Showing 63001 words to 66000 words out of 68990 words

Chapter 22 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

tuwo ɗazu" Sai nayi jigum nace.
To bari in leƙa in tambayo muku in bai ƙare ba." Salis na saɓa a kafadata yinwa kamar zata kayar dani, na nufi ɓarayin Bilkisa. Ashe mugun gyara akaima falon namu. Wasu ɗima_ɗiman kujeru aka baje, da ƙaton kafet, harda kayan kallo, ko ina sai hasken wuta. Gargaɗin dana tuno Kaila yayi mun ne yasa na canja akalata zuwa ɓarayin Hajiyayye. Jama'a sun soma sassautawa a ɓarayin nata. Da sallama na shiga falon. Abun mamaki ƴan uwanta suka watso mun wani kallo. Daga masu jan tsaki, sai masu cewa wari suke ji, harma da masu toshe hanci. Wani ƙududu na haɗiye ya faɗa cikina da zafi. Da ƙyar na buɗe bakina, dan jikina yayi mugun sanyi. Da ba dan bana son yarana su kwanta da yinwa ba, da juyawa ma zanyi in haