Showing 45001 words to 48000 words out of 93605 words

Chapter 16 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

Allah ya Garkuwa karka tursasani nayi ƙarya dan Allah kabar wannan maganar hanyar gyara tana da yawa mu nemi wata, wannan dai ya riga ya shige."

Dole yasa Khalil yin shuru ba tare da ya kuma cewa komai ba, duban A'illo Jummo tayi tace.

" Ɗauko mana bag ɗin mu, mu shige school."

Tashi A'illo tayi bata juma ba kuwa sai gata ta fito da bag ɗin, karɓa Jummo tayi tare da cewa Ya khalil.

" Mun shige school sai mun dawo."

Dubu biyu khalil ya basu tare da adawo lafiya sannan su Jummo suka fice da kallo khalil ya bita cike da sha'awar rayuwarta sam bata ɗauki duniya da zafi ba simple take rayuwa, numfashi ya sauƙe tare da haurawa bedroom ɗinsa, Zarah na tsaye jikin wadrop tana gyara kayanta, ya khalil ya shigo, ko inda Zarah take bai kalla ba, ya ɗauki towel zai shige tollet yaji muryar ta.

" Ban haɗa ruwan wankan ba, yanzu zan haɗa maka, ka ɗan jira."

Hanu KHALIL ya ɗaga mata tare da cewa.

" Bana buƙata ina da hanu zan haɗa kayana."

Yayi Maganar yana shigewa tollet ɗin zaro idanunta Zarah tayi tana kallon Khalil a zaton ta, zai bata haƙuri ya rarraaheta akan abinda ya faru jiya, shine ma zai ɗau fushi da ita, kanta ta girgiza tare da cigaba da abinda take.



✨✨✨✨✨✨✨✨✨





" Ina jinki Asabe kika ce ya zanyi da maganin.?"

" Kin gani Hajiya Zainab ki tabbatar kinje kin zuba maganin nan a ƙofar bedroom ɗin ta, kuma ki tabbata ba wanda ya ganki wallahi Hajiya Zainab kinji na rantse miki muddun ta tsallake wannan maganin wallahi sai faɗi jinyar da baza'a taɓa sanin maganin sa ba, har ta mutu a haka kuma babu mai zarginki."

" Masha Allah, insha Allah babu saƙo da kaina zanyi wannan aikin shegiyar Yarinyar ta tafi makaranta, saura Khalil ne kawai a gidan yanzu zai fita yana fita zanje na aiwatar na gode Asabe sai munyi waya."

Ta katse wayar tana dariya, tare da juya ƙaramar kwalbar dake hanunta mai cike da wani farin ruwa tamkar Madara.

"Hmmm!!! Mamma kenan na rantse da Allah kafin kiga bayana ni sai naga bayanki bazan taɓa zuba idanu ina gani wani yayi mulki a gidana ba, dole ni kaɗai zan bada umarni a gidan nan, daga yau Mamma kin daina takawa da ƙafofinki mu zuba mu gani ni da ke shege ka fasa."

Ajiye kwalbar tayi tare da sheƙewa da dariya, khalil ne ya shigo cikin shirin fita office, kusa da Momy ya zauna tare da cewa.

" Zan fita Momy hope baki buƙatar komai ko.?"

" Dubu arba'in nake buƙata, zan kaiwa Hajiya mairo zatayi bikin ƴarta, kuma ya kamata na bata wani abu, Khalil wai ya zancen dana maka ne, na ka ƙara Aure bazan fa zuba idanu na kalleka zaune da wannan juyar ita kaɗai ba, bata haihuwa sai ajiye ƙaton kashi ka bata taci tasha mai kyau ta ajiye kashi bazai yiwu ba, dole zaka ƙara Aure ko kaima zakaga jininka nima naga jikana, dan haka gara ka fara neman mata kafin raina ya ɓaci na nemo maka da kaina.?"

" Haba Momy meyasa kike wannan maganar, koda zan ƙara Aure bazan ƙara Aure da niyar haihuwa ba, domin kuwa ita haihuwa ta Allah ce shike bawa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso, badan baya sonsa ba, sai dan girman ikonsa, Momy kika sani ko nine bana haihuwar Momy............"

" Kai dalla dakata haka da wannan zancen banzan kaikam kana haihuwa domin kuwa jinki jinin zuri'a ne, tashi ka tafi karka kuma min Maganar banza, kuma Aure dole ka ƙara Allah ya tsare."

