana mana ya kamata yau ku samu zama da Daddy kuyi hira yaji matsalarki, sannan ki faɗa masa damuwarsa, ni zanje ni kasuwar na zauna Allah Daddy duk abinda zakayi nima zanyi shi normal please Daddy."

Momy zirawa GARKUWA idanu tayi cike da zargin sa, yanda ya dage sai famar magiya yake taɓe bakinta tayi, Daddy ne yace.

" Garko anya lafiyar ka kuwa, waima kana da gaskiya kuwa, ka dage lallai karna fita, to me zai faru idan na fitan, kai bana son iskanci da zancen banza babu abinda zai hanani fita."

Idanunsa Garkuwa ya rufe tare da cije leɓensa, wani irin takaici yake ji, ina ma zaiga wannan mai ƙoƙarin saka rayuwarsa cikin tagayyara wallahi da babu abinda zai hana ya kashesa, Mamma ne ta ce

" Buba dan kawai yace ka zauna muyi hira shine kake masa wannan masifar har kake kiran maganar sa da zancen banza, zancen nawa ne na banza Yaro yana son kayi abin arziki ka samu lada kana kaucewa, shifa wannan yaron yafi dukkan yaran ka nutsuwa da hankali har uwar tasu, ita waccar Ashfarta take kowa da suna ka kaita can wata uwa duniya karatu inda babu mai kwaɓa sai yarinya ta lalace kuzo kuna danasani, to Buba nace yau babu inda zaka fita, ka zauna ina da magana da kai, kai Garko kaje kasuwan shi BUBA nace yau kan bazai fita ba."

Numfashi mai nauyi Garkuwa ya saki yana dafe ƙirjinsa tare da furta (Alhamdulillah!!) A cikin zuciyarsa, murmushi ya saki tare da cewa Mamma.

" Ke kin fahimce ni Mamma, ina son Daddy shima ya huta, ni gabaki ɗaya wannan satin ma zan ke fita kasuwar tunda ina hutu ba aiki nake ba, sai naje masa kasuwar dukka wannan satin."

Murmushi Mamma tayi tace.

" Allah dai ya maka albarka, muje Ina da magana da kai BUBA."

Tashi Daddy yayi yana rankwashin kan Garkuwa yace.

" Zaka dawo ka sameni ne ja'iri"

Dariya Garkuwa ya yiwa Daddy, suka wuce shida Mamma itama Jummo tashi tayi tabar wajen, Momy ne ta kama kunnen Garkuwa ta murɗe tare da cewa.

" Wannan dagewa da marairaicewa da kayi ba banza bane akwai dai lauje cikin naɗi."

Dariya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Babu wani lauje cikin naɗi, dan kawai ɗa yace ubansa ta huta shikenan sai ya zamo da biyu, Momy akwaki da fassara."

Murmushi Momy tayi tace.

" Hmmm!!! Kuma halinka ne ban sani ba Garkuwa, sai ka tashi ka tafi ai tunda ka yi Nasara."

Dariya Garkuwa yayi yana miƙewa tsaye tare da ɗaukar wayarsa ya fice yana dariya da adawo lafiya Momy ta masa sannan ya fita itama Momy nata bedroom ɗin ta shige tare da ƙwalawa Zarah kira Zarah da tun ɗazu ta shige bedroom ɗin ta ne ta amsa tare da fitowa ta shiga cikin bedroom ɗin Momy tana zaune bakin bed dinta ta sameta a ƙasa Zarah ta zauna tare da cewa.

" Momy gani."

Murmushi Momy tayi tare da gyara zamanta tana kwantar da murya tace.

" Zarah so nake mu haɗa kai dake, domin kuwa a yanzu a cikin gidan nan na fahimci bani da kowa sai ke, sai yanzu nake danasanin abubuwan da na miki marassa daɗi, ban gane hakan ba sai yanzu da Mamma tamin nasan ina ƙuntata miki, ki yafemin Zarah."

Murmushi Zarah tayi kanta na ƙasa tare da jin wani farin ciki ya sauƙa mata, taji daɗi sosai da Momy ta fahimci abubuwan da take mata basu da kyau, numfashi Zarah ta sauƙe tare da cewa.

" Momy dama ban taɓa ƙullatanki a raina ba, dan haka na yafe miki Momy naji daɗi sosai da kika gane gaskiya."

Murmushi Momy tayi tace.

" Ba komai Zarah, zanyi Magana insha Allah a cikin satin nan za'a kawo ƴar aiki, mai wanke wanke da shara da kuma gyaran ɗaki girki kawai zaki dinga yi a cikin gidan nan, kinga ai aikin ya ragu miki."

Sosai Zarah tayi farin ciki da wannan aikin da aka rage mata tana dariya ta yiwa Momy godiya, ba komai Momy tace tare da ce mata zata iya tafiya cike da farin ciki Zarah ta koma bedroom ɗin ta dama Momy ce kawai matsalar ta a gidan gashi kuma yanzu Allah ya kawo mata karshen matsalar ta.


Momy bayan fitar Zarah murmushi ta saki tare da furta.

" Da wannan zan fara yaudarar ki Zarah har sai kin amince dani kin shiga jikina Kafin na bullo miki da ƙudiri na wanda dole sao kin tayani yaƙi babu makawa."

Ta ƙarisa Maganar tana sakin murmushi mai sauti.

