Showing 42001 words to 45000 words out of 93605 words

Chapter 15 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

yana zaro rafar dubu hamsin ya miƙa mata ya cigaba da cewa.

" Yau kinyi kyau sosai ga wannan ki sayo kayan kwalliyar da zasu ƙara miki kyau, ina fatan dai har yanzu kina son Garkuwan ki, domin a yanzu a shirye garkuwa yake da karɓar Aishan sa a matsayin Mata, zaki Aure ni Jummo."

Kamar sauƙar aradu Jummo taji maganganun sa, murmushi ta saki kanta na ƙasa zuciyarta cike da farin ciki, ganin tana murmushi yasa Garkuwa zare wayarta daga hanunta " infinix hot9 plus, Wannan wayar ai ta miki ƙarama, dole na sauya miki waya" yayi Maganar yana saka numbern sa plashing ɗin wayarsa yayi sannan ya danƙa mata wayar a dawo lafiya yace mata ya shige yana murmushi, murmushi Jummo tayi tare da bin bayan sa da kallo cike da matsananciyar soyayyar sa harya ɓacewa ganinta murmushi tayi tare da ficewa motar meenat ta hango ƙofar gidan nasu, buɗe motar tayi ta shiga tana dariya.

" Ja mota muje Malama."

Motar meenat taja tana duban Jummo, sun ɗan yi nisa da tafiya meenat ta juyo tana kallon Jummo tace.

" Hajiyata, wai ya naga sai famar murmushi kike tamkar wacce kikayi tsintuwar saurayi meye sirrin.?"

Dariya Jummo tasa har dimple ɗinta yana lotsawa tace.

" Shegiya Uwar ƙwaƙwaf ke dai akwai ki da hasasho muradin mutum, babbar tsintuwar saurayi nayi, Meenat yau dai Ya Garkuwa na ya furta min yana sona zai Aure ni."

" Wow!!!! Congratulations ƙawata, kai Masha Allah, dama ai na faɗa miki mai haƙuri yana tare da Nasara dole ne dama ya Garkuwa ya soki, domin kuwa samun dirarriyar mace tamkarki abune mai wahalar gaske, ƙawata kema fa dole sai kin ja masa aji kafin ki amince, shima yaji yanda kikaji, amma dai bari mu koma gida na ƙarisa miki sauran karatun."

Dariya Jummo tasa tare da cewa.

" Haba dai ƙawata!!! Dama haka kawai zan amince masa dole nima sai na rama,ke nifa sai ma tukunna na jarabasa kafin na amsa masa, yanzu wani makay zamuje.?"

" Kina burgeni ƙawata domin kuwa kin iya takunki, mtss ina ga Alhusain zamuje."

Meenat tayi Maganar tana ƙara gudun motar.

A Alhusain SUPER MARKET sukayi parking tare da fitowa suka nufi cikin SUPER MARKET ɗin, da ɓangaren takalmi suka fara kafin suka nufi fannin turaruka, Jummo tana cikin tafiya taji an bigi kafaɗarta wayar ta da jakarta ya faɗi ƙasa, cike da ɓacin ran wani makahon ne zai bige mutum Jummo ta ɗago kanta, idanu biyu suka haɗa da Safreena wani irin bugawa da ƙarfi zuciyoyinsu yayi a tare, Safreena ne tayi saurin cewa.

" Kiyi haƙuri dan, wallahi ban lura dake bane yaro ke min kuka duk ya gigitani sorry."

Shuru Jummo tayi sai cewa tayi.

" Babu komai ƴar uwa" Abdul dake kafaɗar Safreena yana ta ihu ta kalla tare da sunkuyawa ta ɗauki jakarta da wayarta hanunta ta saka ta amshi Abdul daga hannun Safreena tare da cewa.

" Meya sameshi yake wannan kukan haka gashi kyakkyawa ɗanki ne?"

Ɗan murmushi Safreena tayi tace.

" Ehh ɗana ne, rikici kawai yake ji dashi."

" Ayya yi shuru kaji beautiful boy, ko dai Momy ne ta mintsineka, nasan dai baza kayi kuka haka kawai ba, rabu da Momy zamu rama."

Dariya Safreena tayi haka kawai taji Jummo ta burgeta, yanda take rarrashin Abdul Jummo tambayarta tayi.

" Ƴar Uwa menene sunan sa?"

" Abdul!!! Ni kuma Safreena, kefa.!!!"

