Showing 21001 words to 24000 words out of 68990 words
Chapter 8 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
ya sallameki a koma kwana a ƙarƙashin gada. Ai dama ance mana a ƙasan gadar legas aka haifeki da rana" Ji nayi zuchiyata na harbawa da ƙarfi, jinin da take watsawa ya wuce kima. Ƙafafuna sun gaza motawa kaina kamar zai tarwatse nama rasa wanne irin tunani ma zanyi. Ana cikin haka na jiyo muryar Inno tayi sallama da yaran. Shigowa tayi da sallamarta, tana duƙe riƙe da ƙafarta kamar yadda take. Ganin Baba Rammai ya faɗaɗa fara'arta tace .
"Rammai kece a garin? Maraba lale ga jikokin naku na kawo miki su, nima duk sun isheni suna san ganin uwasu." Sama da ƙasa Baba Rammai tayi ma Inno wani kallon wulaƙanci, cikin ba'a tace.
"Ai fa ga jikokina, daga yawon barar kuke ne naga duk kun haɗa zufa Inno ƙafafunku duk ƙura" Da dariyar wulaƙanci ta ƙarashe maganar tana jayo hannun Balaraba. Inno da bata san ba'a tayi mata ba tace.
"Wallahi daga bara muke can muka wuni dasu, shine dai nace bari in kawo su" Hindatu ce ta ƙaraso inda muke dan gulma ta gaisa da Inno. Kaila kuwa bai ma kalli inda inuwar Inno take ba yayi shigewarshi ɗaki. Baba Rammai taja hannun su Sulaiman suka zauna a tabarma, Hauwa da rarrafe ta bisu tana murna taga ƴan uwan nata.
Inno muje daga ciki kici abinci ko?" Baki Inno ta washe tace
"Kamar kuwa kinsan yinwa nake ji wallahi, dan tun fitarmu rogo na sai mana na nera ɗari kawai" Ɗakina na da tayi ƙoƙarin shiga cikin dakiya nace
Inno na canja ɗaki kin mance ne?" Bata ce dani komai ba, na shige ta biyo bayana. Sai ga Hajiyayye da wata koɗaɗɗiyar nera ishirin ɗinta a hannu, muna haɗa idanu ta wani yamutse fuska.
"Inno ga sadaka ko?" Juyowa Inno tayi ta kalli Hajiyayye kana ta dawo da kallonta gareni. Sai lokacin ta fahimci halin da nake ciki. Ajjiyar zuchiya inno ta sauke ta kalli Hajiyayye a karo na biyu tace.
"Allah shi karɓa Allah yasa a mizani ƴannan, amman ki bar kuɗinki ai kema ƴata ce. Rammai Allah ya bamu alkhairi ni zan koma" Baki Hajiyayye ta taɓe tayi komawarta tana ƴan surutan da bazan ce ga abinda take cewa ba. Sallama Inno tayi da Baba Rammai. Muna shiga zaure tace.
"Me kika yi musu haka Tani, in ce dai ba Auren kike son kuma kashewa ba a karo na biyar? Ki buɗe kunnenki da kyau a wannan karon in kika sake aurenki ya mutu sai dai ki nemi wasu iyayen ba mu ba, Baffa ma zai iya tsine miki kibi duniya. Ina fatan ba akan auran da Kaila zai ƙara bane ko? Hawayene suke fita a idanuna wasu kan wasu sai kai kawai na girgiza ma Inno amman na kasa magana.
"Abincin ki samun ko a leda ne in naje gida maci da ƙannenki, ni bazan shiga ba kar uwar mijinki ta zargi wani abun, ni da nasan tazo ma babu abinda zai kawo ni gidan" Bance mata komai ba na shiga ɗaki na zuba mata abinci a kula dukka na juye musu, nasa musu miya da nama ban ma ko ɗumama miyar ba tunda na dawo, dake soyayyar miya ce babu abinda ya sameta.na fito da ledar abincin a hannuna."
Inno ina zuwa bari in tambayi izinin Kaila sai in kai ki gida dan ba zaki iya riƙe kayan ba" Kafin tace wani abun sai ga shi ma ya shigo zauren shi da su Sulaiman da dukkan alama masallaci zasu je, dan anata kiraye_kirayen sallah.
