Showing 51001 words to 54000 words out of 68990 words

Chapter 18 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

ta juyo ta dubi Kaila ta dubi Bilkisa, zuchiyarta kamar zata fashe, harara ta sakar ma Bilkisa Kaila yace.
"Yaya jikin naki iya rigima?
Bata tanka ba. Bilkisa ta gaishe da su Ta Bizaro, suka amsa babu yabo babu fallasa dai. Shamwila kuma ta dire basket ɗin abincin a gefe. Agogo Bilkisa ta kalla tace.
"To Gwanda ina ganin mu koma gida ko, mun gaishe da mai jiki ai" Jakarta ta zuge ta ƙirgo dubu biyar ta ajjiye a gefen fulon da Hajiyayye take kwance.
"Ga wannan ko ayaba a siya ma mai jikin. Hajiyayye Allah ya ƙara sauƙi sai kun dawo gida kuma" Ficewarta tayi waje ita da Shamwila, Kaila kuma ya tsaya yana tambayar babu matsala dai ko? Daga ƙarshe yai musu sallama a gurguje ya fice. Da Amadudu da Hindatu suka ci karo a wani ɗan dogon falo da zai sadaka da da waje. Dan daga bakin ƙofar ana hango titi kai tsaye.
"Amadudu kun samu ƙarasowa kenan?" Cewar Kaila, Amadudu ya shagala sosai wajan kallon shamwila, take ran Kaila ya ɓaci yace.
"Kai me kake kallo haka ne, meye haka wai?" Sai lokacin Amadudu ya dawo nutsuwarshi, ya ɗanyi tsaki yace.
"Yaya wallahi yaron da Tani ta tawo dashi daga ƙauye baka ji yanda ya ɗume gidan da wari ba. Yanzu haka mun fito mun tarar yana wanka a tsakar gida, wata ƴar budurwar yarinya na kulawa da su Sani. A gaskiya bazai yiwu mu zauna da wannan yaro a gida ɗaya ba. Wannan ai sai wata cutar ta kama mu ko ta kama namu yaran." Duk maganganunnan da Amadudu yake yi, idanunshi na kan Shamwila, ita kuwa sai ƙasa take yi da fararen idanunta. Ganin haka Kaila ya miƙa ma Bilkisa keyn motar Isa daya aro yace.
"Ku je mota Ɗanyan gwal ku jirani" Bilkisa tayi gaba ba tare data karɓi keyn motar ba, sai daddanna wayarta take yi.
"Shamwila karɓo car key ɗin mu je" Tace a gadarance, tare da yin wucewarta tana taku ɗaiɗai. Hindatu ta taɓe baki ta yi shigewarta cikin ɗakin da Hajiyayye take kwance. Dan ko gaisawa basa yi da Bilkisa, ba ma wani fitowa tsakar gidan take yi ba sam, in ma ta fito Bilkisa ba ubanda take kulawa, bata ma nuna ta san da mutane a tsakar gidan. Shamwila tasa hannu ta amshi key a hannun Kaila. Fatar hannunta da fatar hannunshi suka samu haɗuwa, ɗumi da laushin fatar Shamwila ya jijjiga tunanin Kaila. Kusan mutuwar tsaye yayi a wajan, tare da bin bayan Shamwila da idanu. A yau ne yayi mata kallon ƙurulla har ya gano lallai akwai sirri tattare da'ita. Ita kuwa Shamwila sai kaɗa mazaunanta take yi suna wani irin rawa tamkar an ƙulle ruwa a leda. Gata gwanar iya tafiya tamkar mage, takunta a harɗe take yi. Ajjiyar zuchiya ce ta kubce ma Kaila da Amadudu. Harara Kaila ya doka ma Amadudu kafin yace.
"Shanono ai bata da hankali. Ashe ɗanta ne dake ƙauye ta tawo dashi, tunda ta zaci Ni ɗin ɗan mahaukaciya ne, ko dan ta ga na aureta ina saurayi ita kuma bazawara mai aure huɗu, ko shi yasa tayi tunanin lusarine ni ohon mata. Zata bar gidan daga ita har yaron ka sha kuruminka. Yanzu dai bari muje kar in bar su Shamwila suita jirana kaga babu daɗi. Sannan zan yi ma gargaɗi ka ɗauke idanunka akan Shamwila in kana son kan ka da arziki. Kar ka kuma yi mata irin wannan mayunwacin kallon" A wajan ya bar Amadudu. Yana shiga mota ya ja fuu suka koma gida, a lokacin har azahar tayi"



Caji office:


Shanono:
Muna zaune sama da awa uku ni da Yaya Use babu wanda yace da ɗan uwanshi wani abu, sai tubka da warwara nake yi. Babban damuwata ƙunzugun dake jikina ya jiƙe sharkab da jini, bansan yaya zanyi in sake wani ba. Ga tunanin Dauda, da sauran yaran, duk da nasan Sabira zata kula min dasu, amman ba lallai ta iya jure wari da tsutsotsin jikin Dauda ba. Ina cikin taɗin zuchi wata ƴar duma dumar ƴar doka ta shigo ɗakin da muke.
