Showing 51001 words to 54000 words out of 93605 words
Chapter 18 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
da Zarah yadda kike wulaƙanta ta, bata da ƴanci a gidan mijinta, kawar da kaina kawai nake a matsayin ki na mahaifiyata, bana son ɓata miki rai, ina son na gama da duniya lafiya, kuma dole sai na miki biyayya haka zata kasance, Momy!!! A wannan karon bazan bi bayan ki ba, bayan gaskiya zanbi."
Yana gama faɗin haka ya fice da sauri yana huci, dafe ƙirjinta dake buga mata Momy tayi tana riƙe bakinta ( Cap innalillahi, tana shirin rusa min farin cikin gidanae, Allah ka kashe Yarinyar nan na huta addababbiya nacacciya) Momy ta furta tana jingina jikin bango, shuru tayi cike da tashin hankali ta tsani Mamma da Jummo saboda tunda suka shigo cikin gidan komai nata yake neman lalacewa .
Ya khalil kuwa sosai yaji ransa ya ɓaci game da halayyar mahaifiyarsa, ya rasa Momy wata irin mutum ce mai son kanta, tun kafin Jummo suzo cikin gidan ya juma da fahimtar haka, sai dai bai gane suna zaman rashin shaƙuwa ba sai zuwan Jummo, numfashi ya sauƙe tare da tura ƙofar bedroom ɗinsa ya shige, zama yiyi tare da zama gefen bed ɗinsa, Zarah tana kwance ɗagowa tayi tare da cewa.
" My dear! Lafiya kuwa.?"
Bakinsa ya cije tare da ciro wayarsa, yana dannawa Daddy kira ringin ɗaya Daddy ya ɗaga cike da damuwa Ya khalil ya sanar da Daddy abinda ke faruwa sosai hankalin Daddy ya tashi, sai dai Ya khalil ya kwantar masa da hankali sosai har sai da Daddy yaji damuwar tasa tayi sauƙi sannan khalil ya katse kiran, duban Zarah yayi yace.
" Wannan shine damuwar"
Tare da tashi ya shigewa tolet, Aunty Zarah Sosai ta tausayawa halin da su Jummo suka tsinci kansu duk a yanzu ba wai wani shiri bane tsakanin su, sai dai har cikin zuciyarta ta tausayawa Jummo musamman ace mutum ya manta komai na rayuwarsa ai abun babu daɗi.
Mamma kuwa har yanzu tana nan yanda take babu wani canji a lamarin ciwon ta, yayin da INNO ta duƙufa wajen mata magani a wunin Ranar bata gajiya ba, sai dai duk binciken INNO ta kasa gano ainihin abunda ya faru da Mamma.
Koda A'illo taje taga Jummo ko motsi batayi sosai hankalinta ya tashi, ƙarfe sha ɗaya na dare Garkuwa ya buɗe idanunsa a hankali yana ɗan jin jiri kaɗan, haka yaji ƙirjinsa ya masa nauyi nurse din dake wajensa ne ta fita da gudu kiran DOCTOR a hankali abubuwan da suka faru suka fara dawo masa, Jummo zuciyarsa ta furta tare da yunƙura zai tashi dai-dai doctor sun shigo, da sauri likitan yazo ya riƙesa tare da maidashi ya kwanta, oxygen ɗin dake maƙale a hancinsa ya cire masa, yatsansa ya saka a daidai hancin nasa sai yaji numfashin nasa yana tafiya dai-dai alhamdulillah doctor ya furta, tare da miƙewa daga kansa yace.
" Sannu ya kake jin jikin, me yake maka ciwo yanzu?"
Lumshe idanunsa ya Garkuwa yayi yana dafe ƙirjinsa, cije leɓensa yayi a hankali ya furta.
" Ƙirjina ke min nauyi, kaina shima yana min ciwo, amma doctor bashi yafi damuna yanzu ba, Jummo ina Jummo take, ina son sanin halin da take ciki.?"
Numfashi doctor ya sauƙe tare da sunkuyar da kansa baya son faɗawa Garkuwa halin da take ciki, nurse lura da halin da doctor ya shiga ne ya sata cewa.
" Itama jikinta alhamdulillah ta dawo normal harma ta samu bacci."
" Ina son ku kaini na ganta."
Ya furta maganar yana ƙoƙarin zai miƙe, saurin riƙesa DOCTOR yayi tare da cewa.