Kaila dan Allah zan raka Inno gida kaga dare yayi hankalina bazai kwanta ba in ta tafi ita kaɗai" Sake shan kunu yayi ba tare da girmamawa ba yace.
"Wanne irin zaki rakata kuma, naga har dare kuke kaiwa a wajan bara, kuma da ƙafa kuke zuwa gida kuna tafe kuna bara. Yau kuma sai kin rakata? To adawo lafiya" Yana dasa aya ya raɓa ta bayan Inno ya wuce, yaran suka bishi a baya, dake Sani yaro ne mai hankali naga ranshi bai yi mishi daɗi ba. Kuka mai sauti na saki da naga fitarmu.
"Banda kuka Tani, kiyi haƙuri ba komai bane ai wannan mu dai in zai riƙe mana ke ai shikenan, wuce muje ki rakani titi in kika sani a abun hawa ma ya'isa inna sauka a kan layinmu zan samu matasa su kai mun ledar gida" kiran Balaraba nayi, da gudu tazo nace.
Ku zauna a wajan Baba Rammai zan kai Inno gida. In Yaya suka dawo daga sallah ku jirani a cikin nan ɗakin kinji ko? Wannan shine ɗakinmu yanzu" Fita mu ka yi ni da Inno, muna zuwa titi na tara mana abun hawa mu ka shiga. Babu mai iya cewa komai tsakanin ni da ita. Ita kanta cikin tunani take. Ban bar Inno ba sai da na kaita har gida nayi sallar magriba kafin nayi mata sallama a gurguje su Baffa basa gidan basu dawo ba tukunna. Tun daga ɗan nesa da gidanmu nake jiyo kukan Hauwa hakanne yasa na ƙara sauri dan in shiga gidan. Ina shiga na ji kukan a cikin ɗaki da sauri na shiga. Hauwa na bayan Sani yana jijjigata sai kuka take ta haɗa hawaye da majina. Sauran yaran suna zaune jigum daga gefen katifarsu. Zare Hauwa nayi a bayan Sani na nemi kujerar tsakar gida na zauna, sai da na zura mata nono tayi shiru sai ajjiyar zuchiya take faman yi, nima ajjiyar zuchiyar nake ta faman saukewa. Ga haki daya dame ni..........
MRS BUKHARI[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE...
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 7
*Ina miƙa ɗinbun miliyoyin godiya ga duk ɗaukacin masoyana, masoyan Shanono. Haƙiƙa littafinnan yayi karɓuwar da ni kaina banyi tunanin zai yi ba. Ta dalilin wannan labarin manyan mutane sun kirani a waya sun jinjina mun. Zawarawa suma sun kira sunce na taɓo musu inda yake musu ƙaiƙayi. Ina godiya ga duk makaranta wannan littafin, Mrs Bukhari gidan ƙamshi taku ce*
*Yana da kyau ko wacce mace ta karanta littafinnan tun daga farkonshi izuwa ƙarshenshi. Domin makaranta ne mai zaman kanshi wannan labarin*
Me yasa baka kaita ko da wajan Baba Rammai bane ka barta tana ta kuka?" Sulaiman ya dube ni yace.
"Koro mu tayi har Abba yana ce mana jikokin makafi da guragu. Umma Hajiyayye kuma ta daki Balaraba dan tace yinwa take ji" Da sauri na miƙe na fita tsakar gidan, ruwan wanka dana ɗaura a wuta yana ta tafasa har ya ƙune kusan rabi. Saɓa Hauwa nayi a baya na sauke tukunyar na girgije kurbo ɗin na ƙara gawayi, kana na mayar da tukunyar kan wuta. Taliya na ɗakko a kitchen guda ɗaya na zuba a ruwannan. Sai da nayi sallar isha na juye musu taliyarnana a babban faranti da miya. Sai da suka ci sannan su kai Sallah. Ni ko ruwa na kasa kurɓa sam. Ina zaune a bakin katifa yara duk sun yi bacci, mazan katifarsu daban, matan kuma muna katifa ɗaya. Kaina ya ɗaure da tunani nama rasa wanne irin tunani zanyi ma. Ga yinwa data addabeni yaron dake cikina sai juyi yake yi, ni kuwa ko ruwa bazan ma iya kurɓa ba, hawaye kawai nake zubarwa. Ina tuno irin so da kulawar dana samu a wajan Kaila a lokacin farkon aurenmu. Wallahi in wani ne yace mun Kaila zai ƙyamace ni har haka bazan yarda ba. A yau na gane nadamar aurena yake yi, ko ko in ce nadamar haɗa tsatso yake yi da ɗiyar mabarata wanda ubanta yake makawo, uwarta kuma take gurguwa, ni Shanono wacce aka haifa a ƙarƙashin gadar legas a tsakiyar kutare da guragu, da makafi. Ni na yarda wannan itace ƙaddarata, na aminta cewar maza basu karɓeni ba, Aure biyar amman babu wanda naji daɗinshi, gashi wannan ma lilo yake yi.
