Showing 12001 words to 15000 words out of 68990 words
Chapter 5 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
kenan. Wajan Hindatu naje na aro dutsen guga. A daren na goge kayan da Inno ta bani dukka ƙaramar jakar tafiyata na ɗakko nasa leshi kala ɗaya da mayafi a ciki, nasa ma hauwa kaya kala biyu da famfams guda uku dana tsaya na siya a bakin layinmu, ɗayan kuma na ajjiyeshi gobe in zamu tafi zan sa mata. Na daɗe a kwance ina tunanin yanzu shikenan rayuwata ta mutu a haka zanta rayuwa kenan ni. Nice har karfe ɗayan dare ban runtsaba. Dana ga dai baccin ya ƙauracema idanuna saina miƙe na fito dan ɗaura alwala. Abun mamaki na jiyo tashin muryoyin Kaila da Hajiyayye, yana ambaton.
"Ki bani wayata, wallahi kika sake fasamun waya a bakacin aurenki. Wawuya mahaukaciya kinga Shanono tana irin wannan haukar ne? Ko da aka auroki kin taɓa ganin ranar da ku kai cacar baki ne. Amman kin kira yarinya a waya kunyi zage_zage sabida ki nuna mata kin rainani ina cikin wayata kin fisge." Baki na taɓe na tuno wata rana da daddare da muna mu'amular Aure ni da Kaila Hajiyayye tayo kiran wayarshi lokacin suna ganiyar soyayyarsu. Haka Kaila jiki na rawa ya zare jikinshi a nawa ya shiga amsa wayar Hajiyayye kwanciyar da ba'a gamata ba kenan. Har batsa yake yi da'ita a waya a gabana. Ina gani suna waya gabanshi zai miƙe ƙyam sabida musayar maganganun batsa da suke yi da junansu. Hmm ashe wanzami bai son jarfa. Alwala nayi na shige ɗaki abina, na dinga gurgura Sallah, dan ɗan karatun sallan ba wasu masu yawa na iyaba, ko izifi biyu ban cika ba, ɗan abinda na haddace dasu nake gudanar da ibadar tawa. Washe gari sassafe nayi wanka naima ƴata wanka. Masa na siyo a gidan maƙota ta ɗari biyu muka ci ni da Hauwa. Nasa mata pampas da kaya. Wannan atampar ta jiya da inno ta bani na saka ɗinkin riga da zani ne. Nayi ɗaurin ɗankwali na maryam babangida. Na ɗauki baƙin mayafin jiya na yafa a kaina, na ciro baƙar ɗaya_ɗayar jakata na ɗan zuba kuɗaɗena a ciki da ƴan tarkace, wayata, chaja, da dai sauransu. Banyi kwalliyar komai ba ko turare ni bani dashi, bama ni da kuɗin saye. Kayan kwalliyar ma bani dasu kwalli kaɗai nake murzawa, in banda jar hoda ta zazzzage Zainab da rannan Yaya Use tazo ta mance da'ita shine na samu na ɗan barbaɗawa, haka nake yin wani janƙau in na shafata. Fitowa nayi na rufe ɗakina Hauwa tana baya. Jakata a ajjiye a zauren na shiga cikin gidan Kaila yana tsakar gidan yana zaune akan kujerar tsugunno yana waya sai wani ƙanƙance idanu yake yi, wandonshi na kalla ya cika fam. Hmm maza mutanen mu. Banza nayi dashi na wuce Hindatu nayi ma sallama zani Bauchi. Na dawo nayi sallama a ƙofar ɗakin Hajiyayye tana fitowa naga sai bin ƙasan zanina da kallo take yi cike da mamaki tace.
"Yaushe kika ɗinka kayannan umman Sulaiman, sunyi miki kyau?"
Da sallarnan na ɗinka. Nagode" Na bata amsa kafin na ɗaura da cewa
Ni zanje Bauchi sallama nazo yi miki." Nan da nan naga ta murtuke fuska ta shiga jijjiga kai ni dai wuce ta nayi a tsaye a wajan. Nazo zan wuce Kaila ya ɗaga mun hannu dan gudun kar in yi magana budurwar tashi taji in kwabsa mishi. Haka ya dinga mun lokacin Hajiyayye gashi lokaci yayi ana rama ma kura aniyarta. Fita nayi abuna zuwa Bauchi road a gefen hanya na samu motoci masu zuwa Bauchi nera dubu. Shiga nayi baya mu uku ne a ciki dukka mata mutum ɗaya ake jira na gaban mota sai mu kama hanya. Gaggaisawa nayi da matan motar. Wayata ta shiga ruri ina ɗagawa naga Habiba Bala ce ke kirana. Karawa nayi a kunne.
