Showing 36001 words to 39000 words out of 68990 words
Chapter 13 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
Duk da dai mu marasa ƙarfine, amman ya kamata ace ko yayane mun ƙwato ma yaron hakkinshi." Kai Shehu ya jinjina yace.
"Me sunan wanda yayi mishi hakan wai? Mu bamu san komai ba, kullum kuma zaki ga Dauda yana baccinshi a tsakar gida, ko a ɗakin iya." Cikin jin haushi nace.
Alh Zangina ne wai yake yi mishi, haka yace" Ido Shehu ya zare yace.
"Alh Zangina fa? Wallahi zai aikata dan yana shiga da yara gidan gonarshi cike da mota. Kuma ko ɓatan ɗan liman an yi zargin dasa hannunshi. An tasarma maganar, ana cewa hukuma zata yi aiki. Wallahi Alh Zangina yabi dare yaje ya samu malam Liman ya cika shi da barazana. Maganar bata sake tashi ba. a wata ruwayar ma cewa akayi yace in yayi magana sai ya ɓatar dashi. Ku rufama kan ku asiri damu kanmu maganar nan ta mutu kawai. Karma ku sake kama sunan Alh Zangina wallahi, in dai kuna son kan ku da arziki" Mun tsorata sosai da jin wannan labarin. Haƙiƙa nasan mai ƙarfi ma sai ya shirya zai iya tunkarar Alh Zangina da irin wannan maganar. Dan shahararren mai kuɗine sosai, yana da gonakai da wani irin wawakeken gidan gona. Abun dubawan Alh Zangina babu wanda yasan mutumin inane daga kuma wanne nahiya yake. Kuka na fashe dashi nace.
Na barshi da faɗuwar rana da tsaiwarta. Allah kana ganin abinda wannan bawa naka yaima Dauda, mala'ikun Allah ku shaida, Allah ya saka ma Dauda, ubangiji Allah ka tagaiyara Alh Zangina ka haɗashi da jafa'in duniya kafin ya tarar dana ƙiyama" Yaya Use ma kuka take yi sosai. Muna cikin wannan tashin hankali Narani ya fito a gaggauce ya nufomu sai yarfe zufa yake yi.
"Yaya ake ciki Narani?"
"Wallahi Use a taƙaice dai sun bamu gado. Jibi za'ayi mishi aiki, kuma sunce bama zasu taɓashi ba har sai mun biya kuɗin aikin. Amman suna maganane akan wasu mahaukatan kuɗin da ni banma taɓa riƙe irinsu a rayuwata ba. Ni harma nace su sallamemu mu koma gida sai ayi na hausa mu jaraba ko Allah zai sa a dace." Nunfarfashi na shiga ja da saukewa. Yanzu Daudan da yake buƙatar taimako shi za'a mayar gida? Ya Ubangiji Allah ka kawo mana agaji" Yaya Use tace.
"Har nawa ne kuɗin haka Narani da zaka ce a komar da yaro gida? Shakirar tashi fa naga tayi fata fata har ɗiwa take fitarwa, ya zaka ce haka" A rainace cikin ɗiban albarka Narani ya soma magana da Yaya Use.
"Magana suke akan sai an sauke duɓu ɗari biyu da hamshin kwatan miliyan kafin ma a taɓashi, banda kuɗin gado da magani. Lissafin rabin miliyan suke yi mini. Dani daku nayi imana har mu mutu hanyar inda kuɗaɗennan suke bama zamu gansu ba wallahi. Yaro dai ɗanane gida zan koma dashi ayi mishi na gargajiya. Ni dama tun farko da aka sanar dani gaku a hanyar asibitin Birni, sai da nace ma a sanar muku ku koma. Kai Shehulle shiga ka fito da yaron mu koma gida." Fuu Shehulle ya shige ɗakin da aka shigar da Dauda. Sai gashi saɓe dashi a wuyanshi.
"Ka saukeshi ɗan ƙwal uba ai yana iya tafiya. Ba sai da aka nemo shi a waje ba ma" Shehulle da jin haka ya dire Dauda a ƙasa. Ni kuwa sai tsiyayar ruwan hawaye kawai nake yi. Na kasa cewa komai, Yaya Use ma ta kasa magana. Fuu suka wuce suka barmu a tsaye. Dauda sai waigena yake yi, shima kukan yake yi. Sai da na dena ganinsu sannan na sake fashewa da wani irin kuka mai kama da fitar rai. Duk waɗanda suka zo wucewa sai sun tsaya sun tambaya lafiya ko rasuwa akayi mana ne? Da "E" Yaya Use take amsa musu.
