Showing 81001 words to 84000 words out of 93605 words
Chapter 28 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
bara na fita na samu Sadiq yazo ya duba mana gas ɗin nan."
Da adawo lafiya Jummo ta masa ya fita ita kuma tayi bedroom ɗinta ta kwanta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Safreena yanzu ya kukayi da Khabeer ɗin kin sanar dashi tafiyar taki, sannan ya yadda zai nemo miki izini daga Companyn nasu."
" Zee ai kinsan zai tambaya min ko Saboda Soyayyar da yake min, kuma kinga Companyn sune, munyi waya ɗazu yace ya tambaya kuma sun bani izini sai dai za'a dakatar da albashi na har sai na dawo aiki ."
" Kuma kin amince da hakan.?"
" To Zee ya zanyi idan ban amince ba, kin sani Case ɗin dake gabana idan banga ƙarshen kawu Ibrahim ba, hankalina bazai taɓa kwanciya ba, dole zanje Egypt domin lalata masa duk wani farin cikinsa zan bar Abdul a hanunki jirgin 11 zamubi da Baba ki kula da ABDUL sannan dan Allah kije gidan Jummo zataji daɗi."
" Hakane Allah ya kaiku lafiya, nama ga Mama ma ta yiwa Abdul wanka."
" Ehh nima bara na shiga wankan."
Tayi Maganar tana shigewa tollet.
Washegari da safe misalin sha ɗaya jirgin su Safreena ya tashi zuwa Egypt, Zee kuwa ta riƙe Abdul, abun mamaki juyowar da Zee tayi zata shiga mota a airport ɗin sukayi kiciɓus da Ya Garkuwa, shigowarsa kenan airport ɗin yazo amsar saƙo a wajen Shetima, da kallo yabi Zee cike da mamaki rabonsa da ita tun sanda ta kirasa take sanar dashi Safreena ta rasu, ita kuwa Zee saurin kawar da fuskar Abdul tayi gefe gudun kar Ya Garkuwa ya gansa tare da buɗe mota ta sashi cikin sauri tana ƙoƙarin shiga Garkuwa ya taho da sauri yana cewa.
" Zee dama kina duniyar nan, na nemeki sosai ban ganki ba, amma meyasa daga ganina za kiyi saurin tafiya."
Da sauri Zee ta rufe motar tare da cewa.
" Ina nan bana ƙasar nan ne, sati ɗaya kenan da dawowata yanzu ma Baba na rako zai tafi Egypt, ya kk."
Ɗan murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.
" Ina lafiya Zee da alamu dai har yanzu kina jin haushina, hmmm Zee ina kewar Safreena ina kuma takaicin abinda na mata a rayuwata, sai dai babu yanda muka iya ƙaddara ta riga fata, ita Safreena rayuwarta ta ƙare babu yanda muka iya Allah ya mata rahama."
" Hmmm!!! Bana jin haushinka domin kuwa komai ya riga ya shige, ameen ya Allah, Allah yasa muma idan tamu tazo mu cika da kyau da imani, ina sauri Momy na jirana."
Ta ƙarisa Maganar tana buɗe motar da sauri ta shiga Ya Garkuwa na Magana ta basa number bata sauraresa ba taja motar ta da ƙarfi tabar wajen, girgiza kansa ya Garkuwa yayi tare da shigewa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Rayuwa tana gudu yayin da abubuwa suke cigaba da tafiya, Rayuwar Jummo a gidan mijinta alhamdulillah!!! Komai na tafiya mata cikin farin ciki sai dai har zuwa yanzu Momy da Zizah basu daina ƙoƙarin kawowa Jummo hari ba, domin kuwa sun rantse sai sun kashe mata Aure, ya wata huɗu kenan da Auren Jummo, sai Allah yana kareta daga duk wani hari da Momy take kawo mata, zaman lafiya da ƙaunar juna kuwa sosai yake wakana tsakaninta da mijinta, a cikin waɗannan watannin Jummo ta fara laulayin ciki, koda sukaje asibiti aka tabbatar da ciki gareta sosai Garkuwa yayi farin ciki kamar bazai mutu ba tsabar daɗi, Ya khalil dake cikin garin Abuja sai da Ya Garkuwa ya sanar masa sosai ya taya ɗan uwansa murna, da kansa ya sanar da Momy wayyo baƙin ciki Wajen Momy ba'a Magana, A'illo dake zaune gidan sai da ta fahimci baƙin cikin da Momy take da samun cikin Jummo, sai dai a yanzu tayi rantsuwa da Allah cewa kota halin yaya sai Jummo tabar gidan.
