Showing 45001 words to 48000 words out of 68990 words

Chapter 16 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

uwarki Inno da ubanki Nanoma sunci ubansu ne kawai baice ba. Amman ya zage su tas. Hakan bai mishi ba yasa ƙafa ya shureni sai da na shige ɗaki. Sai gani a tsakiyar yarana. Kuka na kuma sakawa, ganin ashe kuka suke yi suma. Hauwa da Balaraba ne kawai basa kuka, amman suma sun yi shiru kamar ruwa ya cinyesu. Ban yi aune ba, Kaila ya shigo da bulala mai baki biyu. Yanda yake dukan Sani da Sulaiman in sun mishi laifi haka ya shiga tabkata. Tsabar zafin duka da gigicewa sai da na kusa tsirara a gaban Isa dake ta faman kokawar ƙwace dorinar a hannun Kaila, amman ya kasa. Amadudu ne ya shigo da gudu da ƙyar suka ɓanɓare kaila a ɗakin.
"Zaki ci ubanki ne ƴar iska ƴar mabarata, ni zaku kashe ma ɗa dan baƙin hali." Allah kawai nake ambato har zuwa lokacin ina jin zugin dukan na ratsa jikina. Yarana duk sun takure a lungon katifa sun cure waje guda sai kuka suke yi. Jaririna dana tumirmushe na ɗauka da sauri. Ashe shiɗewa yayi. Sai da na jijjigashi da ƙarfi sannan ya saki wani irin kuka mai karaɗe kunnuwa. Nima na sake sakin kuka. Ina jiyo Bilkisa tana yima Kaila magana akan rashin dacewar dukana da yayi. Sai faɗa yake yi kamar zai ari baki. Yana ta tsinkani a wajan Bilkisa, yana faɗa mata a kwaroro ya tsinceni ya wankeni ya aureni ina bazawara mai aure huɗu, shi kuma yana saurayi fil. Jaririna na duba, sai ajjiyar zuchiya yake yi, nono yake ja a hankali. Su Sani na duba, haƙiƙa ƙaddarar zuwansu duniya ne ya haɗa aurena da Kaila. Dani dashi bamu da tsimi bamu da dabara. Wannan shine karon farko da Kaila ya sa madoki ya dokeni. Ya kan mareni, ko ya sa hannu ya hankaɗeni in faɗi, amman bai taɓa mun mugun duka irin wannan ba.
Da ƙyar na lallaɓa na rarrashi yaran su kai shiru. Ina zaune ina karanta wasiƙar jaki har wajajen sha biyun dare, na rasa inda zan tsoma raina, fargabar abinda kaje kazo nake yi. Na san zaman gidannan ya ƙaremun, to yarana fa wazai riƙe mun su? Jibi rayuwar Dauda yadda ta samu giɓi sakamakon rashin uwa majingina a tare dashi. Taya zan tafi in bar gidannan, in tsallake yarana ababen alfaharina? Ina cikin wannan taɗin zuchi wayata tayi kuka Yaya Use ke kira da sauri na ɗaga"
"Tani ince dai babu wata matsala data biyo baya ko?"
Babu Yaya Use, kiyi haƙuri da abinda Kaila yayi miki"
"Hmmm Tani kenan, akwai ranar da zan mayar ma da Kaila wannan cin kashin da yayi mun. Halin da kike ciki shi yafi damuna a yanzu, rintsawa wannan na kasa yi. Baban yara sai tambayata yake yi, jikina yayi sanyi. Ki yarda dani Tani wallahi ban daki Hajiyayye a ciki ba, makircine kawai irin namu na mata. In ce dai ƴan uwanta basu zo ɗaukar fansar dukan ƴar uwarsu da akayi ba ko?" Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace.
Basu zo ba, amman a cikin zulumi sosai nake Yaya Use, dan ƴan uwanta sunce ba zasu yarda ba. Kuma Yaya Use makircin Hajiyayye yafi da haka wallahi, tayi mun abubbuwan da bansan iyakarsu ba a rayuwa. Amman babu komai, kema nasan kin yi ne domin ki ƙwatar mun ƴanci ba dan ki jefa ni cikin matsala ba. Amman tsorona tsinuwar da Baffa zai mun in ya ji mutuwar aurena a karo na biyar. Dan ina da yaƙinin Kaila sakina zaiyi, Ɗa ba wasa bane yaya Use " Mun jima muna tattaunawar da ba zata fisshemu ba, face mu ɓata bakunanmu da ƙone katin waya kawai. A taƙaice kwana nayi kusan a zaune, kafin asuba jikina ya kumbura yai suntum, ko idona bana iya buɗewa sosai. Kasancewar jikin nawa ɗanyene kuma gashi na daku iya duka, dama goshina in da Baffa ya raɗa mun sanda a kumbure yake dama. Ko da na tashi yara su yi Sallah, da suka ga fuskata sai tambayata suke yi banda lafiya ne? Ni kuwa shiru nayi musu kawai, Dauda kuma yayi ƙuri abun tausayi. A ranar dai a ɗaki nayi ma Dauda wanka a bawo na shafe mishi takashinshi da man da mai maganin ya bamu. Abun tausayi har wani ajjiyar zuchiya Dauda yake ta saukewa, wari kuwa ya cika ɗakin fam. Ruwan wankan na fita dashi a bawo na zubar. Nan da nan tsakar gidan ta kaure da ɗoyi ina jiyo Amadudu daga ɗaki yana faɗama Hindatu.
"Ina ga bara gurbi ne ya fashe a maƙota kinji wani azabar wari?" Ina jin haka na koma ɗaki da gudu, gudun karma su fito su ganni. Ina cikin yima jaririna wanka na jiyo tsaiwar mota a dai_dai windo na, ni dai na jiyo muryar mace tana cewa.
"Ga gidannan, mun yi waya da mai gidan yana ciki" Sai muka jiyo sallama a zaure da wata ƙatuwar murya. Ba'a jima ba na jiyo takun tafiyar Kaila. Ni ko gudawa harya taru mun. Yara su kai tsuru_tsuru duk a cikin tsoro muke. Kaila ne ya bankaɗe labulen ɗakina. Ba shiri ya toshe hancinshi harda runtse idanunshi. Tabbas na san warin da Dauda yake yi ya kai ayi fin hakan ma. Nima dake uwace shi yasa ko a jikina.
"Ke kam ba dai ƙazanta ba. Ji warin da ɗakinnan yake yi. Ashe dama warin da Ɗanyan gwal tace mun ta jiyo a tsakar gida daga nan yake fitowa? Ko da yake ba abinda ya kawo ni ba kenan. Ƴan sanda na jiranki a waje sai ki goyo ɗanki ku je, nima zan biyo bayanku" Miƙewa tsaye nayi a zabure ina kuka nace.
Kaila kayi mun rai dan Allah. Wallahi Allah Yaya Use bata naushi Hajiyayye a ciki ba. Kaga jego nake yi banda lafiya, ka tausaya mun dan Allah kar ka bari su tozarta ni"
"Kinga dakata Shanono. Dangin Hajiyayye suna da hakkin yin shari'a daku akan ƴar uwarsu. Dan baki san girman laifin naku bane shi yasa ma har kike wannan magiyar ai. Wuce dallah" Kaila ya hankaɗoni waje, sai gani a zaure kusa da wata ƴar doka mace. Goyona ya miƙo mun na ɗamare shi, jikina fa bai daina kakkarwa ba. Yara suka fito suna kuka. Sai a lokacin kaila ya kula da Dauda.
"Shi kuma wannan yaron fa Shanono daga wacce duniyar yake?" Ruɗun sai ya ƙaru mun, in yi magana na kasa. Ƴar doka ce ta katse mana uzuri, wanda ni hakan yayi mun daɗi.
"Wannan kuma maganarku ce ta cikin gida. In ta dawo kwa tattauna, muje baiwar Allah " A gaba ƴar dokar nan ta tusani, ina jiyo kukan Hauwa a kunnuwana, dukkansu yaran kuka suke suna ambaton.
"Umma Umma" Babbar yar su Hajiyayye na gani a ƙofar gidan, da ƙaninsu Namiji. Haka aka sani a motar ƴan sanda kamar ɓarauniya. Kai tsaye hanyar gidan su Yaya Use muka nufa. Lamarin daya sake tunzura tashin hankalina. Damuwata ta ƙaru ainun. Ai kuwa sai gamu a ƙofar gidan su Yaya Use. Basu jima da shiga gidan ba, sai gasu da ita an taso ƙeyarta. Ganin Fatima yasa nace.
"Fatima ki je gida ki kula mun da su Sani, ki faɗama Sabira halin da muke ciki. Dauda ma yananan, Saudat ta kula da su Inno ƙarama" Yaya Use sai kuka take yi. Ni ko idanuna a bushe, haka mu kai ta tafiya tiryan tiryan har caji office. Bamu taɓa shiga caji office ba sai yau. Haka aka zube mu bayan kanta. Suka ci gaba da aikinsu. Mu dai muna zaune jigum.
"Tani me ya same ki, naga jikin ki yayi ja ja ja halamun shatin bulala kaddai Kaila ne ya dokeki da ɗanyan jego a jikinki? Kinga yanda halittarki ta canja kuwa Tani. Ga wajan da Baffa ya kwaɗa miki sanda ma ya sake aunewa" Kafin in bata amsa Babbar yar su Hajiyayye ta shigo ita da ƙaninsu, Kaila na biye dasu. Ya ɗau wanka sai ƙamshi yake yi, ba ka ce kaila mijina bane. Shi yasa ma bai son a dangantasho dani, na sani yafi karfina nesa ba kusa ba."
Zuwansu ne yasa har aka kulamu. Nan yar Hajiyayye ta shiga ba da labari ma ƴan doka. Yaya Use tace.
"A'a Ta bizaro kar ki bada wannan shaidar. Wallahi ban naushi Hajiyayye a ciki ba. Tsautsayine da ƙaddara su ka kashe abinda ke cikinta" Buɗar bakin Kaila yace.
"Zaki ga tsautsayi ganin idanki. Tsautsayi da ƙaddara su zasu kai ki gidan kaso kema" Yaya Use tai ma Kaila kallon banza tace.
"In aka sani a gidan kaso a baka ɗan mabuɗin ka jefa a bahar maliya. Kaga in ba zamu tsaya a gaban Ubangiji ba... Wata ƴar sanda ce ta daki teburi tace.
"Kuyi mana shiru anan. Ke kina bayan kanta amman bakin ki bai mutu ba ko? Zaki yi bayani ai. Ku taso ko wacce ta rubuta statement, kuma ku sani duk abinda kuka rubuta zai iya zama hujjarku a gaban kotu. " Cikina ne ya juya da naji ta ambaci kotu. Yaya Use tace.
"Mu bamu iya rubutu ba" Ƴar sandar nan tace.
"Zan dinga rubuta muku kuna faɗa mun. Sannan in kuna da lauya ku neme shi, dan ba ma zamu ba da belin ku ba, dan maganar kisa akeyi. Ita kanta me jegon bama tasan in da kanta yake ba har yanzu. Dan haka ku nemi lauya dan tattare bayananku zamu yi mu miƙa ku kotu." Muryata na rawa na dinga karanto iya abinda na sani. Ƴar sandar nan nata rubutu. Haka na gama Yaya Use tayi nata. Ana cikin haka sai ga Sabira da Baban Mustapha sun shigo. Sabira ƙawa ta gari tana ganina ta fashe da kuka. Baban Mustapha kuma yayi iyakar ƙoƙarinshi a bashi ko da belinane wallahi su ka ƙi. Sha'anin hukumomin ƙasarnan sai adda'a.
"Tani ki bani jaririn in tafi dashi, kema ki samu kiji da kanki. Zan dinga bashi madarar yara. Su Sani ma suna gidana, harda yaronki Dauda"
"Dauda yaronta? Kut lallai Shanono kin ci ƙarya kin kwana da yunwa, nine ɗan iskan da kike tunanin zan riƙe miki agolan ɗanki, bacin ubanshi yana da rai? Ai ko bashi da rai wallahi bazan riƙe agola ba, kina fitowa daga gidan yari ki tattare ki mayar da yaro gidan ubanshi. In kuma kina son ku koma gidan uban nashi tare ne ai shikenan Shanono" Cewar Kaila, Yana dasa aya ya fice. Baban Mustapha ne ya bishi da sauri. Ni kuma na sunto goyona na ba Sabira.
Sabira wayata tana ɗaki, ki duba zaki ga number Habiba Bala a ciki. Ki kirata ki mata bayanin halin da nake ciki dan Allah, nayi imani zata zo yau ɗinnan."
"Shikenan Tani, zan kirata. Kuma in Allah ya yarda ba zaku kwana a tsare ba" Keyarmu aka tasa cikin cell. Zama nayi a ƙasa ina murmushi kawai. Yaya Use tace.
"Sai da na faɗa miki kar ki ɗakko Dauda Tani. Kinga yanzu abinda ya faru ko. Yanzu yaya yaronnan za'ayi dashi? In kika ce gidansu Inno zaki mayar dashi bara zai dinga zuwa kema kin sani. Mu ma kuma kinga halin da muke ciki. Amman wacece ita Habiba Balan da kika ce a kirata?" A taƙaice na faɗa mata wacece Habiba Bala.
"To Allah ya rufa asiri. Baban yara yana ciki fa. Amman Sabida ɓacin rai ko kallona yaƙi yi. Shi yasa ma baki ganshi ya fito ba. Kuma nasan ko ɗaureni za'ayi igiya tayi saura bazai zo ba...........✍🏻