Ban taɓa yarda da masu cewa yanda suka ga rana haka suka ga dare ba, sai lokacin da matsalolin gidajen aurena suka farma rayuwata. Kamar kullum yau ɗinma banko iya runtsawa ba. Washe gari na tashi da zazzaɓi da ciwon mara mai tsanani ko tashi bana iya yi."
Sani zaka iya hura mun wuta?" Na tambayeshi cikin muryar tsananin ciwo, yaran duk sun kewayeni sai sannu suke yi mini.
"Umma zan iya, nasan yadda akeyi"
To ka hura mun wutar, sai ka ce da Ammanku dan Allah tazo banda lafiya" Da sauri Sani ya fita, ni kuma naci gaba da juyi a tsakar ɗaki. Kamar minti goma sha biyar da fitarshi sai ga Kaila ya buɗe labulen ɗakin yana tsaye a kaina sai wani ajjiyar zuchiya yake faman yi.
"Lafiya kike neman Hajiyayye? Mun kwana gida ɗaya baki iya fitowa kun gaisa da Rammai ba balle ki dafo abinci ki kawo mata ko? Jiya haka kika kwashi abinci tab leda mai zane kika ba Inno, amman ita Rammai baki iya bata ba ai." Baki na cije nace.
Kai haƙuri bani da lafiya ne, shi yasa ma nace a kira mun Hajiyayye ta taimaka ko asibiti ne ta raka ni"
"Allah ya ƙara sauƙi ko haihuwar ce?" Sai kuma ya sassauta murya ganin halin da nake ciki.
Wallahi ban sani ba, Amman zai iya yiwuwa haihuwarce wata takwas da ɗan ɗoriya ne. Naga sai cikina ya kusan wata goma nake haihuwa ne" Baki ya taɓe.
"To bari in kira unguwar zoma zaifi, in ma asibitinne sai ku tafi tare. Kike wani raki haihuwa ke da kika ɗauketa kamar ki saki ƙaton kashi. Ba za'a fi wata biyu ba zaki sake shiga wani laulayin ai in dai kece Shanono ciki da goyo shi kadai kika iya ai, duk wani abun arziki baki sanshi ba. Ga shegiyar ƙazanta ɗaki sai warin annakiya da tsummokin bara " Ana cikin wannan halin Hajiyayye ta iso, ganinshi a bakin ƙofar ne yasa tace.
"Baby lafiya kuwa inata jiranka karyawa fa kake yi?" Murmushi yayi mata.
"Kinga naƙuda inaga take yi, ki kira mata Rammai. Yaran kuma ki ja su basu karyaba zan shigo musu da masa sa ci nasan kin gaji. Bari ina zuwa, sannu Shanono Allah ya raba lafiya " Nan ya fice ya barni a tsakar ɗaki. Ji nake dama zan iya haɗiye zuchiyata in mutu ko na huta"
Sulaiman ka kira mun Sabira maza" Da gudu Sulaiman ya fita, Hajiyayye ta wuce cikin gida da sauran yaran ko uffan ta kasa ce mun. Har sai da Sabira ta ƙaraso kafin Baba Rammai ta leƙo, a dokin ƙofa ta doge."
"To tunda kin iso ma ai shikenan, kinga ni surukace, Hajiyayye kuma kishiyace, Hindatu kishin sauri, kinga ba sa ga tsaraicinta ba sai dole." Tana idasa faɗa ta saki labulen, ba sannu, ba Allah ya raba lafiya. Haka naita gumurzu Sabira na yi mun sannu. Anguwar zoma ce ta shigo ɗakin jikinta saye da fararen kaya na ma'aikatan asibiti.
