Showing 84001 words to 87000 words out of 93605 words
Chapter 29 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
dani da ɗana, dan Allah bana son rigima ka mayar min da yarona ka kuma manta dani a rayuwarka."
Ta ƙarisa Maganar tana sakin numfashi, shuru Garkuwa yayi kafin yace.
" Har abada bazan taɓa fita daga cikin Rayuwarki ba, bazaki taɓa mutuwa a zuciyata ba, na yarda zan baki ɗanki amma bisa sharaɗi da kuma alƙawari, idan har kin amince zan baki ɗanki amma wallahi kinji na rantse da Allah idan baki yadda da wannan yarjejeniyar ba, bazan baki Abdul ba, koda kuwa zaki kaini kotu duniya tasan halin da nake ciki bazan baki shiba.."
" A karo na biyu kana kuma neman zaluntata, duk halin dana shiga a rayuwata kaine sanadi, ka faɗi sharaɗinka ina jinka."
Numfashi ya saki tare da cewa.
" Ki sanar dani me kikaje yi a Egypt.?"
" Ɗaukar fansa, nabi kawu IBRAHIM na ɗaukawa iyayena fansar ransu."
" Amma dai kinsan Egypt ba Nigeria bace sannan Ibrahim ya fiki wayo zai iya cutar da rayuwarki kafin ke ki cutar da nasa, ya kamata ki dawo Nigeria."
" Na fika sanin Egypt ba Nigeria bace tunda ba mahaukaciya bace ni, matuƙin jirgin Egypt, babu kuma ruwanka da hatsarin da zan shiga wannan ba damuwarka bane.
Da okay ya amsa tare da cewa
"sharaɗina shine, zan baki Abdul muddun kika min alƙawarin haɗuwa dake, saboda ina da buƙatar tattaunawa dake."
Shuru Safreena tayi na ɗan wani lokaci tana tunani, ɗanta kawai take ji domin tasan zuwa yanzu yaci kuka ya ƙoshi, yana buƙatar Zee ce masa tayi.
" Zamu haɗu ka mayar da Abdul."
" Hmmm!!! Ba haka nake son ki amsa min alƙawarin ba, so nake kice ni Safreena na ɗauki alƙawari tsakanina da ubangijina zan haɗu da Garkuwa."
Runtse idanunta Safreena tayi cike da jin haushin garkuwa shida..........
*Kuyi manage yau ina busy kuyi haƙuri dan Allah.*
*Ummu Nasmah ce*
[5/29, 4:19 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*
➰➰ *72 to 73*
"Naji Na ɗauki alƙawari tsakanina da ubangijina zan haɗu da kai, dan Allah ka je ka bawa Zee Abdul please dan Allah."
" Okay ki turo min numbern wayarta zan bawa Shetima ya kai mata shi yanzu."
Numfashi mai nauyi Safreena ta sauƙe tana godewa Allah, tare da amsawa da to ta katse kiran, bata juma da kashe kiran ba ta turo masa numbern haka kuwa akayi ya bawa Shetima ya kaiwa Zee Abdul, shi kuma ya zauna gadin Jummo cike da tashin hankali.
INNO bata iso ba sai daf da kiran sallar magaruba, Shetima ne yaje ya ɗauko ta, koda INNO ta shigo sosai hankalinta ya tashi jin yadda Jummo ke bige bige tamkar ta haukace.
" Garkuwa buɗe ƙofar."
Babu musu ya buɗe ai kuwa Jummo tamkar jira take ta fito da sauri sai kuma ta haɗa idanu da INNO, tamkar bata san INNO ba zata wuce INNO ta capko hanunta da ƙarfi ta fisge zata fita da gudu Garkuwa yayi sarin tareta, INNO mari ta ɗauke Jummo dashi tare cewa.
" Baki sanni bane Jummo.?"
Ta mata tambayar tana kallon ƙwayar idanunta, kanta ta ɗaga alamun ehh, murmushi INNO saki tare da cewa.
" Yanzu ina kike son zakije na rakaki."
Cikin rawar murya tace.
" Nima ban sani ba"
" Zaki bini gidan mu.?"
Nan ma kanta ta daga alamun ehh, hanunta INNO ta kama tare da cewa.
" Ɗauko mota ka kaimu gidan ku."
Zaro idanunsa Shetima da Ya Garkuwa sukayi tare da cewa.
" Gidan mu kuma INNO, INNO bana son Jummo ta zauna a gidan mu."
Murmushi INNO ta saki tare da cewa.
" Jummo dole a gidan ku zata zauna, karka min musu kazo ka kaimu kawai."
Kansa ya kaɗa cike da sanyin jiki, ya je ya dauko motar suka fita ya jasu.
Momy da Zezah suna zaune a falon sukaji Sallamar su, da sauri Momy ta kallesu zuciyarta na mungun tsinkewa, INNO murmushi ta saki tare da ƙarasawa cikin falon ta zauna gefen Momy tana cewa.
" Barka da hutawa Zainabu, kawai sai kikaga baƙi na bazata, kallon Ya Garkuwa tayi tare da ce masa, Garkuwa aje a share ɗakin Mamma anan zamu zauna."
Da to ya amsa yana fita tare da turo Asma'u tazo ta share, massalaci suka wuce INNO kuma taja Jummo bedroom ɗin da Mamma ta zauna, ta sata tayi Sallah, sannan ta fito har yanzu Momy da Zezah suna nan inda ta barsu kina ganin idanunsu zaki hango tsoro, zama INNO tayi tana murmushi tace.
" Ohh Zainabu bokan ki ya iya aiki tunda harya iya karya tsarin dake jikin Jummo, nawa kika biyasa."
A matuƙar razane Momy tace.
" INNO me kike cewa haka, ban gane ba, meya samu jummon."
Dariya INNO tayi tare da girgiza tace.
" A binda dai kikaji shi nake nufi, kinyi Nasara akan Jummo domin kuwa nasan kin mata sihiri kuma ya kamata, sai dai inaga kin manta da cewa, tana da INNO tana kuma da Baffa, ƴar malamai ce gaba da baya, karkiyi tunanin kinci Nasara, umm ummm!!! Ko rabin Nasara baki samu ba, ki zuba kiyi kallon yanda sharrinki zai dawo kanki."
Tayi Maganar tana barin wajen ba tare da ta tsaya taji me Momy zata ce ba, a razane Momy ta miƙe tsaye tana kallon Zezah tace.
" Zezah na shiga Uku, lallai akwai matsala domin kuwa nasan INNO sarai Zata iya juyo da sihirin nan kaina kafin hakan ta faru gara mu karya sihirin, kije maza kafin Garkuwa ya koma gidan ki samu ki ɗauko layoyin nan mu ƙonasu."
" Haba Momy yaya kawai dan tazo tana miki barazana shikenan sai ki tsorata, babu fa abinda zata miki wallahi, ki barta kawai cikin rashin hankalin idan ya gaji da ganinta a haka ai dole zai saketa."
" Zezah bana son rashin hankali domin kuwa naga alama baki da ita, baki san waye INNO ba, duk abinda ta faɗa zata aikata, dan haka ba shawarinki nake nema ba umarni nake baki, tashi kije."
Tura bakinta Zezah tayi tare da miƙewa ta haura ta dauki mayafinta ta fice, numfashi Momy ta sauƙe tare da haurawa ta kira Sarah, ringin ɗaya sara ta ɗaga cike da tashin hankali take sanar da sara abinda ke faruwa.
" Hajiya Zainab tun farko fa sai da na hanaki, domin kuwa da alamu wannan Yarinyar ƙaddarar ɗanki ne, kawai ki ƙyalesu, sai kika ki kika biyewa shawarar Zezah da ta Hajiya Saude, gashi yanzu sun jefa ki rami sun barki, mtsss"
" Banyi tunanin zan juye haka ba, da bazan fara ba, Sarah kece kawai kike bani shawara idan nabi nake samun hanyar bullewa, yanzu meye abunyi, na saka Zizah tayi maza taje ta ɗauko asirin, da cewa nayi zan ƙonesa ke me kike gani."
Numfashi Sarah ta saki tare da cewa.
Yauwa Gara da kika turata ta ɗauko, ni kuwa wannan INNOn wacce irin shegiyar tsohuwa ce gagararriya, mtsss, yanzu abinda zai faru idan Zizah ta kawo miki, ki tabbatar a tollet kika ƙonesa,, idan kika kuskura kika ƙonesa a waje to asirin kanki zai dawo, makarinsa shine ki ƙonesa a tollet, karki kuskura ki ƙara ƙoƙarin kai Yarinyar wajen boka domin kuwa babu Nasara a kanta, zanzo zan baki shawarar yadda zaki zauna da matsiyaciya."
" Shikenan ƙawata na gode sosai, shiyasa nake ƙaunarki domin kuwa akwai da ɓulalliyar hanya, sai kinzo."
Tayi Maganar tana katse kiran zama tayi tana dafe kanta, cike da tashin hankali da tsanar Jummo, ta juma sosai har Zizah tazo ta kawo mata asirin, kamar yadda Sarah ta faɗa mata haka tayi ta ƙona a tollet, ranta a matuƙar ɓace.
Daren ranar haka Momy tayisa cike da baƙin ciki tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu.
Washegari da sassafe Jummo ta farka a firgice, cikin tsoro tana dube dube ba dai a ROOM ɗin ta take ba, to meya kawota nan tuno da abinda ya faru ya sata dafe kanta tabbas ta tuno zuwan Zee da abinda ya faru tsakanin su da Ya Garkuwa, tasan ta shiga tollet ta kuma ji Sallamar wata kamar Muryar Zizah ta fito ta zauna bakin gadonta daga nan bata kuma sanin meke faruwa da ita ba sai yanzu, kanta dake ɗan sara mata ta riƙe INNO dake bacci ta kalla cike da mamaki tace.
" INNO kuma, meya kawo INNO cikin Gombe?"
Tashi tayi ta shige tollet wanka tayi tare da brush tayi alwala,. Sallah ta gabatar, ta juma tana addu'a, yayin da kishin Safreena na tokare mata ƙirji, harta Ya Garkuwa shima zafinsa take ji, sai dai zata danne zuciyarta bazata yadda kishi yasa ta bijirewa mijinta ba Za tayi iya kokarinta wajen ganin ta rage kishin duk da tasan dole zataji ciwo a ranta, Tabbas ya faɗa mata komai na rayuwarsa bai ɓoye mata ba, zata zauna da mijinta za Kuma ta tayasa neman mafita a cikin lamuransa.
Numfashi ta saki, muryar Daddy taji yayi sallama amsawa tayi kafin Daddy ya shigo a kujerar dake cikin room din ya zauna cike da girmamawa Jummo ta gaishe da Daddy ya jiki ya mata, ta amsa da cewa da sauƙi, INNO ne ta buɗe idanunta ta dubi Daddy tare da tashi ta zauna tana cewa.
" Sannu Garba, jiya kawai sai kaji labarin munzo, lamarin ciwon ne lokaci ɗaya kamar hauka ya firgita mu, amma alhamdulillah ta dawo hayyacinta tun daren jiya, ka yiwa Mamma gini na zamani mai kyau, Allah ya maka albarka!!! Allah yasa ka gama da duniya lafiya."
Da ameen Daddy ya amsa yana cewa.
" Ni kaina da Garko yake sanar dani ciwon nata hankalina ya tashi, to mun godewa Allah da ta samu sauƙi cikin hanzari, dama jiki da jini dole za'a cutu, amma dai bazata koma gidanta ba sai jikinta yayi kwari Kinga ga ƙaramin ciki, dole tana buƙatar hutu ta zauna tukunna har muga yanayin jikin nata kafin ta koma ɗakinta, ni bara na shige kasuwa."
Adawo lafiya INNO ta masa kafin Daddy ya fita, INNO duban Jummo tayi tare da cewa.
" Yaya kike jin jikin naki."
" Bana jin komai sai kaina kawai dake min ciwo."
" Shima kan zai daina a hankali, ki dai dage da yawan azkar karkiyi wasa dashi Allah ya tsare gaba."
Ameen Jummo tace, Asma'u ne ta shigo ta kawo musu breakfast, Ya Garkuwa bai zo ba sai wajen 11am sosai yaji daɗin yanda yaga jikin Jummo INNO waje ta basu, Ya Garkuwa duban Jummo yayi tare da cewa.
" Harna tsorata da lamari ki jiya, nayi zaton Maganar Safreena ne ya sa kika hasala."
" My love meyasa zan hasala bayan ka faɗa min gaskiya tun kafin ka aureni karka manta nine fa na amince zan zauna dakai a duk yanda kake meyasa yanzu zan sauya, ko kaɗan bana fatan na juya maka baya, yanzu wani irin hukunci ka yanke akan Abdul."