"Tani daure ki lallaɓa mu koma Shanono. Kinga mu kanmu bamu da kuɗin da zamu iya lura da Dauda ko da da maganin gargajiyanne, ballantana wannan maɗuɗun kuɗin da lukitoci suka yanko. Mu yi ta mishi adda'a, zo mu tafi" Da jan ƙafa na bar asibitin. Muna cikin motar komawa Shanono Baffa yayo kiran wayar Yaya Use "
"Use Yaya kun isa asibitin dai ko, yaya jikin yaron?" Cewar Baffa da yake magana ihu ihu. Ajjiyar zuchiya Yaya Use tayi tace.
"E Baffa, amman gamu a hanyar komowa Shanonon ma." Baffa yace.
"Dashi Daudan ko an kwantarku ne?"
"Dashi zamu dawo, sai mun dawo zaka ji komai"
Gidan su Baffa muka wuce kai tsaye, a lokacin naƙuda ta kawo kai, ba shiri su Goggo mai riga suka rufeni a ɗakin Goggo Marka. Nan na shiga sabuwar azabar naƙuda. Duk zafi irin na naƙuda, da fita hayyaci da akeyi, sai wannan karon yazo mun da sauƙi. Dan raɗaɗin dake cinye ƙasan zuchiyarta yafi naƙudarnan zafi. Cikin gumurzun awa uku na suntulo ɗana namiji ƙato dashi lafiyayye. Cikin da babu awo bare shan ƙwayar bature ta masu ciki. Amman cikin hukuncin Allah gashi na sauka lafiya, shima yaron yana cikin ƙoshin lafiya, dan ya karaɗe gidan da inya_inya. Yara_yaran gidan sai murna suke an siyo musu jariri wai. Ni kuwa sai jinyar zuchiyata nake yi.....✍🏻
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 11
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
Bayan nayo wanka na dawo. Na tarar da Goggo Marka tana gasama Jariri cibi, an sa mishi kayan jirajirai yayi kyau abinshi, yana duƙunƙune a cikin zanina. Ina zama Inno ta shigo da ɗumamen tuwo da kunun tsamiya.
"Shanono maza ki yayyanki tuwonnan da zafi_zafi. Ni kuma bari in kira Kaila in sanar dashi haihuwar." Dubanta nayi bayan na tusa tuwon a gaba nace.
Inno inason inna gama cin tuwon in koma can gidansu wannan yaron dan in ji me ake ciki dan Allah Inno kar ki hanani."
"Da ɗanyan jiki zaki fita Tani, ko Use da take can kina nufin kin fita iyawa, Karime ma tana can gidan tama riga Use yin gaba." Goggo Mai riga ce tace.
"A'a Inno kada mu tauyeta in ta gama ta goya jaririnta taje ɗin tunda Allah ya sauketa lafiya. Hankalinta ba kwanciya zaiyi ba muddin bata je taga yaron ba. Ke kuma Tani batun shigar da ƙarar Alh Zangina wallahi karma ku kuskura a ta da zancan. A burne wannan maganar a cikin gida, wanda yaji ya riga da yaji, waɗanda basu ji ba kuma shikenan , kuyi Allah ya isa kawai" Ni dai sanyi naji da har suka fahimceni kuma basu hanani fita ba. Batun shigar da ƙara tuni mun tsorata har mun haƙura .A gurguje na cinye tuwon na sha kunun rabi. Goggo Marka ta goya mun baƙon duniya ta lulluɓemun shi da zani biyu lub_lub. Sallama nayi musu zan fita, ina jiyo sanda Inno take waya da Kaila tana sanar dashi an samu ƙaruwa, jibi ma zan tarkato in komo. Ni dai nayi ficewata, ina tafe Kaila ya kirawo wayata, sai da na samu gefe na rakuɓe sannan na amsa wayar.
Assalamu alaikum Abban Sulaiman barka da yamma an wuni lafiya?" A daƙile yace.
"Lafiya lau. Yanzu Inno take faɗamin kin haihu, Allah ya raya, dan haka gobe sai ki kamo hanya ki tawo gida ki nutsu." Da sauri na tari numfashinshi dan naji yana shirin kashe wayarshi.