" Bata cikin wannan asibitin tana can ƙasa damu anan ake kula da ita, a yanzu bazai yiwu mu barka ka fita ba, kayi hkr har zuwa mu sallameka, itama tun jiya take cewa a kawota wajen ka, dan Allah duk kuyi haƙuri har a sallameku."
Doctor ya yiwa Garkuwa ƙarya duk dan saboda hankalinsa ya kwanta, an kuma yi Sa'a jin cewa itama tana son zuwa wajensa yasa Garkuwa hankalinsa ya kwanta yayi tunanin tana lafiya, da wannan Garkuwa ya haƙura."
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
*Bayan kwana uku*
Yau tun safe Ya khalil yake asibitin shida Daddy, suna nan tsaye akan Jummo tun safe suke tsammanin farfaɗowarta amma shuru har shida na yamma, sosai likitan ya tsorata domin kuwa yana tabbacin cewa muddun ta wuce yau bata farfaɗo ba, ya tabbata zata farka da cutar mantuwa, shi kansa Ya khalil ƙirjinsa dukan uku Uku yake, idanunsa na runtse baya ƙaunar wannan mummunan lamari ya faru da Jummo zuwa wannan lokaci kowa ya fidda rai ga farfaɗowarta, Daddy ne ya dubi DOCTOR tare da cewa.
" Doctor me hakan yake nufi, kunce kwana uku zata farfaɗo gashi kuma lokaci yayi har yana neman ƙurewa amma shuru babu wani alamar zata farfaɗo."
Shuru doctor yayi cikin jagulewar rai yace
" Mu ɗan ƙara jira mu gani idan Allah yasa ta buɗe idanunta zamu mata tambaya Uku idan ta amsa dai-dai to ƙwaƙwalwar ta ta dawo dai-dai idan kuma bata amsa ba to sai dai muyi hkr ta kamu da cutar mantuwa, sai..........."
Bai ƙarisa Maganar ba nurse fa'iza tace.
"Lah!!! Doctor duba kaga yatsanta yana motsi."
Da sauri dukkansu suka maida kallonsu kanta, doctor cikin hanzari yace a rufe dukkan ƙofa da window dake room ɗin tare da sawa aka kashe wuta ita kuwa Jummo a hankali numfashin ta ya fara harbawa sai kuma ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta, tana hango hotunan accident ɗin da sukayi, a hankali harta buɗe idanunta hawaye na gangarowa daga idanunta duhu sosai take ganin room ɗin sai sautin numfashin mutane da take jiyowa kusan 15 minute da farfaɗowarta sannan DOCTOR ya kunna wutar room ɗin gaba ɗaya kallonta sukayi, itama da kallon take binsu ba tare da tayi magana ba, doctor ne ya sunkuya a gabanta tare da kiran sunan ta.
" Jummo!!"
Shuru tayi tamkar bada ita yake ba, waro idanunsa yayi wannan fa shine tambaya ta farko da zai nuna tana hayyacinta, sau Uku ya kira sunanta bata amsa ba, yawu mai ɗaci ya haɗiye tare da nuna mata uniform ɗin jikinsa dake fari fat yace.
" Wannan baƙi ne ko fari.?"
Nan ma Jummo kau da kanta gefe tayi, jawo hannun Ya khalil yayi gabanta yace.
" Kinsan wannan."?
Sai yanzu ta ɗago kanta ta kalli Ya khalil a hankali tamkar mai koyon Magana tace.
" Yaya khalil!!! Ya Garkuwa ya mutu ko?"
Gabaki ɗayan su alhamdulillah suka furta, cikin dariya Ya khalil ya zauna gefenta tare da kamo hanunta ya girgiza mata kai.
" Bai mutu ba, yanzu ma zai shigo ki gansa, ya kike jin jikin naki."?
Kanta ta riƙe tace.
" Kaina yana min nauyi kamar dutse ya khalil sai dai nauyin da yake min bai dameni ba, kamar yadda zanso ganin Ya Garkuwa, Ya khalil dan Allah ka kaini wajen sa."
Doctor ɗago kai yayi ya kalleta cike da mamaki kusan maganarta ɗaya da wanda GARKUWA ya masa sanda ya farfaɗo, da alamu dai akwai wani abu tsakanin su, Ya Garkuwa kam murmushi yayi tare da miƙewa tsaye ya fita, room ɗin Garkuwa yayi tare da samunsa ya kifa kansa yayi shuru idanunsa sun cika da kwalla, kusa dashi Ya khalil ya zauna tare da dafa kafaɗarsa.