Ita kuwa Safreena tana can tana bincike akan Kawu Ibrahim game da kisan da ya yiwa mahaifinta da kuma dukiyarsu daya cinye sai dai har zuwa wannan watannin tayi rantsuwa da Allah cewa bazata dawo Nigeria ba har sai tayi Nasara akansa.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Yau Jummo ta zaune ita kaɗai a falo kasancewar yanzu laulayin nata da sauƙi taji ƙarar wayarta hanu tasa ta ɗaga kiran ganin baƙuwar number, daga can Zee ta amsa tare da cewa.
" Sunana Zee ƙawar Safreena."
" Ayya sannu Zee fatan kina lafiya ina Abdul."?
" Lafiya Alhamdulillah, ABDUL gashi nan amm yanzu ma shirin zuwa gidan ki muke shine nace bara na sanar dake idan mun shigo shango Estate ɗin sai mu kiraki."
Cike da murna Jummo ce.
" Kai naji daɗi sosai wallahi Allah ya kawo ku lafiya."
Da ameen Zee ta amsa tana katse kiran, Ya Garkuwa ne ya fito daga ROOM ɗinsa daidai sanda Jummo ke ƙoƙarin tashi cike da zumuɗi tana dariya zata kitchen ta haɗawa Su Zee abinci, zama yayi yana kallon ta tare da cewa.
" My Dear murnar me kike haka ne ko dai Baby nane yau take saki farin ciki."?
Murmushi Jummo tayi tare da kallon cikin ta dake wata biyu da sati biyu, dariya tayi ta koma ta zauna tare da kamo hanun Ya Garkuwa ta ɗaura a cikinta tace.
" My love, ina matuƙar ƙaunar ɗan da ke cikina, ina son na haifesa lafiya, ka tayani da addu'a Allah yasa na haihu lafiya."
Murmushi Ya Garkuwa yayi ya sunkuya ya yiwa cikin kiss yace.
" Na fiki ƙaunarsa Insha Allah zaki haihu cikin ƙoshin lafiya, yanzu faɗa min me ya saki farin ciki."?
" Ai ina baka labarin ƙawata Maman Abdul, to yau ƙawarta zata kawo min ziyara, ita bata nan tayi tafiya, da Abdul da ƙawarta sune zasu zo suga gidana, shine zanje na musu girki."
" Umm ƙawar Maman Abdul, to jeki musu Allah ya kawo su lafiya."
Ameen Jummo tace tare da shigewa kitchen tana murmushi tabar Ya Garkuwa a zaune a falon, kitchen ta shiga ta hau aiki Ya Garkuwa ya juma a zaune a wajen kafin ya tashi ya fita, Jummo ta gama komai na gidanta da kusan minti talatin kafin Zee ta kirata ta sanar da ita tana cikin Estate ɗin, da kanta Jummo ta fito ta ɗauko su Zee tare da amsar Abdul, suka yo part ɗinta.
" Sannunku da zuwa, Abdul mamanka ta gudu ta barka ko.?"
Dariya Zee tayi tare da cewa.
" Ta kusa dawowa ai insha Allah, masha Allah gidanki yayi kyau sosai."
" Na gode bara na kawo muku ruwa."
Jummo abinci da ruwan ta kawo musu har tsakar falon, tayi seving ɗinsu da kanta a cinyarta ta ɗaura Abdul ta hau fasa dankali tana basa, cike da farin ciki da kuma sabo Jummo ta sake da Zee kamar sun shekara, Abdul zamewa yayi daga jikin Jummo yayi bakin kofa yana wasa, Jummo ne ta dubi Zee tare da cewa.
" Zee Maman Abdul ta juma sosai a ƙasar waje aiki take a canne.?"
Zee ta buɗe baki kenan da niyyar bawa Jummo amsa aka turo ƙofar Turus ta tsaya tana bin ya Garkuwa Da kallo, cike da firgici ta furta.
" Garkuwa!!!"
Jin ta ambaci Garkuwa yasa Jummo kallon wajen, shi kuwa yana tsaye cike da tsoro yana kallon yaro mai kama dashi sak babu ta inda ya barsa, ko kaɗan bai kula da Zee ba a falon, murmushi Jummo tayi tare da cewa.
" Oh Mijina ne shi, sannu da dawowa My Love."