"Ku taso kuna da baƙi a kanta" Zungui_zungui muka fice tare da ɗaura ƙafafunmu a inda ta ɗaga. Habiba Bala na hango tare da Sabira a zaune a binci. Tana ganina ta miƙe tsaye tare da ƙaremun kallo.
"Shanono meya same ki haka, kaddai dukan ki suka yi Shanono?" Murmushin ƙarfin hali nayi mata nace.
Babu wanda ya dake ni Habiba Bala. Nagode da kika amsa kirana a lokacin da bamu da kowa sai ke." Ajjiyar zuchiya Habiba Bala ta sauke tace.
"Oficer a fito mun dasu kamar yadda dpo yace. Ni kuma da kaina zan dinga kawo muku ita a duk sanda ake da buƙatarta" Wanda ta kira officer yace.
"Sa mana hannu a wannan takaddar Hajiya. Kuma duk sanda kotu ta buƙaci ganinsu ba'a same su ba. Ki sani ke zamu kama. Dan mika kes ɗin za'ayi gaban kotu kamar yadda masu kes ɗin suka buƙata. Kuɗin beli kuma ko wacce dubu goma_goma, sai dubu biyu kuɗin biro da takarda. Jaka Habiba Bala ta zuge ta ciro damin kuɗi ta ƙirga ta basu dubu ashirin da biyu kamar yadda suka buƙata. Ta kuma kaɗa hannunta a kan takaddar. Mayafinmu suka miƙa mana kana suka bamu hanya muka fito. Sai lokacin naji salama. A motar Habiba Bala muka wuce.
"Habiba Bala ni kam ba zani gidan Tani ba. Dan mijinta yace in na kuma zuwa kotu ce zata raba mu. In ji da wannan sharrin da Hajiyayye tayi mun ma
Kinga in na kuma taka ƙafata na shigar mishi gida, da laifin maita ƙila za'a kamani, ace na lashe kurwar Amaryar Tani" Sabira tace.
"Yanzu yaya Use shi Baban Sulaiman ɗinne ya hana ki zuwar mishi gida, bacin ƙanwarki yake aure?" Yaya Use tace.
"Ke dai bari Sabira ai sha'anin mijin Tani sai adda'a zamu ce. Nima tsautsayine yasa na daki Hajiyayye da ciki. Amman wallahi da ba ciki a jikinta saina karairayata." Ni dai ina zaune jigum. Habiba Bala sai girgiza kanta take yi kawai. Nan yaya Use tayi mata kwatancen gidanta muka ɗauki hanya. A ƙofar gida muka haɗu da Baban yara mijin yaya Use. Da halama fita zai yi kasuwa. Motar da muke ciki ya ƙurama idanu, bai ƙibta ba har sai da yaga fitowarmu daga motar. Duk yanda yaso ɓoye farin cikin ganin an sakomu kasa boyuwa yayi, sai ga Murmushi shinfiɗe a fuskarshi, har yana tararmu.
"Use an sako ku? Kin ganni a tsaye a nan nafi awa uku ina tubka da warwara. Malam zailani nake jira ma ya fito mu je can caji office ɗin mu dubo ku. Malamai sannunku da zuwa. Tani dukan ki su ka yi a caji office ɗinne?" Kai kawai na girgiza mishi halamar a'a. Bayan mun gaggaisa muka shiga cikin gidan muka bar yaya Use a tsaye da mijinta. Muna shiga yara na ganinmu sai murna suna faɗin.
"Sun dawo, sun dawo, sun dawo" Murmushi nayi musu domin in ƙarfafi murnarsu. Inno ƙarama na kalla nace.