" Lafiya ɗan uwana, kake ƙoƙarin kuka, karfa ka manta cewa, baka da lafiya, kwanciyar hankali kake buƙata ba damuwa ba, just tell me pls what happening."
Karo na farko da Ya khalil ya fara tambayar ɗan uwansa damuwarsa, runtse idanunsa Ya Garkuwa yayi tare da jin wani sanyi, da Ya khalil ya tambaye sa maike damunsa, maimakon da da idan ya gansa a wannan halin sai dai yace, (Kai kuma a wannan ƙarnin mai zai maka zafi harka zauna sawa kanka damuwa a banza, just share koma meyene ka cigaba da rayuwarka) shima hanu yasa ya dafa kafaɗar Ya khalil, duk da a yanzu bazai iya sanar daahi damuwarsa ba, saboda akwai kunya yace Sadiya ta kira ta ci mutuncin sa, bare kuma ya faɗi abinda ke faruwa tsakanin su, juya Maganar yayi kan Jummo tare da cewa.
" Na gaji ne ina buƙatar ganinta sunƙi bani dama zuciyata kuma ƙuna take min, ganinta kawai zaisa naji sauƙi."
Murmushi Ya khalil yayi yana dukan kafaɗarsa yace.
" To mister romio tashi muje ka ganta, kaikam ma yau za'a sallameka mu koma gida, ita dai Jummo nata sallamar sunce ba yau ba."
Ɗan murmushi Ya Garkuwa yayi tare da miƙewa suka jera tare da Ya khalil, suna fitowa ya khalil ya doshi room ɗin dake kusa dana Ya Garkuwa, tsayawa Garkuwa yayi tare da cewa.
" Bros, me kuma zamuyi a wannan room ɗin."
" Wajen Mrs Love ɗin naka zamuje a nan take ba'a waje ba."
" Okay!!! Wayo kuka min kenan, kun maidani yaro, kaikam Bros bashi kaci kuma zan rama."
" Sai dai ka rame" cewar ya khalil yana shigewa room ɗin bayansa Garkuwa yabi, a zaune ta hangota tayi shuru, da sauri ya nufota, shi kuwa Ya khalil ya tare gabansa yana dariya, hanun Ya Garkuwa ya kama dana Jummo ya haɗa waje guda yana runtse idanunsa, har cikin zuciyarsa yaji zafi, sai dai duk da zafin da zuciyarsa ke masa hakan bai hana annuri bayyana a saman fuskarsa ba, cewa yayi.
" Ka kula da ita saboda kayi dace idan har ka samu aurenta duk rintsi duk wuya karka sake ko da wasa ka rabu da ita nasan akwai danja da ƙalubalen da zai fuskanto soyayyar ku, ka daure ka tsallake wannan siraɗin" Daddy Ya khalil ya kalla tare da cigaba da cewa.
" Daddy ga Jummo da Garko suna son junansu, sai dai ina da tabbacin zasu fuskanci matsala a cikin Soyayyar su, dan Allah Daddy ka zamo musu katangar da zata ƙetarar dasu siraɗin dake gabansu, idan ka samu a matsayin suruka, Daddy zakayi alfahari da ita."
Ya ƙarisa Maganar idanunsa yayi jajur tamkar garwashin wuta, Ya Garkuwa da kallo yabi Ya khalil bakinsa cike da tambayoyin ina khalil yasan akwai Soyayya tsakanin sa da Jummo, sannan menene ƙalubalen da yake tunkarar su cike da nauyin baki yace.
" Ƙalubale kuma Bros, wani irin ƙa............"
Hanu Ya khalil ya ɗaga masa tare da cewa.
" Daga kai har Daddy dan Allah karku min tambaya game da wannan ƙalubalen, lokaci shi zai baku amsar ku."
Daddy shuru yayi ba tare da yace komai ba, ya kalli doctor tare da cewa.
" Zaku iya bamu sallamar Garko, ita kuma sai ku taimaka ku bani takaddar transfer daga wannan asibitin zuwa medical center, saboda nan ɗin ya mana nisa sosai please help you Doctor."
Shuru doctor yayi yana tunani kafin daga baya yace.
" Okay ba damuwa ku biyoni office."
