Showing 54001 words to 57000 words out of 93605 words

Chapter 19 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

Sadiya har kamar haushinta taji, tsumewa tayi tare da cewa.

" Oh nine ma na shiga tsakaninku ko, kuna son junanku na rabaku to meyasa yanzu bazan fita a rayuwar taka ba, idan yaso kuje ku babbake ma ba soyewa ba."

Tayi Maganar tana tura baki, hango kishi ƙarara yayi a idanun Jummo, dariya yayi sosai har dimple nasa yana loɓawa yace.

" Malama kece fa kika tambayeni ni kuma na faɗa miki gaskiya, to meye kuma na haɗa fuska, bayan kece mai tambayar, bari ma da kiji wato ni da Sadiya ko munsha.................."

Yatsanta Jummo tasa ta toshe kunnenta tare da cewa.

" Ni ya isheni haka bana son ji, dan Allah kayi shuru karka ƙarisa na roƙeka."

Dariya Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Ashe dama haka kike sona sosai, duk wannan kishin wani kike mawa, alhamdulillah!!! Kwantar da hankalin ki farin ciki na, Sadiya dai mun ɗanyi Soyayya amma ba mai tsawo ba, asali ma babu zancen Aure tsakanina da ita, itace take ɗaukar Soyayyar da mukayi a matsayin zan aureta amma babu alƙawarin Aure tsakanina da ita, a yanzu haka albishir ɗin da nake son na miki, shine babu wata alaƙa tsakanina da Sadiya, mun raba Gari kowa ya kama gabansa."

Murmushi Jummo ta saki tare da juyowa ta fuskanci Ya Garkuwa tace.

" Dole nayi kishi a kanka karka manta da tun kafin nasan meye Soyayya zuciyata take ƙaunar ka, har zuwa yanzu da nasan darajar so, matsuguninka bai sauya a zuciyata ba, sai ma wajen zama ka ƙara samu a gareni, Ya Garkuwa daga yau sunanka ya sauya daga Ya Garkuwa zuwa Heartbeat wato bugun zuciya ta, kaine murmushi na kuma haske na, ban san Soyayyar wani namiji ba, bayan taka, ina sonka zan kuma kasance da kai a ko wani hali ka tsinci kanka a rayuwa bazan taɓa juya maka baya ba, zan tayaka mu rungumi dukkan wata ƙaddarar da tazo maka mai kyau ko marar kyau wannan alƙawari na ɗauka mutuwa ce kawai zata rabani da kai."

Tunda ta fara Maganar Ya Garkuwa ya lumshe idanunsa cike da jin daɗin zantukanta, ya sani itace kawai ke masa Soyayyar gaskiya har abada bazai samu mai sonsa da gaskiya irinta ba, sunanta ya furta a hankali.

" Jummo!!"

Ɗago idanunta tayi tare da amsawa tana murmushi kansa Ya Garkuwa ya kawar gefe tare da cewa.

" Karki ɗauki alƙawarin kasancewa dani ta ko wani hali domin kuwa ina tare da aibun da zaki iya tsanata kiji bazaki iya zama dani ba bare kuma Rayuwa ta har abada, a kullum ina son na sanar dake wannan aibun nawa kuma ina tsoron yanda zaki ɗauki zancen wata ƙila ma ki tsaneni ko ki gujeni, ni mai tarin zunubai ne Jummo, duk da tawa ƙaddarar ce tazo da haka, amma a yanzu na tuba nayi tuba ta haƙiƙa shin Jummo zaki iya kasancewa dani idan kikaji mungun halina, ina tsoron kiji ki rabu dani, rabuwa dake a wannan lokacin zai iya zamowa ƙarshen numfashi na.?"

Shuru Jummo tayi tana kallon ya Garkuwa cike da mamaki, mungun hali tarin zunubai da yake ambaton yana dashi, cike da ƙwarin gwiwwa tace.

" Ka faɗa koma menene ni zan tayaka mu rungumi ƙaddarar, tunda har kace ka tuba, shima kansa Allah ai gafurun rahim ne, bare kuma ni wata banza Jummo, ka faɗa min komai ba tare da tsoro ba, ni kuwa zan karɓi ko mai munin halinka a matsayin ƙaddarar rayuwata."