(MASU CEWA IN SASSAUTAMA SHANONO MASIFAR TAYI MATA YAWA. TO KU SANI KO WANNE BAWA DA IRIN ƘADDARARSA. KUMA WASU MATAN SUNA FUSKANTAR MATSIN RAYUWA NINKIN NA SHANONO. WANNAN LABARIN BA ƘIRƘIRARSHI NAYI BA. LABARINE DAYA FARU A GASKE. BABU ABINDA NAKE DAƊAWA SAIMA RAGEWA DOMIN MAKARANTA SU FAHIMTA. SHANONO TANA GAISHEKU, TACE KUYI MATA UZIRIN ƘAZANTAR DA KUKE JIFANTA DASHI. KUMA KU BIBIYI LABARIN DA SANNU ZA'A WARWARE MUKU KOMAI. NAGODE)




*OUM SOOFEEYYER GRAPHIC AND DATA*

*INA Marubuta da masu business*


*Maza ku hanzarta mun shirya tsaf domin kayatar da ku da graphics kalakala Kuma cikin farashi me sauki*

Logo
2d Logo
Flyer
Invitation card
Invitation vedio
Save the date card
Save the date vedio
Book cover
Account sticker
Makeup Flyer
Business Flyer
Da dai sauransu

Sannan Kuma Ina koyarwa ga duk me bukata cikin sauki
08069638776

*All netwk Data is available*
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 12



_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_

_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_

*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*


*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S

*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224

*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*

*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*

*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*

*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*

*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*

sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*

KAMARSU👇🏻👇🏻

*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*

DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻




"IYALI kake magana, wannan ƴar marasa tarbiyyar itace iyalin? A zafafe take magana cikin rufewar idanu. Bilkisa wacce tunda suke abinsu bata ce komai ba, sai yanzu da taji ana neman taɓa mutuncin iyayenta shine tace
"Kul kalmar aibanta iyayena ya sake fitowa daga bakin ki. Dan ko wanda ya haɗamu ni da ke bai isa ya aibanta iyayena ba. Dan sun yi mishi riga da wanda bashi ni da su kayi. Ko ba haka ba Gwanda?" Ta ƙarke maganar cikin rausaya murya. Dariyar mugunta Kaila yayi, yana ganin anzo gaɓar da zai sa Hajiyayye ta fita da ƙafafuwanta."
"Ƙwarai kuwa kuwa ɗanyan gwal, Dady ai yayi mun sutura daya bani cikakkiyar buduwa ba ɓari ba. Ba irin matan da samarin sawo ke luguiguitawa ba. Ga mamannan a cikkike gwanin banƙawa. Ni mai zance da Dady sai adda'a ai"
"Allah ya isa tsakanina da kai Kaila macuci ka....." Bata ƙarashe zancan ba taga Kaila ya jefa Bilkisa gado yana neman danneta, da mugun gudu ta fita har tana tuntuɓe, tana tsoron ganin tsaraicin Bilkisa. Zuchiyarta sai fat_fat take yi. Kai ta gyaɗa tana jinjinama ƙarfin zuchiyar Tani ita data gansu tsirara ma, kuma ranar kwananta, amman washe gari kamar ma ba'ai komai ba" Nadamar ba ma Kaila jikinta ya shigeta, yau ga Kaila da su ka watse tare shi yake mata shaguɓe kuma abun takaicin shine a gaban kishiya. Ta lura sai ta sassauta kishinta zata kai ga cimma manufarta akan Bilkisa. Amman in ta ga Bilkisan ne sai taji zuchiyarta na ingizata. Sai dai muce da Hajiyayye kash ta bar kari tun ran tubani daga ranar da ta fisge waya a hannun Kaila su kai zage_zage da Bilkisa, daga ranar raini ya shiga tsakaninsu babu sauran ragowar mutunci ( uwayen gida ƙalubale a gareku) Haka dai daren ya kasancema Hajiyayye ko rintsawa ta kasa yi, tana kwance tana ƙirgen silin ɗin ɗakinta. Yayin da Kaila yake jikin matarshi suna aikin samun lada. Haka ta ɓangaren Tani ba ta iya bacci ba a wannan dare.