Garkuwa dagowa yayi ya kalleta sai idanunsa suka sauƙa akan Zee dake gefen sa.
" Zee!!! Zee!!!"
Ya furta yana kuma kallon Abdul, numfashi ya sauƙe tare da sunkuyawa gaban yaron yana kallon sa sosai, da sauri Zee tazo ta sunkuya zata ɗauki Abdul, Garkuwa yayi saurin saka hanu ya ɗaukesa yana kallon ta tare sakin murmushi yace.
" Ina kuma zaki ɗaukesa ki kaisa bayan kuma kin kawo sa gidan ubansa."?
Zaro idanunta Jummo tayi, Zee kuwa wani irin tsinkewa zuciyarta tayi cikin tashin hankali tace.
" Me kake nufi Garkuwa, ka bani ɗana na tafi, bana son tashin hankali."
Murmushi mai sauti ya Garkuwa yayi tare da cewa.
" Kinfi kowa sanin abinda nake nufi, ni kuwa meye tsakanina dake da har zanyi tashin hankali dake, kince na baki ɗanki ki tafi, ina kika samu ɗa Bayan baki haihu ba.?"
" A layi na samesa, sai ka bani kayana na tafi."
"Hmmm!!! Ko makaho ne yaga Abdul zaice ɗana ne, Ina Safreena take."?
Runtse idanunta Zee tayi tare da cewa.
" Kana haukane GARKUWA!!! Ya kake tambayata matar da ta juma da mutuwa, kaga ka bani ɗana na tafi."
Jummo cike da mamaki gami da tashin hankali tace.
" Wai meke faruwa ne kam, kun san junane, ɗanka fa kake kiran Abdul anya kana lafiya."
Dariya Garkuwa yayi tare da cewa.
" Kema mahaukacin zaki kirani kenan, ita ta sani Abdul jinina ne."
" Ƙarya yake ni bansan komai ba Abdul jinina ɗana ne, ta ina zai zamo ɗanka."
Jummo runtse idanunta tayi cike da kullewar kai gami da tashin hankali tace.
" Wai ya kuke neman juya min ƙwaƙwalwa ne, shi yace ɗansa ke kince ɗanki bayan Kuma Abdul ba ɗanki bane!!!! Kai kuma ya Garkuwa masifa kake neman jawo mana daga ganin yaron Mutane kace naka!!! Iya sanina da hankalinka kabar falon nan yanzu, amma gashi ka shiga tamkar wanda ya taɓu."
Kallon Zee yayi tare da furta.
" Wasan naki ya ƙare, ki faɗa min ina Safreena!!! Ki faɗa min ina buƙatar ta a rayuwata.!!!!!!!!!!!!!!!!
*UMMU NASMAH CE*
[5/29, 4:19 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*
➰➰ *70 to 71*
Key ɗin ta saka jikin kubar sai dai me ƙin shiga yayi kasancewar na nasa bane, cike da haushi Jummo ta yasar da key ɗin da ƙarfi ta doki ƙofar tana cewa.
" Kazo ka buɗeni nabar gidan nan tunda ba gidan ubana bane, na rantse da Allah yau sai nabar gidan nan na tsaneka Garkuwa, na tsaneka!!!!! Zan kasheka idan baka ƙyaleni na tafi ba."
Tamkar mahaukaciya Jummo ke doka ƙafar tana surutai sai dai shuru kukeji babu kowa, dole tasa ta neman Waje ta zauna domin kuwa tayi laushi tare da sake wani marayan kuka mai ban tausayi.
A ƙofar gidan su Shetima yayi parking tare da kiransa bai juma ba ya fito, tare da buɗe motar ya shiga ya zauna da kallo yabi Abdul kafin ya dubi Garkuwa yace.
" Abokina waye wannan kuma ina ka samosa.?"
Numfashi Garkuwa ya saki ya amsa masa da cewa.
" Abinda ya kawo ni kenan, Shetima wannan yaron da wa ya maka kama."?
Shetima sosai ya ƙarewa Abdul kallo tare da cewa.
" Kamar yana ɗibin fuskarka,. Akwai kuma wani fuskar da yake min kama da ita na kuma rasa gane mai fuskar, meke faruwa.?"
" Abubuwa da yawa sun faru yau domin kuwa wannan yaron da kake gani, ɗan Safreena ne, ɗana kuma Cikin da na mata shine wannan yaron."
Tsuka Shetima yaja cike da ɗaukar Garkuwa ya haukace yace.