Da ameen Khalil ya amsa yana fita, sanda Momy ta tabbatar Khalil ya juma da tafiya sannan ta ɗauko wannan kwalbar a hankali ta fito tana dube dube cikin dalon shuru ba kowa har Zarah tana room ɗinta, murmushi Momy ta saki tare da zuwa cikin gaggawa ta zuba wannan ruwan kwalbar a ƙofar room ɗin Mamma da sauri tabar wajen tana murmushin ƙeta.

Mamma kuwa hankalinta kwance tayi wanka tare da ɗaukar mayafinta, zata gidan Hajja Atine, ƙawar da Jummo ta sama mata nan ƙasa da layinsu, bakin room ta nufo tare da sako ƙafarta ta taka wannan ruwan, ta fito falon Momy dake laɓe tana hango dukkan abinda ke faruwa ne ya sata sakin murmushin nasara, Mamma tazo DAI-DAI fita daga falon taji jiri ya fara ɗaukarta, falon ya fara juya mata komai bibbiyu take kallonsa, yankan jiki tayi ta faɗi ƙasa a sume.

Jummo dake cikin class ne taji zuciyarta ta tsinke da ƙarfi ƙirjinta ya fara harbawa, tamkar ana buga ganga, saurin dafe ƙirjinta tayi tare da runtse idanunta................"




*INA GODIYA SOSAI DA SHARHIN KU PAID GROUP NAJI DAƊI SOSAI A CIGABA DA SUBURBUƊO MIN COMMENTS🥰🥰🥰🥰🥰*








*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:22 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*




➰➰ *43 to 44*


Tashi Jummo tayi tare da shigewa bedroom ɗin Mamma A'illo ta samu zaune gefen Mamma ta haɗa tagumi, numfashi Jummo ta sauƙe tare da kamo hanun A'illo tace mata.

" A'illo zanje Cilo yau zan taho da INNO, domin ta duba Mamma, insha Allah zamu samu maganin matsalarta, sai dai yanzu abinda nake so da ke, karki kuskura kibar Mamma ita kaɗai koda wasa Saboda ina zargin mutum biyu a cikin gidan nan, Aunty Zarah da Momy su nake suspecting, dan haka ki kula dasu karsu cutar da ita a karo na biyu kina ji ko"

Kanta A'illo ta kaɗa tare da cewa.

" Shikenan Jummo insha Allah zan kula, Allah ya tsare hanya, kiyiwa INNO bayani sosai dan Allah ta taimakeni tazo ta duba Mamma."

" Karki damu A'illo kinsan INNO babu abinda bazata iya yiwa Mamma ba, ni na tafi."

" Allah ya tsare a dawo lafiya."

Da ameen Jummo ta amsa tana kallon Mamma harta fice, tare suka jera da Garkuwa har cikin mota yaja tare da dannawa Baba mai gadi hom, da sauri ya buɗe get din suka fice daga cikin gidan, suna shan kwanan gidan Safreena na sauƙa a adaidaita, hanunta ta ɗaura a kanta ganin motar Garkuwa ta gifta ta shige da gudu tabi bayan motar tana kwalawa Garkuwa kira sai dai ina shi sam baima jita ba bare ya juya dreving ɗinsa kawai yake, ganin ya ɓacewa ganinta ya sata zama a wajen cike da tashin hankali da fargaba ta shiga Uku idan Garkuwa ya mutu, hawaye ne masu ɗumi suka zubo daga idanunta, sharewa tayi tare da ciro wayarta daga jaka ta kira numbern sa kusan 10 miss call bai ɗaga ba wanda shi wayar tasa ma tana silent bai lura da kiran ba.

" Na shiga Uku!!! Yau kuma zanyi kisan kai da wani ido zan kalli Ubangiji na idan ya mutu?"

Cike da sanyin jiki ta miƙe adaidaita ta tare tace ya kaita Federal locost ranta sam babu daɗi ta ɗebi hanyar gidan su.

Shikuwa Garkuwa dubansa ya kai ga Jummo tare da sakin murmushi ya furta.

" Ina cikin farin ciki yau daya kasance zanyi tafiya mai nisa tare da ke, da na kusa yiwa kaina asara na ƙin amincewa da Soyayyar ki, sai daga baya na fahimci cewa kece alkairi na ina sonki Jummo."

Numfashi Jummo ta saki fuskarta sam babu farin ciki tace.