Ya Garkuwa sunkuyar da kansa ƙasa yayi ba tare daya kalli Jummo ba ya fara cewa......."




*UMMU NASMAH CE*


✨✨✨✨✨✨✨✨✨
[4/19, 9:51 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*




➰➰ *49 to 50*




" Rayuwata ta kasance ne cikin mungun saɓon Ubangiji wanda Allah ke fushi da mai aikata sa, na kasance mutum mai jarabar tsiya wanda sam bana iya riƙe buƙatata, ni mutum ne ma'abocin jarabar mace, akwai wata yarinya mai suna Safreena!! School ɗin mu ɗaya da ita munyi karatu da ita a Oxford University dake ƙasar Amurika, ita set ɗin ƙasan mune, a lokacin da idanuna suka sauƙa akanta naji zuciyata ta aminta da ita naji ina sonta, sai dai ita macece mai kamun da sanin darajar kanta, Asali ma ko ƙawa bata dashi a cikin school ɗin, bare kuma aboki namiji, a sanda naga Safreena na kuma ji ina sonta na fara tunanin ta yaya zan ƙulla alaƙa da ita wanda har zan samu ta saurareni, na kai sati Uku ina nazarin yanda zan fara tunkarar ta, kwatsam wata ranar monday, aka basu assignment Wanda Wannan assignment ɗin shine zai zamo S'A test ɗinsu assignment ne mai matukar wahalar gaske akan biological sciences wanda shi kansa lecturer ɗin daya basu wannan assignment idan aka ajiye sa ba lallai ya iya amsa dukkan waɗannan Quation ɗin ba, hankalin su ya tashi suka haɗa group domin ganin sun amsa wannan Quation amma suka gagara sun karaɗe dukkan school ɗin suna neman amsar amma basu samu ba, hmmm!!" Shuru yayi tare da kallon Jummo ya cigaba da cewa.

" kinsan meya faru a wannan lokacin?"

Girgiza kanta Jummo tayi alamun a'a cike da sanyin jiki da kuma jin kishin wacce ake bata labari a kanta, cigaba da Magana ya Garkuwa yayi.

" Abokina Shetima Ladan ne yazo yake sanar dani zancen assignment ɗin da aka bawa ƴan Cause ɗinsu kuma sun gagara samu, a wannan lokacin wani tunani ya faɗo min, me zai hana naje na ƙarɓo Quation ɗin da zumar zan amsa musu, duk da nasan bazan iya ba tunda ba Cause ɗina bane, amma na ɗauki wannan kasadar da wannan tunanin naje na tunkari Safreena, da farko da naje bata saurareni ba, sanda na nawa ƙawarta Zee bayanin abinda ya kawo ni sannan Zee ta sata saurarana dole, na karɓo assignment ɗin, tare da alƙawarin da safe zan kawo musu, room ɗin na koma na dafe kaina ina tunanin taya zan amsa abinda bani da ilimi a kansa, nakai 11 na dare ina nazari, kafin daga baya tunanin Bro khalil Cause ɗin da yayi kenan ya kuma zo first class, numfashi na sauƙe tare da kiran wayarsa nake sanar dashi halin da nake ciki sosai ya min dariya kafin daga bisani yace na turo masa Quation ɗin ta WhatsApp, haka kuwa akayi na tura masa cikin ikon Allah a 1 hours Bro khalil ya amsa dukkan tambayoyin ya aiko min dasu, cike da farin ciki washe gari na kai mata sosai taji daɗin abinda na musu, da wannan alaƙa Mai ƙarfi ta shiga tsakanina da Safreena, ya zamanto dukkan wani assignment idan aka bata bata gane ba, sai ta kawo min ni kuwa na bawa Bro khalil ya amsa mata, da haka muka shaƙu har Soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin mu, sosai muka shaƙu da juna yayin da idan ɗaya baiga ɗaya ba hankalinsa baya kwanciya, muna tsaka da tsaftacacciyar Soyayya, na kammala karatuna, mukayi graduation, Sosai hankalina ya tashi ina tunanin ta yaya zan iya rabuwa da ita, itama hakanne a wajen ta harma ta zarta ni shiga cikin tashin hankali, ranar Sunday itace ranar walimar kammala karatun mu, a kuma ranar wani mummunan al'amari ya faru tsakanin mu da Safreena hmmm!!! Wannan baƙar rana ce a gareni wanda bazan taɓa mantawa da ita ba a rayuwata, Jummo Safreena tamin alƙawarin zuwa walimar kammala karatun mu, a wani holl da muka kama, a ranar dukkan abinda ya faru, nafi Safreena amma itace ta janyo hakan, Safreena ta shigo wannan holl ɗin da wani irin shiga wanda sam bai dace da shigar ɗan musulmi ba, ni kaina ban taɓa zaton Safreena zatayi irin wannan shigar ba, saboda kamun kanta, sai kuma aka samu akasi tayi wannan shigar wanda ita ba wai tayisa da nufin komai bane, rigace fara tas wacce ta kama jikinta sosai da wando jeans Wanda shima yayi mungun kamata tamkar zai fasa jikinta, komai na surar jikinta ya bayyana, gashi kuma ta saka ƙaramin gyale wanda ko ƙirjinta bai rufe ba, tunda na saka idanuna akanta a wannan daren, hankalina ya tashi sha'awa ta ta motsa na gagara control ɗin kaina, duk da haka nayi ƙoƙarin korar sheɗan daga zuciyata, amma banci nasarar korar sa ba, sai ma tunzurani daya yi, Jummo na taƙaice miki a wannan daren sanda nasan yanda nayi na sawa Safreena maganin kawar da hankali a ruwa tasha, na jata zuwa wani room, a wannan daren na lalatawa Safreena budurcinta........."