Inno ɗaura mun ruwan zafi dan Allah. Habiba Bala, Sabira mu shiga daga ciki." Ɗakin Yaya Use muka shiga, muna zama sai gata ta shigo. A dofane Habiba Bala ta zauna a gefen tarin tulin tsummokin kayan wanki. Ɗakin da kaɗan yafi nawa fasali. Sai dai baya zarni sam dan yaranta sun girma, sai dai warin dauɗa, da warin jinin kuɗin cizo. Inno ƙarama ce ta lego bayan ta gaishemu tace dani.
"Umman Sulaiman na kai miki ruwan ban ɗaki. Yaya Use tace.
"Ki gargasa jikin ki da kyau Tani dan dole ki sha fanado ma. Ni dai to kawai nace. Ban jima ba na fito, illahirin jikina ciwo yake yi, duk inda na watsa ruwan zafi sai in ji kamar an watsa mun wuta. Da zafin ya isheni sai na haƙura da wankan na wanke tsumman jinin dake jikina, da ɗan diras ɗins, na shanya a langa_langar data kewaye bayan gidan. Na ɗaura zani na fito. Ɗakin kwanan su Inno ƙarama na shiga. Kayanta na saka, ta bani ɗan diras ɗinta da tsumma na yi sabon ƙunzugu kafin na koma ɗakin Yaya Use, Habiba Bala na kalla itama ni take kallo.
"To Yaya mu kam zamu gudu zan saukesu a gida, ni kuma zan koma Bauchi yau. Amman zan ɗaukar muku lauya da zai kareku. Dan na fahimci so suke Shanono ta wulaƙanta, in sha Allah muddin ina da rai Shanono tafi ƙarfin wani yai mata wulaƙanci ko cin zarafi. Ku kwantar da hankulanku ina tare da ku, ga Sabira da mijinta ma. Dan Sabira ta tsokata mun kaɗan daga cikin irin zaman da Shanono take yi a gidan kaila" Yaya Use tace.
"Mun gode Habiba Bala, da ace du ƙawaye irinku ne ke da Sabira da kawance yayi daɗi sosai. Allah ya saka muku da Alkhairinshi" Da "Ameen" Muka amsa dukkanmu. Har bakin mota yaya Use ta raka mu, sai da taga tashin motarmu kana ta koma ciki. Kai tsaye Habiba Bala naga ta nufi Nalele pharmacy dake Bauchi road
"Bari in shiga in siyo magani, dan kina buƙatar magani da wadataccen bacci." Bata jima a cikin Nalele ba sai gata da ledar magunguna. Kasuwa ta wuce, nan ma tayo mun siyayya ni da jaririna, Sabira kuma ina ganinta ta fita . Na dai ganta a teburin mai nama amman bansan abinda ta siya ba. Daga nan muka wuce gida kai tsaye. Da sallama muka shiga gidan. Zurub sai ga Hindatu ta leƙo zauren ganina yasa ta riƙe bakinta.
"An sako ku ne Umman Sulaiman?" Murmushi nayi nace.
Allah ya nufa Hindatu" A wajan na barta muka shige ɗakina. Habiba Bala ta toshe hancinta tace.
"Meye haka shanono, wannan ai iskanci ne. Wannan warin na meye kuma haka, ɗakin yara ne amman nan?" Tsuru_tsuru nayi, na bisu da kallo, Sabira ma hancinta a toshe yake. Kuka na fashe musu dashi kamar ƙaramar yarinya. Ganin hakan yasa duk suka saki hancinsu, Habiba Bala ta kama ni ta zaunar dani. Itama ta zauna a gefena. Da sauri ta miƙe tana duba mazaunanta, fitsarine sharkab ya jiƙe mata tsadaddiyar rigarta. Sabira tace.
"Habiba Bala. Inaga mu je gidana mu tattauna, amman kafinnan bari in fitar da komai na ɗakin a samu ɗakin ya sarara."
"A'a Sabira babu damuwa. Mu fitar da kayan tare. Shanono ga kujerar tsugunno ki zauna" Cewar Habiba Bala. Zama nayi jiki ba kuzari, Sabira ta kunto mun jaririna ta samun shi a cinyata. Nono na zura mishi a baki, su kuma suka fita da katifu suna yararin ruwan fitsari. Harda kayayyakin wankinmu dukka Habiba Bala ta janye buhun zuwa tsakar gida.
"Ki fito waje Tani ki zauna, a samu a wanke ɗakin."
To Sabira na fa gode." Fitowa nayi na nemi inuwa na zauna. Habiba Bala na ciki tana wanke mun ɗaki. Sabira kuma tana haɗa gawayi a kurfo, naga ta cika tukunya da naman kan saniya. Hindatu da jin kaya_kaya sai gata ta ɗakko kujera ta dasa a bakin ƙofarta. Wannan ƴar kyakkyawar budurwarce ta fito daga turakar Kaila hannunta rike da bokiti mai cike da kayan wanki. Kayan Bilkisa ta soma shanyawa, su bireziya da ɗan diras, da wasu rigunan baccin da kallansu suka sani na ji kunya. Yanzu ta yaya mace zata sa irin kayannan ta tsaya a gaban miji? Kayan Kaila naga tana shanyawa, wandunan ciki, da singileti, da shaddajinshi, da dai kaya da dama. Tana gamawa ta koma cikin turakar ta rufo ƙofa. Sai na jiyo wani irin daddaɗan turaren wuta na shigar mun hancina mai daɗin gaske" Habiba Bala ce ta fito tana sharce zufa. A kusa dani ta zauna da ledar magunguna da ruwa. Tana zama yara suka shigo a guje harda Mustapha yaron Sabira. Habiba Bala ta bisu da idanu tana Murmushi.
Kuje ku gaisa da ummanku Sani" Dauda na ƙurama idanu, babu kuzari sam a jikinshi da gani yana cikin raɗaɗin ciwo, gashi bai saba da ƙannen nashi ba sam. Hawaye na soma zubarwa. Habiba Bala ta dubeni tana riƙe da hannun Amina da Balaraba, cikin ƙasa da murya tace.
"Menene kuma Shanono?" Hannun Dauda na riƙo na juyar dashi, na zame mishi wandonshi ƙasa. Salati Habiba Bala ta saka tana kallona.
"Me ya same shi, waye shi Shanono? Shine aka barshi a gida sai ya mutu. Jibi tsutsotsi fa yanda suke fito mishi." Wani irin kukane ya turniƙeni mai tuƙuƙin gaske. Sabira da Hindatu sai kallonmu suke yi, amman basa jin abinda muke cewa, kukana ne ya jawo hankalinsu garemu ma. Habiba Bala ta ce ma yaran su je su yi wasa, sai da ta ga sun fice sannan ta dawo da hankalinta gareni.
Ɗanane Habiba Bala. Dauda shine yarona na farko. Yana hannun matar ubanshi ne a shanono fyaɗe akayi mishi. Rashin kuɗine yasa kika gammu zaune a gida. A gidan uban nashi ma an rasa wacce zata kula mun dashi. Shine na ɗakko abuna, duk da nima a ɗofane nake a nan ɗin."
"Shine ba zaki kira ni ba? Na taimaki waɗanda ban san su ba balle ke Shanono. A gaskiya baki kyauta ba. Zan tafi da Dauda asibitinmu za'ayi mai duk abinda ya dace. Ba dole sai kin yi ta sunturin zuwa Bauchi ba. In Allah ya bashi lafiya sai in dawo miki dashi. Ki share hawayenki. Ni kaina fa Shanono babu irin rayuwar da ban gani ba a baya." Ajjiyar zuchiya na shiga saukewa. Duk wannan maganar da muke yi cikin ƙasa_ƙasa da murya mu ke yi, babu mai jin mu. Magunguna ta dinga ɓallemun tana bani ina korawa da ruwa. Sabira ta dure mun tea mai zafi.
"Gashi ki sha Tani ki warware hanjinki"
Nagode sosai Sabira." Muna cikin haka sai ga Bilkisa ta fito daga ɗaki cikin kwalliyar shuɗiyar atamfa, tayi kyan da ba'a buƙatar kwatanta ma masu bibiyar labarin. Tana ganina ta ɗan yi dariya.
"Umman Sulaiman kin dawo ashe, ai banji dawowarki ba da na fito mun gaisa" Murmushi nayi mata.
Ayya Bilkisa bamu daɗe da shigowa ba. Nagode" Gaggaisawa akayi baki ɗaya. Tayi shigewarta turaka tana lanƙwasa.
"Ita wannan ɗawisuwar daga ina Shanono?"
Amaryar Kaila ce daya auro" Kai kawai ta girgaza bata ce komai ba ta leƙo ɗakina ta dawo.
"Mu je ɗaki ya bushe mu yi magana ni inason in kama hanya" Binta nayi zuwa cikin ɗakin
"Shanono ashe haka kike tabka ƙazanta. Ƙazanta taci uban na da ashe. Yaya ba zaki sha wuyar zaman aure ba? Ɗaki sai ɗoyi yake bugawa, ke kan ki wari kike yi, haka yaran. Ni ina ganin ai Kaila fa kamar yayi ƙoƙari da yake zaune dake a haka, kuma a haka yake ɗirka miki ciki duk shekara sai kin jiye. Dubi katifunku duk yanda suka mace. In fa anason ɗakinnan ya dena wari sai fa an siyar da katifunnan an sai wasu tukunna, suma sai an sa musu irin rigar katifar nan irin wacce bata barin fitsari ya ratsa katifa Jibi jinin kuɗin cizo a ɗakin ki shanono ko kunya ke ba kya ji dan Allah? Ba dole sai Kaila na kulaki ba zaki tsabtace yaranki, da ke kanki, da muhallin ki ba. Wannan ƙazantar fa zata iya taɓa ƙwaƙwalwarki. Kuma ƙazanta zubar da mutunci take yi, kuma raini dole ya shiga tsakaninki da kishiyoyi, maƙota, da ma miji. Kuka na saka mata ni kaina bansan me yasa nake hakan ba. A ganina ba wani abu bane dan na dena jin daɗin komai da kowa. Wa zai fahimci macen da ta auri mazaje biyar, kun tambayeni yaya rayuwata ta kasance ne a sauran gidajen?. Duk da na san ban taso na ga iyayena a cikin gida ba, balle har su koya mun gyaran jiki dana muhalli. A titi na taso na ga kaina, wasu garuruwan muna da ɗakuna mai cike da tulin tsumma, wadu garuruwan a ƙasan gada muke rayuwa. Jina nake bani da maraba da mahaukaciya, bana ɗaukar kaina a matsayin mace. Duk wannan maganganun a cikin zuchiyata nake aiyanasu.
"Shanono ki dena kuka, in na fahimta a cikin deepretion kike wanda ke kan ki baki sani ba, baki san kina ciki ba, baki san tsawon lokacin da kika kwashe a ciki ba. Abunda zan faɗa miki shine. Ki tabbatar kin koma makaranta, arabi da boko. Akwai boko ta matan aure ai a garinnan ko? Shine hanyar da zaki samar ma kan ki nutsuwa shanono"
E akwai zan bincika ni ko zuwa gobe ne, tunda dai zaki tafi da Dauda. Shima islamiyyar zan bincika ko ta su Sabira ne sai in shiga, duk da ma dai tasun da ɗan tsada.
"To shikenan, sana'a itama ya kamata ki soma Shanono, ki ji tausayin kan ki da ƙwaƙwalwarki, da ma yaranki. wani abun rashin ilimine duk yake ja kiyi shi." Kuɗi ta zaro a jakarta masu yawa ta saka mun akan cinyata.
"Ki nemi makaranta duk inda take ki soma zuwa. Kuma kar ki yi sake ki bari yara ko miji su hana ki karatu. Sannan shawarar da zan baki shine, ki fita sha'anin maganar haihuwa haka. Ki yi ƙirgen kwanaki kamar yadda na faɗa miki a baya, duk abinda ya shige miki duhu ki kira wayata. Shanono so nake ki kama kan ki ki nutsa, ki fita harkar kowa a cikin gidannan, ki zauna a gefe, shi kanshi kailan ki ba banza ajiyarshi, tunda yana da wasu matan ki matsa gefe ki zama ƴar kallo. Ga wannan ku yi shawara da Sabira wacce sana'a zaki soma. Ta sake ajjiye mun wasu kuɗin.
"Ni kam zan tafi, ina da aiki da yawa a asibiti, tiyata zan shiga lokacin da Sabira ta kira ni. Tiyatar da ban shiga ba kenan. Sai abokin aikina ne ya shiga ɗakin tiyatar." Godiya marar adadi na dinga rakarkatoma Habiba Bala, har bakin mota muka raka su ni da Sabira. Dauda yana gaban mota. Suna tafiya sai ga Kaila da dillalai masu duba gida sun shigo. Mamakine ya kama shi da ya ganni a gida. Rai ya ɗaure da mu ka haɗa idanu, har wata harara da ƙuta duk yayi mun. Ɗakin shi ya leƙa ina jiyowa yana ce ma Bilkisa karta fito akwai maza masu ganin gida a tsakar gidan. Ni ko haka su kaita wuce ni nono a waje ina ba jaririna. Wato dake ba sona Kaila yake yi ba, babu batun kishina sam.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login