Da to Daddy ya amsa suka bi bayan doctor har Garko, Jummo jingina kanta tayi jikin gadon tare da yin shuru ta rufe idanunta, Mamma take hangowa "ko wani hali take" ta furta a fili.
Can kuwa DOCTOR ya basu sallama yayin da ya bawa Daddy takadda ya kai medical center, su kula da Jummo, haka kuwa sukayi daga sj gaɗam ɗin suka wuto medical, tare da yin duk wani cuku cuku daya dace aka basu room, Ya khalil ne ya bawa Jummo wayarta, wanda cikin ikon Allah babu abinda ya samu wayar, karɓa tayi suka barta da A'illo sannan suka koma gida, koda suka koma Momy da sauri ta rungume Garko tana dariya tace.
" Alhamdulillah!!! Allah mun gode maka, sannu Garko sannu."
Murmushi Garkuwa yayi yana ƙanƙame Momy cike da so da ƙauna, Ya khalil ne yace.
" Momy baki tambayi jikin Jummo ba."
Harara Momy ta watsa masa gudun bakin Daddy yasa ta cewa.
" Ya jikin nata."?
Murmushi Ya khalil yayi tare da cewa.
" Da sauƙi" yana shigewa room ɗin Mamma, tana nan kwance yanda take jikin babu wani sauƙi, sai Zarah dake zaune gefen INNO yayin da INNO ke haɗa wani ruwan magani, kallon khalil tayi tace.
" Kalilu ya jikin Jummo ta farfaɗo kuwa."?
" Ehh ta farfaɗo kuma Alhamdulillah ta dawo cikin hankalinta, INNO ya labarin jikin Mamma har yanzu babu wani sauyi."?
Shuru INNO ta yi cikin sanyin jiki, domin kuwa ita kanta rashin lafiyar Mamma ya fara bata tsoro.
" Kalilu gashi nan dai babu wani sauƙi, kullum jiya i yau, hmmm!!! Amma tabbas sihiri ne, sai dai na rasa gane ta ina zan fara karyasa, ni ba duba nake ba bare na duba taya abin ya faru addu'a kawai ya kamata mu dage dashi amma ciwon nata baya jin magani."
Shima ya khalil cikin sanyin jiki ya zauna tare da furta.
" Allah ya bata lafiya, sun juma sosai suna hira da INNO, a yanzu Aunty Zarah ta ɗan sauƙo daga gabar da take dashi.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Akwana a tashi babu wuya a wajen Ubangiji yau har satin Jummo Uku a asibiti ana kula da ita saboda suna tsoro matsalar ƙwaƙwalwa shiyasa suka riƙeta, sai yau suka bata sallama sosai Jummo tayi sauƙi tamkar bata samu matsala ba, haka suka dawo gida, baƙin cikin dawowar Jummo tamkar zai kashe Momy, ko sannu da jiki bata cewa Jummo ba, Aunty Zarah kuwa ta mata sannu tamkar babu abinda ya haɗa su.
Haka Rayuwa ta cigaba da garawa a cikin wannan gidan yayin da Mamma jiki kam babu sauƙi, Jummo kuwa da Momy ƴar tsama a tsakanin su sai ma ƙaruwa da yayi.
Ya Garkuwa dake zaune a cikin room ɗinsa ne yaji wayarsa ta ɗauki kuka, ganin Sadiya ke kira ya sashi ƙin ɗaukar wayar kusan 10 miss call ta masa bai ɗaga ba, shigowar text yaji wayar ya ɗauka tare da duba saƙon yaga abinda ta rubuta.
*_Shi dai butulu duk inda yake wallahi yayi asara, Garkuwa ka cuceni ka lalata min rayuwata kai kawar min da mutunci na, sannan ka gujeni, na baka duk wata Soyayyar gaskiya amma ka cutar dani ta hanyar amfani da Soyayyar da nake maka, bazan ce zan tona maka asiri ba, domin kaina zan tonawa, sai dai ka sani na barka da Allah insha Allah a cikin ƴaƴan da zaka haifa sai Allah ya saka min, daga yau bazan kuma shiga rayuwarka ba, kaje kai da Allah, Allah Ya isa tsakanina da kai mungu azzalumi._*
Runtse idanunsa ya Garkuwa yayi da ƙarfi yana jin ƙunar maganganun ta, bude idanun nasa yayi take har sunyi jajur, text ɗin ya goge cike da sanyin jiki, cikin zuciyarsa yana neman afuwar Ubangiji.
