Showing 30001 words to 33000 words out of 93605 words
Chapter 11 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
ABDUL MOMYN AHLAN* sonso nake fisabilillah.
*_________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_________________________________*
*LAST FREE PAGE WANDA YA BIYA KUƊIN SA NE KAWAI ZAI CIGABA DA GANIN WANNAN BOOK ƊIN, IDAN KINA RA'AYI ƳAR UWA MAZA HANZARTA KIZO KI BIYA KUƊIN KI NAIRA 100 NE KACAL BABU YAWA BATA FI ƘARFINKI BA, DOMIN KEMA A DAMA DAKE CIKIN WANNAN CAKWAKIYA MAI RIKITARWA 08147537180*
*Masu tambayar daga Farko idan kinji kina ra'ayin book ɗin biya ɗarin ki kawai sai ki samu daga farkon🥰🥰*
*LAST FREE PAGE*
➰➰ *29 to 30*
Murmushi Zee ta saki tana faɗawa saman kujera tace.
" Ƙawata aiki ya fara daga yau, na kuma san wasan zai fara armashi ne da zarar Garkuwa yaci karo da wannan saƙon ke dai kwantar da hankalin ki ki naɗe ƙafafunki ki bawa Garkuwa nan da awa ɗaya, zai fara cin karo da ruɗani."
Murmushi mai sauti Safreena tayi tare da cewa.
" Zee ai a yau kam na fara jin nutsuwa amma fa hankalina bazai taɓa kwanciya ba har sai naga Garkuwa a ƙasƙance."
" Hmmm!!! Saurin me kike Safreena, ai Garkuwa kam ya shiga tarkon mu, a yanzu mune zamu ke juya rayuwarsa muna wasa da ita ta yanda ƙwaƙwalwar sa zata gaza jurewa wannan wasan."
" Hmmm!!! Na yadda dake ƙawata kuma nasan duk abinda kika faɗa tabbas zaki iya, muje muyi dener dan yunwa nake ji sosai."
Dariya Zee tayi tare da cewa.
" Da kuma duk bakiji yunwar ba, sai yanzu sorry na manta ban sanar dake ba, Baba da Mama suna hanya gobe zasu shigo Nigeria."
Tsalle Safreena tasa tana dariya tace.
" Alhamdulillah wallahi naji daɗi dama na tsani zaman mu mu biyun nan, Allah ya kawo mana su lafiya."
Da ameen Zee ta amsa suna tashi suka nufi daining table.
Khalil shigowar sa cikin gidan babu kowa cikin falo, bedroom ɗin Mamma ya shiga tana zaune ta kunna sigari sai zuƙa take idanunta sunyi jajur dasu gefen ta Jummo ce da A'illo, saurin toshe hancinsa khalil yayi a rayuwar sa ya tsani warin sigari, ransa ne ya ɓaci cike da jin haushin Mamma yaƙi kulata Jummo ya kalla tare da cewa.
" Jummo zo falo ki sameni."
Tsaki Mamma tayi tare da cewa.
" Idan ma ka kulani ka raina Uwar da ta haifeka shege mai baƙin halin tsiya."
Khalil bai kulata ba ya fice abinsa
Da to Jummo ta amsa ƙirjinta na bugawa domin kuwa tayi zaton Momy ko Aunty Zarah ne suka sanar dashi abinda ya faru, tashi tayi tabi bayan sa a zaune ta gansa, itama zama tayi tare da cewa.
" Sannu da dawowa yaya khalil."
" Yauwa sannu Jummo"
waya ya ciro daga cikin wata ƙaramar leda ya ɓareta da kansa infinix hot9 plus mai shegen kyau ya miƙa mata tare da cewa.
" Ki riƙe wannan naki ne, ni na sai miki, zata ɗebe miki kewa, sannan gobe ne malamar da zata fara koya miki lesson zata fara zuwa takwas na dare, wayar ki sakata a chaji idan ta cika ki min magana zan koya miki yanda zakiyi Amfani da ita, sannan akwai alfarmar da nake nema wajenki nasan kuma zaki iya."
Cike da murna Jummo ta amshi wayar tana dariya tace.
" Yaya khalil Allah wannan wayata ne da gaske ni ka sayawa."
Dariya khalil yayi tare da ɗaga mata kai alamun eh naki ne.
Dariya tayi tace.
" Kai amma na gode sosai yaya khalil, ya khalil faɗa min alfarmar da kake so na maka ni kuma insha Allah zan maka shi."
Murmushi khalil yayi tare da gyara zaman sa ya fuskanci Jummo yace.
" Jummo So nake ki taimakeni ki taimaki kanki ki taimaki Daddy, ki dakatar da Hajjo daga shan sigari, Jummo kin san illar shan sigari kuwa."
Girgiza kanta Jummo tayi alamun a'a, khalil cewa yayi.
" Sigari tana haifar da hujewar huhu ta lalata kayan ciki, a ƙarshe Mutum ya mutu a wulaƙance, ƙarin illar sigari, da zarar mutum ya mutu, duk sigarin da yasha sai ya fita daga jikinsa haka zai lalata masa likkafani, Jummo idan muka bar Mamma ta cigaba da shan sigari dole ne zai illata rayuwarta ga shi ta tsufa shekarunta sunja, zai yi saurin illatata, Jummo idan har da gaske kina ƙaunar Mamma mu haɗa ƙarfi ni da ke mu cirewa Mamma ƙaunar sigari a zuciyarta."
Shuru Jummo tayi jikinta yayi sanyi, ba Mamma take tunani ba INNO take tunani da bata da wanda zai hanata lallai lafiyar INNO tana cikin hatsari, numfashi ta sauƙe tare da duban khalil tace.
" Yaya khalil ba sai mun haɗa ƙarfi ba, ni kaɗai zan iya hana Mamma shan sigari insha Allah amma bazai yiwu ta daina lokaci guda ba dole sai a hankali."
" Ba damuwa Jummo, Allah ya bamu Nasara, Jummo dan Allah ki dage kiyi ƙoƙari ki maida hankalin ki ga karatu, karki bani kunya dan Allah, nima monday zan koma Abuja wajen aikina."
" Insha Allah Ya khalil bazan baka kunya ba, zanyi ƙoƙari sosai, Ya khalil dama a Abuja kake aiki to aikin me kake a can."
" Ni jami'in soja ne, Jummo."
Zaro idanunta Jummo tayi tace.
" Cap hmmm!!! Soja mugaye ne fa yaya khalil"
Dariya Khalil yayi tare da cewa.
" Oh mu ɗin mugaye ne, to yanzu kinga nima na miki kama da mungu."
" A'a kaikam kana da kir.............."
" Khalil!!! Khalil!!! Kai Khalil!!!"
Muryar Momy dake tsaye sama ne ya doki kunnen su, tana kiran sunan Khalil a fusace.
Ɗago kansa khalil yayi ya kalli Momy tare da amsawa tsawa Momy ta daka masa tare da cewa.
" Zancen uban me ka zauna kana yi da wannan tambaɗaɗiyar marar albarka!!!! Har dariya kake da ita?"
Cike da mamaki khalil yake kallon Momy tambaɗaɗɗiya kuma, wai meyasa duk macen da yake so Momy bata sonta.
" Tambaɗaɗɗiya kuma Momy ban gane ba."?
Cike da masifa Momy tace.
" Eh tambaɗaɗɗiya zaka gane idan na sauƙo na ci ubanka, ina ruwanka da ita meye haɗinka da ita da har zaka zauna da ita, to kul ka sake koda kallon tane ban yarda ba wallahi.!!"
Garkuwa daya fito daga bedroom ɗinsa ne ya zo gaban Momy ya tsaya tare da harɗe hanunsa a ƙirjinsa yana sauraron abinda Khalil zaice.
" Momy wai me kike faɗa hakane me jummon ta miki kike mata wannan munanan zagin."
Jummo bakin ta taɓe tare da miƙewa tsaye ta ɗaga idanunta suka haɗa ido da Garkuwa, murmushi ya sakar mata tare da ɗaga mata gira ɗaya yana kanne mata ido, wani irin zubawa tsikar jikin Jummo yayi tare tare da jin sonsa ya taso mata murmushi ta saki tare da shigewa daga wajen tayi bedroom ɗin Mamma, murmushi Garkuwa yayi cikin ransa yana zayyano zumar da Jummo zatayi, duban Momy yayi tare da ƙara maida kallonsa ga khalil yace.
" Ɗan uwa dan Allah rabu da zancen Momy, da alama dai yau Daddy ya kunnata ne shiyasa zata huce akan budurwar ka."
Yayi Maganar yana dariya tare da kallon Momy, tsinkewa zuciyar Momy tayi tare da furta.
" Budurwa kuma!!! Kai budurwar fa kace kana nufin Khalil ke son Jummo.?"
Shima khalil murmushi yayi tare da kaɗa kansa, shi kuwa Garkuwa ya faɗi maganar ce kawai cikin wasa amma madadin ya cewa Momy wasa yake sai ma ce mata yayi.
" Eh mana budurwar sa, ba kece kike so ya ƙara Aure ba, gashi dai ya samu budurwar ƴar cas da ita ƴar rugar su Daddy da Momy."
Yayi Maganar yana dariya cike da masifa Momy zata fara zagin khalil kamar walƙiya taga baya wajen harya tashi, gira Garkuwa ya dagawa Momy yana shigewa nasa bedroom ɗin.
Cike da masifa Momy take hargowa tana khalil ɗin zaizo ne ya sameta.
Shi kuwa Garkuwa datar sa ya kunna yana dariyar Momy kasancewar sa mutum mai barkwanciya, facebook ya shiga ya gama abubuwan da zaiyi har zai kashe datar sai kuma ya shiga WhatsApp saƙonnin mutane ya fara dubawa wani yayi dariya wani kuma yayi tsaki MUSSAMAN na abokan aikinsa, saƙo na karshe daya saura wata baƙuwar Number ya gani wanda bai santa ba, shiga cikin saƙon yayi, video yaga an turo a hankali ya danna video ɗin, ya hau Reading ɗin buɗewa, harya buɗe, danna videan yayi, shigar su bedroom ɗin hotel ɗin ya fara gani shi da Sadiya zaro idonsa yayi yana cigaba da kallon, a matuƙar razane ya miƙe tsaye gumi na keto masa wani irin tashin hankali ne ya ziyarce sa, shine fa tsirara da Sadiya suna zina.
" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Hmmm!!! Na shiga Uku waye wannan waye ne yamin wannan ɗaukar!!!?"
Hanunsa na rawa yake kallon wayar tare da runtse idanunsa yana jin zuciyarsa na tsinkewa, idanunsa ya kai kan profile ɗin ta, online ya gani alamun wanda ya turo saƙon yana online, da sauri hanunsa na rawa ya rubuta saƙo ya tura.
" Please waye kai?"
Safreena dake riƙe da wayar ce ta dubi Zee tana dariya ta tura masa.
" Meye damuwarka da sanin ko ni waye.?"
Runtse idanunsa Garkuwa yayi tare da tura mata.
" Damuwata itace wannan video da ka turo min, dan Allah waye kai meye ribarka idan ka tozarta Ni, kuɗi kake buƙata to faɗi farashin ko nawa ne zan kawo maka ka goge ɗaukar."
Kallon Zee safreena tayi tare da ce mata.
" Kinga matsiyaci yayi zaton da namiji yake chat, shi fa zaton sa kuɗi nake buƙata daga garesa."
Hanu Zee tasa ta amshi wayar daga hannun Safreena ta Rubutawa GARKUWA sako kamar haka.
" Kai!!! Matsiyaci wanda bai san darajar Mace ba, kai kam idan ba Allah ne ya rufa asiri ba, zaka iya zina ma da uwarka, to bari kaji na faɗa maka, nafi ƙarfin amsar ƙazantattun kuɗi daga hanun ka, ka sani cewa wannan video sai na ya ɗasa a ko wacce kusurwa ta social media WhatsApp Facebook Twitter Instagram Snapchat etc da dai sauransu, sai na tona maka asiri duniya tasan ƙazantarka, sai na raguza farin cikin ka dan ubanka Buba, sai na saka ƙuda ma bazai bi FAMILYN ku ba shasha marar BASIRA."
Wani irin gumi ne ya ketowa GARKUWA hankalinsa yayi mungun tashi cikin tsawa ya mata voice.
" Wanene kai!!! Me kake nema dani!!!!!!!!!!!!!."
Murmushi Zee tayi ta kuma tura masa.
" Karka kuma min tsawa, ka fara lissafin kwanakin tozartar ka domin kuwa ta kusa, a ko wani numfashi da sakanni da zakayi a yanzu zakayi ne cikin tsinkewar zuciya da nadama, nine Ajalinka *IBRAHIM BUBA GARKO* Inkiyar ka GARKUWA Garko, ka sani farin sani na maka, hakan yasa bazan sha wahala ba wajen ganin ƙarshen ka."
Tana gama faɗin haka ta kashe datar.
Shuru Garkuwa yayi yana tunanin waye zai mishi wannan tozarcin lallai idan wannan videon ya fita shikenan ya gama yawo,( meye abinyi, anya kuwa ba Sadiya bace tayi wannan ɗaukar saboda na amince na aureta, tabbas Sadiya ce zata raina min hankali)......................."
*To fa yau ake yinta wanda ta ɗauki videon daban wanda yake zargi dabam tabbas akwai tarin matsaloli da ƙalubale a cikin wannan gida shin waima wacece SAFREENA wacce irin cuta Garkuwa ya mata, shin Momy zatayi Nasara akan su Mamma gefe guda kuma ga ya khalil yana nuna alamun Soyayyar Jummo ita kuwa Garkuwa ne a ranta shi kuwa Garkuwa mungun nufin ya lalatawa Jummo rayuwa ne a ransa to waye zaiyi Nasara tsakanin su, shin Momy zata samu nasarar haɗin kan AUNTY Zarah, duka wannan amsar tana sanƙame cikin wannan littafin zaki sami wannan amsoshin da jarar kin biya Nairar ki 100 kacal domin kuwa Free Page ya ƙare bazaki kuma ganin wannan littafin ba sai kin sanƙamomin kuɗinki*
*Ki biya Naira 100 ta wannan account numbern 0006064512 Rashida Usman jaiz Bank ko kuma ki turo hoton Mtn card ta wannan numbern 08147537180 sannan ki turo shaidar biya*
*Ƴan payment group ina mungun alfahari daku ina jin daɗin comments ɗinku sosai Allah ya saka da alheri ya bar ƙauna UMMU NASMAH na sonku muah😘*
*UMMU NASMAH CE*[4/15, 9:21 PM] UMMU NASMAH❤️: *wannan littafin na kuɗi ne bisa amana, idan kin san baki saya ba karki karanta min novel kizo ki biya Nairar ki 100 ki saya ki karanta cikin lumana, idan kuwa kin saya dan Allah karki fitar min da littafi idan kuma kin fitar keda Allah kuma bazan yafe ba.*
*Payment group Only*
➰➰ *31 to 32*
A matuƙar fusace Garkuwa ya fito daga bedroom ɗinsa idanunsa sun kaɗa sunyi jajur, bedroom ɗin su Jummo ya faɗa tare da ƙwalawa Sadiya kira.
" Sadiya!!! Sadiya!!! Sadiya!!!"
Sadiya dake zaune tana famar chat da wayarta ne ta dago idanunta cike da tsoro ta mike tsaye tare da furta.
" Lafiya Ya Garkuwa kake min wannan kiran."
Cike da zafin rai gami da duhun kai yace.
" Munafuka annamimiya kin san komai, harma tambayata kike lafiya, lafiyar uwarki, hanunta ya jawo tare da buɗe tafin hannunta ya ajiye mata wayarsa yace buɗe ki gani munafurcin da kika ƙulla min, wato nace bazan aureki ba, shine bari ki ɓullo min ta bayan gida saboda na aureki dole ko to kinyi ƙarya ki razana ni Wallahi Sadiya!!!".
Shuru Sadiya tayi cike da mamaki take kallon Garkuwa harya idda Maganar (me kuma na masa ) Jummo dake zaune da kallon mamaki duk take binsu sai yanzu ta fahimci dalilin da yasa Sadiya ke mata kallon banza a gidan taɓe bakinta tayi tare da kawar da kanta gefe, Garkuwa kuwa tsabar tashin hankali yasa idanunsa sun rufe kwatakwata bai lura da Jummo dake zaune a wajen ba, a hankali Sadiya ta saka hanu zata danna video ɗin sai kuma ta juya ta kalli Jummo, inda Sadiya tabi kallo Garkuwa ya juya yana kallo, saurin zaro idanunsa yayi (dama tana wajen).
" Keeee!!!! Jummo tashi ki fita kibar bedroom ɗin nan muna magana."
Taɓe bakinta Jummo tayi tare da miƙewa tsaye ta kalli Garkuwa tace.
" Yo ni kuwa ina ruwana da zancen ku, waima kuwa anya kana da gaskiya dan dai ina hango tsantsar rashin gaskiya a tare da kai, amma koma menene idan tayi tsami ma ji, Oh su Oh Oh anyi asara anabin namiji ya Aure ni dole Allah ya sauwaƙa namiji ya zagi uwata na bisa koda shine autan MAZA, wanda dai bashi da zuciya yayi asara.!!"
Tayi Maganar tana hararar Sadiya, Garkuwa haushi ne ya kamasa ya miƙa hanu da niyar jawo Jummo ya fasa mata baki, ta ruga da gudu tana cewa.
