Showing 63001 words to 66000 words out of 93605 words
Chapter 22 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
ma nayi farin ciki daka samu madadinta Garko, domin Jummo ma kyakkyawa ce kuma tana da kyan hali sai dai fa bazata taɓa kaimin Safreena ba, domin Safreena ta MUSSAMAN ce ta maka hallaci a Rayuwa Garko."
Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.
" Wai kai Shetima kishin gawa kake wanda tabar wannan duniyar ba kuma zata taɓa dawowa ba, ka manta da Safreena ka fuskanci Jummo a cikin rayuwata domin kuwa itace take numfashi kuma itace zan Aura a yanzu bata da bambanci da Safreena a zuciyata, nauyin Soyayya ɗaya nake musu babu son Wanda yafi na wani a zuciyata har gobe ina kewar Safreena, Kabir baka san Safreena bani shawarar abinda ya kawo ni kawai kabar zancen Safreena."
Murmushi Kabir yayi tare da cewa.
" Ashe dai ka taɓa Soyayyar gaskiya, nayi zaton yanzu ka fara true ashe akwai wacce ta shuɗe, ni fa zancen Momyn nan ya kulle min kai to meyasa ta tsaneta haka, nifa Garko ina tunanin dole akwai wata matsala koda ba tsakaninta da Jummo ba, ko tsakanin ta da iyayen Jummo, yanzu abinda yafi kaje ka samu Daddy karka kuma tayarwa Momy Maganar sai muga shi kuma Daddy ya zai ɗauki Maganar."
" Okay hakan za'ayi, na ɗanyi let, bara naje sai munyi waya, muje Shetima."
Duk tare suka tashi Kabir ya rakasu har harabar Companyn, sannan ya koma, darect Office ɗin da ake interview ya shiga, ya samu ana yiwa Safreena tambayoyi, zama yayi gefen darecter yana sauraron su yanayin yanda take magana da British American yasa Kabir tsura mata idanu tabbas kyakkyawar gaske ce, " WOW!! She is beautiful Baby" murmushi ya sake tare da saka mata idanu babu ƙiftawa haka kawai yaji ta faɗa zuciyarsa, Soyayyar ta yake ji lokaci ɗaya tamkar shigar iska, har aka gama mata interview ɗin tare da cewa taje za'a nemeta daga baya, tashi Safreena tayi ta fita cikin zuciyarta tana addu'ar Allah yasa ta samu aikin, ko da Safreena ta fita bayanta Kabir ya biyo ta fito harabar Companyn ya tare ta tare da cewa.
" Ji mana ƴan mata"
Sarai Safreena ta jisa ta share tamkar bada ita yake ba ta cigaba da tafiyar ta, tazo daidai get ɗin ya tare gabanta yace.
" Baiwar Allah dake fa nake."
Tsayawa Safreena tayi tare da cewa.
" Ina sauraronka."
Murmushi Kabir ya saki tare da cewa.
" Sunana Kabir kefa.?"
Shuru Safreena tayi tana tuno yanda ta gansa tare da Garkuwa, da alamu kuma akwa alaƙa mai ƙarfi tsakanin su, ƙarya ta masa da cewa.
" Kabir nice name, my name is Safrah"
Ta ɓoye sunan nata gudun karya fahimci wani abu, murmushi Kabir yayi yana tsura mata idanu cike da so yace.
" Like beautiful face like beautiful name, Safrah nice name, hmmm!!! Safrah ni ne manager na wannan Companyn, ina so muyi exchanging ɗin Number, zan kiraki zamuyi Magana."
Murmushi Safreena tayi tana jin a zuciyarta wannan ce damar daya kamata tayi amfani dashi wajen samun wannan aikin, Manager ba wasa ba dole zata samu aikin ta dalilinsa, murmushi ta saki tare karɓar wayarsa ta saka masa, shima nasa ya bata sannan suka rabu Safreena ta tafi.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Bayan kwana biyu
Cike da farin ciki Daddy yake duban Mamma dake tsaye tana murmushi.
" Mamma alhamdulillah!!! Bani da burin daya shige samun lafiyarki, Alhamdulillah!!! Mun gode sosai INNO kinyi namijin ƙoƙari babu abinda zamu ce miki sai godiya"
Murmushi Jummo tayi cike da farin ciki tana ganin yadda Daddy da Garkuwa suke cike da farin ciki, Momy ce kawai fuskarta take ɗaure, kanta Jummo ta kawar gefe tare da ɗaga wayarta dake ringin.
