Showing 48001 words to 51000 words out of 93605 words

Chapter 17 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt

lafiya karka damu, am yanzu haka akwai list ɗin abinda aka kashe na test da abubuwan da aka musu kasan dai nan private hospital ne, zan baka rasit kaje ka biya."

" Okay ba damuwa DOCTOR za'a biya."

Sun juma suna tattaunawa game da yanda za'a biyowa lamarin nasu kafin doctor ya bawa ya khalil rasit yaje ya biya komai da aka kashe musu, sannan ne ya shiga dakin da aka kwantar da khalil yana kwance yana bacci yayinda hancinsa ke manne da wata ƙaramar igiyar tiyo wacce take taimakawa wajen numfashi kasancewar numfashin na basa wahala, a gefen sa Khalil ya zauna tare da zuba tagumi shuru yayi ransa a jagule da rashin lafiyar ɗan uwansa ya juma sosai a wajen kafin ya bar room ɗin wanda ke gefen na Garkuwa ya shiga Jummo ce kwance tamkar gawa, numfashi ko kaɗan batayi, sosai yaji tausayin ta fiye da tausayin Garkuwa, duk da Norse na kula dasu amma yana da kyau a samu jinin su a kusa, yanzu idan yace Momy ko Zarah ɗaya yazo ya zaunawa Jummo babu wanda zai yadda cikin su, saboda shi kansa ya fuskanci ƙiyayyar da Momy ke yiwa Jummo, numfashi ya sauƙe mafita ce ta faɗo masa (mai zai hana tunda yana kusa da dukku bazai ƙarisa ya taho da INNO da mahaifiyar Jummo ba, idan yaso ita INNO ta ji da maganin Mamma ita kuma Sikayel ta zauna tare da ƴarta da wannan tunanin yabar asibitin, ya ɗebi hanyar dukku tafiya ce ta minti arba'in ta kaisa cikin dukku har kauyen CILO, tunda Ya khalil ya shiga cikin CILO yake neman gidan su Jummo saboda bai san garin ba ba zuwa yake ba, dakyar ya samu wani yaro ya kaisa har ƙofar gidan su Jummo wajen Baffa dake zaune cikin almajiransa, ya khalil parking a gefe tare da tahowa ya yiwa Baffa sallama, amsawa Baffa yayi yana masa barka tare da nuna masa gefen tabirmar sa yace ya zauna zama Ya khalil yayi tare da gaishe da Baffa cike da mutunci da karramawa Baffa ya amsa sosai Ya khalil ya yaba karancin Baffa, bayan sun gaisa ne ya khalil ya gabatarwa Baffa kansa tare da masa bayanin abinda ke faruwa da Mamma har Jummo, Sosai hankalin Baffa ya tashi, duban ya khalil yayi tare da cewa.

" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!!! Ikon Allah, ba yadda baya ikonsa, Jummo sunyi haɗari, itama Mamma ba lafiya, ba komai jarabawa ce, babu wanda yafi ƙarfinta, insha Allah zasu sami lafiya, bari muje na kaika wajen INNO daga nan zan ɗan shiga cikin jeji akwai abubuwan da zan tsinko zan bada magani ka tafi musu dashi ka ɗan jirani kaɗan."

Da to khalil ya amsa sannan suka shiga cikin gidan, INNO suka samu zaune a barandarta sai famar tiƙar goro take gefen ta kuwa kararen sigari ne wanda tasha zube a ƙasa, a gefe ya zauna yana kallon sigari cikin zuciyarsa ya furta, (Sai hali yazo daya ake abota da Mamman da INNOn duk kwaryar ƙasa ce da ta sama) a kujera ƴar tsugunno ya zauna, Mamma da kallon rashin sani ta bisa tare da cewa Baffa.

" Kai kuma Baffa akwai da yayiɓo kara da kiyashi shi kuma wannan koɗaɗɗen mutumin ina ka ɗebosa, bari wata rana ka je ka yayo kidnanas."

Zaro idonsa Ya khalil yayi yana kallon rashin mutuncin INNO, kaji tsohuwa da bakar Magana, wato shine ma kara da kiyashin muryar Baffa yaji yana ce mata.

" Jikanki, ɗan gidan Buban Mamma, wajenki yazo, kai kalilu sai kuyi magana ko, ni bara naje na dawo."

Kaɗa kansa khalil yayi alamun to sannan Baffa ya fita INNO dariya tayi tare da cewa.