" Ya Garkuwa, ni kuwa yau bana cikin farin ciki Saboda wacce tayi sanadiyar haɗa kaddarar mu, tana kwance rai a hanun Allah, a halin da Mamma take ciki yanzu na tsakanin rayuwa da mutuwa babu wani farin ciki da zai ziyarce ni, har sai naga motsinta, ina sonka ya Garkuwa."

"Hmmm!!! Naji tausayin Mamma ƙwarai, ba'a mamaki da ikon Allah, amma ace mutum yana zaune lafiya lokaci ɗaya ya gamu da ƙaddara, ba komai insha Allah Mamma zata samu lafiya ."

" Allahu yasha Ya Garkuwa"

Sunyi nisa da tafiya sosai suna zance gwanin burgewa domin kuwa a ɗan wannan awannin Jummo da Garkuwa har ɗan sabo ya shiga tsakaninsu, sun shige Bojuɗe local gvt da kwani, suna cikin Gaɗam birkin motar Garkuwa ya cinke burkin ya ƙwace daga hannun sa, zaro idanun sukayi kusan haɗin baki suka furta.

" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!!"

Garkuwa ne cike da gigita ya dubi Jummo tare da cewa.

" Burki ya tsinke Jummo me yake faruwa? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un allahumma ajirni fil musibati!!!!"

Wani irin mungun gudu motar take yayin da tayar motar ke ƙoƙarin ficewa, duk yanda Garkuwa yaso ya dakatar da motar abu yaci tura, ga tsakiyar titi motaci sai famar gudu suke a Jummo sosai take cikin tashin hankali ta rufe idanunta gam sai innalillahi take furtawa a cikin zuciyarsa, da kanta motar ta yanki kwana ta faɗa wani jeji mai yawan bishiyoyi, bugar bishiyoyin motar take yayin da take gwara kansu jikin glass ɗin motar, tayar gabane ya fice motar tayi sama tare da dawowa ƙasa ta faɗi, ƙofar da Jummo take ne ta buɗu tamkar an wullota ta faɗo waje, kanta ya doku da katon dutsen kwankere wani irin ƙara mai shiga zuciyar mai sauraro Jummo ta danna sai kuma numfashinta ya ɗauke take, shi kuwa Garkuwa ƙirjinsa ne ya doku da jikin sitiyarin motar wani irin numfashi ya saki sai kuma numfashin nasa ya fara sarkewa yana jawo numfashi da ƙyar zuciyarsa sai bugawa take tamkar ganga far!!! Far!!! Far!!! Far!! Haka zuciyarsa ke bugawa, sai kuma ya fara aman jini guda guda, kirjinsa ya danne da hanunsa dake masa azaba tamkar zai ɓalla zuciyarsa zata faso waje, idanunsa sun rune tamkar garwashin wuta, amma tsabar ƙarfin hali irin na Garkuwa baya jin kansa, Jummo kawai yake ji, ƙofar gefensa ya saka hanu da ƙyar ya tura taƙi buduwa, zakuɗawa yayi a hankali yana cije bakinsa cike da azaba ya samu ya fito, layi yake tamkar zai faɗi, wajen sai juya masa yake bakinsa na zubar da jini gumi duk ya lulluɓesa amma a haka yake ta waige waigen ina zaiga Jummo, hangota yayi kwance jini sai zuba yake daga kanta tamkar an kunna fanfo idanunta sun kafe, a hankali ya fara jan ƙafarsa yana ƙoƙarin zuwa inda take sai dai ina taku ɗaya yayi ya yanki jiki ya faɗi a sume.

Mutane ne suketa ƙoƙarin shigowa jejin da gudu, take suka ruhu a kansa, kowa yana tausaya musu, ɗaya daga cikin waɗannan mutanen ne ya je ya kirawo police, cikin gaggawa aka kira amblance, akayi dasu Sj gaɗam hospital.

Ita kuwa Safreena tun da ta koma gida take tirƙar kuka cike da nadamar abinda tayi, bata san wani hali yake ciki yanzu ba, hanu ta ɗaga tare da fara jero addu'o'i.

" Ya Allah ni baiwarka ce mai yawan sadaka, mai yawan ibada, ya Allah nasan naimaka laifi ta hanyar haɗa shinfiɗa da wanda ba muharramina ba, ya Allah na tuba ka yafeni, ya Allah na saka Rayuwar wani a cikin haɗari, cikin raahin sani da kuskure na, ya Allah ka kare wannan bawan naka, ya Allah kasa karya samu rauni Saboda kuskurena, ya Allah ka amshi addu'a ta."