Habiba Bala kin ganni na shiga motar Bauchi kenan amman motar mu bata tashi ba tukunna." Daga cikin wayar Habiba Bala tace.
"To Shanono Allah ya kawo ku lafiya karfa ki mance a zaranda hotel zasu ajjiyeki in kika sauka a bakin hotel ɗin sai ki kira ni zan zo in shigo dake ƙarfe tara muka sa lokacin taron gamu kusan dukka mun hallara ku biyu ne baku ƙarasoba Halima Bawa daga Gombe take tawowa amman tun asubar fari ta tawo duk yanda ake ciki nasan ta kusan shigowa Bauchi. To Allah ya tsare." Sallama mu ka yi akan saina kirata. Ko da na sauke wayar saina shiga mamakin yadda Habiba Bala take magana a mugun yangance. Ni dai da sanin dana mata ƴar karaɗice da son aba hammata iska. Dan ko rigima muka kwaso ita ke shigewa gaba ta tare mana. Gata da kuri kuma ƙatuwace a lokacin mai ƙiba sosai, ɗalibai na jin tsoronta. Ɗan guntun murmushi nayi dana tuno rayuwa. Ban jima da zama ba motarmu ta cika muka biya kuɗi muka kama hanyar Bauchi. Tafiyar awa ɗaya da rabi ne cib ya kaini Bauchi. A dai_dai zaranda hotel na sauka. Ina sauka na ga Halima Bawa tsaye da goyo a bayanta. Duk da ta zama babbar mace amman kamanninta yana nan yanda na santa.
Halima Bawa kaddai sai yanzu kema kika samu isowa?" Na yi magana ina nufota. Da sauri ta juyo sai kawai ta ganni. Baki ta washe tana tafa hannuwa.
"La'ilaha illallah mahammadun rasulillah sallallahu alaihi Wasallama Shanono ashe da rabon zamu gana? Kai Allah yaima Habiba Bala albarka ta da yi ƙoƙarin sake haɗemu waje guda a karo na biyu." Ɗan rungumar juna muka yi ta kafaɗa muna cike da farin cikin ganin juna, ƙamshi jikin Halima Bawa yake yi sosai, gata shar_shar da'ita cikin kwalliya da ado.
"Ga ciki ga goyo kuma Shanono? Dama har yanzu ana haihuwar konika a wannan tsadar rayuwar da muke ciki. Kai Shanono har yanzu kina nan da ƙauyancinki wai?" Kafin in bata amsa muka hango wata mota ta tsaya a gabanmu. Baki dukkanmu muka sake muna kallon Habiba Bala. Ni dai da idanuwanta kawai na ganeta dan wallahi na ɗauka wata balarabiyace ta sauka daga masar. Ni sanin da nayi mata mai ƙiba ce sosai, kuma bata kai haka haske ba. Sai kuma yanzu na ganta ƴar madaidaiciya da'ita, ga mota tana ja.
"Habiba Bala kece kika zama Hajiya haka?" Cewar halima Bawa. Dariya tayi mana haƙoran matanta biyu sama da ƙasa suka bayyana tace.
"To ya sanki? Shegiya Halima Bawa kina nan yadda kike babu abinda ya sauya. Ke kuma Shanono dan ubanki meya kawo wannan ƙanjamewar haka?" Dariya dukka mu ka yi. Motar muka shiga Habiba Bala ta canja akalar motar zuwa get ɗin shiga hotel din. Halima Bawa tace.
"Ba dole shanono ta rame ba. Kinga fa ga ciki tulele a gaba, ga ɗanyen goyo kuma fa. Nima ina ganinta na dirar mata" Ni farin ciki ya hanani magana ma sai dariya kawai nake yi. A wajan ajjiye motoci muka tsaya dukkanmu muka fito. Habiba Bala ta karɓi jakunkunan mu tace.
"Bari in taimaka muku da jakar. Tana tafe muna biye da'ita zuwa sama. A sama ta huɗu muka tsaya a bakin wani ɗaki. Tura ƙofar tayi tana gaba muna biye da'ita a baya. Tangamemen falone babba sosai muka shiga. Ƴan set ɗinmu na soma cin karo dasu. Wasu sun canja irin Habiba Bala, wasu kuma sun lalace ire_irena. Amman kowacce ta zama babbar mace sosai da sosai. Waje na samu na zube a ƙasan kafet ɗin daya malale katon falon. Nan aka shiga gaggaisawa, duk da na ga baƙin fuska har wajan rai biyar.
"Kinga waɗannan daga siniya suka shigo. Lokacin kin gudu gidan aure daga zuwa hutun gama jiniya. Fatima wannan itace Shanono"
Allah sarki sannunku sannunmu. Barkanmu da zuwa dukkanmu ita Habiba Bala Allah ya saka mata a alkhairi a bisa wannan zumunci data kuma haɗawa. Hakan yasa na tuno rayuwarmu a baya lokacin duniyar tana kwance." Nan fa hirar makaranta ta ɓalle. Hauwa na zaro a bayana na miƙa ma Habiba Bala ita. Fatima B Bello kuma ta fita samo mana abinci. Jallof din taliya da kifi sadin muka ci da lemon kwalba. Bayan mun ɗan nutsa kuma sai Habiba ta miƙe tsaye har zuwa lokacin Hauwa tana hannunta.
"Assalamu alaikum ƴan uwana abokan karatuna ina mana sallama irin ta addinin musulunci. Ba komai bane yasa na dage na yi ƙoƙarin ganin na haɗa mu waje ɗaya sai san zumunci da tallafin juna. Duba da yanzu yanda Aure ya taɓarɓare a ƙasashen Hausa. Sai dai muce innalillahiwainnailaihilrajiun kawai. Naso ace na samu damar tattaro kanmu duka. Amman ƴan ajinmu na A ma kaɗan na samu na iya tarkatowa. Kafin in ɗaura jawabina inaso wata ta taso ta buɗe mana wannan taro mai albarka da adda'a" Wani jin daɗi ne mara musaltuwa naji yana lulluɓeni sai nake ganin kamar zan samu sassauci matsalolina ko da da iya shawari ne, kuma ƙila in samu waɗanda zasu fahimtar dani inda maganin matsalata take. Halima Bawa Amirar mu a makaranta ita ta tashi ta buɗe mana taron da adda'a. Kafin kuma Habiba Bala ta ɗaura.
"To kamar dai yadda na faɗa dalilin assasa taronnan badan komai bane sai dan mu dinga zumunci da ƙarfafar junanmu, da ba juna shawarwari masu kyau. Sannan inason mu ware wani asusu na taimakon kai da kai. Ta hanyar ajjiye wasu ƴan kuɗaɗen da zamu taimaki junanmu dashi. Gwargwadon abunda kake dashi shi zaka zuba tunda ba adashe bane, in ma baka da halin zubawa mun ɗauke maka, hakan bazai sa mu kasa taimakonka a lokacin da buƙatar hakan ta taso ba. Ba komai bane yasa nayi wannan tunanin ba face ɗan matsalolin dana ɗan shiga a baya wanda wani sirrina ne, amman alhamdulillah komai yanzu ya dai_daita wannan halin ne yasa na tuno daku. Nasam yanzu mata kaso casa'in na gidan aure haƙuri suke yi kawai. A wannan zamanin ba ko wanne namiji ne yake iya sauke dukkan hakkokin da suka rataya a wuyanshi ba. Kaso hamsin daga cikin mazan talauci ne yai musu katutu, ko yawan yara da tarin mata daya zube a gida yasan bashi da halin kula dasu. Kaso hamsin ɗin kuma mugunta ce da som ganin sun tauye matayen aurensu yake sawa su kasa sauke hakkokinsu. Bance