Showing 1 words to 3000 words out of 68990 words

Chapter 1 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

NA FAƊO DAGA BENE...
NA ZARCE RIJIYA
Hakkin mallakar
Badi'at Ibrahim Mrs Bukhari b4b gidan ƙamshi


Gawurtattu uku

Lamba ta 1


Samfoti! Samfoti!! Samfoti!!!
( ƊANƊANO)


Ƙabilar Hausa dai, ƙabilace dake zaune a arewa maso yammacin taraiyar najeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar. Ƙabilace mai ɗimbin Al'umma, amman kuma a al'adance mai matuƙar haɗaka, a ƙalla akwai mutane miliyan hamsin da harshen yake asali gare su. A tarihi an ce ƙabilar hausawa na tattare a salasalar ko manyan birane. Hausawa dai sun samu kafa daularsu ne tun daga shekarar 1300's, sa'adda suka samu nasarori da dauloli kamar daular Mali songhai, Borno da kuma fulani. A wasu lokutan Hausawa sun samu gagarumin ikon mulki da haɗaka ta kau da baƙi ƴan neman ruwa da tsaki, da kuma neman aringizo a cikinta, da kuma halƙallar ko cinikin bayi. A farko_ farkon shekaru na 1900's, a sa'adda ƙabilar Hausa ke ƙoƙarin kawar da mulkin aringizo da Fulani , sai turawan mulkin mallaka na burtaniya suka mamaye arewacin Najeriya da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida, a bisa ƙarƙashin mulkin burtaniya, ƴan mulkin mallaka sai suka marawa fulani baya naci gaba da manufofin aringizon siyasarsu.
Wannan haɗakar gamin gambizar an farota ne tun asali a matsayin fulani su ɗare madafan ikon a tsararren tsarin siyasar arewa. Akasarin masu mulki na fulani sun kasance a yanzu al'adance Hausawa gwamitse ko da yake Hausawa na farko_farko maharbane, amma ya zuwan addinin islama da kuma karɓansa da hannu bibbiyu ya sanya labari ya sha bam_bam. Ginshiƙoƙin al'adun Hausawa na da matuƙar zaranta, kwarewa da kuma sanaiya fiye da sauran al'ummar dake kewayenta. Sha'anin noma ita ce babbar sana'ar hausawa inda Hausawa ke ma sana'ar noma kirari da cewa, na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya kai yatarar, akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima watau harkar fatu, rini, saka da ƙira. Fannonin dake mutukar samun cigaba a harkokin sana'o'in hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da kullum, tare da masu mulki da masana. Harshen Hausa shine mafi girma da mafi sanaiyar harshe a nahiyar Afirka. Harshen Hausa ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci kana kuma harshen na tafiya tare yanayin mu na zamani bisa al'adar cuɗeni_ in _cuɗeka. Harshen Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a da ba Hausawa bane a nahiyar Afirka. Bugu da kari akwai cincirindon al'ummar Hausawa a manyan biranen yammacin Afirka da arewacinta da kuma yankunan cinikayyar al'ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna bi a hanyar ta zuwa aikin hajji. Akwai kuma rubutattun adabi masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami da aka buga tun kafin zuwan turawa ƴan mulkin mallaka na burtaniya. Har ila yau kuma wani tsarin rubutu a ajami da aka ƙirƙiro tun kafin zuwan turawa da ba kasafai ake amfani da shi ba yanzu. Wannan shine takaitaccen tarihin Hausawa.




Jihar Filato (Jos)
Jihar filato, jihace mai sanyin gaske, garine mai ni'ima, dan Lokacin damina ana samun wadataccen ruwan sama masha Allah, sannan babu yawaitar zafi sam ko da lokacin zafi ne ya shigo. A da yankin Haifam, wannan yanki na Haifam tsabar sanyi ance har dusar ƙanƙara tana zubowa, amman wannan labarin da jimawa sosai tun duniya na kwance. Wannan dalilin yasa turawa suka miƙe ƙafarsu a garin jos . Gasu da arzikin kuza, da noma. Kowa ya sani garin jos sune dankalin turawa, dankalin hauwa ( dandikwali, ko fasa ƙirji), da kayan gwari. Suke raba ma garuruwa da dama kaya, musamman kudu. Suna da atile, suna da risga, suna da lemun tsuntsu, akwai tsada, akwai bado, da sauran kayayyakin ciye ciye iri_iri. Garine mai cuɗanyar yarirrika masu tarin yawa kamar irin su. Hausawa, yarbawa, inyamurai Fulani. Sai kuma ƴan ƙasa irin yaren birom, angas, tsala, tubi, maguzawa, Arago, da dai sauransu. Ada ana zaune zaman lafiya da amana tsakanin ƙabilu mabanbatan ra'ayi da addini, ana rayuwa a cakuɗe cikin soyayya da yardar juna. Daga shekarar 2001 rikece_rikicen faɗan addini ya kunno kai jihar ta filato, wannan tashin hankula shine ya daƙile tattalin arzikin jihar, ya kuma jefa tsoro da fargaba a zukatan mazauna jihar, har ta kai ta kawo, kirista na tsoron gamuwa da musulmai, musulmai na tsoron gamuwa da kirista, sabili da kisan mummuƙe da suke yi a junansu. Yaƙin farko da aka soma gudanarwa an yishi ne ranar juma'a a wata anguwa da ake kiranta ( kongo rosha, a babban masallacin juma'a na gidan Alh jojibes) wannan rana itace ta zama tamkar matattakalar rikici, domin wata kirista aka wakilta tayo shiga irinta banza, tazo ta wuce ta gaban Sallah. Al'amarin daya tada zaune tsaye kenan, an zubar da jini, an yi kashe_kashen rayuka a wannan rana daga ƙarshe aka saka dokar ta ɓaci na ba shiga ba fita tsawon awa ashirin da huɗu. Har izuwa yanzu jihar filato bawai ta zauna lafiya bane. Har gobe ana rikici a tsakankanin fulani makiyaya, da kirista manoma. A baya ma an yiyyi irin wannan tashin hankula tsakanin Fulani da makiyaya a ƙauyan ( dogo na hauwa) Duk ƙasar da babu zaman lafiya talauci ke mata dabaibayi, haka talauci yaima garin filato dabaibayi, talakawa su suka fi yawa a jihar filato, masu kuɗin cikin nasu basu da yawan azo a gani. Sakamakon ƙone babbar kasuwar taminos data kasance kasuwa ta uku a fannin kasuwanci da hada_hada, musamman kasuwancin gwanjo. Kuma har gobe wannan kasuwa a ƙone take, sakamakon ƙone kasuwarnan ya sanya Al'umma da dama a cikin ƙangin talauci, hakan ya sake taɓarɓara tattalin arzikin jihar, sakamakon hakan jihar ta samu ci baya sosai, kuma baƙi ƴan cirani sun rage shiga jihar sasakai.


LAYIN ƊAN MARAYA JOS. Layine da marigayi Alh Adamu ɗan maraya wannan shahararren mawakin na gargajiya ɗaya tamkar da dubu ya zauna, kuma har gobe gidanshi yana cikin wannan layi. A bayan gidanshi akwai rafi wanda wannan rafin shima an yi mishi inkiya da ( rafin ɗan maraya)
Unguwace mai cike da ɗumbin tarihin gaske. ( Allah Ubangiji yai mishi Rahama yasa Aljanna ta zamto makoma a gareshi Ameen)

Gidane madaidaici mai ƙaramar ƙofar shiga da dogon zaune, a cikin zauren akwai ɗaki falle ɗaya a ciki wanda anan mutan gidan suke ajjiye shirginsu. Daga cikin gidan kuma filin tsakar gida na hango madaidaici wanda yaji sumunti sumul sumul, daga gefe akwai rijiya da murfinta. Ɗakuna uku ne a jejjere ko wanne ɗaki ciki da falo ne, sai wani ɗaki falle ɗaya daga can gefe daban. Ga bayan gida a tsakar gidan da kicin duk a tsakar gidan. Tsakar gidan duk datti da tulin kwanukan wanke_wanke harda ma tsunmokaran kayan wanki.

TANI:
Yau da kwalima na tashi kasancewar yau jajiberin babbar sallah ce, gidan ya kacame da tarkacen kwanuka da kayayyakinmu na wanki ni da yaran. Unguwa kuma ta kacame da toye_toyen kayan fulawa da suyar kaji, da suyan miyar sallah, kamshi kamar zai kashe mu. Katifar yara na kinkimo na fito da'ita tana yararin ruwan fitsari, ta jikin bangon ɗakina na jingine katifar dan rana in ta fito ta doketa ko Allah zai sa ta bushe kafin wani daren a kuma jiƙeta ta fitsari sharkab. Hajiyayye dake bakin kofarta ita da ƙannenta suna faman murzar fulawa zata yi toye_toyen Sallah, tayi maza ta toshe hancinta tare da sakin wani tsaki mai ɗan banzan ƙara. A ƙirjina naji dirƙar tsakin na abokiyar zamana, amman sai nayi biris tamkar kurma haka dama nake zaune a gidan. Hindatu ƙanwar facalarmu ce ta fito daga ɗaki hannunta riƙe da baƙin bokiti shaƙe da daƙwa_daƙwa kajin gidan gona. Gawayi ta shiga jerawa a kan kurfo dinta, tana yi tana ƴan waƙe_waƙenta dan Hindatu gwanace wajen rero waƙoƙin ƴan wasan Hausa, musamman waƙoƙin mawaƙi ado gwanja. Balaraba ce ta ja zanina tace.
"Umma Sulaiman ya gama tsefe mun kan ya wanke mun?" Murmushi guntu nayi mata na dubi gashinta nace.
Ki zauna ki jirani zan duba miki ko ƙwarƙwatar kan ki sun mutu" Dariya Balaraba tayi tana susa kanta tace.
"Umma ai Yaya Sulaiman ya cire mun guda goma suna ƙirgawa da Sani."
To kije kice mishi yaci gaba da cire miki kafin in gama wanke kwanukannan." Da gudu ta koma ciki, ni kuma na zauna a kujera ƴar tsugunno da ƙyar abinka da mai ciki, kuma cikin ya girma sosai. Ina wanke ƙwanukannan ina tunanin rayuwa, ni tunani nake yi shin Aure ne bai karɓeni ba, ko kuwa haka yanzu mazan hausawan suka zama ne, Aure da saki ya zama tamkar ado a ƙasar Hausa ko ince a ƙabilar Hausawa. Yarinya ƙarama sai ki ganta ashe bazawarace, ko kuma yau ayi aure ringiɗi_ringiɗi gobe a sako mace, na kuma rasa a ina matsalar take daga mazan ƙabilar hausawa ne, ko daga matan ƙabilar Hausawan ne? Wannan amsar ita na gagara samu, amman zukatan mata da iyaye yana soyuwa da wannan yawan mace_macen auren, kuma a kullum abun sake ta'azzara kawai yake yi, ina malamai da hukumomine shin basa ganin halin da ƙabilar Hausawa ke ciki ne ko yaya?. Ajjiyar zuchiya na sauke kaina sai sarawa yake yi, cikin kankanin lokaci na game wanke ƙwanukannan tas na shanyasu a kan tabarma dan su bushe. A gurguje na farma wanki, wankin yana da yawan gaske, dan har sai da ta kai ta kawo bamu da wankakken kaya ko guda ɗaya daga ni har yaran. Sabulun nera saba'in da omon hamsin bazai mun ko kwatan wankin ba, zan dai yi iyakar wanda ya sauwaƙa sauran kuma in koma dasu ciki. Ina cikin wankin Sulaiman babban yarona ya fito shi da ƙannenshi.
"Umma na gama kashe musu ƙwarƙwatar, kan Amina babu sosai, kan Balaraba da Hauwa na kashe yafi hamsin umma."
To sannu yaron kirki, yanzu bari in baka nera ɗari ka siyo kumfar los maza, sai in wanke musu kan maza suje layin kitso." Ɗarin dana daɗe da tanadarta dan wannan ranar na kunto a bakin zanina na miƙa ma Sulaiman ya fita da gudu shi da mai binshi Shafi'i. Su Balaraba kuma suka nufi wajan Hajiyayye data cika gidan da ƙamshin suyan meat pie, ga cincin ma ƙannenta nata taya ta yankawa da almakashi, can gefe ga Hindatu na tafashen kaji, Sani kuma yana zaune a bakin ƙofa sai sannu yake mun. Fatattakosu Hajiyayye tayi har tana toshe hancinta wai kar su sata amai wari suke yi. Murmushi kawai nayi na dubeta da kyau da ƙaton cikinta itama a gaba, ga ƴarta Samira a zaune a can wajen rijiya tana tsefe mata kanta suna hira da Hindatu dake dakan yajin sallah. Kai kawai na girgiza bance komai ba. Ina cikin shanyar kayan dana ɗauraye Sulaiman suka shigo a guje da ledar kumfar los a hannunsu.
To ku ƙarashe mun shanyar, kai Sulaiman ka dinga ɗaurayewa shi yana shanyawa. Ruwan zafin dake kan kurfo ɗina na juye a bokiti, na ɗauki bokitin da tukunyar zuwa bakin rijiya, ruwa na jawo na cika tukunyar na mayar wuta kana na surka ruwan bokitin na dawo inda nake wankin.
To tawo Balaraban umma in soma sa miki ko?" Abunka da yarinta da gudu ta tawo har tana zamewa, na shasshafa mata kunfar los ɗinnan sama_sama ina gamawa na wanke mata tas, sannan na shafa ma Amina, sai autata Hauwa ƴar wata takwas da ɗoriya itama na shafa mata na wanke da sauri, dan ance mun tana maganin ƙwarƙwatane ma shi yasa na shafa musu ko Allah zai sa mu rabu da ƙwarƙwatar. Basilin na shafa musu a kan bayan ya bushe na taje musu shi tas, babu laifi suna da gashi sosai dan ma baya samun kulawa. Bayan yara sun game mun shanya ni kuma na share ruwan tas, sai na zari mayafina nace.
Muje in saku a layin kitson sai in dawo in ci gaba da aikina, ku kuma ku je ai muku aski Sani tawo muje." Dai_dai zan fita nace.
Hajiyayye na fita zan kai yara kitso, Hindatu na fita" Ni dai banji sanda Hajiyayye tace wani abun ba. Na dai ji Hindatu tace sai na dawo. Fita mu ka yi fararam_fararam zuwa gidan kitso, mazan suka suce shagon aski kayan jikinmu duk datti duƙun_duƙun damu. A hannun mai kitso na danƙasu na ciro ɗari biyar na miƙa mata, ɓata rai tayi tace
"Gaskiya umman Sulaiman wannan yaran kitsonsu yafi ɗari biyar, gashinsu da yawa fa yara har uku, ace kitson sallah ne za'a bani ɗari biyar." Haka mai kitsonnan ta tsinkani a gaban yaran mata sa'annina da waɗanda basu kaini shekaru ba. Amman tunda ni nake nema a wajenta dole na karya wuya nace.
Haba Aisha mai kitso ki taimaka, kinsan garin ya ci wuta ba kuɗi, ko guda nawa ne ayi musu nasan kuɗin nawa ya gaza ayi musu a hakan" Da ƙyar a hakan ma ta yarda, ajjiye Hauwa nayi a cinyar Amina ni kuma na fito. Ina tafe ina cizon yatsa harna isa gidan. Tun daga zaure nake jiyo muryar Hajiyayye tana ma Hindatu tsegumi.
"Allah ya kiyaye tun yaushe Kaila ya dena yarda su haɗa shinfiɗa da ita, wari fa take yi yace, kuma nima wallahi ina jin warin, daga ita har yaranta, har Allah _Allah yake yi girki ya dawo hannuna dan ya more ƙuruciyarshi." Hindatu kuma ta saka shewa tace.
"Ahayye daɗi, ai ko ni shigarki ta yamma ta taran mai gida in kika yi tana burgeni balle wanda akayi domunshi. Shi fa kanshi in ya shigo tsakar gidannan ya ganki, kasa gane kan shi yake yi " Jingina nayi a jikin bangon zauren ina haki, har wani duhu_duhu nake gani tsabar tashin hankalin dana tsinci kaina a ciki. Na jima cikin irin wannan yanayin da naji hirar ta lafa sai nayi sallama na shiga.
"Ahh har kin dawo nayi tunanin ai zaki jira a gama musu ne?" Cewar Hindatu kenan cikin fara'a take mun magana"