" Hello Meenat okay to gani fitowa ina room ɗin Mamma ne."
Tayi Maganar tare da katse kiran tana fita da kallo Garkuwa ya bita yana sakin murmushi a rayuwarsa yana mungun son Yarinyar.
A falo Jummo ta taradda Meenat murmushi tayi tare da kamo hanun meenat suka haura sama bedroom ɗin ta zama sukayi bakin bed meenat ce tace.
" Hmmm!!! Wai Jummo meke damunki ne 2days bakya zuwa school, naga alamar kamar Soyayya tana son ta rabaki da karatu to ki dawo hankalinki ki gane cewa karatun da kike yana da matuƙar mahimmanci a rayuwarki."
" Kai Meenat daɗina dake saurin fushi da rashin sauraran uzurin mutum, akan Soyayyane zan daina zuwa school, kin dai san naji jinya, dalilin da yasa Ya khalil ya karɓa min hutu harna tsawon wata Biyar a ƙa'ida Monday zan koma school gashi kun kusa zana neco, amma ai ban isa nabar school ba akan so domin kuwa ilimi shine ginshiƙin al'umma."
" Na sani Jummo amma ai ya kamata ace tunda kin sami lafiya ki koma school ba sai lokacin da aka karɓa miki hutu ya cika ba, ni yanzu ba wannan bama, wai ya Garkuwa ya ƙare da Momy ne ta amince da Auren naku kuwa.?"
" Hmmm!!! Ina kuwa ta amince, ni fa na rasa mena tsarewa Momy bansan wacce irin ƙiyayya take min ba, a zuciyata babu mungun nufi ga Momy kullum neman hanyar da zata rabauta nake amma a hakan nice maƙiyyarta!!! Mtss ina cikin tashin hankali domin kuwa muddun Momy tayi nasarar rabani da Ya Garkuwa zan shiga mungun yanayi, ina sonsa fiye da komai a rayuwata, tun bansan meye so ba nake ɗauniya da sonsa a raina harna girma na san me ake kira Soyayya tun baya sona yana gwada min ƙiyayya ban taɓa jin Soyayyar sa ta ragu a raina ba, sau ma ƙara yawa da take ya zageni ya hantareni babu irin ƙiyayyar da bai nuna min ba a lokacin da nake ƙauye amma ban taɓa jin na tsanesa ba dai-dai da second ɗaya KULLUM ji nake bazan iya numfashi ba muddun babu shi, yanzu kuma Allah ya dubi halin da zan shiga idan na rasashi ya kawo min shi cikin rayuwata ya amince da soyayyata yanzu kuma ace zan rasashi, wani irin hali kike tunanin zan shiga, wallahi kullum da tunani da tsinkewar zuciya nake kwana ina tunanin makomata nida Garkuwa haɗuwa ko rabuwa bansan da wanne zan wayi gari ba, ina tashin hankali Meenat."
Cike da tausayin Jummo Meenat ta dafa kafaɗar Jummo tace.
" Ki daina tunani ko damuwa Allah shine maiyi yana ganin komai, kuma bazai bari ki wulaƙanta ba, baki cucesu ba, Allah bazai barsu su cuceki ba, ki dage da addu'a insha Allah komai zaizo miki da sauƙi kuma cikin Nasara."
" Allah yasa, Ya school ɗin ina buƙatar LESSON ɗinki fa, dan nasan nayi missing ɗin LESSON da yawa."
" Wannan ai kinsan ba matsala bace LESSON, fatan dai kin biya kuɗin neco ɗinki dan sun kusa gama karɓar kuɗin.?"
" Ya khalil ya biya harma sun bashi slip, Meenat ko kin san har yanzu akwai Soyayyar wata a cikin zuciyar Ya Garkuwa, duk da a halin yanzu gawa ce ta mutu, amma ina jin kishi ta a RAINA."
Ɗan zaro idanunta Meenat tayi tare da cewa.
" Whatttt!!! Soyayyar wata kuma ƙawata, shi Garkuwan ne ya sanar dake hakan."
Murmushi Jummo tayi tare da cewa.
" Ehhh shine ya sanar dani Meenat, amma a yanzu bata raye Yarinyar ta mutu, sai dai yana yawan ambaton ta, tare da yabonta cike da Soyayya, a duk sanda naji yana yabonta sai naji ba daɗi tamkar tana raye bana son yana min hirarta sai dai bansan ta yaya zan dakatar dashi da hakan ba."
" Haba ƙawata akan me zakiyi kishi da matacciya, wacce bata raye tabar duniyar ba kuma zata dawo ba, dan Allah ki manta da wannan kishin domin kuwa bashi da amfani shi da babu duk ɗaya ne, ki fuskanci matsalar Momy kawai ta isheki, itama Allah ya fidda ke lafiya, sannan ki maida hankalinki da kulawar ki ga abin sonki ki tarairayesa ki lallaɓasa tamkar kwai ba sai na faɗa miki kwalliya ba domin nasan ke gwana ce, hakan shi zaisa ya manta da wata Mace ya maida hankalinsa gareki ki zamo kece kaɗai Abokiyar tunaninsa a zuciyarki, mantawa zaiyi da ko wacce ke kaɗai zaike kallo."
Murmushi Jummo tayi tare da kwantar da kanta jikin Meenat tana dariya tace.
" Shiyasa nake daɗa kaunarki ƙawata domin kuwa akwai ki da kawo mafita mai kyau."
Murmushi itama meenat tayi sun juma suna hira kafin Jummo ta rakata ta koma gida.
***************
Ƙarfe 4 dai-dai jirgin su Ya khalil ya sauƙa a babban airport ɗin dake cikin jihar Abuja, cike da farin ciki take fitowa daga cikin jirgin hanunta riƙe dana Ya khalil, sai murmushi take rabonta da Nigeria 6 yrs numfashi ta sauƙe mai daɗi tare da duban Ya khalil tace.
" Wow Bros!!! I am very happy today I missing Nigeria"
Murmushi Ya khalil yayi tare da cewa.
" Nigeria ma ai tayi missing ɗin ki Zezah, kin san waye zaizo ya ɗauke mu kuwa?"
Kafadarta Zezah ta ɗaga tare da taɓe bakinta tace.
" Bazai wuce ɗan uwan da bai damu da ƴar uwarsa bane Garko."
Dariya Ya khalil yayi tare da cewa.
" Lallai kin manta waye Garkuwa a tunaninki shine zaizo ya ɗauke ki, Lallai kinyi kuskure, ba shi bane Samuel ne zaizo."
" Samuel Kuma Bros!!! Wai wata irin kalar ƙiyayya Ya Garko yake minne da bazaizo ya tare mu ba, mtsss!!! No problem bashi ya ci."
Murmushi Ya khalil yayi ba tare da yace KOMAI ba har suka hango Samuel motar suka shiga ya dawo dasu, tun a harabar gidan Zizah ta ruga da gudu tana kiran.
" Momy Momy!!! Daddy Daddy!!! Momy I am coming!!! I missing you so much Momy!!!"
INNO da Mamma dake zaune a falon ne suka miƙe tsaye ganin mutum ya faɗo yana kiran Momy Daddy ba tare da sallama ba, INNO ce ta tare ta tare da cewa.
" Ke mahaukaciyar ina ne ke baki da hankali ne, ko baki san gidan musulmai kika shigo bane, ba sallama zaki faɗo mana falo kina wani Momy Daddy, ba Daddy ba Allah yasa Dada ne yau naga shashanci daga ina kika fito marar hankali."
Sake baki Zizah tayi tana kallon su cike da haushi da kuma tunanin su kuma wadannan tsofin su waye daga ina aka yayosu da zasu dinga faɗa mata Magana ita da gidan ubanta, bata gama tunanin ba taji muryar Mamma ds ta ƙarewa shirt da jeans ɗin dake jikinta kallo tana cewa.
" Kema dai INNO da wata tambayar kike, ai daga ganin wannan kinsan arniya ce, duba fa kiga wasu tsinannun kayan dake jikinta na marassa mutuncin arnan nan, wannan ai Esther ce."
Garkuwa dake tsaye a sama yana sauraron su ne ya shiƙe da dariya yana tafawa tare da furta.
" Exactly Mamma, kaman kuwa kin sani Esther ce, domin kuwa dai babu ɗan musulmi mai kunya da zaiyi wannan shigar, welcome ƙaramar fitsararriyar Momy."
