Showing 66001 words to 69000 words out of 93605 words

Chapter 23 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

Garkuwa yace.

" Ina jinka Garko Bismillah kayi maganarka ina da isasshen lokaci."

Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.

" Daddy dama maganar itace, amm amm amm dama Daddy akan batun AURENA nane Daddy na samu matar Aure shine nake son ka shige min gaba kaje ka min tambayar auren ko zuwa jibi ne."

Murmushi Daddy yayi tare da cewa.

" Oh Garko yanzu wannan maganar zaka min shine kake inda inda, wannan ai abun farin ciki ne, naji daɗin wannan maganar taka Garko, a ina ka samu matar waye mahaifinta.?"

" Amm Daddy ba wata bace fa, Jummo ce jikar INNO ita na fitar a matsayin matar da zan aure."

Cike da farin ciki Daddy yayi murmushi tare da cewa.

" Masha Allah, abu yayi kyau shikenan zamuyi tuwo na maina wannan ai duk gida ne Garko babu bare tsakanin ka da Jummo dukkanku ƴaƴana ne, karka damu zanje har ƙauyen next week na samu Baffa muyi magana, insha Allah nan kusa za'a saka lokacin Auren Allah ya maka albarka."

Cike da farin ciki Garkuwa yake duban Daddy alhamdulillah Daddy ya amince Momy ce matsalar kuma.

" Daddy sai kuma akwai matsala fa."

" Matsala kuma Garko wacce irin matsala.?"

" Daddy Momy bata son Wannan auren tama ce muddun na matsa akan dole sai na Auri Jummo zata ɗaga min nono Daddy shiyasa hankalina yake tashe bansan meyasa Momy bata son Jummo ba, ka taimake ni Daddy kayi Magana da ita ko zata hkr ta janye."

Cike ɓacin rai Daddy ya ɗago idanunsa ya kalli Garkuwa tare da cewa.

" Serious ita Hajiya Zainab ɗin ce bata son Auren."

" Ehhh da gaske Momy bata so."

Numfashi Daddy ya saki tare da cewa.

" Garko karka damu wannan Auren za'ayisa babu makawa ko tana so ko bata so ka barni da ita dole zata amince tashi kaje abinka."

Tashi Ya Garkuwa yayi yana murmushi ya fita, yayin da Daddy yake cike da mamakin meyasa Hajiya Zainab zata ƙi wannan Auren, amma koma dai menene yasa a ransa gobe zai kira meeting ɗin gaggawa.

Washe gari da safe bayan kowa yayi breakfast Daddy yayi gyaran murya tare da duban Aunty Zarah yace.

" zara'u maza shiga room ɗin Mamma kice suzo muna falo za'a tattauna magana mai mahimmanci."

Da to Aunty Zarah ta amsa shi kuma Daddy ya miƙe zuwa cikin falon, ya khalil da Ya Garkuwa suka rufa masa baya Momy duban Zizah tayi tace.

" Muje"

Ta ƙarisa Maganar tana miƙewa tayi wajen nasu Jummo kallon A'illo tayi ba tare da ta miƙe ba tace.

" Kije mana A'illo bakya jin Daddy yace kuje ku samesa a falo.?"

" Naje ko muje, ya kina Magana kuma kina cire kanki acikin Maganar.?"

Murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Dole zan cire kaina a ciki domin kuwa wannan meeting ne na FAMILY bayan kuma ni barece a tsakanin ku, Kinga kuwa bani da hurumin shiga cikin ku, ki tashi kije.''

" Ya kamata ki daina kiran kanki bare domin kuwa kin bawa wannan gidan gudumowar da jininta ya kasa bata kin fi ƙarfin bare."

Murmushi Jummo tayi tare da cewa.

" Naji amma dai ki tashi ki tafi."

Kaɗa kanta Jummo tayi tare da miƙewa tsaye tayi cikin falon, Mamma tare suka shigo da INNO suka zauna cike da girmamawa Daddy ya gaishe su haka itama Momy ta gaishe su cike da ƙuncin Zuciya, duban kowa dake wajen Daddy yayi babu Jummo.

" Zara'u ina Jummo take ban ganta anan ba, jeki kirawo min ita."?

Da to Aunty Zarah ta amsa tare da tashi taje ta kira Jummo kusan tare suka shigo Jummo ta nemi gefe da INNO ta zauna, nisawa Daddy yayi tare da cewa Mamma.

" Mamma na tara kowa ne anan wajen domin na sanar daku wani kyakkyawan albishir wanda yamin daɗi Kuma abin ya burgeni."

Murmushi Mamma tayi tare da furta.

" Masha Allah, Garba ai abun alheri shi ake so a dinga ji, muna sauraronka."

" Mamma jiya bayan na dawo daga kasuwa Garko yazo ya sameni da Maganar cewa ya fidda matar Aure kuma Jummo itace ya fitar, har yake neman alfarmar cewa na je na masa tambaya, shine nace bara na fara sanar daku kafin na isa ga Baffa."

Ai kuwa kafin Daddy ya rufe bakinsa Momy tayi carap tace.

" Wani Garkon ba dai ɗana ba, domin kuwa bazai Auri Jummo ba, na riga na yanke hukunci mun juma da gama wannan maganar kuma shima gashi gabanka ka tambaye sa, ya hkr."

Da kallo kowa na Wajen ya bita har INNO Daddy kuwa dariya yayi tare da gyara zamansa yace.

" Naji maganarki Zainab, to amma bara naji hujjar ki kuma na haramta Aure tsakanin su, idan tana da makama sai a duba lamarin sanar dani meyasa bakya son Auren.?"

Shuru Momy tayi tare da jefawa Garkuwa mungun kallo kafin tace.

" Saboda bana ƙaunar haɗa jini da gidan Arɗo Bazan haɗa jini da Jikar gidan ba, kaima ka sani, a matsayina na Uwar da ta haifi Garko, nace bana son Wannan Auren, bazai Auri wannan fitsararriyar Yarinyar ba, dan haka dole a haƙura da wannan Auren."

Murmushi INNO tayi Daddy zaiyi Magana ta ɗaga masa hanu tana cewa.

" Ɗan dakata tukunna Garba na tambayeta"

Daddy shuru yayi yana duban Momy dake famar huci tamkar kububuwan maciji INNO ce tace.

" Lallai Zainabu har yanzu dai kina nan da rashin kunyarki baki fasa ba, yanzu ke idan kina da kunya har kin isa kice bakya son haɗa zuri'a da Arɗo saboda ya ƙarshen ubanki shiyasa kike tsoron itama Jummo jinin sa ta kawo ƙarshen rashin mutuncin ki a cikin gidan nan, kin sani Zainabu Wallahi kaf zuri'ar mu bamu da abun kunya kuma babu Boka ɗan tsibbu a danginmu, malam addini muka tara wanda suka iya karatun Alkur'ani suka san fassarar sa, da littatafan addini, dan haka ki iya bakinki akan zuriata idan ba tonon asiri kike bukatar muyi ba."

Daddy ne ya ɗaura da cewa.

" Rabu da ita INNO wannan soki burutsu ne kawai take babu wani hujja da take dashi wanda zaisa a fasa wannan Auren Garko ɗana ne, nine Ubansa wanda na ɗauki ɗawainiyar rayuwarsa, dan haka wajibi ne wannan auren babu abinda zai hana ayisa sai tsantsar ikon Allah nine nake da iko dashi ba ke ba dan haka ki fita a idanuna Hajiya Zainab."

Miƙewa tsaye Momy tayi a fusace cikin ɗaga murya tace

" Ka daina kiran ɗanka kai ɗaya kasa minjaye cikin sautin ka, kace ɗanmu domin kuwa nice na goyi cikin sa, na shayar dashi daga fatar jikina, naci kashinsa da fitsarin sa, na juri duk wata ɗawainiyarsa karka manta kafin Allah ya ambaci Uba sai da ya ambaci Uwa sau uku, ya kuma ce daga shi sai ita kaga kuwa ai ba ƙaramar daraja muke da ita ba, dan haka nace Garko bazai Auri Jummo ba kuma dole ya hkr muddun yana neman albarka ta, idan ba haka ba na ɗaga masa nono."

Mamma murmushi tayi tare da tashi ta miƙe cikin gwarin hausarta tace.

" *TARIHI YA MAIMAITA KANSA* gaskiyar masu iya magana ne da sukace duk abinda ka aikata mai kyau ko marar kyau ka jira juyowarsa domin kuwa babu makawa sai ya dawo maka, gashi ke yanzu ya dawo miki zaki ɗanɗani wani irin ɗaci naji duk da ni na fiki hujja, ashe dama Uwa tana da wannan darajar da kika lissafo baki taɓa nunawa mijinki shi yabi tasa Uwar ba, ashe Uwa tana da iko da ɗanta, kika nuna cewa Uwa bata da mahimmanci a baya" kallon Ya Garkuwa Mamma tayi cike da ɓacin rai idanunta na ƙoƙarin kawo ruwa tace " Garko a sanda ubankuu zai Auri Mahaifiyar ku haka na nuna tawa ƙiyayyar, duk da ni tawa ƙiyayyar mai hujja ce, da shike gidan uban uwarku ƴan tsubb............."

Saurin katseta Jummo tayi tare da cewa.

" Ya isa haka Mamma dan Allah kar kuyi tone-tone saboda ni, kibar Maganar karki ƙarisa ta riga da ta shige karki tayar da tsohuwar magana idan nine zan hkr da Ya Garkuwa saboda a zauna lafiya, ko da kuwa Soyayyar sa zata kashe ni, zanyi jahadi domin ganin zaman lafiya a cikin gidan nan, dan Allah Mamma kubar maganar nan haka."

Cike da tsantsar ɓacin rai Daddy ya miƙe tsaye tare da cewa.

" A'a Jummo, ki rabu da ita karki ɗaga hankalinki ga Maganar Hajiya Zainab, Mamma gaskiya ta faɗa kamar yadda Zainab bata son Auren ki da ɗanta haka itama Mamma, jajurcewa da haƙiƙancewa na mahaifina dana kakanki Baffa da mahaifiyar Mamma shine yasa Auren mu da Zainab ya ɗauru, amma ki duba ki gani yanzu wai itace take cewa ɗanta bazai Auri zaɓinsa ba, Kuma ba mutumiyar banza ya ɗauko ba, gaskiya Zainab baki da kirki ko kaɗan lallai kinyiwa Baffa mummunan sakamako, to ki sani na gama yanke hukunci aure tsakanin Jummo da Garko za'ayisa kuma a gobe zanje na nema masa Auren ba kuma zamuja lokaci ba za'ayi Auren kina iya ɗaga masa nonon sai mu gani ko zai lalace."

Cike da huci Momy ta kalli Daddy cikin tsawa gami da tashin hankali ta cewa Daddy.

" Wai ya kake ƙoƙarin nuna min gadara ne akan Garko nima ina da iko dashi, wallahi muddun akayi wannan Auren ba tare da izinina ba, wannan auren bazai taɓa albarka ba, ba kuma zasu taɓa samun farin ciki ba, za Kuma kuga abu marar daɗi da zai faru a cikin wannan Auren muddun aka yisa, na muku wannan bakin kaje da umarnin ubanka Garko ka gani idan Rayuwar zata maka kyau babu albarka ta, tunda ni ban isa da kaiba bani da mutunci da daraja a idanunka, har zaka kaini Wajen UBANKA kaje duniya ce, kuma insha Allah bazaka taɓa samun farin ciki a wannan Auren ba."

Tana gama faɗin haka ta juya cike da ɓacin rai Ya Garkuwa cikin matsanancin tashin hankali yabi Momy da kallo tabbas maganganun ta sun munana garesa, anya kuwa zaiyi wannan Auren, Maganar mahaifiya tabbas bata da hijabi ga Ubangiji, INNO da kallo itama tabi Momy harta haura nisawa INNO tayi tare da cewa.

" Wai Zainab ce take cewa jininta bazai Auri Jummo ba, mu bamuce bazamu haɗa zuri'a da ita ba, wai itace take cewa haka, ɗiyar matsafi ƴan tsibbu wacce ta fito daga gidan da yayi tambari wajen Rashin Ɗa'a, hmmm!!!! Lallai Mutum mungun icce, ki duba Mamma abunda ta aika ya juyo mata amma ta kasa fahimtar hakan" duban Daddy tayi tare da cewa.

" Kaga abinda kuskuren ku ya jawo kun aikata abinda ba dai-dai ba ga rayuwar mahaifiyarka, ka zaɓi mace sama da Uwar da ta haifeka, yau gashi kana gani a gabanka tana nuna maka cewa kai uwarka ba uwa bace, yanzu kuma ta nuna cewa ita fa uwace mai ƴanci akan ɗanta, tana da ikon basa umarni yabi, yayinda kai kuma a baya ta nuna maka cewa mahaifiyarka bata da daraja bata da iko da kai, GARBA yanda a wancan lokacin bakaji Maganar Mamma ba, to ka sani yanzu ma Garko bazai ji Maganar zainabu ba, wannan Auren za'ayisa nice kakar Jummo kuma nace na bawa Garko ita duniya da lahira, ka shirya kaje ku tattauna da Baffa" tayi Maganar tana kallon Garkuwa tare da cigaba da cewa.

" Karka damu Garko babu abinda bakinta zai muku yanda akayi aurenta babu yardar Uwar mijinta Kuma suka zauna lafiya cikin farin ciki, haka kaima zaka zauna da taka matar Lafiya, ka ƙyaleta, tana cikin fushi zata sauƙa wata rana ta rungumi auren ku dole."

Shuru Daddy yayi tabbas dukkan maganganun INNO gaskiya ne, yayi watsi da mahaifiyarsa saboda soyayya, hatta ziyara ya daina kai masa, hmmm ashe dukka mata tunaninsu ɗaya ne akan ɗansu meyasa ya aikata wannan kuskuren dole yana buƙatar neman gafarar Mamma, sai yanzu ya fahimci cewa bai samawa ƴaƴansa Uwa ta gari ba, domin kuwa shi kansa wani lokacin yana lura da yadda ake rayuwar da bata da ce ba a gidan sa, a wannan karon zai nunawa Momy matsayinta zai kuma hukunta ta, akan wannan shirmen, zai tsaya da ƙafafuwan sa wajen tabbatar da wannan Auren, domin farin cikin Mamma, nisawa yayi tare da cewa.

" Tabbas nayi kuskure nayi kuskure gareki Mamma a yau idanuna sun buɗe na fahimci hakan, dan Allah kiyi haƙuri Mamma ki yafe min insha Allah zan gyara tsakanina dake kuma zan tsaya da ƙafafuna domin tabbatar da Auren Garko, kuyi haƙuri."

Daddy yayi Maganar cikin sanyin jiki, shi dai Ya khalil ya gagara magana domin kuwa kalaman Momy sunyi mungun tsorata sa, bai taɓa tunanin cewa akwai Uwar da zatayi munanan kalamai akan ɗanta harta nema masa tashin hankali, Lallai ne Rayuwar Momy akwai gyara ita ko wacce suruka bata so, wannan wani irin ɗabia ce, duk da yaji zafin maganganun INNO da tayiwa Momy sai dai yasan koma me aka faɗa mata itace ta jawo, miƙewa tsaye yayi cikin sanyin jiki ba tare da yace komai ba ya juya zai bar wajen muryar Daddy yaji yana ce masa.

" Tunda aka fara wannan maganar baka ce komai, ka shirya gobe da safe zamuyi sammakon zuwa TULDEN FULANI."

Juyowa Ya khalil yayi tare da cewa.

" Allah ya kaimu Daddy"

Yayi Maganar a taƙaice tare da ficewa ya nufi garden, Shima ya Garkuwa tashi yayi yabi bayan sa, Daddy shima kasuwa ya tafi, Aunty Zarah cike da farin ciki ita da Zizah suka miƙe suka nufi bedroom ɗin Momy ita Aunty Zarah farin cikin ta shine, Momy ta shiga ƙunci domin kuwa Allah ya saka mata abinda ta mata, Momy tunda ta shiga room ɗinta ta kasa zama sai kaiwa da komowa take, ta goya hanunta a baya, sosai take cikin tashin hankali, Zizah ne da ta shigo ta doki mirror da ƙarfi cikin fusata tace.

" Why Momy!!! Why!!! Daddy zai ƙasƙantar dake a gaban waɗannan koɗaɗɗun tsofin, ba laifin kowa bane laifin Garko ne Domin kuwa shine baiji maganarki ba, waima meya gani jikin wannan jakar yarinyar, anya kuwa Momy ba asiri suka masa ba, na kasa gane meyake damun Rayuwar Ya Garko, shi a rayuwarsa abinda yaga dama shine yake yi, Ki barta ta shigo gidan Momy, Wallahi sai mun mayar mata dashi kurkuku."

Aunty Zarah ce ta taɓe bakinta tare da cewa.

" Tayani gani dai Zizah nima banga meya gani a jikinta ba, amma da shike kinsan a ruga suka fito, asiri zasu masa."

Girgiza kanta Momy tayi tare da cewa.

" Bazasu masa asiri ba, domin kuwa babu boka a gidan su gidan malamai ne, kissa ce kawai da iya munafurci yasa ta mallake min ɗa, ku barni da ita sai tayi danasanin shiga rayuwata, ku fita ku bani waje."

Ta ƙarisa Maganar tana zama tare da dafe kanta fita sukayi.


Ya khalil zama yayi tare da yin shuru ya rasa me yake masa daɗi maganganun Momy kawai suke masa yawo a kansa.

" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!"

Ya furta tare da sakin numfashi kafaɗarsa Ya Garkuwa ya dafa tare da cewa.

" Ni kaina hankalina a tashe yake Momy tamin baki ta faɗa min mugayen maganganu, Momy tamin baki ina tsoro kar bakinta ya kamani, ya zanyi Bro meye mafita."

Ɗago idanunsa ya khalil ya yi ya dubesa tare da cewa.

" Babu yanda zakayi domin kuwa Daddy ya yanke hukunci, kuma ka sani Magana ɗaya yake yi, Baka da haƙƙin Momy insha Allah bakin ta bazai kamaka ba, kai dai ka cigaba da mata biyayya tamkar yadda kake karka fasa insha Allah komai zai shige Momy zata sauƙo zata gane gaskiya."

Shuru Ya Garkuwa yayi cikin tashin hankali, zama yayi shima yayi shuru dukkan su babu wanda ya kuma cewa ɗan uwansa wani abu.

Ita kuwa Jummo tafi kowa shiga cikin tashin hankali, bata taɓa tsammanin ƙiyayyar da Momy take mata yakai haka ba wannan wacce irin masifa ce, sai dai tasa a ranta zata dake da addu'a da sadaka insha Allah Allah zai karesu.


Yau Daddy da Abokinsa Alhaji Ahmed Sai Ya khalil suka nufi TULDEN FULANI, da niyar Tambayowa Garkuwa Auren Jummo.

MOMY sosai ranta yayi mungun ɓaci ganin da gaske fa wannan Auren zai tabbata, sai dai ta ɗauki alƙawarin bazata taɓa bari wannan Auren ya kasance ba.






*UMMU NASMAH CE*
[5/8, 10:29 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*



➰➰ *58 to 59*


"Wai ke Safreena me zakiyi da wannan aikin ne, just 30k ne fa kawai suke bawa ƙaramin ma'aikaci a wata, kuma ke kina da master's me zai hana bazaki je AA ƊAN DARMA ki nemi aiki ba, wannan ma'aikatar suna bada Salary mai tsoka, a babu suna bawa ƙaramin ma'aikaci 65k amma sai ki tsaya ki nemi aiki a wannan ƙaramin Companyn me 30k zata miki a wata."?

Ɗan murmushi Safreena tayi tare da cewa.

" AA ƊAN DARMA ba Companyn daya kamata nayi aiki a cikin sa bane Zee kema kin sani ko karima kanta da ta samu aiki a wajen ki duba kiga yanda take complain akansu basu da uzuri sannan basu ganin darajar ma'aikacin su, to me zakaje kayi a inda baza'a ga darajar ka ba, Su kuwa I D D BARAU NIG LTD company ne da suka san darajar ma'aikaci sukan bawa kowa mutuncin sa, ba kuma sa taɓa wulaƙanta ma'aikaci koda kuwa mai shara ne, ina son inda za'a mutuntani Zee, gara a bani kuɗi kaɗan aga mutuncina, ba wai a bani kuɗi mai yawa ba ana ɗaukata ƙasƙantacciya, Zee wannan 30k ɗin da zasu bani ta isheni nayi buƙatuna da kuma na Abdul saboda na rufa masa asiri yasa na nemi wannan aikin kuma kuɗin zasu isheni buƙatuna dana ɗana, bani burin ƙarya a cikin rayuwata ki gane haka mutunci yafi kuɗi."

Numfashi Zee ta saki tare da cewa.

" Hakane na fahimta, ɗazu kin fara bani labari, Baba ya shigo kikayi shuru, kikace kun haɗu da Garkuwa a wannan Companyn, ya ganki kuma."

Kanta Safreena ta kaɗa tare da sakin murmushi tace.

" A'a ban bari ya ganni ba, saboda bana son mu sake haɗa idanu dashi, a zuciyarsa na mutu, hakan nake so ya tabbata na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login