Sadiya kuwa bayan ta tura text ɗin ne ta fashe da kuka tare da Kwanciya ruf da ciki, duk da tasan tarayyar ta da ya Garkuwa kuskure ne, amma bata taɓa tunanin akwai ranar danasani ba a rayuwarta, ba mamaki wannan shine hukuncin zunubin da ta aikata, shin yanzu waye zata Aura ya ganni da mutunci, me zan cewa mijin da zai Aure ni, idan ya tambaye ni ina na kai budurcina mai zance mishi, tabbas na aikata kuskuren da bazai taɓa goguwa a idanun mijin da zan aura ba, Allah ya isa tsakanina da kai Garkuwa ka cutar da rayuwata.
Ta ƙarisa zancen zucin tana share hawayen dake gangaro mata tare da alƙawarin mantawa da Garkuwa a cikin rayuwarta.
Safreena sosai taji daɗin labarin da Zee ta kawo mata na cewa Garkuwa ya dawo hayyacinsa harma an sallamesa a asibiti ya dawo gida, hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba, a yanzu ƙiyayyarr da take yiwa Garkuwa yayi sauƙi sosai a cikin zuciyarta, a yanzu bata da burin daya wuce taga bayan Kawu Ibrahim, burinta ta ɗaukawa iyayenta fansa wannan shine kawai a ranta.
Yau tun safe Mamma take wani irin tari tun sanda INNO ta bata wani ruwan magani take wannan tarin, wani irin yalon kumfa ke fitowa daga bakinta, Jummo ke saka tisue ta goge wannan kumfa, INNO ta sani sarai tasirin gubar asirin da aka sawa Mamma ke fita daga jikinta, amma INNO tayi shuru taƙi faɗawa kowa gudun kar wanda yayi asirin yaje ya lalata mata shiri, su duk a zaton su jikin Mamma tsanani ya ƙara Jummo harda kuka, a yayin da a zahiri Mamma sauƙi takee samu Momy kuwa sosai take murna jikin Mamma ya ƙara tsanani.
*******************
Zaune Jummo take a falo tayi shuru cike da tunani, kusa da ita Ya Garkuwa ya zauna ba tare da ta lura da zamansa ba, taɓata yayi a hankali ta juyo tana kallon sa sai kuma ta ɗan saki murmushi.
" Ya Garkuwa yaushe kazo nan"?
Taɓe bakinsa yayi tare da cewa.
" Sanda kike duniyar tunani, meke damunki haka kikayi nisa cikin tunani."?
" Ya Garkuwa kasan ai tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, matsalar Mamma ke ɗaga min hankali tana sani cikin damuwa, ciwo kullum ba sauƙi sai ma gaba da ciwon ya ƙara ga INNO ma tazo amma har yanzu jiya i yau, yanzu haka zamu zubawa Mamma idanu a wannan halin."
Numfashi Ya Garkuwa ta saki yana dafe fuskarsa yace.
" Bazai yiwu a barta haka ba, idan INNO ta kasa ya zamo dole a nemo wani mai bada maganin, ki kwantar da hankalin ki, insha Allah duk inda ake nemo lafiya zamu nemowa Mamma bana son ganinki cikin damuwa."
" To shikenan Ya Garkuwa Allah yasa ya bata lafiya, ya Garkuwa ina labarin budurwar kane.?"
Cike da tsantsar mamaki yace.
Budurwata kuma, waye kuma budurwata bayan ke, kinga nifa gobe zan sanar da Daddy kawai aje Cilo a nemo min Aure ki, ayi kawai mu wuce wajen, na matsu na kasance da ke waje ɗaya Inuwa ɗaya kin san kuwa irin tsantsar Soyayyar da nake miki, ji nake tamkar na mai daki cikina tsabar so ina sonki Jummo."
Dariya Jummo tayi har haƙwaranta na bayyana cikin zolaya tace.
" A'a malam, aje Cilo da izinin waye, waya faɗa maka ina sonka, kaga fara sanar dani labarin Soyayyar ka da Sadiya kafin ka fara zancen Aure na, da alamu dai kun ɗan soye."
Dariya mai sauti ya Garkuwa yayi tare da cewa.
" Ehh mun soye harma mun kusa ƙonewa kwatsam ki shigo rayuwata kika ɓata tsakanin mu."
Wani irin bugawa zuciyar Jummo yayi take taji kishin