Ɗaga idanunta Zizah tayi tana kallon Ya Garkuwa cike da jin haushin maganganun su, nunasa tayi da yatsa cike da jin haushi tace.
" Dama a duniya kai kuma kana da makiyayar da ta wuce ni ne, yo haushin me zanji danka min haka, mtsss."
Taja tsuka tare da kallon su Mamma tace
" Ku kuma waɗannan tsofi, su waye ku da har zaku shigo gidan ubana kuna faɗa min Magana, ji beki fuska duk ta tattare ta yamutse babu kyan gani shine zaki dinga buɗe bakinki duk jan goro kina faɗa min magana shima dai Daddy da kwashe kwashe ko ina ya kwaso ku oho amma dai da ganinku kunfi kama da Barorin jeji"
Tana gama Maganar ta haura sama da gudu, INNO zaro idanunta tayi tana duban Zizah yarinya ƙarama da iya baƙar Magana, murmushi Ya Garkuwa yayi domin kuwa yama yi mamakin da bata zagesu ba, shima ya khalil dake tsaye a gefe ne yasa dariya tare da shigowa yana cewa.
" Wai Mamma jikar taki kika manta Aziza ce fa."
"Aziza kuma yanzu Azizar ce wannan mai shiga irin ta ƴaƴan arna, ka fa duba kayan dake jikinta, hmmm!!! Ko da yake babu abinda ma bazata aikata ba, tunda an ɗauke ta an Kaita ƙasar arna karatu duk laifin ubanku ne ai."
Ɗan murmushi Ya khalil yayi tare da shigewa yana cewa.
" Babu ruwana Mamma kinfi kusa keda Daddy."
Zizah bedroom ɗin Momy ta faɗa tana kiranta Momy dake zaune ne ta miƙe cike da farin ciki suka rungume juna cikin farin ciki Momy tace.
" Wow My Daughter welcome, yaushe kika shigo banji kiba."?
Zizah tana dariya ta laɓe a jikin Momy tare da cewa.
" Tun sauƙata a mota nake ƙwala miki kira Momy baki amsa min ba, naji daɗin ganinki Momy, ina Daddy ina kewarsa Momy."?
Murmushi Momy tayi tace.
" Daddyn ku yana kasuwa sai dare zai dawo, yanzu kije bedroom ɗinki kiyi wanka kiji sanyi, sai ki fito akwai muhimin abu dana tanadar miki."
Murmushi Zizah tayi tare da cewa.
" Shikenan Momy na, bara naje yanzu kuwa zan fito."
Tayi Maganar tana fita cike da fara'a, Momy ma murmushi tayi tabi bayan ƴarta ta da kallo cike da ƙauna ita kenan ƴarta mace a duniya,. Zizah bedroom ɗinta ta nufa kanta tsaye, turus ta tsaya hango mutum kwance sai famar chat take, cike da mamaki da kuma faɗa cikin tsawa ta cewa Jummo.
" You!!! Who is this!!!"?
Jummo da taji Magana cikin tsawa ba zato ta miƙe zaune tana bin Zizah da kallo tare da nuna kanta da yatsa tace.
" Me!!!!?"
" Ehhh ke, waye ke da zaki shigo min room har ki kwanta min a bed sai kace gadon uwarki, wannan ai raini ne, mtsss!!! Wai su waye ne aka samu a cikin gidan nan can naga wasu koɗaɗɗun tsofi, nan kuma na shigo naga wata koɗaɗɗiyar yarinya, dalla sauƙa min akan bed malama."?
Jummo baki ta saki cike da tsantsar ɓacin rai tana kallon Zizah domin kuwa maganar ta tayi mungun ɓatawa Jummo rai, harta kasa maida mata amsa still dai muryar Zizah ta kuma ji cikin tsawa ta na ce mata.
" Cewa nayi ki sauƙa min akan gado, da hausa fa na miki Magana kin tsaya kin zuba min ido tamkar wata mayya.................."
*Ummu Nasmah ce*
[5/4, 11:31 AM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*
➰➰ *56 to 57*
GARKUWA daya naɗe hanu yana kallon Zizah yanda take zagin Jummo tamkar uwarta dama ya sani muddun Zizah ta samu jummo cikin ROOM ɗin zata mata rashin kunya domin kuwa ita a rayuwarta ta tsani wani ya raɓeta a hankali ya tako ba tare da Jummo ko Zizah sun gansa ba sauƙar marin da Zizah taji ya sata saurin ɗago kanta a gigice tana kallon ya Garkuwa tare da dafe fuskarta a fusace tace.