Abban Sulaiman dan Allah ka barni zuwa jibi kaji? Wallahi jibi zan dawo, jikin nawa bashi da ƙwari. Ne ina gudun yin tafiya mai nisa." Katseni yayi da cewa.
"Ko kuma baki gajiya da kallon tsohon mijinki wannan baƙauyen ɗan uwanki baƙauyiya ba ko, ko so kike ki goma gidan tsohon mijinki? Ai in hakan kikeso yanzu sai in rubuto miki takaddarki ta waya kinga ba ma sai kin dawo ba ko? Sai dai in zo in karɓi ɗana" Ƙit ya datse wayarshi. Zuchiyata ta shiga harbawa da sauri, tarihi na shirin maimaita kanshi. Da ƙyar na saisaita kaina naci gaba da lafiya. Ina shiga cikin gidansu Dauda na tarar ana rikici ko wacce daga cikin matan gidan sunce babu wanda zai iya riƙe Dauda sabida wari yake yi, kowa yace ba za'a shigar mishi da yaron ɗakinshi ba. Yaya Use da Yaya Karime sai basu baki suke yi, amman kowa yaƙi, babu ma wanda yasan na shigo sai jiyo muryarta suka yi cikin sanyi ina cewa
In ba'a samu wacce zata riƙe Dauda ba, ina ganin mahaifiyarshi ita tafi cancanta ta kula da abinta. Idan da Dauda zai narke ya zama tsitsotsi ni inason yarona. Narani na roƙeka a karo na barkatai ka bani yarona, ko shari'a ta mallaka mun Dauda. Tunda yaronnan bashi da lafiya a bani kayana" Kowa na tsakar gidan suka zuba mun idanu. Yaya Use da tasan ni kaina a dofane nake a gidan Kaila tace.
"Baki da hankaline Tani, in kika ɗauki Dauda a cikin irin wannan halin kiyi yaya dashi, kina da kuɗin da zaki yi mishi maganine ko yaya, sannan kin tambayi mijinki yace miki zai iya riƙe agola ne?" Yawu na haɗiye nasan tabbas Kaila bazai yarda Dauda ya zauna a gidanshi dindindin ba. Amman a matsayina na uwa ina ganin ban kyauta ma yaron ba in na barshi a cikin irin wannan halin na ciwo. Gashi da dukkan halamu inda za'a barshi ya zauna ai mishi jinyar ma babu. Gani nake kamar in na barshi mutuwa zaiyi, kuma alhakin mutuwarshi gani nake kamar a kaina zai rayata, tunda nice uwarshi, kuma hausawa sunce Inna nafi uba ko da uban sarkine"
"Can dasu gada zomo ya jiyo kiɗan farauta. Gara ma ka bata ɗanta taje ta kula dashi. Dan ba mahaukaciya bace ta yayeni da zan shigar da Dauda ɗakina yana tsaye yana ɓirɓishin tsutsotsi, ɗiwa na gudana" Cewar Ta maulidi kenan. Tana magana tana fari da idanuwa. Iya mai Fura tace.
"Ni gashi ba ƙarfi ba balle ince ni a bani. Nima kula dani akeyi" Shi kuwa gogan duk wannan maganar bai ce komai ba, yana tsaye sai hunhuna yake yi. Na tuno ranar da aka ƙwace Dauda a hannuna yana tsumman goyo a wannan tsakar gidan. Yau gamu a tsakar gidan dai ina shirin karɓar ɗana bayan tarbiyarshi ta samu tawaya ga halin jinya da yake ciki a sakamakon rashin mahaifiyarshi a kusa. Ire_ iren waɗannan dalilinne ke sa iyaye su kasance ma yaransu a matsayin madoraga, ko in ce kendir mai ƙone kanshi dan ya haske wasu. Cikin buyagi Narani ya finciko Dauda ya dire shi a gaban Yaya Use yace.
"Gashi nan ku je dashi, tunda taji zata zame mai biyu a ɗaya ( 2 in 1) Amman ta sani muddin tasa ƙafa ta fita da Dauda daga cikin ahalinshi, to yafita kenan har abada. In Dauda ya gwamutsa sunanshi da sunana ko inkiyar ahalina Allah ya isa ban yafe ba. Aurenki in banda bala'i babu abinda ya haifarmun mai farar ƙafa kawai, tunda na haifi Dauda asarori su kai ta bibiyar rayuwata kuje ko na huta" Hannun Dauda na kama a raunace shi kuma kuka ya fashe dashi, daga ni har Yaya Use kuka muke yi. Yaya Karime me ce idanunta a soye, sai mamakin Narani da irin hukuncin daya zartar mai zafi take yi. Ni kuwa ɗana na riƙe nace.