" Babu abinda na yanke har yanzu, zuciyata cike take da tsoron tunkarar Daddy da Maganar bansan ya zai ɗauki lamarin ba, ko Bro khalil dana kirasa, baya ya juya min cikin hasala da ɓacin rai to ya kike gani kuma idan Daddy ne, ni dai ina cikin tashin hankali."
" Bana son kana ambatar tashin hankali, kuskure dai ka riga ka yisa babu mai iya gogewa, hkr kuma ya zamo dole, ni na yanke hukunci zan tunkari da Daddy da Maganar ta sigar neman alfarma daya yayi hkr ya karɓi wannan al'amari a matsayin ƙaddara, insha Allah komai zaizo da sauƙi, sannan kaima kana son Safreena har yanzu, ka aureta domin shine cikar rufin asirin ku daga kai har ita, sai ta riƙe ɗanta ina faɗa maka wannan maganar ne da zuciyata ɗaya, ya kamata kaje Egypt ka sameta ku sasanta kafin tafi insha Allah munsha kan matsalar gida, ka kwantar da hankalin ka, komai zaiyi sauƙi, nasan kishi da Safreena bazai cutar dani ba dan nasan wacece ita, nasan halinta mutumce ta gari bata da matsala bazata daga min hankalina ba."
Cike da mamaki yake kallon Jummo, cikin sanyin zuciya, domin kuwa ko a mafarki baiyi zaton zata masa wannan alfarmar ba, Tabbas yayi dace da mace ta gari, idan har ƙafa ake ɗagawa mace ta shiga aljanna to shi ya ɗaga tashi Jummo ta shige, numfashi ya sauƙe tare da jawota jikinsa ya rungume ta yana sakin numfashi.
" Ban taɓa tunanin zaki ɗauki wannan maganar da sauƙi haka ba, kamar yadda kika faɗa nima hukuncin dana yanke kenan na Auri Safreena domin Rayuwar Abdul, daga ni har Safreena muna son juna ƙaddara ce ta faɗawa rayuwar mu, bazan taɓa fifita Safreena sama dake ba, har abada kece a samanta WALLAHI Jummo Soyayyar da nake miki a yanzu ta ɗara ta Safreena, da badan Abdul ba, zan hkr da Safreena a rayuwata na riƙeki ke kaɗai domin kin isheni rayuwa, matar rufin asiri ce ke, Allah ya miki albarka Jummo, ina sonki fiye da kaina."
" Nima ina sonka mijina farin cikin ka shine nawa, dole na ƙwato maka farin cikin ka insha Allah Daddy zai ɗauki wannan zancen tamkar ruwan sanyi, Momy ne dai ban sani ba, ya khalil fushin sa na kanƙanin lokaci ne zai sauƙo bazai iya fushi da kai ba, ransa ne ya ɓaci amma zai huce..............."
*UMMU NASMAH CE*
[5/29, 4:19 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*
➰➰ *68 to 69*
Wani irin jiri ne ya kwashi Jummo jin maganganun Ya Garkuwa take tamkar a mafarki, sai kuma kalaman Garkuwa suka faɗo masa tuno fa tabbas ya sanar da ita Labarin Safreena.
"Safreena!! Safreena!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!"
Kalmar da Jummo ke nanatawa kenan, kardai ace itace Safreena da Ya Garkuwa ya bata labari amma ai ita yace ta mutu ya za'ayi wanda ya mutu ya dawo, meke shirin faruwa dani.?
Tayi zancen zucin tana neman Waje ta zauna daɓas jin jiri na ƙoƙarin kwasarta, tare da zuba musu idanu tana dafe da zuciyarta dake famar bugawa, ita babu abinda yafi ɗaga mata hankali sama da kalmar ɗanda yace nasa ne idanunta ta runtse cikin ƙunar rai, ita kuwa Zee juyawa Ya Garkuwa baya tayi, cikin tsawa mai firgitarwa tace.
" Ehhh Safreena bata mutu ba!!!! Bata mutu ba tana nan raye!!! Kuma ta maka zararra domin kuwa babu kai a cikin rayuwarta ta daɗe da kasheka a rayuwarta, dan Allah kamar yadda ta manta da kai kaima ka manta da ita ka yiwa girman Allah ka bani Abdul na tafi, bamu san Jummo matar ka bace ko kana da alaƙa da ita da ba zamuyi kuskuren haɗa zumunci da ita ba, ka bani Abdul dan Allah, wannan yaro ne baisan komai ba."
