Showing 75001 words to 78000 words out of 93605 words
Chapter 26 - GELLE BINGEL BOOK COMPLETE BY UMMU NASMAH.txt
kema haske zai shigo rayuwarki na sani A'illo kinso ya Garkuwa kin danne sonsa ne kawai saboda ni kika manta dashi a rayuwarki na yabawa ƙoƙarin ki, Kuma insha Allah bazaki taɓe ba, tabbas jajurcewa da haƙiƙancewa gami da zuciya ɗaya yakan kawo gagarumar nasara a rayuwa, waɗannan jajurcewan sune suka kawo ni matakin nasarar cikar burina, alhamdulillah!!! Allah abin godiya!!! Allah na gode maka daka mallaka min Ya Garkuwa a matsayin inuwata, Allah ka dawwamar dani a gidan mijina ka kore shaiɗan tare da saɓani gare mu."
Da ameen Meenat da A'illo suka amsa cike da farin ciki, can kuwa su Ya khalil bayan an gama ɗaurin Auren ne suka shigo cikin gidan, yayin da ƴan mata ke famar nuna Ya Garkuwa suna ga nan angon shi kuwa sosai yayi kyau a cikin farar shaddar sa wacce tasha aikin blue ɗin zare hular kansa ma kawai abun kallo ne, Shetima da Khabeer har jabeer shi kansa ya khalil da abokansa uku, duk tare suka shigo, har bukkar Sikayel suka shiga tare da gaishe ta, cike da ladabi, daga nan bukkar INNO sukayi inda sukayi tunanin anan zasu ga su Jummo sai dai wayam babu ita babu alamunta kusa da Mamma Ya Garkuwa ya zauna duk da bukkar cike take da mutane hakan bai hanasa raɗawa Mamma magana a kunne ba.
"Mamma ina Jummo take, ina buƙatar ganinta, dan Allah taimaka min."
Dariya Mamma tasa tana murɗe kunnen sa da ƙarfi inda hankalin mutane ya dawo garesu tace.
" Kunga ja'iri marar kunya, wai matar yake son gani sai kace ba gidansa za'a kaita ba, yau naga yaran zamani, mufa zamanin mu bama ganin miji har sai an kaimu kafin musan wanda muka Aure, to nan ƙauyen bama haka daga kai har waɗannan ƴan koran naka babu mai ganinta har sai an kai ta ɗakinka sai wani tsilli tsilli kake min da idanu yiwa ɓarawo."
Ya khalil ne yayi carap yace.
" A'a dakata tsohuwa kar kuma ki zagemu mana ga duka ga kuma tsinka jaka mutum da matarsa a hanasa ganinta sannan kuma a haɗa da baƙar Magana, to ki tsaya iyaka haka tsohuwa, har wani lissafi kike mana da zamaninku, to mu ina ruwanmu da zamaninku naku dabam namu dabam, mu mun shige wannan ƙauyancin rayuwa muke cikin wayewa da fahimtar juna."
Mamma filo ta ɗauko tare da jefawa Ya khalil tana cewa.
" Allah ya wadaran Wannan wayewar taku ta rashin kunya, to dan ubanka ko kaima yau sai na hanaka ganin wannan kodaɗɗiyar"
Tayi Maganar tana nuna Aunty Zarah da hanu, dariya Ya khalil yasa tare da cewa.
" Wannan ne kuma baki isa ba, sai dai juyi gadara da ta rugar wacce zata raga muku amma badai ta gari ba domin kuwa idanunta a buɗe yake tar, idan kuwa kin musa yanzu zaki ganta a jikina musa kiga ikon Allah."
Yayi Maganar yana kashewa Mamma Ido ɗaya, mit bakin Mamma yayi shuru domin kuwa tasan Khalil zai aikata abinda ya faɗa tunda ba kunya garesa ba rayuwarsa yake simple, harara ta jefa masa tare da cewa Garkuwa.
" Kai Garko, yaushe ne zaku tafi saboda zan kaiku Wajen kakan Yarinyar kuyi sallama."
"Mamma ai bazamu juma ba ƙarfe huɗu Daddy yace zamu juya shima yana shigowa da zarar ya shigo aka gaisa zamu wuce, mu bara mu fita."
Yayi Maganar yana miƙewa suma su Ya khalil miƙewa sukayi.
Da to Mamma ta amsa kafin suka fice Ya khalil na tsokanar Mamma bata kulasa ba, ko da suka fito tsakar gidan sanda ya ɗan dudduba ko Meenat ya samu ya gani bai ganta ba, ga ya kira wayoyinsu a kashe duk baya tafiya haka dole ya fita ba dan ransa yaso ba.
Ƙarfe Uku da rabi Daddy ya shigo cikin gidan, sosai suka gaisa da mutane kafin ya koma Wajen Baffa ba'a juma ba kuwa sai ga khalil da Garkuwa sunzo suka zauna Baffa sawa yayi a sanar da Mamma da Sikayel har INNO su fito da Jummo, haka kuwa akayi suka taho a gefe suka zauna, Baffa ne ya dubi Jummo tare da gyaran murya ya fara magana cike da nutsuwa.
" Alhamdulillah!!! Jummo yau dai nauyi ya ɗauru a kanki, domin kuwa kin samu wata daraja wanda a baya baki dashi darajar kuwa itace Aure, duk ƙanƙantar Mutum idan yana da Aure dole za'a mutuntashi, domin kuwa yafi babba wanda ya girmesa daraja idan har shi babban bashi da Aure, Jummo ina son ki saurareni da kunnen basira domin kuwa zan zayyano miki haƙƙin daya rataya a wuyanki Wanda kuma wajibine gareki ki bisu, Jummo, Ga nan mijinki a yanzu shine aljannarki sai kin bisa sannan zaki shiga aljanna, a yanzu ya fimu iko dake dan haka ya zamo dole a gareki ki masa biyayya ki bisa sau da ƙafa duk abinda yace kiyi, ki masa karkiyi musu muddun ba saɓon Ubangiji bane, haƙƙine a kanki ki basa kulawa, ki kuma kula da shimfidar sa, domin itace sunnar Aure, tsafta Jummo karkiyi wasa dashi domin ita tsafta cikon addini ne sannan tana sawa miji ya ƙara son matarsa, ladabi biyayya wajibine a gareki ki yiwa mijinki, ki kula da abincinsa domin kuwa ko wani namiji yana son ace matarsa ta ƙware a wajen girki hakan na faranta ran miji sai Uwa uba haƙuri dole ki kasance mace mai hkr domin kuwa Aure yana tafe ne tare da ƙalubale dole ne duk yanda ake zaman lafiya wata rana a saɓa, ɗacin dake cikin aure yafi zaƙinsa yawa dan haka dole sai kinsa hkr, Banda yawan kai ƙara na dangin mijinki ko na wani hakan na sawa miji ya tsani matarsa, sannan Jummo iyayen mijinki ki kula dasu ki musu biyayya tamkar yadda zaki yima mu iyayenki domin kuwa yanzu baki da iyayen da suka wuce ki, ki kula da haƙƙin maƙwaftaka da kuma mu'amala da mutane mu'amalar ki ya kasance mai kyauce, babu ruwanki da gulma ko gutsiri tsomen ƙawaye karki yadda wata ƙawa ta kaiki ta baro ki ta hanyar miki mummunan huɗuba, ki kula Allah ya baki zaman lafiya keda mijinki ya albarkaci Auren ku ya baku zuri'a ta gari wannan shine nasiha ta gareki."
Shuru Jummo tayi kanta na ƙasa idanunta na zubar da hawaye a hankali cikin rawar murya tace.
" Naji Baffa kuma insha Allah zanyi amfani da dukkan nasihar ka gareni na gode sosai da tarbiyyar da kuka bani har zuwa aurena ina alfahari daku Baffa."
Murmushi Baffa yayi yana kallon INNO da Jauro da kuma Garbati yace.
" Gareku idan da akwai mai mata nasiha a cikin ku ni na gama nawa."
INNO ce tayi gyaran murya tare da cewa.
" Duk abinda zamu faɗa ka wakilce mu ka faɗesa, mu babu abinda zamu ce sai fatan Allah ya albarkaci Auren."
Suma su Sikayel abinda INNO tace suka ce, Baffa ne ya dubi Garkuwa tare da cewa.
" Na dawo gareka Garkuwa, haƙƙine a gareka ka kula da Rayuwar Jummo da kuma dukkan wasu buƙatunta, ka sani idan ka cuceta ko kaci amanarta Allah bazai barka ba, Jummo amana ce a wajenka a Yanzu bata makusanci ko abokin da ya wuce ka, dan Allah ka kula da amanar ta, idan ta maka ba dai-dai ba ka sanar da ita kuskuren ta, ko ka tsawatar mata, idan bata gyara, ganan mahaifinka a yanzu shine mahaifinta ka sanar dashi na tabbatar da zai tsawatar mata Allah ya muku albarka."
Da ameen Ya Garkuwa ya amsa tare da cewa.
" Insha Allah Baffa bazan baka kunya ba, zan riƙe Jummo bisa gaskiya da amana farin ciki shine zai wanzu a rayuwarta na gode sosai Baffa da kyauta da kuka bani."
Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa.
" Baffa bani da bakin da zan maka godiya domin kuwa kunmin abubuwan alheri da yawa a rayuwata kun kula min da mahaifiyata gashi kuma kun ƙara bamu kyautar yarinya na gode sosai ina kuma tabbatar maka da cewa ƴarka bazata taɓa kuka ko baƙin ciki ba, zan zamo mata gata kuma kariya a gareta muddun ina numfashi babu wanda zan bari ya cutar da ita ciki harda mijinta, mun gode mu zamu wuce."
Cike da farin ciki Baffa da su Kawu Garbati sukaji daɗin Maganar Daddy, Mamma da INNO ciki suka koma da Jummo sannan suka shiryata bukkar Sikayel mahaifiyarta ta shiga sukayi SALLAMA Sikayel ta juma tana yiwa Jummo nasiha kafin ta fito, Yaya Marka da Goggo Adda sai kuma ƙawar Jummo ta da wato Sadiya, sune suka raka Jummo, Jummo sosai tayi kuka na rabuwa da Mamma da INNO, kowa na kewar kowa, mota guda aka bawa su yaya Marka da amarya, ƙarfe huɗu da rabi suka bar cikin Tulde suka nufo cikin Gombe, sanda suka iso cikin garin motocin rabuwa sukayi biyu tasu Daddy tayi gabar yayin da tasu Jummo tayi yamma, hakan shine ya tabbatarwa da meenat cewa Jummo gidanta za'a shige da ita ba gidan momy ba, sosai abun ya ɗaurewa meenat kai, a mahanga ta hankali kamata yayi akai Jummo wajen Momy ta mata faɗa tare da saka musu albarka sai kuma baayi hakan ba, lallai akwai zargi cikin naɗi tabbas akwai abinda yake faruwa, numfashi Meenat ta sauƙe tare da kallon window ɗin motar, ana kiran la'asar suna shiga cikin babban estate ɗin wanda ya tara manyan gidaje, wani haɗaɗɗen part suka shiga tare da yin parking kowa ya fito, Ya Garkuwa Aunty Zarah ya miƙawa kay ɗin gidan tare da cewa.
" Gashi Aunty Zarah ki buɗe ku shiga, za kiga bedroom mai kallon kudu shine na Jummo bari muje muyi sallah mu dawo."
Hanu meenat tasa ta karɓa tare da yin gaba ta buɗe ƙofae dukkan su shiga sukayi su kuma suka shige masallaci,koda suka shiga cikin falon sosai yayi kyau ya ƙawatu da adon pink da fari haka kujerun ta suma pink ne da fari labule ma haka komai yayi kyau musamman kitchen yanda yasha jere, Aunty Zarah Sosai abin ya bata mamaki kasancewar iyayen Jummo ƙauyawa ne,ta ina zasu iya saya mata wannan kayan a zuciyarta ta ayyana ko Daddy ne ya saya mata, domin kuwa bata san Ya khalil ne ya saya mata ba bai faɗa mata ba, bedroom ɗin Jummo suka shiga tare da yada zango wasu kuma suka zauna a falo, Jummo tollet ta shiga ta ɗauro alwala tare da tayar da sallar magaruba, duk har sukayi sallah su ya Garkuwa basu dawo ba, kusan sallar isha'i aka shigo da kulolin abincr wanda akayi a gidan daddyn meenal abokin Daddy bayan sunyi Sallah ne sukaci abincin wanda ita dai Jummo gagara ci tayi da ƙyar ta taɓa kaɗan nan ma sanda Inna Marka tA sata a gaba tukunna taci, su Aunty Zarah Takwas da rabi suka bar gidan ita da matar abokin Daddy, sai ya rage daga meenat sai su Inna Marka, sai wajen tara na dare Ya Garkuwa da Shetima suka shigo, Inna Marka suka samu a falon sannu suka mata tare da ajiye mata leda mai ɗauke da gasassun kaji da nono mai sanyi, suka gaisheta sannan suka shige bedroom ɗin Jummo suna zaune da meenat, ya zauna a gefen gadon yana cewa.
" Amaryata tun ɗazu nake son ganinki kamar kuɗi amma an hanani, ɗago min fuskar na gani farin ciki na."
Ɗan murmushi Jummo tayi tare da ɗago kanta suka haɗa ido lumshe idanunsa ya Garkuwa yayi tare da cewa.
" Tsarki ya tabbata ga ubangin da ya hallice wannan kyakkwawar halittar, kinyi kyau sosai, na kwana biyu ban jiki ba, sai naji kamar shekara nayi ba ganki ba, Mamma ɗazu haramta min ganinki tayi, da fatan komai ya tafi dai-dai ko."
Murmushi Jummo tayi tare da ɗaga masa kai alamun eh dubanta ta kai ga Meenat da kwatakwata hankalinsu baya kansu zancen su kawai suke, tace.
" Dear nayi kewar ka, sosai fa ba kaɗan ba, kaga yanda ka ƙara kyau kuwa, sai ka dawo tamkar balaraben Saudiyya."
Dariya Ya Garkuwa yayi yana ɗan taɓe bakinsa yace.
" No ban kaiki kyau ba, saboda kyawun ki ya dusashe nawa, kyanki fa na musamman ne, amma na shigo ne na duba ki hankalina ya kwanta, kar Inna Marka taji haushina bari muje sai da safe.
" To shikenan, ka tabbatar kaci abinci kafin ka kwanta bana son ka kwana da yunwa."
Murmushi Ya Garkuwa yayi tare da cewa.
" Ko banci abinci ba, iya kallonki kawai da nayi ya ƙosar dani, kiyi bacci mai daɗi."
Duban Shetima yayi yace.
" Kai zancen ya isa haka tashi mu tafi kasa ƴar mutane gaba da zance."
Dariya Shetima yayi tare da cewa.
" Wa yace maka zuba kawai nake, soyayyata nake gyarawa Malam tunda kai taka ta gama gyaruwa ɗinyarka ta nuna a hanunka."
Dariya Jummo da Ya Garkuwa sukayi Ya Garkuwa cike da tsokana ya cewa meenat.
" To fa, ashe cinikin harya faɗa bamu sani ba Meenat to Allah ya sanya alkairi."
Yayi Maganar yana dariya tare da ficewa, shima Shetima bayansa yabi, Jummo dariya tayi tace.
" Hmmm!!! Da alama dai Shetima ne zai kasa samarinki.?"
" Kai Jummo shegen gulma, gaskiya yamin ina jin zan iya rayuwa dashi."
" Hakamma yayi Shetima bashi da matsala."
Sun juma suna tattaunawa akan Shetima kafin suka kwanta.
Washe gari da safe still dai daga gidan abokin Daddy aka kawo musu breakfast, Ya Garkuwa bai shigo ba sai kiranta kawai yayi, sai la'asar lis ya zoshi kasancewar zai mai dasu Inna Marka gida, koda Inna Marka zata tafi sosai Jummo tayi kuka sai dai babu yanda ta iya dole tasa ta haƙura, Ya Garkuwa koda suka ɗauki su Inna Marka shida Shetima gidan Momy suka wuce dasu, a falo ya ajiye su tare da haurawa bedroom ɗinta, gefenta ya zauna, kauda kanta Momy tayi ganin Garkuwa ya shigo domin kuwa sosai take jin zafinsa, cike da sanyi jiki ya kira sunanta, ƙin amsawa Momy tayi kusan sau Uku ya kirata kafin ta ɗago idanunta tana jefa masa mungun kallo cikin tsawa tace.
" Kiran uban me kake min me zaka bani, me ruwanka dani me zai kawoka wajena, ni yanzu ba uwarka bace domin kuwa baka ɗaukeni matsayin Uwa ba!!! Tashi ka fice min daga room karna kuma ganinka gabana!!!"
Kansa ya sunkuyar ƙasa ransa a mungun ɓace hankalinsa na matuƙar tashe yace.
" Kiyi hkr Momy bani da wata Uwar da ta fiki a duniya, Momy komai ya faru ne bisa ƙaddara babu ta yadda kowa zai kaucewa tasa ƙaddarar ni son Jummo shine tawa ƙaddarar, Kiyi dan Allah ki fita ku gaisa da Inna Marka ƙanwar.........."
Tsawa Momy ta daka masa.
" Ƙanwar Uwarka Sikayel ba!!! Haka zakace, na san Marka kaje ka ce mata bazan fito ba, ta riƙe gaisuwarta bana buƙata na baku nan da minti goma kubar min ROOM ɗina ko kuma wallahi na fito na durun uwarku daga kai har Markan cin mutunci zan mata na shan gishiri, fita kabar min room ɗan iska wanda baisan darajar uwarsa ba."
Runtse idanunsa ya Garkuwa yayi idanunsa na cikowa da hawaye ya ce.
" Momy dan Allah kiyi hkr ki taimakeni ki kankaro min mutuncina ki fita ku gaisa dan Allah Momy ki........."
" Ko zaka mutu kana min magiya, WALLAHI bazanje ba, ni sanda nake baka umarni na ke roƙonka ka haƙura da wannan Auren ka min biyayya ne, sai ni zan maka, ka tashi ka fita ko na maka baki kabi duniya ka lalace."
Miƙewa Ya Garkuwa yayi cikin sanyin jiki, ya fito Ya khalil ya gani tsaye duk abinda suke yana jinsu kafaɗar Garkuwa ya dafa tare da girgiza masa kai alamun kar ya bari hawayen su zuba, tare suka sauƙa ƙasa Ya khalil ne ya yiwa su Inna Marka ƙaryar cewa ai Momy ta je asibiti ganin likita tare da basu haƙuri,. Su Inna Marka basu kawo komai a ransu ba, suka tashi tare cewa a gaishe ta ace sunzo su danƙa mata amanar Jummo basu sameta ba, Ya khalil dubu hamsin ya basu, shima ya Garkuwa ya basa 100k drever ne ya ɗauke su suka kama hanyar Tulde, shi kuwa Ya Garkuwa cike da baƙin ciki ya fashe da kuka tare da kwantar da kansa jikin Ya khalil.......
*UMMU NASMAH CE*
[5/23, 9:34 PM] UMMU NASMAH❤️: *PAYMENT GROUP ONLY*
➰➰ *64 to 65*
Shuru ya khalil yayi cike da tausayin Garko, ya rasa wace irin zuciya ce da Momy da bata yafiya, numfashi ya sauƙe tare da cewa.
" Dole fa sai kayi haƙuri Garko, kasan halin Momy dole sai ka mata uzuri uwace babu yanda ka iya da ita hkr dai shine zakayi ka kuma dage da addu'a insha Allah komai zai shige, matsalar dana hango kenan yasa na roƙi Daddy cewa kar a kawo Jummo gidan nan a shige kawai da ita gidan su gudun kar Momy ta jawo mana abun kunya, da ka shawarce ni ma, da bazan barka ka kawo su Inna marka gidan nan ba, hmmm!!! Kayi hkr muna nan muna addu'ar Allah ya shiryi Momy ta gane annabi ya faku."
Guntun hawayen dake fuskarsa ya Garkuwa ya goge tare da cewa.
" Na sani Bro kai ma kuma ka sani ina hkr da Momy amma a yanzu na fara tunzura wani irin ƙiyayyane haka abun yana min ɗaci a zuciyata yanda Momy take gwada min ƙiyayya ni da matata, ka duba kaga abincin da za'a kai min gidana a bawa baƙi, Momy cewa tayi idan an kai daga gidan Ubana Allah ya isa bata yafe ba, sai gidan abokin Daddy ne aka kai, wannan wacce irin masifa ce."
" Hmmm!!! Da alamu bazaka iya yin haƙurin da nayi ba, saboda kafin Momy ta nuna muku ƙiyayya matata ta nunawa, ina ga sai a cikin kwana biyun nan ne Zarah take samun sassauci daga wajen Momy har naga suna hira, meye ya kawo wannan nasarar da Momy take sauraran Zarah yanzu haƙuri da juriya, kai ma ita zakayi ka cinye jarabawarka, ni yanzu Maganar da nake maka, na samu transfer ɗin aiki zuwa Abuja, ranar monday zamu tafi ni da Zarah, za'a barwa Momy gidan ita kaɗai kamar yadda take so sai hankalinta ya kwanta domin abinda na fuskanta zama da wani ne bata so,