duka aka zama ɗaya ba kar maza su samu jakar tsaba. Mu kuma matan bama yi ma kanmu adalci. Mun shigo zamanin da bayan zaman auren dole kina da buƙatat sana'ar da zaki dinga juya taro ya koma sisi. Ko kuma kiyi karatu ki yi aiki. Ta hakane zamu tsira da mutuncinmu a gidajen aure a dena ganinmu a tagaiyare a haɗu a rufa ma kai asiri. In ya kawo ayi, in ma bai kawo ba ke zaki ɗauka da kanki kiyi. Amman fa in ma Allah ya haɗamu da mazaje masu tsoron Allah, nagartattun mazan da suka san darajar mace kuma basa son suga mace tayi kuka ko ta shiga damuwa ba. To zama haka fa bai ganmu ba. In kina da ƴan canjinki wani wulaƙancin ma namiji bazai iya tunkaro inda kike dashi ba. Amman mazan yanzu in ba kya aiki ba kya kasuwanci ganinki suke a matsayin nauyi a kansu. In talaucinshi ya bugoshi ya dawo gida ya sauke miki buhun rashin mutunci. Ni kiran da zanyi mana shine ilimi yana da matuƙar mahimmanci ilimin addini dana zamani, ko zamu haɗa da sana'a mata ya kamata mu yi ilimi ko da mijinki bazai barki kiyi aiki ba, ke a_kan_ karan _kankin_ kanki zaki zauna lafiya jahilci ai babban ciwo ne. Ni nayi karatu na karanta fannin ilimin limitanci ni likitan mata ce ina aiki a babban asibitin Bauchi. Bari in ga waɗanda da suka ci gaba da karatu bayan gama sakandare" Cikin zolaya tayi maganar tata. Naji daɗin maganganunta sosai wallahi, na yarda rashin ilimi bai yi ba a rayuwa, ni dai na addinin ma iyakata makarantar allo da nayi a shanono ina dai dana Sallah. Boko a ƙaramar sakandare na tsaya, kuma na taso da hazaƙa da son ganin nayi karatu mai zurfi. Amman Baffa ya dakatar mun da karatuna yai mun aure. Ƙalilan ne daga cikinmu suka gama jami'a suke aiki. Sune suka fita daban ko a cikinmu. Halima Bawa atampar dake jikina tafi tata kyau a ido. Amman dake ƴar makaranta ce tana da wayewa sai ta fini haskawa, ni ko kashe ma kayan kyau ma nayi. Mu sauran irin su Fatima B Bello iyayene mazauna gida. Habiba Bala tace.
"To ku da ba ku ci gaba da karatun ba bakwa sha'awar karatunne ko sana'a dai kuke yi?" Nice nayi Magana nace.
Ni dai bana siyar da komai Habiba Bala. Ina zaune a gida kusan duk shekara sai na haihu. Yarana bakwai ga na takwas a cikina. Amman yanzu naji ina sha'awar karatun addini dama kasuwancin ko da sai da daddawa da kanwa a cikin gida ne" Ai kamar na buɗe ƙofa ne, wannan tace itama sana'ar take son tayi, sai masu son komawa islamiyya nan dai muhawara ta ɓalle."
"To duk abinda kuke son yi zaku yi da izinin Allah, kusa a ranku zaku yi. Zamu dinga tara kuɗi duk wata, sai a dinga raba ma mutum biyu. Duk abinda Allah ya hore muku ku kawo a soma tarawa. Sannan zan ajjiye muku account number ɗina ta cikin group in wata yayi ko ɗari biyu ne da ke turo. In baku dashi an yafe miki. Masu son makaranta kuma zamu yi magana in sha Allah. In akwai me abun cewa tace sai mu rufe taron da adda'a" Da ƙyar na yunƙura na tashi tsaye sunai mun tsiyar duk shekara da nace saina haihu, wasu daga ciki sai jinjina mun suke yi.