Shuru Garkuwa yayi tare da neman waje ya zauna yana nan riƙe da Abdul a hanunsa, rungumo yaron yayi a jikinsa cike da Soyayya irin ta ɗa da Uba, wani irin soyayyar Safreena ce ke bijiro masa, tabbas yana sonta tsawon rayuwarsa, numfashi ya sauƙe tare da ɗago idanunsa ya kalli Zee cewa yayi.
" Shiyasa na kasa mantawa da Safreena a rayuwata, na kasance da sonta tsawon shekaru dai-dai da kwana ɗaya ban taɓa jin koda ɗigon santa ya ragu a zuciyata ba, KULLUM cikin zancenta nake, ashe inuwarta yana yawo a duniya, meyasa kuka min ƙaryar Safreena ta rasu bayan ni masoyine gareta ba maƙiyi ba, meyasa kuka ɓoye min ɗana jinina saboda meyasa shin Safreena bata sona ne, hmmm!!! Lallai zunubai nane Sukayi yawa shiyasa Safreena guduna, ki sanar dani Zee ina Safreena take.?"
Shuru Zee tayi cike da sanyin jiki, idanunta na ziraro da hawaye cikin rawar murya ta fara magana.
"Saboda munanan kalamanka akan Safreena, Idan bazaka manta ba kasha alwashin cewa sai kaga bayan Safreena muddun bata zubar da cikin jikinta ba, a wannan lokacin hankalin Safreena yayi mungun tashi har ta shigo gidan mu a tsorace take cemin ga abinda ka faɗa mata amma ita hankalinta ya tashi ta hango gaskiya zaka iya aikata ikirarin ka a idanunka, a wannan lokacin ni ne na kwantar mata da hankali na tabbatar mata da cewa bazaka aikata abinda ka faɗa ba, na nuna mata cewa barazana kawai kake mata saboda ta zubar da cikin jikinta, hmmm!!! Da ƙyar na samu hankalinta ya kwanta, a wannan daren ƙin kwana tayi a gidan su saboda tsoro, ta kwana a gidan mu, a cikin wannan daren gobara ya tashi a gidan su wanda duk agajin da aka kawo sanda wutar nan ta cinye komai, na gidan da kowa dake cikin gidan itama Safreena ta tsirane kawai Saboda a gidan mu ta kwana, tun daga ranar da wuta taci gidan su da iyayenta, zargin kaina kasa wutar ya ɗarsu a zuciyar Safreena, iƙrarin daka mata suka fara yawo a zuciyarta, akwai wani Isma'il mai gadin gidan Alhaji badamasi, ya tabbatar da cewa yaga wani matashin saurayi da wasu Uku sun jefa ƙulli da jarga cikin gidan su Safreena, basu juma da juyawa ba wutar ta tashi, tun daga ranar da ni da Safreena da iyayena muka yarda cewa kaine ka saka wuta cikin gidan su domin kashe Safreena karta tona maka asiri, sai tsanarka ya ɗarsu a zuciyarta taji a duniya bata da maƙiyin da ya wuceka, wutar fansar iyayenta ne kawai yake yawo a zuciyarta, mahaifina cike da tsoro ya sa aka yiwa Safreena visa tare da nunawa duniya cewa Safreena ta mutu, ya turata American wajen Momy Atine ta zauna gudun karka kuma cutar da rayuwarta, Safreena bata dawo wannan ƙasar ba sai da ta haifi Abdul har yayi wata Uku sannan ta dawo Nigeria da niyyar ɗaukar fansa tayi niyyar ta kasheka ta ko wani hali, ni da ita muka fara ƙoƙarin saka maka tsoro cikin ranka ta hanyar zuwa hotel muka haɗa baki da ma'aikacin hotel muka ɗauki video ɗinka tsirara kai da Sadiya, muka turo maka domin mu ɗaga maka hankali, mun maka abubuwa da yawa na firgitarwa, a ƙarshe muka haɗa baki da mai gadin gidan ku muka basa kuɗaɗe ya since maka tayar mota saboda kayi hatsari ka mutu, haka kuma akayi a wannan ranar tabbas kayi hatsari kai da wacce zaka Aura, a Kuma wannan Ranar Momy Atine ta sanar damu cewa ba kai bane ka kashe iyayenta, saboda Mahaifiyar Safreena ta sanar da ita cewa ƙanin mahaifin Safreena yana shirin