" Ayyo ai sai da kafaɗa na gano katon kan Buban, ɗan nema falafalan kunnen kuwa kamar kosai, ko da yake na uwarka ne, itama haka nan kunnen ta, kai Oh Zainabu ai hatsabibiya ce, wai na tambayeka, har yanzu uwarka zainabu tana nan da tsiyar ta ko ta daina, dan dai ƴaƴan hayin gada badai tsinantaka ba, kuma ko kaf unguwar gidan su Zainabu sunfi tsiya, shegu ga talauci kamar zai kashe su,sai tsiya, bari kaji kakanka mahaifin Zainabu wallahi cikakken matsafi ne, tsabar tsafi fa Irin nasa, sanda yayi mutuwar walaƙanci, wallahi hauka yayi tuburan sanda aka dauresa da sarƙa, kai karshe fa kafin ya mutu sanda ya makancce ya kurmance, sunmun bukumun kenan kurame makafi, hai inke faɗa maka.............."

" INNO ya isa.............."

Ya khalil ya furta yana runtse idanunsa tare da cije leɓensa, sosai yaji ƙunar maganganun INNO, da ganin idanunta zaka fahimci gaskiyar ta take faɗi irin matan nan marassa tsoro da faɗar magana ba bu shakkar ido, cikin zuciyarsa ya furta (haka dangin Momy suke da mummunan tarihi?) Muryar INNO yaji tace.

" Umm to shikenan nayi shuru tunda gaskiyar ne baka son na faɗa, sai famar zuba ma nake kamar kanya ban tambayeka aminiyata Mamma da jikata Jummo, oh shegiya Jummo tana can binni ta samu duniya ta manta da INNOn ta, ni kuma kullum sai nayi mafarkinta, kasan me, ko jiya sai da nayi mafarkinta wai tana kuka tana nazo na taimaketa."

Shuru ya khalil yayi ya zuba mata idanu yanda take Magana ko gajiya batayi ba tare daya ce komai ba " ita ko gajiya da surutu batayi" ya furta a cikin zuciyarsa yana kallon ta.

" Wai mayene kai ka tsura min idanu tamkar zaka haɗiye Ni, to kur kurwa ta tafi ƙarfinka da wasu ƙanƙanan idanunka."

Dariya Maganar ta bawa khalil lallai wannan tsohuwa akwa comedy yo ko shi mayene mai zai tsinta a jikinta."

" Kinga INNO, nifa ba zuwa nayi ki isheni da faɗi ban tambayeki ba, zuwa nayi na sanar dake zan ɗaukeki mu tafi Birni keda Mahaifiyar Jummo."

" To ubanmu zoka ɗaukeni ka jani mu tafi, yo ni ko naman ɗawisu ake dafawa a binni ai bani zuwa, anan dai ƙauyen dai zan ƙarisa rayuwata.

" Bafa zuwa zakiyi ki zauna ba INNO, Mamma bata da lafiya, tana buƙatar taimakon ki, INNO Mamma tana matuƙar buƙatar ki taimaka mata dan Allah karki ƙi."

A matuƙar razane INNO ta dubi Ya khalil tare da cewa.

" Mamma bata da lafiya subahanallah!! Meyake damunta."

Duk abinda yake faruwa sai da Ya khalil ya sanar da INNO har accident ɗin su Jummo a hanyarsu ta zuwa, jiƙewa INNO tayi sharƙaf da gumi, shuru tayi tare da rufe idanunta, sai kuma ta miƙewa tsaye cike da tsawa da faɗa take cewa.

" Babu inda Sikayel zataje, bazamu watse mubar gida mu duka ba kowa ba, ni da ya zamo dole naje zanje ni, gidan naku babu mata ne waɗanda zasu kula da Jummo har sai Uwarta taje to bazata ba, ku barta ta mutu, wallahi wallahi khalilu idan na tabbatar da zargina asiri aka yiwa Mamma na rantse da Allah duk wanda ya mata sai ya gwammace kiɗa da karatu kuma nasan ba wata bace zatayi wa Mamma asiri sai Uwarka Zainabu saboda nasan halinta tamkar yunwar cikina."

Tayi Maganar idanunta sunyi jajur tare da shigewa bukkar ta, kayanta na magani ta tattara da abubuwan da take buƙata sannan ta ɗauki mayafinta, wajen Sikayel taje ta mata bayanin abinda ke faruwa sosai Sikayel hankalinta ya tashi game da damuwar Jummo.

La'asar lis Baffa ya gama haɗa duk maganin da ake buƙata ya bawa khalil a hanunsa yace a dinga shafawa Jummo a kanta, a kuma dinga ɗiga mata a kunnen ta, insha Allah zata farfaɗo lafiya, wannan kuma ku dinga shafawa Mamma a jikinta kuna bata tana sha Insha Allah zasu sami lafiya."

Sosai Ya khalil yaji daɗin abinda Baffa ya masa suka kamo hanyar Gombe da INNO.


✨✨✨✨✨✨✨✨✨


A matuƙar gajiye suka shigo cikin gidan, tare yana riƙe da boron INNO, bata yadda ta shiga cikin falon ba sai da ta ciro wani abu cikin boron nata, ta samu wajen dake da ƙasa ta sunkuya tare da tona rami ta binne wani abu tamkar mulmule, sannan ta miƙe ta cewa Khalil muje, cikin falon suka shiga da sallama, Momy dake zaune ne ta miƙe a razane tana kallon INNO cike da tsoro, mungun kallo INNO ta jefa mata tana kallon kwayar idanunta, sunkuyar da kanta Momy tayi cike da tsoron INNO.

" Kalilu ina Mamman take?"


. shuru Ya khalil yayi yana kallon Momy da ta sunkuyar da kanta cike da tsoro da alamu abinda INNO ta faɗa akan gidansu gaskiya ne, idan kuwa hakane tir da zuriar Momy, shigewa gaba yayi INNO ta bisa a baya har bedroom ɗin Mamma, da sauri INNO ta matso kusa Mamma tana riƙe hanunta, tafin hannunta ta buɗe tare da ƙarewa tafin hannunta kallo duban A'illo dake zaune tayi tace.

" Tunda ta kwanta, akwai wanda ya shigo ya dubata."

Hawaye ne ya gangaro daga idanun A'illo cikin rawar murya ta ce.

" Babu wanda ya shigo yace ya jikinta tunda ta kwanta sai yaya khalil kawai da Daddy da suke shigowa, da kuma yaya Garko, amma Momy da Aunty Zarah babu wanda yazo yace ya jikin Mamma."

Murmushi INNO tayi tare da cewa,

"sammu aka mata, kuma insha Allah zan cire mata daga jikinta, na mai dashi jikin wanda ya aikata, karki damu A'illo, ki kwantar da hankalin ki, ki cigaba da addu'a nima zanyi iya ƙoƙarina, ki shirya yanzu zaku tafi da kalilu ya sauƙeki wajen Jummo kije ki kula da ita ga wannan maganin da Baffa ya bayar ki dinga shafa mata a kanta duk bayan awa biyar tare da ɗiga mata a kunnen ta, insha Allah babu abinda zata manta, zata farka cikin hankalinta."

" INNO wajen Jummo kuma jummon bata da lafiya ne, mai ya sameta."

Tayi Maganar a gigice, INNO cike da kwanciyar hankali tace.

" Ki kwantar da hankalin ki A'illo, sunyi haɗari ne a hanyar zuwan su cilo amma alhamdulillah da sauƙi, ki dai kije kiyi abinda na umarceki."

Da to A'illo ta amsa tare da ficewa daga bedroom ɗin tayi nasu, Sadiya ta samu tana ƙoƙarin haɗa kayanta sai kuka take tamkar wacce zaa zare mata rai, A'illo bata kula Sadiya ba ta shige tolet.

Momy tashin hankali iya tashin hankali ta shigesa ganin INNO a cikin gidan, domin kuwa tasan kashin ta ya bushe

"wani irin rashin tunani ne ma ya sani na aikata wannan aikin meyasa ban kasheta ba kawai na huta gashi yanzu na jawowa kaina masifa da hanuna, kona kira Asabe ne ko zan saamu mafita, mtsss to me zata iya min INNO tana cikin gidan nan, mtsss bari dai na kirata muji."

Tayi Maganar tana kiran wayar Asabe ringin ɗaya Asabe ta ɗaga cike da tashin hankali, Momy take sanar da Asabe abinda yake taruwa, sun juma suna kitse kitsen yadda zasu sami mafita kafin suka yanke shawarar Asabe zata koma wajen boka domin nema musu mafita."

Ta ɗan juma da gama wayar Ya khalil ya shigo tare da zama gefen Momy kansa ya ɗaura a kafaɗar Momy sai kuma idanunsa suka ciko da hawaye cikin sanyin murya yace.

" Momy ina son sanar dake wani al'amari sai dai ban san ta ya zan iya faɗa miki ba, dama zakiyi hkr ki rungumi ƙaddara kiyi addu'a, Momy da na sanar dake sai dai ina tsoron sanar dake saboda ban san ya zaki ɗauki maganar ba."

Cike da tsinkewar zuciya Momy ta ƙara jawo khalil jikinta tana shafa kansa tare da cewa.

" Karka damu da yadda zan dauki Maganar ka sanar dani kawai insha Allah zan ɗauki hkr da koma meye."

Hawayen da ya khalil ke ƙoƙarin boyewa ne suka zubo masa, numfashi ya sauƙe tare da cewa.

" Momy ɗazu da safe, Garko da Jummo sunyi accident a hanyarsu ta zuwa Cilo"

A wani irin gigice Momy ta miƙe tsaye tare da yin baya zata faɗi, Ya khalil yayi saurin taro ta yana cewa.

" Subahanallah!!! Momy shiyasa nake ta tsoron sanar dake saboda bansan wani hali zaki shiga ba."

Cike da tashin hankali Momy tace.

" Yanzu Garko yana ina yana wani hali, ina dai ba mutuwa yayi ba innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!!! Na shiga Uku ɗana."

" Oh Momy Garko fa bai mutu ba da ransa, kawai ya samu rauni ne, amma fa da sauƙi sosai harma ya samu bacci, ki kwantar da hankalin ki."

Ya khalil ya boyewa Momy cewa Garkuwa ya kamu da ciwon zuciya gudun tashin hankalin ta, wani numfashi Momy ta sauƙe tare da furta.

" Alhamdulillah!!! Yanzu yana wani asibiti bara na ɗauki mayafi na ka kaini."

" Momy a can gaɗam fa sukayi haɗarin, yanzu kuma dare yayi babu halin muje ki bari sai da safe."

" Na bari sai da safe kuma haka za'a barsa babu mau kula daahi a'a bazai yiwu ba, ni zanje na kula da ɗana bazan barsa cikin kaɗai ci ba."

" Oh Momy wa yace miki babu mai kula dashi private hospital ne special, akwai nurse masu kula da marar lafiya yanda ya dace dan haka ki kwantar da hankalin ki ɗan lelenki yana nan cikin kulawa."

" Shikenan zanyi hkr iya na yau kawai, amma dai gobe dole na je na kula da yarona."

Murmushi Ya khalil yayi yana kallon Momy cike da mamakinta hankalinta duk ya tashi akan ɗanta, amma ita Jummo ko ta tambayi wani hali take ciki.

" Momy!!!"

Ya kira sunanta a kasalance, ɗaga idanu Momy TAYI ta kallesa tare da amsa.

" Na'am khalil menene?"

" Momy nikam Garko kam shi kaɗai ne ya tafi Cilo.?"

Momy ko a jikinta ta amsa da cewa.

" Shi da wannan annabor Yarinyar ce, wataƙila ma itace ta sashi yayi wannan accident ɗin, tsinanniy............"

" A'a!!! A'a Momy!!! Karki ƙarisa ta juyo kanki, annoba fa kikace Momy, ta ya ta zamo annoba."

" Khalil annoba ce tunda Yarinyar suka shigo cikin gidan nan komai na gidan nan ya lalace, babu walwala, bamu da nishaɗi komai ya kacame mana ta watsa mana da farin cikin mu."

Murmushi Ya khalil yayi yana kallon Momy yace.

" Farin ciki!!! Ina farin cikin yake!!! Dama can babu wani farin ciki, a gidan nan!!! Gidan da iyalansa basu san su haɗu su zauna suyi hira koda na lokaci kaɗan ba, bamu taɓa zama na minti talatin domin jin damuwar ɗan uwan mu ba, hatta mahaifin mu bai damu daya jawo mu a jikinsa ba, kullum da safe zaiyi gaggawar fita kasuwa, da ya dawo kuma zaice a dauko masa system ɗinsa zaiyi lissafi anan lokacin sa yake ƙarewa, kullum rayuwar a cikin haka take, kowa sha'anin gabansa yake babu ruwan wani da wanii babu wanda zai damu da ɗan uwansa, to ki faɗa min ina zumuncin yake, babu Momy!!!babu shaƙuwa mai ƙarfi a tsakanin iyalan mu, misali Momy, Sajida ƙanwar muce Uwa ɗaya uba ɗaya, Daddy ya kaita karatu can Egypt, yau shekarar ta Biyar Daddy dake baku taɓa kai mata ziyara ba, bakwa tunanin wani hali take ciki, nima da Garko sau biyu kawai muka ziyarce ta, bamu san ya take rayuwarta acan taba da wa take mu'amala bamu sani ba, sai kuɗaɗe kawai da muke tura mata, haka shine zumuncin, Babu abinda ya lalace a cikin gidan wanda Jummo ta lalata, dama can gidan mu babu nishaɗi mune muka lalata gidan mu da kanmu!! Ki daina zargin Jummo bata da laifi sai ma ƙoƙarin da take wajen ganin gidan mu yayi kyau."

Girgiza kanta Momy tayi idanunta sunyi jajur, nufo Ya khalil tayi ta ɗaukesa da mari tare da nunasa da yatsa.

" Ya isheka haka khalil, rayuwarmu muke dai-dai a cikin gidan nan babu wani kuskure, kar zuciyarka tayi gaggawar aminta da zantukan wannan hatsabibiyar Yarinyar, ƙarya take maka ko wani gida rayuwa suke dai dai da tamu, neman watsa mu take, ka kasa ganewa, wai ma na tambayeka shin sonta ka fara da har kake ɗaukar zancen ta.?"

" So!!! So!!! So!!! Hmmm, ai kun duƙursar min dashi sanadin kuskuren ahalina, dalilin da yasa zuciyata ke ƙuna a duk sanda na tuna hakan."

" Kuskure!!! Wani kuskure muka maka wanda har zai duƙusar da kai...................."







🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️ Nima zanso sanin wannan kuskuren na dai yi nan.





08147537180





*UMMU NASMAH CE*
[4/15, 9:22 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*




➰➰ *47 to 48*



" Hmmm!!! Yaushe naji daɗin Soyayyar wacce nake tare da ita ma, babu soyayya tsakanin ki da Zarah kullum cikin hantarar ta kike da kyara hakan yasa matsaloli suka dinga gudana tsakanin mu kullum nakan danneta aduk sanda kika ɓata mata na bata laifi duk da laifinki ne, saboda karta raina min ke, nafi son ko yaushe a dinga daraja minke, Amma ina Momy kin kasa fahimta bare ki gyara, Momy a karo na biyu naji Soyayyar Jummo bazan ɓoye miki ba sai dai kash sanadin rashin shaƙuwar dake tsakanina da ɗan uwana yasa na kasa gane muna son Abu ni dashi, saboda bamu san damywar juna ba, da na sani Wallahi Momy bazan sake sonta ya shiga zuciyata ba, sai daga baya na fahimci Soyayyar dake tsakanin su, na kuma gane duka suna son junansu ta hanyar jinsu da kunnena suna hirar, tun daga ranar na ɗauki alƙawarin cire Soyayyar ta a zuciyata abun baƙin ciki shine har yau na kasa, mtsss!!! Hmmm!!! Sai dai fa Momy dole ne zan haƙura na barwa ɗan uwana saboda ya fini buƙatar ta, wannan shine kuskuren ki keda Daddy kun ɗauki rayuwar boko, babu ruwanku da ƴaƴan ku, kowa yaje yayi abinda yake so, kun kasa saka shaƙuwa a zukatan mu, hmmm!!! Jummo haske ta kawo gidan mu, kuma na yabawa ƙoƙarin ta, ina kuma bayanta zan bata gudumowa ta kowacce hanya."

" Zan kuma tsine maka!!! Muddun ka cigaba da bin wannan Yarinyar kana ɗaukar huɗubar ta, wallahi zan tsine maka, idan yaso kaje ka lalace a duniya."

A matuƙar razane ya khalil ya ɗago idanunsa yana duban Momy cike da mungun mamaki, kansa ya girgiza tare da cewa.

" Momy zaki tsine min kike cewa, ke da kanki kike furta wannan kalmar?!! Hmmm!! Meyasa kika fiye son kanki ne Momy fiye da kowa bakya son gaskiya, na juma da fahimtar haka tun kafin su Jummo suzo gidan nan, na fahimci hakan ne tsakanin ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login