" Wannan wani irin banzan magana ne,. Wacce Safreenan, bayan ta mutu, mtss anya kuwa hankalinka ɗaya da alamu dai baka cikin hankalinka."
" Hmm!!!! Gaskiya fa nake faɗa maka Safreena bata mutu ba, ka saurareni da kyau kaji abunda zan faɗa maka."
" Hmmm!!! Shiriritar banza ina jinka gama tatsuniyar sai muje asibiti a dubaka da alamu dai ƙwaƙwalwarka ta fara samun matsala."
" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, haba dan Allah wai meyasa kake min haka ne Shetima ya zanzo maka da damuwata cikin tashin hankali, sannan ka dinga ƙoƙarin mayar dani mahaukaci, why Idan bazaka saurareni ba sai nayi tafiyata."
Numfashi Shetima ya saki tare da cewa.
" Maganar taka ce tayi kama da almara, amma ina jinka faɗi muji."?
Cike da tashin hankali Ya Garkuwa ya sanar da Shetima dukkan abinda ke faruwa, cike da ɗimuwa gami da matsanancin mamaki cike da tsoro yace.
" Whattt!!! Whattttttt!!! Serious abinda kake faɗa min gaskiya ne, idan kuwa hakane tabbas akwai babban tashin hankali, Huuuuu!!! Hmmm!!! Me zaka cewa Daddy da Momy da kuma khalil akan wannan yaron, bama wannan ba, yanzu ita Jummo tana ina, mu fara zuwa wajenta kafin muyi tunani akan lamarin Safreena."
Ya Garkuwa baice komai ba, ya ja motar suka koma cikin gidan sa, a yanda yabar Jummo a haka ya sameta sai dukan ƙofar take, tana surutai, shuru Shetima yayi yana sauraronta tare da matsowa jikin ƙofar ya kira sunanta.
" Jummo!!! Ki saurareni."
Shuru tayi jin muryar Shetima sai kuma da ƙarfi tace.
" Shetima ka buɗeni zan mutu zuciyata tana tsinkewa a bedroom ɗin nan, ku buɗeni ko na kashe kaina, bana son GARKUWA na tsanesa, ku buɗe ni zan shiga duniya ne, na lalace kowa ma ya huta."
Zaro idanunsa Shetima yayi cike da tsoron kalamanta Ya Garkuwa kuwa yafi kowa tsorata, duban Garkuwa yayi yace.
" Garkuwa anya kuwa Jummo bata haukace ba, bata maganganu irin na masu hankali, ba kishin Safreena take ba, dole akwai wani abu da yake faruwa da ita, bama buƙatar magana da Jummo yanzu ko budeta, abinda zai faru, ka kira Baffa kakanta ya haɗaka da INNO, ka sanar da ita abinda ke faruwa tazo da gaggawa, maza kira wayar."
Ya ƙarisa Maganar yana karɓar Abdul dake famar kuka yana neman abinci a hanun garkuwa ya hau jijjigasa, Ya Garkuwa numbern Baffa ya kira, bayan Baffa ya ɗaga ne suka gaisa ya buƙaci a bawa INNO wayar babu jumawa kuwa aka haɗasa da INNO bayan sun gaisa, Garkuwa ke sanar da INNO abinda ke faruwa, numfashi INNO ta saki tare da cewa.
" Karku buɗeta ku jirani zan hau mota yanzu ina tahowa."
Da to Ya Garkuwa ya amsa suna jin masifar Jummo, duban Shetima yayi tare da cewa.
" Ina cikin tashin hankali, yanzu abinda nake so ya za'ayi na warware matsalar Safreena."
Shetima kansa ya dafe tare da cewa.
" Shima ka kira Bro khalil ka sanar dashi abinda duk ya faru tsakanin ku da Safreena, na tabbata ransa zai baci amma tabbas zai kawo mana mafita."
" Kai ina tsoron sanar da Bro Wannan Maganar ina tsoro domin bansan ya zai ɗauki Maganar ba."
"Sanar dashi shine kaɗai mafitar da kake dashi, kaga kawai ka kirasa ba tare da tunanin mai zaice ba burin mu kawai shine mu sami mafita, sannan kana buƙatar haɗuwa da Safreena."
" Okay shikenan bara na kirasa."
Yayi Maganar yana dannawa ya khalil kira ringin ɗaya Ya khalil dake zaune cikin Office ɗinsa ya ɗaga tare da cewa.
" Ya akayi Bros."