"Tun yaushe kika soma jin halamun naƙudar?" Ta tambayeni tana duba ni"
Da safennan ne kamar wasa naji ciwon sai tsananta yake kuma yi. Cikin bai kai haihuwa ba amma" Dubani tayi da kyau tace.
"Ai kuwa ba haihuwa bace juyi ne. Amman ki je Asibiti likitoci su duba ki." Kaila ne ya leƙo ɗakin. Ba shiri Sabira ta rufe wuyanta zuwa ƙirjinta da gyalenta, shi kuwa yaƙi ɗauke ido a kanta. Ni kuma ina zaune zaman ɗabaro a ƙasa, marar na lafawa kaɗan_kaɗan.
"Yaya akayi haihuwarce dai ko?" Ya tambayi unguwar zoma.
"A'a bazai wuce juyi ba, ba haihuwar bace. Amman ya kamata taje asibiti" Hanya Kaila ya bata ta fita dan sauri take yi da gani wajen aiki zata. Tsaki Kaila yayi yace.
"Sabida shegen raki irin naki juyin cikin kike ma murƙususu haka sai kace mai haihuwar fari, haihuwa ta barkatai? Allah ya kyauta, sai ki fito da tsunmokin ki ai, da gaiyar kuɗin cizo masu fenti in sun gama na ɗakin Bilkisa sai su yi miki kamar yadda nayi alƙawari." Ni dai na ma rasa ta cewa, Sabira kanta a sauke har Kaila ya gama magana ya tafi. Ita ta fitar mun da komai na ɗakin nawa zuwa tsakar gida, ni kuma ina zaune akan taburma a tsakar gidan. Baba Rammai ce ta fito daga ɗakin Kaila da waya riƙe a hannunta tana waya da amaryar Kaila. Masu fentin ɗakin Amarya suna ta tayi, wasu suna fentin tsakar gidan namu. Har haf door akayi a ƙofar ɗakin Amarya, daga gefen ɗakin kuma kafinta na buga kitchen irin na langa_langa, da dukkan Alamu Kaila na ji da wannan Amarya dan shima kwalima yake yi a ɗakinshi. Ana gama fentin ɗakin Amarya aka shiga fente ɗakin ango. Hajiyayye sai kumbure_kumbure take yi, motsi ɗaya ta jibgi ɗiyarta. Ni dai ina zaune jigum, Sabira ce ta kama yaran tayi musu wanka suka yi ficewarsu waje. Ita ta ɗaura abincin masu aikin fenti da Kaila yazo yace in ɗaura. Amadudu da Baba Rammai kuma fita su ka yi zuwa kasuwa. Ni dai ina kwance a kan taburma ciwon jiki dana zuchiya na neman rayuwata. Bayan masu aiki sun gama aikinsu Sabira ta zuba musu abincinsu, ni kuma sai da nayi Sallah na ɗan taɓa abincin, ta haɗe yaran du ta zuba musu abincinsu. Kaila yana ta kai kawo tsakan kanin ɗakinshi da ɗakin Hajiyayye dan fishi take yi dashi sosai, shi kuma babban tashin hankali ne fishinta gareshi, har sabunta mata fenti itama akayi. A haka dai ya shirya ya fice a gidan. Ko awa bai yi ba sai muka jiyo sallamsrshi da wasu maza suna kiciniyar shigowa da setin gado. Gado da wadrope Kaila ya sake filla_filla daga kamfanin ɗan sogai. Tsofaffin kuma aka fice dasu. Sabira kuwa sai hidima take yi dani, ita ta share mun ɗaki ta goge ƙasan ɗakin Sani da Sulaiman su ka kama mata suka shigar da katifun da buhunhunan tsunmokaranmu.
Sabira nagode sosai Allah ya bar zumunci. Ya kamata ki tafi gida kinga magriba ta kawo kai, kije ki ɗaura ma mai gidan Abinci, ragowar abincin dake cikin tukunya zai ishi yaran, naga ma kin dumama musu." Murmushi tayi tace.
"Babu komai ai Tani, in ruwan wankan naki yayi zafi sai ki sa Sulaiman ko Sani su juye miki. Su Balaraba kuma zan aiko Mustapha zuwa bayan isha ya zo ya tawo mun dasu gidana, zuwa gobe sa dawo kya samu kiyi bacci sosai " Sabira ƙawace wacce samun irinsu da wuya a wannan zamanin. Godiya marar iyaka nayi mata, sallama tayi mun ta tafi, ni kuma na lallaɓa na tashi. Fitowata daga banɗaki kenan Baba Rammai suka shigo ita da Amadudu kici_kici da kaya, harda su katan_katan na ruwa da lemo. Sannu da zuwa nayi musu zan wuce, Baba Rammai tace.