ALLAH YAYI DARE GARI YA WAYE:


SHANONO:
Tun duku_duku nayi wanka fes. Inno ta kama Dauda ta wankeshi tsab, farin ruwan ciwo sai fitowa yake daga shakirarshi, shi ke haddasa mishi wari mai shiga har maƙogoro. Zuwa karfe taran safe har mun fito, Yaya Use ce za tai mun rakiya zuwa Jos ɗin. Su Inno kuma sai wa'adin da suka yanke ma kansu ya cika zasu dawo gida. Sallama mu kai ma kowa a gidan muka fita. Mashin ne ya kaimu har zuwa bakin titi. Baffa Janaidu bai barmu ba har saida motarmu ta cika dam misalin sha ɗayan rana Sannan ya tafi. Tunda na zauna a motar nan gabana ke faɗuwa domin bansan me zan je gidan in tarar ba ma, bansan ta inda zan yi ma Kaila bayani ya fahimce ni ba. Dauda yana zaune a cinyata, jaririna yana bayan Yaya Use. Sai mutsu_mutsu Dauda yake yi, baya iya zama waje guda, sabida tsutsotsin dake fitowa a shakirarshi suna ci mishi jiki, musamman dana sanya mishi ƙunzugu. Hankalina take ya kuma tashi sai kuka.
"Wai meye hakan Tani? Kin tusa yaro a gaba sai aukin kuka kike yi. Kiyi haƙuri kiyi ta mishi adda'a Allah zai bashi lafiya da yardar sa, harma ya zama tarihi. Kaila kuma kafin in koma gida zan same shi mu yi magana, dan zan ɗan miki kwana biyu kafin in koma gida. Baban yara ma bai san ina hanyar dawowa ba." Allah sarki ɗan uwa rabin jiki, ɗan uwa abun wuya. Muna tafe Yaya Use tana ta bani kalma, sai tausata take yi. Sai na ɗan ji dama_dama a raina kaɗan. Fargabata yanzu biyu ce. Na farko Kaila ne, na biyu ciwon Dauda ne. Matsalolina na jingenesu a gefe ba ta su nake yi ba. Domin na yanke ma kaina wani hukunci da nake ganin shi zai fiye mun alkhairi, kuma hakan zai taimaka ƙila Kaila ya amince yaci gaba da zama dani. Motarmu sai gudu take yi. Maza da mata sai hira suke yi. Kowa na kalla sai in ganshi yana dariya, ko in ganshi cikin walwala. Allah sarki walwala ko sai yaushe zata sake kawo min ziyara cikin rayuwata oho. Ƙila ni da walwala munyi hannun riga har abada. Amman ina fatan ƴaƴana su dawo mun da walwala cikin rayuwata. Allah ka bani damar da zan dama har in tsaya akan karatun yarana su zama wani abun. Allah ka dubeni yaran sune kaɗai sanyin idaniyata. Da yamma sakaliya muka iso tashar farar gada, daga nan muka hau abun hawa zuwa gida, ni dai gabana sai faɗuwa yake yi kawai, hankalina duk a tashe yake. Da sallama a bakunanmu muka shiga cikin gidan.
"Shiga ciki ke Tani, Bani keyn ɗakin naki mu mu shiga, bai dace ki shiga da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login