A"a Amina zata kula dasu ni zan ƙarashe kwalima ne. Ɗakina na shige na soma kintsa kayayyaki, babu komai a ɗakin a falo dai ledar tsakar ɗakine shinfiɗe kawai sai tarkacen kayan sawan yara, bangon ɗakin cike da jinin kuɗin cizo da yara ke kashewa a bango, haka uwar ɗakin ma take, katifa ce yashe a ƙasa sai buhunhunan kayan sawata dana yara. Share ko'ina nayi na tattare kayayyakin yara na ɗura a buhu, in banda zarni babu abunda ɗakin yake yi. Tawa katifar na kinkimo na fito da'ita. Hoɗar kuɗin cizo na dinga zazzagama katifun. Ina cikin wannan aiki mai kitso da lalle tazo yi ma Hajiyayye. Nan da nan aka soma yarfa mata jan lalle mai kyau sosai, ni kam in kai mari in kai gwauro inata mayar da kwanuka kichin ɗinmu ina jerasa a gefe ta inda kwandona yake da tukwanena. Bayan na gama na jawo tran silver da salateb da reza na soma yankama yara wanda zanyi musu lalle zuwa dare. Hajiyayye har an gama yarfa mata kitso lallen ya bushe wankewa ma take yi. Ado ne yaron aikin Kaila ya shigo kici_kici da buhun bako har guda biyu, ɗayan sai ɗigar da jini yake yi. Gaisawa mu ka yi ya wuce ƙofar ɗakin Hajiyayye ya dire mata"
"Amarya gashi in ji Oga Kaila kaji ne sai tumaturi na miya da su magi, wannan kuma yace in baki kuɗin niƙa " Karɓan kuɗin tayi tana washe bakinta Ado yayi mana sallama ya fice. Nan Hajiyayye ta shiga kacaniyar wanke kayan miya, bayan ta gama wanke kaji ta ɗaura tafashensu a babbar tukunya. Ƙanwarta ce ta kai mata niƙa yayin da ita kuma ta soma jera gawayi a wani kurfo ɗin. Ina zaune sai ga sallamar Habu ƙanina da leda mai zane a hannunshi. Baki na washe dana ganshi
Habu kaine a tafe daga ina haka?"
"Daga wajan bara Inno tace in kawo miki nama ne da muka samu a wajan sadaka da yawa shine ta ɗibar muku, harda tumaturi" Haƙiƙatan nayi farin cikin samuwar namannan da tumatur matuƙa. Baki na washe nace.
Ai kuwa na gode sosai. Habu wanke mun kayan miyan ka kai mun niƙan shi su Sulaiman sun tafi layin aski babu wanda yasan yaushe zasu shigo gidan" Bai yi musu ba ya juye kayan miyan a ƙaramin bahun ya ja ruwa a rijiya ya zuba. Tas ya wanke kayan miyar, na ɗebo tafarnuwa da ɗanyar citta dana gyara su yanzu na watsa. Bai jira kuɗin niƙa ba ya fice, nasan akwai kuɗi a jikinshi dan ba ƙaramin kuɗi suke samu a wajan bara ba. Naman na juye a ƙaramar tukunyar miya ta, naman kuwa cikin tukunyar dam, ɗaurawa nayi a wuta nasa magi da su citta da tafannuwa na rufe. Alwala nayi na shiga ɗaki na gabatar da sallar azahar ina zaune ina tasbihi Habu ya shigo da sallama. Kallonshi nayi futu_futu dashi fuskarnan tashi duk waskane ƙayayau_ƙayayau.
Inno dawa ka barta a wajan barar Habu?"
Ita kaɗai na bari tace kar in zauna, Indo tana wajan barar Baffa tana mishi jagora, da tare muke zuwa bara da Baffa, amman sai yai ta dukana da sanda shine mu kai canje da Indo" Kai kawai na girgiza haka kam Baffa yake, muma wanne irin duka da sanda ne bamu sha ba, in mun rakashi yawon bara daga ƙarshe Yaya Use dena yima Baffa jagora tayi. Dubu ɗaya ya ciro a aljihunshi ya mika mun.
"Inno tace in baki ayi ma su Balaraba kitson sallah. Yaya Tani ni kam na tafi sai kunzo wunin sallah" Godiya nayi ma Habu har zaure na rakashi, ina tsaye ina kallonshi sai sauri yake yi, ƙafarnan tashi ba ko takalmin arziki, wasu hawaye masu ɗumi suka sulalo mun, da sauri na juyo na shigo cikin gidan. Har zuwa yamma sakaliya aiki muke yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login