Wani razana Jummo tayi ta miƙe tsaye tare da dakatar da Ya Garkuwa ta hanyar furta.

" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! What!!! Y..y...y...y... ya garrrrrkuwa!!! Kai ɗin ne kayi wannan mungun aikin.!!!"?

Jummo ta furta maganar cike da in'ina daƙyar Maganar ke fita tana nuna Ya Garkuwa Da yatsa.

Share hawayen daya wanke masa fuska Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Kin firgita ko, baki taɓa tunanin zaki sameni da wannan mugun tabon ba, ko shiyasa na ce dole zaki tsan.........."

" Shittttttt!!!! Karka ƙarisa, ka cigaba da bani labarin kawai."

Tayi Maganar itama tana share hawayen ta.

Hankalina bai dawo jikina ba sai bayan na gama haye mata daga nan ne na fara jin takaicin abinda ya faru, ko da Safreena ta farfaɗo sosai hankalinta ya tashi ta shiga cikin damuwa da tashin hankali ta dinga kuka tamkar ranta zai fita, a wannan lokacin bani da bakin mata Magana saboda kunyarta, cike da haushina da tsanata Safreena ta miƙe taje tolet ta gyara jikinta ta mayar da kayan jikinta, tana ɗan ɗingishi ta bar holl ɗin gaba ɗaya, a ranar koni ba'a tashi walimar dani ba, hankalina ya tashi na shiga cikin damuwa sosai, na kasa hkr har sai da na sanar da abokina Shetima abinda yake faruwa shima sosai ransa ya ɓaci, yamin masifa tamkar zai dakeni, abun mamaki duk da abinda ya faru tsakanina da Safreena banji sonta ya ragu a cikin zuciyata ba, sai ma ƙaruwa da yayi, munje nida Shetima domin bawa Safreena hkr, amma taƙi ta haƙura ko sauraronmu batayi ba, sai ma Allah ya isa da take jamin, na shiga cikin ɗimuwa da ganin tsanata a idanun SAFREENA, haka dole muka barta ba dan naso ba, tun daga wannan Ranar Safreena ta fita daga rayuwata ta daina kulani, ni kuwa na shiga cikin damuwa, ga kuma zan koma gida, har ƴar wata rama nayi, haka na dinga yiwa Safreena naci ina bata hkr, komawa gidan ma na hkr dashi, ko da ban koma gida ba nasan babu mai tambayata meyasa ban dawo ba, saboda kowa rayuwarsa yake a gidan mu babu ruwan kowa da ɗan uwansa, muddun zamu shekara muna waya da gida bazasu tambaya meyasa na gama karatu ban dawo ba, hakanne ya bani damar zama har sai na samu Safreena ta haƙura, nayi iya yina Safreena taƙi saurarata, kuma ina da tabbacin Zee ke sake nisantani da ita ita a nata tunanin na ɓatawa aminiyarta rayuwa, an kai wajen Wata shida Safreena bata saurarata ko kallo na bata yi, ni kuwa Soyayyar ta tamin kamun da bazan iya hkrn rasata ba, daga nan ciwon ƙirji da tari ya fara sanɗata sakamakon damuwa da nake ciki, tun ina jin ciwon kaɗan har sai da ya yasar dani, ƙarshe har sai da na kwanta a asibiti, nasha rashin lafiya na ciwon ƙirji tamkar zan mutu, kafin Safreena ta dawo gareni, ganin ina ƙoƙarin rasa rayuwata saboda ita, daga nan ta kuma yarda dani a karo na biyu zuciyarta ta aminta son gaskiya nake mata"