" Mena maka zaka gaureni da mari, mena ma."?
Ta jefa masa tambayar tana sakin kuka, Jummo miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
" Subahanallah!!! Haba Ya Garkuwa meta maka haka zaka mareta wannan ba dai-dai bane."?
Ransa ɓace ya Garkuwa yace.
" Tamin tunda ta miki, ki daina bin bayan wannan fitsararriyar Yarinyar domin kuwa ba mutunci gareta ba, bata ganin mutuncin manya ni nafi sanin waye Zizah, kuma wallahi Zizah ki buɗe kunnenki da kyau kiji, kin sanni sarai kin san halina to Wallahi ki shiga hankalinki ki nutsu domin kuwa yanzu ina cikin gidan nan, idan kika ce zaki ɗaga mana hankali na rantse da Allah saina mai dake jaka a cikin gidan nan a ƙarshe na karyaki na wurgarki, shasha marar lissafi, Wannan da kike gani zaginta tamkar ni aka zaga a kanta sai na iya nakasa ki, wannan ɗakin anan take zaune ba kuma zata fita ba saboda ke, idan bazaki iya zama da ita ba kina iya neman wani room ɗin, ki shiga hankalinki kin dai sanni."
Yaƙarisa Maganar yana ficewa daga Zizah har Jummo binsa da kallo sukayi sosai kan Zizah ya kulle, ita wannan ɗin wacece da Ya Garkuwa zai mata barazana a kanta, muryar Jummo taji tana cewa.
" Kiyi hkr ƴar Uwa abinda Ya Garkuwa yayi bai kyauta miki ba, karki sa a rank............."
" Dallah dakata min Malama!!! Karki kuma kirana da ƴar uwarki domin kuwa bani da ƴar uwa, sai ɗan Uwa, ta ina na haɗa jini dake, har akanki zai mareni dake ya tsaneni, kuma wallahi sai kin bar wannan room ɗin tunda ba gidan ubanki bane stupid girl.?"
Tayi Maganar tare da shigewa tolet, Jummo shuru tayi cike da jin zafin maganganun Zizah tabbas idan ba a gidan ubanka kake ba, zaka fuskanci wulaƙanci halinta sak da na Momy babu inda ta barta wannan wani irin gida ne mai cike da tarin matsaloli, idan kayi ƙoƙarin kawar da wannan sai kuma wani yazo hmmm!!! Ya Allah ka kawo wa wannan gida sauyi, tayi Maganar tana ficewa tayi room ɗin Mamma.
Ko da Zizah ta fito bayan ta kimtsa bedroom ɗin Momy tayi cike da farin ciki, a zaune ta taradda da Momy itama ta zauna tana dubanta Momy kallon Zizah tayi tare da rungumota jikinta tana murmushi tace.
" Welcome Zizah nayi missing ɗinki da yawa, dafatan komai dai-dai karatu dai yayi kyau ko.?"
Murmushi Zizah tayi tare da cewa.
" Momy karatu yayi kyau domin kuwa nice nazo second class a department ɗinmu na samu kyautuka masu yawa Momy saura kuma na samu aiki."
Dariya Momy tayi tare da furta.
" Masha Allah abubuwa sunyi kyau Allah ya yiwa karatun albarka, insha Allah jibi zan haɗa taron tayaki murnar kammala karatun ki, yanzu tashi muje kici abinci ko, Zarah ta haɗa miki abincin da kika fi so."
Miƙewa Zizah tayi tana cewa.
" Oh Momy ina Aunty Zarah take ban ganta ba."?
" Zarah taje gidan su barkan Zaliha matar wanta ta haihu."
Da okay Zizah tace tare da fita suka nufi daining.
Shi kuwa Ya Garkuwa yau tunda Daddy ya dawo ya maƙale a room ɗinsa kasancewar yana buƙatar magana dashi haka kuwa akayi bayan Daddy ya ci abinci Momy ta kauce sannan Ya Garkuwa ya dubi Daddy cike da nutsuwa yace.
" Daddy nazo ne ina son nayi Magana da kai."
Gyara zamansa Daddy yayi tare da duban