Ɗan shuru ya Garkuwa yayi kafin yace.
" Bro ya aikin."
"Aiki alhamdulillah, amma ba daɗi, ya naji muryar ka da sanyi kamar dai kana cikin damuwa, meke damunka domin dai tabbas kana cikin matsala a yanda na fahimta."?
" Bro, GASKIYA akwai matsala kuma bansan ta inda zan fara sanar da kai ba, ina tsoron yanda zaka ɗauki Maganar, ban kuma san kallon da zaka min ba idan ka sani."
Ɗan murmushi Ya khalil yayi tare da cewa.
" Baka da wanda zaka sanarwa matsalarka sama dani domin kuwa nine ɗan uwanka na jini wanda zai iya rufa maka asiri, idan baka sanar dani ba wa zaka sanar, kaga faɗa min meke faruwa karkaji tsoro.?"
Ya Garkuwa kallon Shetima yayi jikinsa a sanyaye, ɗaga masa kai Shetima yayi alamun ya faɗa, cike da in'ina ya fara sanar da Ya khalil labarin sa da Safreena da cikin da ya mata har zuwa abinda ke faruwa yanzu da kuma halin da Jummo ke ciki, ai kuwa wani irin ɓaci ran ya khalil yayi bai taɓa jin haushin ɗan uwan nasa irin na yauba, Sosai ransa ya ɓaci kansa ya kulle, halin da Jummo ke ciki ne ma yafi ɗaga masa hankali a matuƙar fusace yace.
" Dole kace kana tsoron sanar dani wannan mungun aikin daka aikata a rayuwarka mai cike da abun kunya, tir!!! Ba dole Jummo ta shiga wani hali ba, taji abinda yafi karfin zuciyarta, na rantse da Allah wani abu ya samu Rayuwar Jummo, ni da hanuna zan jefaka a prison, domin kuwa bazan yarda ka cutar da Rayuwarta ba na zuba ido yarinya mai hkr da burin kawo gyara a rayuwar mutane, shine zakayi burin ka kasheta, wannan wani irin abun kunya ka jawo mana, ɗan layi fa, ya Momy zata ɗauki wannan lamarin so kake ka kasheta, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Ka bani kunya Garko ban taɓa zaton za'a sameka da irin waɗannan mugayen halayyar ba, me kake so nace yanzu naje na samu su Daddy da Maganar ko, nasan shine yasa ka kirani, to ka sani bazani ba, sanda kaje ka tafka abun kunyarka ka yiwa ƴar mutane ciki, ban sani ba, dan haka yanzu kuma sai kaje da kanka ka tari iyayen naka da Maganar idan yaso idan ZUCIYARSU ta buga ka kashesu shikenan sai burinka ya cika."
Yana gama faɗin haka ya kashe wayarsa cike da tashin hankali Ya Garkuwa ya dubi Shetima yace.
" Kaji ko, abinda nake gudu kenan yanzu ya zanyi shima ransa ya ɓaci, ta ya zan tunkari Momy da wannan maganar ko Daddy."
Shetima ne yace.
" Kaima kaine ka ɓata shirin meyasa zaka amshi yaron daga hanun Zee, tunda ka gansa ka kuma fahimci ɗanka ne, sai kabarta da yaron, hakan shi zaifi bamu damar bin komai a hankali, saɓanin karɓesa da kayi gashi sai famar kuka yake babu yadda zamuyi dashi,da ace........."
Ringin ɗin wayar Ya Garkuwa ne ya hana Shetima ƙarisa Maganar da yayi niyya baƙuwar number a HANKALI ya ɗaga muryar daga can yaji muryar ta cikin tsiwa da faɗa.
" Wannan tsakanina da kaine babu ruwan ɗana, dan haka kayi gaggawar mayar min da Abdul hanun Zee, ba ɗanka bane kuma bazai taɓa zama ɗanka ba, wato bibiyata kake shiyasa ka haɗa baki da matarka saboda ka tozarta Ni, ka nunawa duniya ina da ɗan shege, asirina a rufe yake babu wanda yasan ina da ɗan shege kowa ɗauka yake bayan tafiyata American nayi Aure ne shiyasa na dawo da yaro, dan Allah karka tozarta ni, ka ɓata min sunana dana ɗana ina buƙatar farin cikin ɗana, dan Allah ka bari ka fita a rayuwata, na sauya ƙaddarata daga mantawa da ko wani namiji, na shiryawa rayuwa