Kallon Jummo yayi ya cigaba da cewa.

" Nayi mamaki da DOCTORn daya kula dani Asibitin Sj gaɗam bai gane ciwon zuciyar dake jikina tsohon ciwo bane, domin kuwa na samu wannan ciwon zuciyar ne ta sanadin Safreena, sakamakon rasata da na kusa yi, ban sanar da kowa damuwata ko soyayyata a gidan mu ba, hatta ciwon da nayi babu wanda ya sani a gidan mu, na ɗauru akan maganin zuciya shekara biyu da suka wuce ba tare da kowa yasan ina da wannan ciwon ba, sai Shetima kawai shima na roƙesa da karya sanar da kowa, harta ita kanta Safreena bata san ina da ciwon zuciya ba, haka Soyayyar mu ta koma tamkar da da Safreena, sosai muke bawa juna kulawa, duk wata hirar mu muna yinta ne akan Maganar Aure, Jummo kuskure na na biyu shine ya shiga tsakani na da Safreena har mukayi rabuwa ta har abada.

Jummo kallon Ya Garkuwa tayi tare da cewa.

" Bayan wannan kuskuren da ka mata mai muni har kuma akwai wani kuskuren bayan shi.?"


" Eh akwai Jummo, Tun daga randa Safreena ta gama zaucewa a soyyayyata daga ranar ta fara amsar umarnina, nakan yawan jin sha'awar Safreena, yayin da bana iya riƙe sha'awata, akwai ranar da Safreena ta zo room ɗina ta sameni ciwon mara tamkar zai kasheni, tun da Safreena ta shigo hankalina ya tashi ciwon marata ta ƙara tsanani, babu abinda nake buƙata fa ce jikin Safreena, a wannan daren na shiga cikin wani irin tashin hankali, a yayin da na jawo Safreena ina roƙonta ta amince min karna mutu tare da mata alƙawarin cewa Soyayyar ta bazata taɓa gushewa a zuciyata ba, na mata alƙawarin cewa zan aureta ta ko wani hali, Soyayyar da Safreena take min ya sata jin tausayin halin da nake ciki, a wannan daren Safreena ta ƙara bani kanta a karo na biyu tun daga wannan Ranar Safreena ta yadda dani na maidata tamkar matar da na biya sadakinta, na kai kusan shekara guda a ƙasar Amurika bayan kammala karatu na, a lokacin ita kuma Safreena sauranta shekara ta kammala nata karatun, ni kuwa na dawo gida Nigeria, sanda zan tafi sosai hankalin Safreena ya tashi tayi kuka sosai, a haka muka rabu kowa zuciyarsa babu daɗi, koda na komo Nigeria kullum muna maƙale ni da Safreena a waya, Soyayyar ta ko kaɗan bata ragu a zuciyata ba sosai nake sonta Soyayya ta gaskiya, kuma har a wannan lokacin ina jin a zuciyata Safreena ce matar da zan aura."

Bayan Safreena ta gama karatun ta, ta dawo gida Nigeria a lokacin ni kuma na fara aiki, sai muka cigaba da Rayuwa kamar yadda muke a America, gidan su Safreena kowa ya sanni yasan Soyayyar dake tsakanin mu, haka gidan mu ma, a wannan lokacin an san da maganar mu da Safreena, kwatsam rana ɗaya ciki ya ɓullo a jikin Safreena, sosai hankalinta ta tashi, ko da take sanar dani ban mata musu ba, domin kuwa ina da tabbacin cewa cikina ne, saboda na yarda da tarbiyyar Safreena bata mu'amala da ko wanni namiji sai ni, sai dai na buƙaci Safreena da muje a zubar da cikin, amma Safreena taƙi tace bazata sake aikata wani zunubin ba, bayan na zina ga kuma na kisan kai, duk yanda naso yiwa Safreena dabara a zubar da cikin nan taƙi, mun kusa sati biyu muna bugawa da ita sam taƙi amincewa hakan yasa harna hasala na mata barazana wai ko zataji tsoro ta yadda muje a zubar da cikin, nace mata, idan har bata yadda an zubar da wannan cikin ba, to ta cireni cikin rayuwarta, babu ni babu ita ban sanki ba, sannan karki alaƙanta wannan cikin dani, muddun kuwa kika alaƙanta wannan cikin dani sai naga bayanki da na iyayenki zan ɓatar daku a duniya a daina jin labarin ku, da wannan kalaman na yiwa Safreena barazana wai ko zan samu ta amince a zubar da cikin amma Safreena taƙi, tace ta amince mu rabun amma cikin jikinta sai ta haifesa da wannan muka rabu kuma shine rabuwa ta ta ƙarshe da ita, da kwana biyu sai naji labarin cewa gidan su Safreena yayi gobara dukka mutanen gidan sun mutu babu wanda ya rayu a cikin su sosai hankalina ya tashi nayi baƙin cikin mutuwar Safreena nayi kuka kamar zan mutu, hankalina yayi mungun tashi nayi kewar Safreena."

" Jummo wannan shine mungun kuskuren dana aikata amma har yau da nake baki wannan labarin dai-dai da kwayar zarra Soyayyar Safreena tana raina ina sonta tamkar yadda nake sonki, babu bambancin Soyayyar da nake miki da wacce nake yiwa Safreena, Soyayya ɗaya nake muku."

Cike da sanyin jiki Jummo ta zauna tare da cewa.

" Allah Sarki har naji tausayin ta, ta koma ga mahallicinta da cikin da bana sunnah ba, Allah ya ji ƙanta ya gafarta mata, naji tausayin ta matuƙa, to amma ita kuma Sadiya fa."

Kallon Jummo yayi tare da runtse idanunsa yace.

" Itama mun taɓa bariki da ita amma babu zancen Aure a tsakanin mu, itace kawai ke sona amma ni banyi mata alƙawarin Aure ba, a yanzu haka mun rabu da Sadiya, na kuma yi sahihiyar tuba insha Allah bazan kuma zina ba, na tuba wa mahallicina."

Numfashi Jummo ta sauƙe tare da cewa.

" Na fahimci komai, zan kuma kasance da kai har abada, sai dai dole idan kana son zamanmu yayi nisa mu kasance har abada dole ne kayi tsaftacacciyar tuba, Wanda babu gurbata a cikin sa, idan har ka kasance a haka zamu zauna har abada ni da kai, idan kuma kayi tuban muzuru, dole ne zamu rabu, kuma dole muje muyi test kafin ka fito da Maganar Aure tsakanin mu."

" Na yadda da duk sharuɗanki kuma zaki sameni mai cika alƙawari."

Yana gama faɗin haka ya tashi yabar wajen, da kallo Jummo ta bisa harya shige bedroom ɗinsa, sannan itama ta tashi.

A wannan daren sosai Jummo ta ninƙaya tunanin Rayuwar Ya Garkuwa wanda ko da a mafarki bata taɓa zaton haka yake ba, sai dai tana jin a zuciyarta Garkuwa ya sauya, Kuma insha Allah tana jin a ranta zata kawo haske a rayuwar Ya Garkuwa, da wannan tunanin bacci ya ɗebeta.






✨✨✨✨✨✨✨✨✨


*Bayan Wata Shida*



Zuwa yanzu Soyayyace mai ƙarfi ta shiga tsakanin Jummo da Ya Garkuwa, kullum suna maƙale a waya idan kuwa yana gida to suna tare a yayin da Momy ta hango shaƙuwar Jummo da Garkuwa sai hankalinta ya tashi ƙwarai, domin kuwa ta fara zargin Soyayyace a tsakanin su da wannan tashin hankalin ta kira ya Garkuwa.


" Ka faɗa min meye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login