Showing 60001 words to 63000 words out of 68990 words

Chapter 21 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

sallar magriba ne yasa ya fice daga ɗakin jiki a mace.



SHANONO.
Ina tsakar gida ina jiran ruwan tuwo ya tafasa in zuba talge. Littafin lissafi ne a hannuna ina duba shafin da akayi mana, ina bin misalan ciki a hankali a hankali. Haya_hayar yara ce tasa na rufe littafin na kallesu.
Yaya akayi yinwa ko Sulaiman?"
"Lefi yayi ma malam shine ya zane shi" Cewar Amina uwar kanzagi kenan. Shi Sulaiman ashe a wuya yake, sai yasa hannu ya shararama Amina mari. Tas naji sauran hannun kaila a fuskar Sulaiman. Yaron ya fashe da kuka ya durƙusa. Tsaki Kaila yayi tare da bin mu da kallo yana muzurai.
"Kizo shanono mu yi magana" Jin yace haka sai Hajiyayye ta ɓata rai daga dariyar data gama yi ina ganinta. Nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ilai kuwa ina zuwa na same shi a tsaye kamar soja.
"Bani kayan da Bilkisa ta baki maza" Suna kan katifa dama. Ɗakkowa nayi na bashi abinsu.
"To daga yau sai yau in kika sake tsaiwar minti uku da Bilkisa ranki zai ɓaci. Wallahi Shanono ki fita sabgarta in kina son aurenki ya tsira" Yana kaiwa nan ya fita. Kaila na lura barazanarshi gareni bata wuce ta saki. Domin yasan babu abinda na ƙi jini irin saki. Kuma yasan wahalhalun da na shiga sanadiyyar mutuwar aure. Wannan dalilin ya riƙa yake tsorata duniyata da kalmar saki. Sabida ya lura zaman auren nake so, burina in zauna da daɗi babu daɗi. Kai na girgiza kawai, na fita nayi talge abuna, na ci gaba da duba littafina.
"Ni da su Gwamma, oh ni Hajiyayye in da ranka ka sha kallo, an koma makarantar balagaggu, dan miji ya auro kishiya likita." Ni dai hankalina yana kan littafina domin na soma fahimtar yadda abun yake, saura ƙiris in gano bakin zaren. Amman in na kwashe tuwo zan leƙa Sabira ta ɗan ƙara ɗaurani bisa layi. Kafin isha na game tuwo na baje ma yara a faranti, nima na zuba nawa. Sai da naci na yi ƙat, na goge miyar a kaina tas na mayar da ɗankwalina. Sai na miƙe na goya Salis.
Yaya ka kula dasu zan je in dubo Sabira. Haka dai kiki_kiki Sabira ta koya mun abinda ya samu, sai taran dare na baro gidan. Duk aikin gida da aka bamu a makaranta sai da mu ka yi tukunna. Ko da na shigo gida yara sun jima da Bacci. Amina harta tsula fitsari tana cikinshi. Salis na sauke a baya a daddafe nima na haye katifar nan nayi kwanciyata.
Gaga_gaga dai anata rayuwa a haka, kullum da sabon tashin hankalin da kaila zai sani a ciki, bayan kwana biyu da kawo sammaci. Habiba Bala tazo mana da lauya. A gidan yaya Use mu ka haɗu, acan muka tattauna, yai mana tambaoyi cikin ƙwarewar aiki. Iyakar abinda muka sani muka sanar mishi. Shi kuma ya ɗaura mu a kan matsaya ɗaya. Habiba Bala bata daɗe ba ta koma, sabida Dauda. Ranar dana kwana bakwai da haihuwa da safe ina ɗaki yara duk sun tafi makaranta. Nima aikin gida da malamar Physics ta bamu nake yi, da kuma aikin gida da aka bamu a islamiyya, Baƙaƙen larabci zamu rubuta daga farko zuwa ƙarshe, inata fama na barbaje sai cin rubutu nake yi. Makaranta da daɗi sosai, naji daɗin makarantar islamiyya dana je sosai, gashi muna da yawa ainun, akwai ƴan mata da matan aure, harma da zawarawa. Ga manyan mata ƴan gayu sosai a ajinmu, ko wacce tas da'ita. A bencinmu mu uku ne, dukkanmu muna da goyon yara ƙanana, kuma naci sa'a suma sababbin zuwanne, sai kowa ya sake da kowa dai.
Kaila ya ɗago labule ba ko sallama yace.
"Ki shirya kaya nan da awa biyu motar ɗiban kaya zata iso. Za'a kwashi kayanku zuwa sabon gida" Kafin in yi magana ya saki labule ya ficewarshi. Ina jiyo dirin lifan ɗinshi." Ba shiri na haɗe littattafan sai gidan Sabira. A falo na sameta tana turarashi da kayan ƙamshi daga Mrs Bukhari. Ko ina tsab sai ƙamshin daɗi.
Ka ga mata ƴan lelen miji. Wallahi kya yi Sabira Abban Mustapha yana yabawa kuma yana ba da gudunmawa" Zama nayi a kujerarta, ita kuma ta ajjiye kaskon tace.
"Yaya karatun, yanzu na kira Habiba Bala na ji jikin Dauda, mun gama wayar kenan na soma turara gidan sai ga ki"
Hmmm yau zamu tashi Sabira. Yanzu ya leƙo ɗakina yake sanar mini. Wai nan da awa ɗaya motar ɗiban kaya zata iso." Waya kawai naga Sabira ta zara, ta yi danne dannenta ta kara a kunne. Jim kaɗan ta soma magana.
"Hello Ahmad kana ina yanzu haka? Kaya nake son ka ɗaukar mun daga gida zuwa masallacin ƴan dankali. Wajan masu sai da kaya na hanu.? " Daga wayar ina jiyo Ahmad na cewa.
"To Anty motar ma tana ƙofar gidanki, in shigo in ɗebi kayanne?" Da jin haka Sabira ta miƙe tsaye.
"Mu je Tani maza bamu da lokaci sosai." Fita mu ka yi, Ahmad ya taimaka mana muka saka katifunnan a mota. Yayi gaba dasu, mu kuma mu ka bi bayanshi a Napep. Da waɗannan katifun guda biyu Sabira ta amsar mun gado 6 by 6. Sai mu ka sai katifu guda biyu a cikin kuɗin da Habiba Bala ta bani. Sabira ta siyamun kafet na hannu mai kyau ja da kuɗinta. Cikin awa guda muka gama siyan komai Ahmad ya dawo damu. Motar mu na tsaiwa motar ɗiban Kaya itama ta tsaya. Kaila ne a gaba a lifan ɗinshi. Kamar bai ganmu ba haka yayi.
"Ahmad ga motar nan, ka zuba kayan a ciki. In ka zuba ka shiga ɗakin su Mustapha zaka ga doguwar kujera ka fito da'ita ka haɗa mata." Godiya naso yi, amman Sabira ta doka mun harara ta ja hannuna zuwa ciki. A lokacin me motar kaya da Kaila, da Amadudu sun soma fitar da kaya waje. Sabira ta zazzage tsunmokaranmu tas a ƙasa ta sake zaɓewa, ta cire mana marasa yawa, sauran kam ni kaina nasan babu amfanin da za'ayi dasu. Tsabar sabo da tulin tsunmokine kawai. A buhu ɗaya ta haɗe ma yara kayansu. Ni kuma nawa ta je gidanta sai gata da katuwar jaka. A ciki ta shirya mun kayana. Ta kirawo Ahmad ya fita dasu. Kayana dana Bilkisa su kai gaba. Kayan Hajiyayye da Hindatu kuma sai an dawo. Hajiyayye ta kai wuya kuwa da ita da ƴan uwanta da tayo gayyarsu. Itama Bilkisa ƴan uwanta biyu sun zo jiya daga Zaria, ga me aikinta kuma. Allah sarki, ni ko daga ni sai Sabira, Yaya Use sai dai waya kawai mu ka yi da'ita nake sanar mata. Habiba Bala kuma, dana kirata ɗazu a wajan siyo katifa tace in yi haƙuri sai gobe zata iya shigowa.........✍🏻



*OUM SOOFEEYYER GRAPHIC AND DATA*

*INA Marubuta da masu business*


*Maza ku hanzarta mun shirya tsaf domin kayatar da ku da graphics kalakala Kuma cikin farashi me sauki*

Logo
2d Logo
Flyer
Invitation card
Invitation vedio
Save the date card
Save the date vedio
Book cover
Account sticker
Makeup Flyer
Business Flyer
Da dai sauransu

Sannan Kuma Ina koyarwa ga duk me bukata cikin sauki
08069638776

*All netwk Data is available*


_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_

_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_

*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*


*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S

*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224

*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*

*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*

*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*

*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*

*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*

sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*

KAMARSU👇🏻👇🏻

*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*

DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 17









Ana cikin wannan Gaga_gaga sai ga ƴan makaranta sun dawo. Ganin mu a tsakar gidane yasa suma suka shigo ɗu. Amina ta kusan murjema ƙanwar Hajiyayye ƙafa. Ai kuwa ta lailayo ashariya ta mako mata ta ɗaura da cewa.
"Shegiya mai kama da uwarta, dangin ƴan maula, masu kwana a bakin masallaci" Wani zafi naji a zuchiyata, nasan haushi suke ji da abinda ya faru da Yaya Use da Hajiyayye, da kuma haushin an soma tafiya da kayana ita nata gasu nan jibge a tsakar gidan. Ina ganin haka na miƙe dan take takensu so suke a tanka su yi buyagi a tsakar gidannan. Su ja mun sale salin tsiya.
Sabira mu soma yi ma maƙota sallama, kafin lokacin tafiyar tamu tayi, yau dai ba zuwa islamiyya sai kuma gobe." Fita mu ka yi a gidan har da yaran. Bilkisa tana ɗakin Kaila ita da ƴan uwanta. Muna fita mu ka samu isa a waje isowarshi kenan da matarshi uwar gidanshi Jamila. Itace muke mutunci, amaryarta kuma ƙawar Hajiyayye ce unguwarsu ma ɗaya.
Jamila kece a tafe? Gashi kin zo zamu shiga yawon sallama da maƙota" Ɗan dariya tayi tace.
"Ai sai mu je. Da fatan ba ki yi fishi ba. Kin haihu ko barka banzo ba, an muku amarya ma banzo ba"
Babu komai. Isa barka da rana" Muka gaisa da Isa tare da mun murnar komawa sabon gida.
"Kaila ne yace in soma kai ku can gidan. Ku shiga maƙotan ku fito sai mu wuce in soma ajjiyeku, sai in kwashi sauran matan nashi" Tare da Jamila mu kai ta bin maƙota muna musu sallama. Sai Allah sanya alkairi suke yi mana. Muna fitowa Isa ya figemu a mota sai sabon gida. Kaila ne ya buɗe mana get da sauri, ni naga sai dariya yake yi. Muna haɗa idanu ya gintse dariyar tashi, ya sau get ɗin. Masha Allah gida yayi kyau ya sha fenti mai ruwan ƙasa, ga filin tsakar gida masha Allah. Muna firfitowa Kaila ya soma masifa.
"Haba isa dana san haka zaka yi mun ai da ni zan ɗauki motar in je in ɗakkosu. Bilkisa baka ganin baƙine suka zo mata daga Zaria? Da direba ma suke tafe, direban nasu yaje Bauchi ɗakko wani saƙone. Da sai ka bar su Shanono su zama ƙarshe." Isa ya hararashi yace.