Tawo mu tafi Dauda in sha Allah ni Tani Naroro Shanono zan tsaya ma a rayuwarka, zan zame ma tsayayyar uwa." Juyawa muka yi zamu fita, idanuna ya rufe bana ji bana gani."
"Tani ki bar yaronnan a gidan mahaifinshi ina jiye miki kar Dauda ya zama sanadin mutuwar aurenki. Kinsan furucin da Baffa yayi. Kaila bazai yarda ya riƙe Dauda ba" Cewar Yaya Use da take ƙoƙarin farkar dani, dan a tunaninta na saki layi. Ni kaina zuchiyata cike take tab cikin taraddadin me kaje kaxo. Sai dai ina roƙon Allah yai mun mafita ya kareni daga sharrin Kaila" Dauda yace.
"Iyata dan Allah kar ki barni, ni zan biki." Murmushi nayi na share hawayena, wani irin ƙarfin guiwane ya zo mun. Fuu na fice a cikin gidan riƙe da Dauda a hannun dama na. Ban nufi gida ba. Wajen maganin gargajiya na nufa, ban ko bi ta kan su Yaya Use ba. Bayan na sa Dauda a layi, sai da na keɓe kaina na ragema zuchiyata nauyi. Nayi kuka kamar bazan dena ba. Sai da nayi ma'ishina sannan na fito daga ciyayin dana ɓuya na dawo kan layi. Sai wajajen magriba muka samu shiga ɗakin maganin. Cikin ikon Allah jaririn dake bayana tunda na goyashi yake bacci, sai dai yana ɗan motsi lokaci zuwa lokaci. Malam Mamuda Maƙeri ya zame ma Dauda wandonshi ya duddubashi. Sai toshe hancinshi yake yi da tsumma. Bayan ya gama dubashi ya mayar mishi da wandon nashi.
"Ciwonshi mai girmane kuma yana buƙatar kuɗi da jajircewa wajan bin ƙa'idar shan magani. Zan baku na sha da shafawa kamar na kimanin wata ɗaya. In maganin ya ƙare sai ku dawo." Har ƙasa na zube ina godiya, cikin rauni nace.
Malam meye abun sadaka to?" Murmushi yayi yace.
"Hala yau shine karonki na farko na zuwa karɓar magani ko?" Tsurewa nayi, cikin dibibicewa nace.
E hakane, yau ne ranar farko Malam "
"To shi yasa. Ai ko ƙwandala bana karɓa har sai marar lafiya ya gama shan magani, in ya warke sai in yanka abinda za'a bani. In kuma bai samu waraka ba bana cin sisin kobo. Amman sau ɗaya na taɓa bada magani ba'a samu waraka ba. Shima ajaline ya cin mishi. Shekarata hamsin ina aikin ceto" Wani sanyi naji a raina sosai. Godiya nayi mishi na fito. Muna tafe raɓe_raɓe da Dauda, duk inda muka wuce sai wari buu, ga kudade sai bibiyarmu suke yi. Baƙon duniya sai lokacin ya saki wani irin kuka mai zafi, inaji yai ta canyarawa. Abun hawa muka hau muka nufi gida. A ƙofar gida naga su Inno harda Baffa sun yi cirko_cirko. Yaya Use tana hangoni tace.
"Baffa ai ga Tani nan zuwa ita da Daudan" Ina isowa Baffa ya ɗaga sandarshi ya rabɗamun ita a goshina, ji kake gab. Take wajan ya fashe jini ya soma wanke mun fuskata, jini har cikin ƙwayar idandunana. Kuka na fashe dashi kawai, ina jiran me Baffa zaice. Cikin ɗaga murya yace."
"Wallahi muddin ki kai sake akan Dauda auranki ya mutu a karo na biyar. Kwarankwatsa Tani tsine miki zanyi kibi duniya, ba za ki yi albarka ba tunda kin kasa faranta mun raina. Ke ba ma zaki tafi da Dauda ko ina ba. Kai Muttaƙa ka kama hannun yaronnan kai da junaidu, Ige ta raka ku." Ni dai ina dafe da kaina sai kuka nake yi, hannuna rike da Dauda. Ige ce tace.