Tayi addu'ar tana runtse idanunta, Aunty Batul ne ta dafa ta tare da sunkuyawa a gabanta tace.

" Lallai kinyi kuskure bisa rashin sani, sannan tabbas Baba yaji wannan ɗanyen aikin da kikayi ransa zai ɓaci hankalinsa kuma zai tashi, sannan sai ya miki faɗa tamkar zai dakeki, dan haka kiyi shuru da wannan maganar muyi addu'ar Allah ya karesu, kawai, kai duniya ba AMANA tun ɗazu naketa tunani, wai ace da mutumin da ka sashi cikin inuwarka za'a Cutar da rayuwarka, mtsss!!! Nayi mungun jin haushin mai gadin gidan su Garkuwa, kana cin albarkacin ubansa sannan ka nemi kashe masa ɗa, Allah ka haɗa mu da mutanen ƙwarai."

Da ameen Zee ta amsa itama tana jin haushin Safreena domin kuwa da ta sanar da ita bazata barta ta aikata wannan mungun kuskuren ba Allah ya kyauta.

Tana nan zaune Safreena tayi shiru taji ringin ɗin wayarta dubawa tayi, layin da sukayi connecting da layin Garkuwa ne, wanda take jin duk wani kiran da zaiyi da wanda za'a kirasa, saurin ɗaukar wayar tayi Bros taga ake kira sai da layin ya kusa tsinkewa aka daga daga inda take zaune take jin maganar tasu.

" Assalamu alaikum."

Da ameen wa'alaiku mussalam ya Khalil dake zaune a office din sa ya amsa yana cewa "Bro har kun isa kenan?"

" Bashi bane"

Yaji muryar wani ya doki kunnen sa, cike da mamaki Ya khalil yace.

" Ba shi bane waye kai ɗin."

" Police ne mai wannan wayar sunyi haɗari, a cikin ƙaramar wayarsa muka samu wannan numbern muka kira, kuzo Sj Gaɗam suna asibitin."

" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! A wani hali suke ciki suna raye ne ko sun mutu, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!

" A halin yanzu bazamu ce ga halin da suke ciki ba gaskiya saboda accident ɗin nasu babu kyau, mun dai shigar dasu asibitin basa motsi, kuzo dan tabbatar da rayuwarsu."

Yana gama faɗar haka ya ajiye kiran dafe kansa Ya khalil yayi cike da tashin hankali yana jin wani irin jira zuciyarsa na tsinkewa da sauri ya tashi tare da kwasar wayoyinsa bai kira kowa ya sanar dashi ba, har Daddy saboda gudun sasu cikin damuwa, da motar sojoji biyu Ya khalil ya kama hanyar gaɗam, cike da tashin hankali.

Kallon su Aunty Batul tayi ta rintse idanunta hawaye na gudu bisa kuncin ta, wannan shine danasani na Biyu da tayi a rayuwarta.

" Aunty Batul na kashesu, nayi kisan kai Aunty Batul, ina zan kai haƙƙin rai, na shiga Uku.!!!"

" Baki shiga Uku ba Safreena, baki shiga Uku ba, insha Allah bazasu mutu ba, zasu rayu, sai dai kuskuren kin ɗauki alhakin muddun basu yafe miki ba, sai Allah ya tsaidaku ranar gobe kiyama, hmmm!!! Allah ya ɗaga kafaɗunsu, gacan Abdul yana kuka kije ki rarrashesa."

Miƙewa Safreena tayi ta ɗauko Abdul wani irin ihu yaron ya kurma yana ƙoƙarin zillewa daga jikinta, sai kuma ajiyar zuciya yaron keyi, zaro idanunta Safreena tayi tana kallon yaron yanda yake ihu tamkar da wuta a hanunta ta ɗaukesa, Zee ce ta saka hanu ta karɓesa shuru yayi tare da kwantar da kansa jikin Zee, hanu Safreena tasa ta ƙara ɗaukar sa ya kuma cilla kuka, Zee na kuma karbarsa yayi shuru.

" Meke damun yaron nan ne, dana karbesa sai kuka tamkar wacce nake jona masa wuta."

Bakinta Zee ta taɓe tare da cewa.