" Ni sunana Jummo."

Murmushi safreena tayi tare da cewa.

" Nice name kin burgeni sosai baki da girman kai, zamu iya ƙulla abota."

" Ƙwarai kuwa Ƴar Uwa kin burgeni sosai nima."

Dariya dukkan su sukayi sannan sukayi exchange ɗin Number, Zee ce ta iso wajen tare da cewa Safreena muje, karɓar Abdul tayi sukayi sallama da Jummo suka tafi.



Suma su Jummo basu wani juma ba a cikin SUPER MARKET ɗin suka fito.




✨✨✨✨✨✨✨✨✨



Runtse idanunsa yayi yana hango ta cikin idanun nasa, murmushi ya saki tare da furta.

" Ashe haka take da kyau tabbas na kusa asara samun mace irinta a yanzu zaiyi matukar wahala, idan har na sameta a matsayin Mata tabbas na dace."

Buɗe idanunsa yayi yana murmushi tare da juyawa daga kujerar yana lilo da ƙafarsa, Shagari ne ya turo door ɗin office ɗin ya shigo da sallama, amsawa Garkuwa yayi yana cewa.

" Yaushe jirgin ka ya sauƙa."

Zama Shagari yayi tare da cewa.

" Tun ɗazu, meya samu naga sai murmushi kake."


Dariya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Hmmm!!! Abokina yau naga matar AURENA."

Zaro idonsa Shagari yayi cike da matuƙar mamaki yace.

" Whatttt!!! Matar Aure yau kai da bakinka kake kiran ka samu matar Aure, waye wannan haka wacce ta cire tuta."

Murmushi Garkuwa yayi tare da cewa.

" Ina tunanin a yanzu lokaci yayi da ya kamata na watsar da Rayuwar bariki, nayi Aure, hmmm Jummo itace macen daya kamata na samawa ƴaƴana a matsayin Uwa saboda tana da kamun kai, macece da babu ruwanta da maza, bata taɓa zina ba, ita ya dace na aura.!!"

Numfashi Shagari ya saki tare da cewa.

" Allah Sarki Safreena ita naso ace ka aura a matsayin matar ka ta Aure domin kuwa ta soka tsakanin ta da Allah, ka lalata mata rayuwarta ba tare da saninta ba, kaine ka saka mata ƙwayar gusar da hankali sannan ka lalata mata rayuwa daga baya Soyayyar ka tasa ta amince da kai, naji baƙin cikin mutuwar Safreena na."

Kansa Garkuwa ya dafe idanunsa sukayi jajur ɗagowa yayi ya kalli Shagari tare da cewa.

" Na fika jin baƙin cikin mutuwar Safreena, wallahi Shagari koda na lalata rayuwar Safreena ina sonta saboda nasan ba mutuwar banza bace naso auren ta, sai dai mutuwa tamin yankan ƙauna, na rasa meya ƙona gidan su Safreena da ahalinta gaba ɗaya, hmmm!!! Duk sanda na tuno Safreena sai naji raina ya baci hankalina ya tashi, ta mutu da cikana a jikinta duk da naso ta zubar da ciki tace min bazata ƙara saɓawa ubanginta a karo na biyu ba, Allah Sarki kamar tasan mutuwa zatayi Allah ya jiƙanki Safreena ya yafe miki kuskurenki.................."









*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *Wannan littafin na kuɗi ne bisa amana idan kin san baki saya ba karki karanta min littafi kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba*.



*Payment group Only*



➰➰ *39 to 40*



"What!!! Matsiya!!! Matsiya fa kika ce mata Zarah!!! Anya kina da hankali kuwa yau a jikinki? Jummo ce fa, nake tare da ita ba wata ba, waima dakata duk meye na tada jijiyoyin wuya haka, meya ɗaga miki hankali dan kawai kin ganni da Jummo kin dai san ba yau na fara zama da Jummo a cikin falon mu ba, ko baƙuwa ce jummon? to me zai dameki, Please karki kuma ce mata matsiya, idan kuwa kika Kuma wallahi sai na ɓata miki rai."