"Naroro ni gaskiya ina ganin kabar ma yarinyar nan ɗanta tai mishi jinya. Ala bashi in ya warke sarai sai ta dawo dashi gidan ubanshi. Ke Tani karma ki sanar ma Kaila cewar riƙon Dauda zaki yi sam. Ki faɗa mishi jinya kika tawo dashi ki yi mishi, yay haƙuri da zaran ya warke shikenan, sai ki dawo dashi. Ni da kaina zan mayar dashi. Junaidu Yusufu, Muttaƙa, me kuka ce ko ba gaskiya ba?" Akan hakan duk su kai na'am Inno ta jawo hannuna muka shiga ciki yarare_yarare jini na bina. Sai lokacin na samu ɗan kuzari har nayo wanka da ruwa mai zafin gaske, kafin in fito daga wankan goshina ya kumbura yai suntun, kaina dan ciwo kamar zai dare gida biyu. A tsakar gida na tadda Inno ta tuɓe Dauda zata yi mishi wanka. Sai toshe hancinta take faman yi, tsutsotsi sai yawo suke ɗaiɗaiku a gefe_da_gefen cinyarshi. Kasa tafiya nayi har sai da Baba Marka taje.
"Ki shigo daga ciki sanyi na kaɗaki da ɗanyan jiki" Sannan na shiga ciki na sake kaya, aka bani tuwo naci, sai bacci ya shiga yanko mun. Amman tunanin yadda zamu yi da Kaila in yayi tozali da Dauda tuni ya yakice mun baccin. Nan kuma na harba duniyar tunani. Su Inno suka yi tafiyarsu zuwa gidan biki. Ni kuwa maƙota sai abkin shigowa yi mun barka su ke yi. Dauda yana ɗakin yaran gidan a kwance, Baba Marka ce ta kaishi tace ya kwanta acan, dan duk matan da suka shigo barka sai sun tambaya abune ya mace a ɗakin ne yaketa busa wari. Ni a karan kan kin kaina warin isata yake yi, nima kenan uwa, ballantana kuma su Baba marka. Allah sarki rayuwa Allah ka kawo mun sauyi na alkhairi a cikin rayuwata, kasa goben yarana tayi kyau, a wajensu kawai nake fatan samun salama. Sune kaɗai zasu ji ƙaina su sani Murmushi.
JOS KWATA TA YAMMA DA BAUCHI:
GIDAN KAILA:
Anty Maryam ce ƙanwar mahaifiyar Hajiyayye ta tusota a gaba dab magriba suka shigo gidan. Idanun Hajiyayye yayi luɓu_luɓu da halama anci kuka an ƙoshi, rannan nata a mugun murtuke. Shigowarsu tayi dai_dai da fitowar Bilkisa daga cikin turakar Kaila. Taci wani irin uban kwalliyar da ba mijinta Kaila kaɗai bane zai gwaɗa. Duk wani mai idanu muddin ya gani tabbas yasan anba kyau hakkinshi ta hanyar ƙara ƙawatashi da kayan ƙawa. Sanye take cikin gajeren baƙin wando iyakarshi guiwarta. Sai wata riga ɓaka ɗamammiya mai hannu ɗaya. Gashinnan yasha gyaran Amarci sai sheƙi yake yi, babu ko ɗankwali a kanta, da baƙin ribbon ta tubke sumar tata. Ba wani gashi gareta can ba, tana dai da nayin kwalliya, da yake ta gyarashi tsab sai yayi mata mugun kyau. Fuskarta tasha janbaki da hoda, sai ƙamshi kawai take. Hatta tsakar gidan ya cika tab da ƙamshin turaren wutan da aka sa Shamwila ta bunka a ɗakin Kaila. ( Turaren wuta ne na matan aure, wanda ake kunnawa da yamma domin jawo hankalin da nutsuwar mai gida. Matan Kanuri suna saka wannan haɗin turaren in suka kintati dai_dai lokacin dawowar mai gida sai su kunna. Da zaran mai gida ya shigo gida da gajiya ko ɓacin rai. Yana shaƙar wannan ƙamshin sai yaji wata iriyar nutsuwa na gangaromai. Hakanne yake sa miji ko a ina aka ɓata mishi rai Allah _Allah yake yi ya dawo gida dan ya samu nutsuwa. Ga masu buƙatar wannan turare sui mun magana) Cikin yanga Bilkisa ta dubesu tace.
"Sannunku da zuwa,