"Kai dai kaji kunya. Shanonon zan kawo a ƙarshe gidan da tare kuka zaɓi yanda fasalin gidan kuke son ya kasance. Ko ka mance tare kuka dinga zuwa sauke block ne? Duk wani wahalar ginin gidannan da itafa akayi. Dan kawai kayi amarya shikenan sai itace zata zama ƙarshen shiga gidan?" Ni dai ina gefe kamar yajin ƙosai. Yara kuwa guje_gujensu ma suke faman yi a tsakar gidan. Isa ya nuna mana hanyar babban falo, inda shine mahaɗar ko wanne pat na cikin gidan.
"Bismillah ku shiga daga ciki, ai kinsan ɗakinki" Sai lokacin Kaila yayi magana yace.
"In kin shiga ki jirani a falo in na dawo zan nuna miki ɗakin ki. Kai kuma ka bani keyn mota in ka gama soki burutsun zancan" Fisge keyn motar yayi a hannun me shi. Isa ya koma ɓarayin mai zaman banza ya zauna, suka fita a gidan. Mu kuma muka shiga ciki. Masha Allah, ko ina yaji tayil, ga ƴan kayayyakina a gefe a cikin babban falon, amman banga na bilkisa ba. Kuma duk ƙofofin ɓangarorin uku a rufe suke da ƙwaɗo, dan Jamila sai da ta murɗa ko wacce ƙofa ta ji ta gam. Doguwar kujerar da Sabira ta bani akai muka zauna, jikina kamar an watsa ma kaza gishiri haka nake ji. Sai haɗiɗiyar yawu kawai nake yi. Minti ashirin bayan zuwanmu sai ga Kaila da Isa motarsu ta shigo. Sabira ce ta leƙo take sanar mana.
"Gama su nan sun dawo, Amarya a motar da ƴan uwanta suka zo aka kawo su, Abban Sulaiman kuma ya ɗebo Hajiyayye da ƴan uwanta. Ni dai ina zaune jigum, har su Bilkisa da tawagarta suka shigo. Hajiyayye kuma suna wajan motar kaya data shigo yanzu. Ƴan uwanta suka shigo cikin falon da muke, tare da Kaila. Key ya jefo mun cinyata, tare da nuna mun ƙofar ɗakin dake gefe can. Ciki biyu da falo ne ɗakin sai bayan gidu a ko wanne ɗaki in ban manta ba Dan da sunan Amadudu aka yanki ginin ɗakin. Ashe ni zan zauna a ciki. Hajiyayye kuma ya miƙa mata keyn ɗakin da a da nasan turakarshi ne, Bilkisa kuma ya buɗe mata ɗakin da aka gina shi da sunana, ɗaki mai babban falo da ɗakuna har uku, bayan gida biyu, ga kitchen yalwatacce, har kantocin cikin kitchen ɗin ni da kaina na zaɓi samfurin wanda nake so, ashe rabon wata ne. Wannan shine kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi. Ana cikin haka sai ga Amadudu da Hindatu sun shigo babban falon da sallama. Key ya miƙa ma Amadudu.
"Ɗakunan dake tsakar gida, kai da Hindatu sai ku jera kayanku a ciki. Ɗayan yaranku sai su dinga kwana a ciki. Ɗayan kuma Shamwila sai ta dinga kwana a ciki " Gaba mu ka yi abin mu, Jamila ta buɗe ƙofar ɗakin muka shiga. Dukkanmu tsuru_tsuru mu ka yi a tsakar ɗakin muna kallon abun mamaki, ni ko hawaye ne kawai yake gudana a Idanuna tsabar damuwa har wani jiri ne yake ɗibata. Jan fentin mai kaila ya shirɓinamun a ɗakunan nawa babu ko sofane kalar jinin kare ( maron). Ni ɗakin ma tsoro ya bani wallahi, dan tunda uwata ta haife ni ban taɓa ganin fenti mai kalar jinin kare ido da idoba sai yau. Numfashi na ja mai zafi. Sabira ta kawar da tunanina da faɗin.