"Na tada jijiyoyin wuya!!! Nace na tada jijiyoyin wuyan!! Ƙarya nayi ba matsiyaciyar bace, Khalil nace mata matsiya ko zaka ɗauka mata fansa ne? Ehh Lallai da gaske Jummo ta gama da kai Khalil, wai wannan wace irin ƙaddararriyar yarinya ce, to wallahi muddun baka fita a harkar ta ba, ka daina kulata ba, wallahi yanzu zamu saka ƙafar wando daya da kai, masifa da bala'i shine zaike wanzuwa a tsakanin mu, ni zaka munafurta kake Soyayya da wannan abar Wallahi bazai yiwu ba, kuma Wallahi bazaka kwana a cikin ROOM ɗin nan ba, ko ance maka bata sanar dani kana sonta bane itace da bakinta ta faɗa min!!!"

" Hmmm!!! Sai yanzu na fahimci inda haukar taki ta dosa, Oh ke wai yanzu wannan haukar da jahilcin da kikeyi duk akan kishi ne, Oh ke taki kalar kishin kenan na hauka, Zarah idan zan ƙara auren zaki hanani ne, nace zaki hanani ne, baki isa ba, ni ba irin waɗannan sususun mazajen bane, shasha, zan fita daga bedroom ɗin nan ne na kwana a falo ba dan saboda shakka ko tsoron ki ba, zan fita ne saboda rantsuwar da kikayi."

Ya ƙarisa Maganar yana ficewa daga room ɗin tsuka Zarah taja tana riƙe kunkumi, sosai hankalinta ya tashi, amma duk yanda za'ayi bazata taɓa yadda mijinta ya Auri Jummo ba, tsuka taja tana rufe room ɗin ta koma ta kwanta.

Ita kuwa Jummo ta kai kusan sha ɗaya na dare tana assignment ɗin kafin ta shige bedroom ɗin ta harta yi shirin bacci cikin riga da wando, tare da Kwanciya gefe A'illo, Sadiya tana can dungun bed ɗin sai famar yamutsa fuska takeyi, tana chat, Jummo wayarta ta ajiye tare da duban A'illo tace.

" Me kikeyi haka har yanzu bakiyi bacci ba?"

" Ba komai Aunty idanuna ne kawai suka bushe, hankalina yana tashe da lamarin gidan nan sai nakeji a jikina tamkar wani mummunan al'amari zai faru da Mamma, Jummo ni fa nayi wani tunani mai zai hana mu haƙura da zaman wannan gidan mu koma ƙauye hakan zaifi mana kwanciyar hankali."

Murmushi Jummo tayi tare da kallon Sadiya da tayi shuru alamun maganganun su take saurara, numfashi ta sauƙe tare da juya harshe da fullanci tace.

" Ki kwantar da hankalin ki A'illo babu wani abu mummuna da zai faru da Mamma ke dai ki cigaba da mana addu'a insha Allah zamu samu mafita, kiyi baccin ki kinga gobe akwai school."

" Shikenan Allah ya mana mafita mai kyau" da ameen Jummo ta amsa tana jiyo ringin wayarta baƙuwar Number ta gani hanu tasa ta ɗaga kiran.

" Amincin Allah ya tabbata a gareki, har yanzu bakiyi bacci ba?"

Jin Muryar Ya Garkuwa yasa Jummo sakin murmushi ta furta.

" Ya Garkuwa, kaine.?

Saurin ɗago kanta Sadiya tayi jin Jummo ta ambaci sunan Garkuwa, tana dubanta cike da mungun mamaki sai kuma taji wani kishi ya taso mata shuru tayi tana jiran taji me Sadiya zatace.

" Ni ne kinga baƙuwar Number ko? Na kasa bacci ne sai tunaninki nake, A'ishah sonki ya min mungun kamu, anya kuwa kina sona kamar yadda nake sonki.?"

Murmushi Jummo ta saki tare da cewa.

" Ya Garkuwa kaima ka sani Soyayyar ka bata yanzu bace a cikin zuciyata, Ya Garkuwa ina sonka fiye da yadd............"

Wafce wayar Sadiya tayi tare da furta.

" Kina sonsan ubanki, to dan ubanki ruwa ba sa'an kwando bane, Garkuwa yafi ƙarfinki kisha ruwa dai-dai cikin ki Wallahi" wayar ta kara a kunnen ta tare da cigaba da cewa " Kai kuma na dawo kanka!!!! Ni zaka munafurta, wai meyasa jarabar mata ya maka yawa ne, kai ko wace mace kana so, to baka isa ba wallahi dani kaɗai zakayi rayuwa, ka jawa wannan jakar ƙauyen kunne ta fita a harkar ka, idan ba haka ba wallahi sai na illata rayuwarta."

Murmushi Garkuwa yayi tare da juyi a bed ɗin da yake cike da kasalalliyar muryar sa yace.

" Sorry Sadiya, daina mini tsawar haka ko, ki bawa mai wayar wayarta bani da lokacin ɓatawa dake a yanzu muryar matata kawai nake buƙatar ji."

Wani munduƙun baƙin ciki Sadiya taji ranta ya baci tace.

" Ya Garkuwa ni kake cewa baka da lokacin ɓatawa a kaina, nine fa Sadiya.?"

" Keee!!! Sadiyan fa ai na ganeki, kinga duk haukar da zakiyi ki jira har na dawo sai min, amma dai yanzu bata wayarta."

Runtse idanunta Sadiya tayi, tana jin baƙin ciki, Jummo murmushi ta saki tare da wafce wayarta daga hanun Sadiya tace.

" Yi hkr farin ciki na, wannan marar lissafin ta ɓata min rai, zamuyi waya da safe, kai dai ka kwantar da hankalin ka ka samu nutsuwa, ina dai-dai da haukar ta."

Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Nasan wacece ke, na kuma san zaki iya da ita, kiyi bacci mai daɗi, I love You."

Kashe kiran Jummo tayi tana murmushi ta dubi Sadiya tare da cewa.

" Daɗina da jaki duk yanda akayi dashi sai yaci kara, karki ƙara kuskuren waftar wayata daga hanuna bare kuma ki kuma zagin ubana yanzu zan miki afuwa saboda wannan shine karon farko, idan kuma kika kuma Wallahi saina banbance miki tsakanin aya da tsakuwa mtsss."

Tsabar mamaki da tashin hankali kasa Magana Sadiya tayi a hankali ta sidaɗe ta zauna a ƙasa hankalinta a matuƙar tashe.






✨✨✨✨✨✨✨✨✨




Safreena zaune ne tana sauraron dukkan maganganun da Garkuwa yayi dasu Jummo ne, ta saki murmushi tare da duban Zee tace.

" Kinga dan tsiya, ya samu wata ita kuma wannan jakar zai jefar da ita, lallai Garkuwa ya cika cikakken taure, ya haɗa ƴan mata biyu a gida ɗaya, hmmm yanzu me zamuyi."

" Hmmm!!! Da alamar ita wacce yake kira da Aishan ba son yaudara yake mata ba, yanayin maganganun sa ya nuna aurenta yake son yayi, da ita ya kamata muyi Amfani wajen ruguza farin cikin sa, bari mu bincika lambarta mu fara da aika mata saƙo"

Shuru Safreena tayi, tana duban wayarta tare da cewa.

" A'ishah to waye ce A'ishah, hmmm?!! Zee binciko numbern ta."

Da to Zee ta amsa tana ta ƙoƙarin neman numbern, ta layin Garkuwa, tana isowa dai-dai numbern taga ansa Private number.

" Kash!!! Numbern bazata ɗauku ba private number ya ɓoye numbern, Safreena da alamu wannan Yarinyar tana da mahimmanci a wajen Garkuwa ya zama dole mu nemo ta!"

Cike da takaici Safreena ta dafe kanta tana jin haushin rashin samun numbern da batayi ba, wayarta ne yayi ringin ta dubi wayar *Jummo* ta gani rubuce, hanu ta saka tare da ɗaga wayar ta na cewa.

" Assalamu alaikum"

"Ameen wa'alaiku mussalam Barka da dare mom Abdul"

" Barka Jummo, ɗazu nake niyar kiranki sai kuma wasu abubuwa suka riƙeni, ya kike kun koma lafiya.?"

" Lafiya alhamdulillah ina my boy Abdul.?"

" Abdul gashi nan yayi bacci, yasu Mama."

"Duk suna lafiya, ki shafa min kan Abdul sai da safe."

" Insha Allah na gode."

Ta ƙarisa Maganar tana katse kiran.

" Jummo ce wacce muka haɗu da safe a super market, yanzu ya zamuyi mu sami yarinyar."

" Gaskiya yanzu dai bana ce ga yadda zamu sameta ba, amma mu cigaba da bibiyar layin wayarsa insha Allah zamu sameta."

Mama ce ta shigo cikin bedroom ɗin nasu jin alamun kamar Magana.