Shi kuwa Garkuwa cike da tashin hankali yake dreving, ya rasa ta ina zai fara solving ɗin matsalarsa, domin kuwa yaga alamun wannan video ɗin yana ƙoƙarin zamo masa barazana ga rayuwar sa, da wannan tunanin ya ƙarisa kasuwar, a ƙofar tafkeken makay ɗin mahaifin nasa ya yi parking tare da ɗaga kansa ya kalli serying boad ɗin wanda akayi rubutu da manyan baƙi, *ALH BUBA GARKO SUPER MARKET* numfashi ya sauƙe yana raba idanun ta ina zai za'a ɓullo kawowa Daddy saƙon video ɗin sai dai shuru harya shiga ciki baiga saƙon komai ba.

Shuru shuru har dare yayi suka rufe shago babu saƙo babu alamar saƙon, harya dawo gida kuma alhamdulillah duk aikin da ya dace Daddy yayisu a shop ɗin Garkuwa yayi su, gida ya dawo a gajiye.

Garkuwa yana kwance misalin goma da rabi na daren sai yaji shigowar saƙo saurin dubawa yayi.

*_KAYI MAMAKIN KO, DA SAƘON BAI SHIGA HANUN UBANKA BA, TO KARKAYI TUNANIN KA TSALLAKE WANNAN TARKON DOMIN KUWA TARKON GABA BAZAKA SAN INDA ZAMU ƊANASA BA, INA SANE NA FASA BAWA UBANKA WANNAN VIDEO ƊIN SABODA NASAN HANKALINKA ZAI TASHI KAYI DUK YANDA ZAKAYI KA DAKATAR SHI DAGA FITOWA KASUWA, KUMA NASAN KO RANTSEWA NAYI BAZANYI KAFFARA BA, YAU BAKA BAR UBANKA YA FITA KASUWA BA, TO BA DABARAR KA BACE TASA VIDEO ƊIN BAI SHIGA HANUN SA BA, RA'AYINA NE KAWAI YASA NA FASA DA NASO VIDEO ƊIN NAN SAI YA SHIGO HAR CIKIN GIDAN KU A YAU SAI DAI BANSO HAKAN BA, KA KIYAYE TARKON GABA DOMIN KUWA ZUWAN SA BAZAI MAKA DAƊI BA_*

text ɗin Garkuwa yabi da kallo yana tunanin wani mataki zai ɗauka, domin gano wanda ke masa wannan barazanar " *ABDUL JAY* " GARKUWA ya furta " shine kawai zai iya gano min ko wanene" ɗan cije bakinsa yayi tare da ajiye wayar ya miƙe ya shige tolet.

Gyara zamanta Safreena tayi ta kalli Zee tace.

" Na tabbata yanzu Garkuwa zaiyi yunƙuri gano wanda ke masa barazana yana da bala'in wayo zai iya gano mu, wani mataki kika dauka domin kaucewa gano mu a wajen Garkuwa."

Murmushi Zee ta saki tare da cewa.

" Ban shiryawa wannan mission ɗin ba, sai da na toshe dukkan wani Hanyar da Garkuwa zai gano kina raye, dalilin kuwa bana son ya gano mu yanzu har sai mun jijjiga sa ya wahala ya galaibata kafin mu bayyana masa kanmu muda kanmu, karki damu Garkuwa bazai taɓa gane mu ba duk wayonsa."

" Hmmm!!! Shikenan Zee, na yiwa Garkuwa wani mungun shiri wanda zai girgizasa fiye da wannan girgizar da yayi, yanzu abinda zamuyi muyi amfani da layin wayarsa wajen gani dukkan wani motsinsa, mu dinga bibiyar duk wani kiran da zaiyi daga nan zamu gano duk wani binciken da zaiyi akan mu, mu kuma sai mu lalata masa dukkan wani shirinsa akanmu."

Murmushi Zee ta saki tare da cewa.

" Kin yiwa Abdul wanka ne Yakamata fa muje mu taro su Baba sun kusa sauƙa."

Murmushi Safreena tayi tare da cewa.

" Eh na shirya sa tun ɗazu amm dan Allah Zee karki sanar dasu Baba da Mama fansar da zan ɗauka idan Baba yaji zai hanani, tunda kinga cewa yayi na manta da Garkuwa a rayuwata, ni kuma bazan iya hakan ba dan Allah muyi komai cikin sirri ba tare da sanin su Baba ba."

Numfashi Zee ta saki tare da cewa.

" Karki damu Safreena bazan taɓa bari Baba susan abinda muke ba, na sani muddun Baba ya sani zai mana faɗa sannan ya hana mu, ni kuma bazan iya ganin Garkuwa yana farin ciki ba, bayan ke ya kassara miki rayuwa insha Allah har mu gama ɗaukar fansar mu Baba bazai sani ba."

" Zee tabbas ke Aminiya ce ta gari ina jin daɗin zama dake Saboda kina ƙaunar dukkan farin ciki na, kina ɗaukar damuwata tamkar damuwarki, iyayenki sun rungumeni sun ɗaukeni ƴarsu bani da banbanci dake a wajen su sun mantar dani rashin iyayena, a wannan lokacin samun Irin Ahalinki yana wahala, na godewa Allah daya suturtani da samun wasu iyayen nagari bayan na rasa nawa."

Murmushi Zee tayi ta dafa kafaɗar Safreena tace.

" Babu godiya tsakanina dake Safreena, mun zamo Jini ɗaya yanzu ahali guda zan iya komai domin cikar muradinki..........."






*INA NEMAN AFUWAR KU YAU NA MUKU READMORE KADAN WALLAHI YAU BANJIN DAƊI NE KUYI HKR*




*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *Wannan littafin na kuɗi ne bisa amana idan kin san baki saya ba karki karanta min littafi kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba 08147537180*.




*Na gode ƙwarai da gaske tabbas bani da bakin muku godiya ƴan uwana na cikin wannan group ɗin, ina mungun jin daɗin comments dinku kuna ƙara min ƙwarin gwiwwa Sosai ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login