" Da yiyuwa akwai Soyayya ne tsakanin ɗa da Ubansa, wataƙil yana jimamin ubansa ne, da kuma haushin kina neman ganin bayan jininsa ko iya wannan ya kamata ki fahimci kin aikata zunubi, komai tare muke kina neman shawarata kafin ki zartar da hukunci, da kika tashi aikata zunibinki kuma sai kika ware kanki ki aikata a ɓoye, sai ki girbi abinda kika shuka ke ɗaya.

" Haba Zee ya..........."

Zee bata tsaya ta ji abinda Safreena zata faɗa ba ta fice ranta a matukar hasale, Aunty Batul ce tace.

" Ranta ne ya ɓaci amma zata huce, Zee bazata iya fushi da ke ba, nima bara naje na watsa ruwa."

Tayi Maganar itama tana ficewa, kwanciya Safreena tayi tare da yin shuru cike da nadama.





✨✨✨✨✨✨✨✨✨


Ƙarfe ɗaya dai-dai Ya khalil ya shiga asibitin, su Daniel suna biye dashi a baya duk wanda ya gansa yasan cikakken soja ne ya iso duk da uniform bane a jikinsa, darect office ɗin doctor ya nufa tare da nocking, UMARNIN ya shiga aka basa sannan ya shigo zama yayi tare da miƙawa doctor hanu Sukayi musabaha.

" Doctor nine ɗan uwan waɗanda aka kawo ɗazu da misalin 11 am sunyi hatsarin mota mace da namiji."

Gyaɗa kansa DOCTOR yayi tare da cewa.

" Tun ɗazu ake jiran isowar ku baku iso ba, har muka fito daga emargency meyasa."?

" Doctor muna cikin Gombe ne tsakanin mu da Gaɗam akwai tazara, yanzu ya ake ciki a wani hali suke."?

Shuru doctor yayi yana fargar abinda zai sanar da Khalil sai da yayi shuru kafin yace.

" I am sorry to say da abinda zan faɗa maka, shi dai namijin mun masa treatment yanzu haka yana ɗakin hutu, a bisa buguwar da yayi a kirjinsa yasa zuciyarsa ta taɓu ma'ana ya kamu da ciwon zuciya sai dai da yiwuwar zai warke idan har aka bi ƙa'idar mu, saboda ciwon zuciya yana warkewa idan baiyi ƙarfi a jikin mutum ba, bugun zuciya ne baya warkewa shine har ya kashe mutum, amma ku godewa Allah ba bugun zuciya bane, amma dai har yanzu bai farfaɗo ba mun masa allurar bacci."

Dafe kansa Ya khalil yayi cike da tashin hankali yace.

" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Allahumma ajirni fil musibati wa'akfilni kairan minha!!!! Hmmm!!! Doctor ita kuma macen fa tana wani hali."


" Gaskiya nata yafi muni, saboda ta bugu sosai a kanta har yanzu bata farfaɗo ba, kuma bama saka ran zata farfaɗo nan kusa doguwar suma ta tafi da yiwuwar zata kai kwana uku kafin ta farfaɗo, sai dai inda matsalar take ƙwaƙwalwar ta ta juya saboda ta bugu sosai muna tsamanin ma, tayi missing ɗin memory ta ma'ana muna tsamanin zata manta komai na rayuwarta idan ta farfaɗo, idan kuma Allah ya taimaka ta farfaɗo normal, AMMA dai munfi tsammanin tayi missing ɗin memory ɗinta."

Wani irin zabura Ya khalil yayi cike da tsantsar tashin hankali ya furta.

" Whatttt DOCTOR!!! Tayi missing ɗin memory ɗinta kake nufi....................?"










*08147537180*




*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:22 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*



➰➰ *45 to 46*




" Cool down!!! Cool down!!! Bafa nace maka ta kamu da cutar mantuwa bane ce maka nayi muna tsammanin zata iya kasancewa, ba wai ya kasance bane, dan sai mu dage da addu'a Allah yasa ta dawo normal."

Zama khalil yayi yana huci har yanzu zuciyarsa a tsinke take dafe kansa yayi tare da cewa doctor.

" Doctor yanzu ya ake ciki, da zancen maganin su, duk yanda za'ayi su sami lafiya doctor ayi, idan Maganar kuɗi, bana jin wannan ko nawa ne zan iya kashewa domin su sami lafiya."

" Ba damuwa insha Allah zasu sami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login