" Yi hakuri malam bafa ni na kar zomon ba rataya aka bani.''
Bakinsa ya cije Garkuwa idanunsa sun dawo tamkar gauta ya jawo gashin Sadiya da ƙarfi sanda ta ɗan danna ƙara cike da tsantsar ɓacin rai yace.
" Ki danna playing ki ƙara ganin abinda kika ɗauka, wato ni zaki tozarta Sadiya ni zaki ɗauka tsirara haihuwar uwata."
Sadiya cike da azaba gami da rashin fahimta ta danna video ɗin, saurin toshe bakinta tayi tana zaro idanunta cike da tsoro zuciyarta ta tsinke hankalinta ya tashi.
" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! What waye ya ɗauki wannan videon, na shiga Uku idan aka ga wannan video kashina ya bushe, Ya Garkuwa waye ya turo maka."?
Ɗauketa da mari Garkuwa yayi tare da furta.
" Karki raina min hankali mana, ni zaki yiwa pretending ki nuna baki san komai ba, uban waye zai ɗauka idan ba ke ba, na ce uban waye zai ɗauka idan ba ke ba!!! Ni da waye mukaje hotel ɗin duk duniya bani da maƙiyin da zaimin wannan aikin, wannan aikin kine!!!!"
Ya ƙarisa Maganar yana ƙara ɗauketa da mahaukacin mari, dafe kuncinta Sadiya tayi idanunta na zubar da hawaye cike da tashin hankali tace.
" Ta yaya!!!! Ta yaya!!! Ta yaya kake tunanin zan ɗauki kaina tsirara duk rashin hankali na, na rantse da Allah daya busa min numfashi wallahi bani bace na ɗauki wannan video na rantse da Allah bani bane ka yarda dani yaya GARKUWA bani bace."
Shuru Garkuwa yayi yana zubawa Sadiya idanu tsantsar gaskiya yake hangowa a ƙwayar idanunta, jikinsa ne yayi sanyi zuciyarsa ta ƙara tsinkewa, silalewa ƙasa yayi ya zauna daɓas a ƙasan tayels yana dafe kansa.
" Na shiga Uku to wanene wannan wanene yake ƙoƙarin tozarta Ni, Waye shi Sadiya, me yake nema a gareni yaushe yayi wannan ɗaukar ban sani ba innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Tabbas ina cikin masifa."
Shuru Sadiya tayi tare da zama itama ta dafe kanta tace.
" Muna cikin masifa zakace ba kana cikin masifa ba, wannan video yana fita shikenan na shiga Uku na gama yawo, to ka kira layin wayar mana."
Runtse idanunsa Garkuwa yayi tare da saka hanu ya ɗauki wayar, numbern ya kwafa daga WhatsApp tare danna kira switch Off yaji wayar.
" Tana kashe" ya furta, shuru Sadiya tayi tare da cewa.
" Abinda za'ayi yanzu shine mu jira zuwa Safiya mu gani ko za'a buɗe wayar."
Tashi Garkuwa yayi ya tashi ba tare da yayi magana ba ya fice daga bedroom ɗin, nasa ya koma tare da shiga cikin WhatsApp ya tura mata saƙo kamar haka.
" Ko waye kai dan Allah ina roƙon ka da karka watsa video ɗin nan a duniya ka faɗa min nawa kake buƙata zan bawa."
Ya tura saƙon tare da Kwanciya ruf da ciki yana tunani, haka Garkuwa ya kwana cikin tashin hankali ko baccin kirki baiyi ba saboda tashin hankali.
Washe gari da safe Jummo ta shiga kitchen da niyyar ɗaurawa Aunty Zarah breakfast, harta ɗaura towa ta saka ruwa, Zarah ta shigo, Jummo cike da murmushi tace.
" Ina kwana Aunty Zarah."
Da LAFIYA Aunty Zarah ta amsa tana haɗa fuska tare da cewa.
" Kije kawai zanyi aikina ni kaɗai."
Shuru Jummo tayi tana kallon Aunty Zarah girgiza kanta tayi tace.
" Haba Aunty ban sanki da fushi ba, a tunanina duk inda gaskiya yake zaki bi bayansa, kin sani Momy ce bata da gaskiya a cikin wannan lamarin amma kike ƙin bin bayan gaskiya saboda kina tsoron Momy, Aunty Zarah tsoron Allah ya kamata kiji