"Ungo wadannan ledojin kayan miya da kayan lambu ne a ciki, wannan kuma kaji ne an fige an yanka ma. Gobe sassafe sai ku tashi da aikin ƴan jere zasu tawo daga Zaria kuma fitowar safe zasu yi." Ledojin na karɓa a hannunta, sauran suna ƙasa. Kayan ruwa da lemun kuma Amadudu ya shiga dashi ɗakinshi. Ɗaki na kai kayan sai da nayi har sallar isha sannan na aika Shafi'i kitchen ya ɗauko mun bahun ƙarami. Kajin na juye sai da suka cika madaidaicin bahun dam. Haka na kinkima da ƙyar zuwa tsakar gida na shiga aikin gyaran kaji nan. Mustapha yayi sallama ya tafi da su Sulaiman Hauwa kawai suka bar mun. Ina wanke kajinnan marata na karta mun. Gawayi na haɗa na ɗaura tafashen kajinnan a ƙatuwar tukunya dan kajin sun yi guda takwas masu abun ne to da abunsu kura da kallabin kitse. A kan kujerar tsugunno Kaila ya shigo ya same ni, ni ni kaɗai a tsakar gidan gashi ba wuta, sai hasken waya na kunna. Sannu da zuwan da nayi mishi ma da ƙyar ya amsa ni, yayi shigewarshi ɗakin ƴar gwal. Sai goman dare na sauke tafashe na tafi dashi ɗaki, ko lomar tuwo ban kai bakina ba. Haka na kwana ina ciwon mara, washe gari kuma na shiga hidimar aikin ƴan jere, Hindatu da Hajiyayye babu wanda yayi yinƙurin taya ni. Tun sassafe na kira Anty Use da Anty Karime a waya na sanar musu da batun abincin jeren, sun ce zasu zo da safen su taya ni aikin. Kuma na aika ma Sabira. Zuwa ƙarfe taran safe duk suka hallara, har mun soma tuyan kaji, Sabira kuma tana zaune tana gyaran kayan lambu. Ganin su Yaya Use ne yasa Hindatu zuwa ta kama mana aikin. Kayan miya ta gyara yara suka tafi kai niƙa, ni kuma ina gefe ina ɓarar maggi ina cije leɓe na ciwo.
"Tani ki je ki tambayo Rammai me za'a girka ma baƙin kinga na gama da suyar naman." To kawai nace, na yi sallama a ɗakin Hindatu Baba Rammai na can. Bayan mun gaisa nake tambayarta mai za'a girka"
"Wannan ai ya rage naki Tani. Komai na hannunki du abunda kuka san zai burge baƙin sai kuyi. Dan Allah ayi abinci mai daɗi dai ga kaji nan wadatattu mutanennan masu arziki ne sosai, a kamanta musu."
To shikenan Baba Rammai"
Fitowa nayi na same su.
To tace mu yi koma meye, ya kuke gani me za'a girka?" Yaya Use tace.
"To ni dai ban san kalolin abincin zamani ba, ban iya ba ko ba gaskiya ba, nafi ƙwarewa a abincin gargajiya." Yaya Karime tace.
"Nima dai wallahi ko jallof ɗin taliya ban iya girkata ba, in nayi duk sai ta raɓe a cikin romon" Sabira tace.
"Babu damuwa ni na iya, sai ku taya ni muyi. Party jallof rice za mu yi, da pepper chicken, sai ayi musu coslow tunda akwai kayan lambu da yawa" To da taimakon Sabira data kasance kan gama komai muka kammala girke_girken mu. Ni dai bani da manyan kuloli na zamani, Hajiyayye nayi_nayi da'ita ta ba da nata a zuba abincin taƙi, daga ƙarshe da Baba Rammai tasa baki sai kawai ta fashe da kuka ta kuma rantse ba zata bayar ba. Sai Sabira ce ta je gidanta ta ɗakko mana manyan kuloli na Alfarma, tsabar ƙyalli ras nake ganin fuskata a kular nan.