" Safreena me kuke har yanzu bakuyi bacci ba, sha ɗaya da rabi fa!!! Me kuke yi."

Dibirbircewa Sukayi, Zee tayi saurin cewa.

" Babu abinda muke fa Mama bacci ne kawai baizo ba, shiyasa muke fira."

" Fira da laptop a gabanku, kun san fa bana son firan daren nan har sha ɗaya da rabi, ku kashe laptop ku kwanta karna kuma jin muryar ku, ke kuma Safreena ki gyarawa Abdul kwanciyarsa."

" To Mama"

Fita Mama tayi Safreena ta sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.

" Alhamdulillah!!! Mama bataji zancen mu ba."

Murmushi Zee tayi ta kashe laptop din, gyarawa Abdul kwanciya Safreena tayi suka kashe wutar ɗakin tare da Kwanciya.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨






Washe gari da safe bayan anyi breakfast ne khalil ya dubi Mamma dake zaune ranta a haɗe yace.

" Hajiya Mamma Wannan irin haɗa fuska haka tamkar zaki tada bom, ɗan saki fuskar mana sai kifi kyau."

Lumshe idanunta Jummo tayi tare da sakin murmushi da alamu Ya khalil ya farga da zantukanta na jiya, Mamma dubansa tayi har yanzu ranta a haɗe tace.

" Taya zan saki raina ana ƙuntata min ana kona min rai a cikin gidan nan."

Daddy ne yace.

" Ana ƙona miki rai kuma Mamma, meya faru.?"

" Ina ruwanka da abinda ya faru ka damu dani ne, da har zaka tambaye ni abinda ya faru, to ban sani ba, sai ka bari idan na mutu sai ka tambayi gawata meya faru?"

Cike da tashin hankali Daddy yace.

" Subahanallah!!!! Na damu dake mana Mamma dan Allah ki sanar dani me yake faruwa."?

Momy zuciyarta ne ta tsinke tare da kallon Mamma taji me zatace, jikinta har bari yake domin kuwa idan har Daddy yaji abinda ta yiwa Mamma jiya kashinta ya bushe, tashi Mamma tayi tabar wajen bata kulasa ba, numfashi mai nauyi Momy ta sauke tana godewa Allah miƙewa Daddy yayi zai bi Mamma Jummo ta dubi yanda Momy ta kuma ruɗewa murmushi ta saki tare da dakatar da Daddy.

" Aa karka je ranta na ɓace bazata saurari kowa ba, nine na ɓata mata bisa kuskure kuma na bata haƙuri nace bazan kuma ba insha Allah.!!!"

Cike da masifa Daddy ya hauro kan Jummo tamkar zai daketa.

" Baki da hankali ne zaki dinga ɓatawa tsohuwa kamar Mamma rai, irin su ai rarrashin su ake ba wai a samusu damuwa, amma saboda baki da hankali sai kije ki daga mata hankali to kul karki kuma idan kuma kika kuma Wallahi ranki sai ya ɓaci."

" Kayi hkr Daddy insha Allah bazan kuma ba, nayi laifi!!!"

" Ki dai kiyaye" Daddy ya furta tare da ɗaukar jakarsa ta aiki ya fice, Momy baki sake take kallon Jummo duk takun saƙar da suke da ita, sai taga tana tare mata duk wata masifa da ta tunkarota " to meye hakan yake nufi"? Kallon ta ta mayar ga khalil tare da tashi tabar wajar, Aunty Zarah tsuka taja tare da miƙewa tsaye ta furta. "Makircin banza neman gindin zama" tayi Maganar itama tana barin wajen, Sadiya dama tun safe ta kasa fitowa kukan ta tasha a boye sosai take cikin damuwa da tashin hankali, ya khalil duban Jummo yayi yace.

" Ba ke bace kika ɓatawa Mamma rai, meyasa kika karesu.?"

Murmushi Jummo tayi tace.

" Meyasa kace bani bace bayan kuma nice na aikata, babu wanda na kare gaskiya na faɗa Ni ce na bata mata rai.?"

" Ƙarya kike Jummo ba ke bace kika ɓatawa Mamma rai ki faɗa min gaskiya waye ne muddun kuna son na kawo gyara cikin gidan nan tell me?"

" Ya khalil meyasa kake so ka tursasa min dole sai nayi ƙarya da gaske nake maka nine na ɓata mata rai."

" Jummo............"

" Dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login