"Kai Tabarakalla masha Allah. Waje yayi kyau. Tani Allah ya sanya alheri, Jamila mu soma shigo da kaya ciki ko, mu kafa mata gado?" A tsaye suka fice suka barni ina kalle kalle. Ɗayan ɗakin ma an toshe ƙofarshi da bulo ga halama nan ana gani. Shi yasa naga wata ƙofar a cikin falon, kuma wannan ɗakin da aka toshe yafi girma, bayan gidan ɗakin kuma yafi kyau. A wannan gidan ɗinma a falo yarana zasu dinga kwana kenan, gashi su Hindatu har nasu yaran sun samu ɗakin kwana, Allah mai iko" Kama musu na yi mu kai ta shigo da kaya. Dake kayan nawa babu yawa cikin ƙanƙanin lokaci muka kammala komai. Durowar dake jikin bangon uwar ɗakina Sabira suka buɗe suna ta jera kayan yara. Ni kuma ina saman turmi ina buga labule da ƙusa dan bani da ƙarfen labule amman mancewa nayi da zan siya na hannu a masallaci. Zama nayi a kujera ina ba Salis Mama. Jamila tace.
"Umman Sulaiman me za'a dafa ne ya kamata ace an ɗaura abinci, naga gidan ya soma ɗinkewa da mutane."
To Jamila bari in nemi Abban Sulaiman tukunna riƙe mun yaronnan ina zuwa" Kafin ta karɓi yaron sai ga sallamar Bilkisa daga bakin ƙofa.
"Umman Sulaiman ki kawo kwano a zuba miki abinci ke da jama'arki"
To Bilkisa zan aiko yara su kawo" Komawa nayi na zauna. Sabira ce ta ɗakko wata kwaraɓaɓɓiyar kulata babba ta kira yara ta basu su ka kai. Sai gasu da masa da miyar gyaɗa, harda sinasir, da lemukan roba har katan biyu, da fiya wata leda biyu. Yaran Sabira ta soma cira ma, su kuma sai da su kai sallar la'asar sannan suka zuba mana namu a tare muna ci suna hirarsu har da dariya. Duniya lallai ta nai musu daɗi. Ga ƴan uwan Hajiyayye ma a babban falo sai shewa da surutu suke yi. Dan Hajiyayye tayo gayya sosai, har maƙotanmu ƙawayenta duk sun zo. Ni ce dai koma baya akan komai, komai nawa yana zuwar mun ba irin na gama gari ba. Yau da Kaila bai hana Yaya Use zuwa inda nake ba da yanzu tana nan, yaranta. Nayi_nayi ta turo mun su ma taƙi gudun fitina, ga shi Yaya Karime tana Shanono sai jibi zasu dawo.
"Tani kayayyakin kitchen ɗinki ina zamu jera miki ne, naga kitchen a falo ko nan ne zamu jera naki kayan?" Cewar Jamila ba tun yau ba na fahimci Jamila tana da son dukan cikin mutum dan taji zance. Murmushi kawai nayi mata nace.
Ku barshi ai kuma kun gaji, kayan kitchen ɗin ba wani kaya ba, ni kaɗai ma in na nutsa zan gyara, dan akwai gyaran da ba'a ƙarasa a kitchen ɗin ba" Ni kuma harga Allah tsoro nake ji in ba da umarni a jera mun kayan kitchen a kitchen ɗin falo in zo Kaila yai mun watsi da kaya a gaban kishiyoyina, ya tsinkani kamar yadda ya saba. Gaga_gaga haka mu ka wuni cur muna abu guda. Sai yamma lis Jamila, Isa ya zo ya mayar dasu gida, ashe Amaryar a gidan ta wuni a ɓarayin Hajiyayye. Har gaban mota na kai Jamila sai godiya nake yi mata. Jamila ta kawo mun gudumawar kofunan roba dozin guda. Ban jima da shigowa ba Sabira ma tai mun sallama, sai kuma gobe in mun haɗu a makaranta. Abun sha'awa yara sai facaka suke da ruwan fanfo a bayan gida, su shiga ciki da gudu, su fito da gudu, wannan rigimar harda Hauwa akeyi. Tana biye dasu tana ihu da dariya. A babban falo kuma ina ta jiyo hayaniyar maza da muryar Kaila. Har zuwa bayan Isha, nan fa yunwa ta soma sasuƙar yara, ni bansan tudun da zan dafa ba. Ragowar masa guda goma sha biyu na basu, na juye musu miyar a kai. Nan da nan suka cinye, ba sai sun ce mun basu ƙoshi ba, ni kaina nasan basu ƙoshi ba. Lallaɓasu kawai nayi.
Ku yi haƙuri babu abinci ne a gidan. Ai kuna gani yau muka dawo sabon gida ko? Sai gobe zamu soma ɗaura sanwa." Buɗar bakin Sani yace.
"Umma Munga su Samira, da Jaxuli suna cin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login