Hakika na ji daɗin wannan taron, kuma zuchiyata tayi mun fari tamkar audiga. Kuma taron ya haskamun wata hanya wacce ta zamto hanyar cikar burina. Allah ya sani ina da son karatu ku abokan karatuna kun sani. Wannan buri nawa bai cika ba a baya nazo mahaifina ya turani gidan aure domin neman aljannata da ɗanyen shekaruna sharab. Amman in sha Allah zan shiga makaranta in yi yaƙi da jahilci ƴar sakandare ɗinnan in kammaleta sai in ci gaba da zuwa ta muhammadiyya kuma. Sana'ar ma in sha Allah zan soma kamar sai da daddawa ko kanwa da kuka. Madallah da abokan karatu irinku. Kamar yadda muka haɗu a ɗakin hotel ɗinnan Allah ya haɗamu a Aljanna haka" Ɗan tafa mun su ka yi. Nan aka tsai da matsaya mai kyau mu da bama karatu muke son ci gaba Habiba Bala ta bimu da dubu biyar biyar bayan kowa ya bada kuɗin shi na wannan watan kenan. Ɗari biyar na zaro na danƙa mata. Kafin ta bimu da wannan kuɗin tace mu samu islamiyya mu soma zuwa tukunna, ni da nake son in karashe sakandare kuma tace zamu yi magana. Ledoji viva ta bi kowa dashi ciccike kai Habiba Bala tayi ƙoƙari. Mun kai bayan azahar kafin muka gama, mun rufe taron da adda'a sai da mu kai sallar azahar, muka ɓalle da hirar yaushe gamu, kuma aka shiga haramar komawa. Musamman ƴan nesa da mazauna ƙauyen Bauchi. Da dukkan alamu babu mai kwana dan ƴan cikin. Garin ma kowacce ta yafa mayafinta a ka.
"Wai kuna nufin har kowa zai tafi kenan. Halima Bawa, Shanono kuma tafiya zaku yi yau. Mai makon ku bari sai gobe sai ku tafi, sai mu je gidana mu kwana ai, akwai waje fa. Ni kam har ga Allah dama banyi niyar komawa yau ba sam, ni da so samu ne in kwana biyu ma zuchiyata ta huta tukunna kafin in koma.
Ni da da niyyar kwana biyu ma nazo kinga jakata fa. Halima Bawa muje mu kwana a gidan Habiba Bala mana" Itama Halima Bawa bata ja ba da dukkan Alamu da shirin kwanan tazo, kuma itama tamkar cikin damuwa take. Dukkanmu muka ɗunguma zuwa waje. A wajan ajjiye motocin muka tsaya jiran Habiba Bala. Aisha Aliyu itama mota take ja ashe, ita da Karinatu Jibril sai Habiba Bala. Mutane duk suka ɗuɗɗura a mota muka fice a tare bayan mun yi sallama da juna. Zukata sun yi sanyi, kowa yaji daɗin ganin kowa. Sai da muka shisshiga gidajen su Fatima a tsattsaye dai haka bayan mun gama saukesu mu kai sallama Habiba Bala ta nufi hanyar gidanta dake bayan tsohuwar Airport.
Ni dai muna tafe na lula cikin tunani mai zurfin gaske. Hoton tsaraicin Hajiyayye yana yawan dawo mun, dana tuno sai gabana ya faɗi naji tsigar jikina ya tashi. Haka ina hango wandon Kaila yanda ya cika dan kawai yana waya da budurwa. Magidanci mai yara takwas, shine da irin wannan aiki, mazanmu na hausawa sun ɗaura zuchiyoyinsu a son tara mata da kula mata, da zantuttukan batsa marasa daɗin ji. Ka rasa ina matsalar take laifin mazan ne, ko laifin ƴan matan ne, ko kuwa laifin matan cikin gidane, a'a ko kuwa laifi na iyayene?"
"Shanono....." Wannan tunani haka lafiya meke damunki ne haka?" Cewar Habiba Bala kenan. Har motar ta tsaya ashe ni ban sani ba ina can duniyar tunani.
"Ki yi iya ƙoƙarinki wajan ganin ɗa namiji bai sa zuchiyarki tayi bindiga ba, yaranki ne zasu yi maraici shi kuwa bashi da asara." Idanu na zuba mata ƙur ban da zarafin iya furta komai. Fitowa nayi ina ƙarema haɗaɗɗen gidan kallo. Muna baya tana jagorantarmu har zuwa cikin matsakaicin falo mai kyau mara shirgi da hayaniya. Setin kujerune dak blue a falon irin ƴan ƙanana na zamani. Sai tv na bango dake ajjiye akan t v sitan, sai kafet na tsakar ɗaki wanda ya dace da kujerun, haka ma labulen falon ya dace da kujerun. Sai wani guntun firji a gefe da disfensa ta shan ruwan sanyi ko tea iyakar abunda ke cikin falon kenan ya fito yayi ƙwasƙwas sai sheƙi tayil ɗin falon yake yi. Zama nayi a kujera ina kallon Habiba Bala da maɗaukakin farin ciki yalwacce akan fuskata .......✍🏻
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE....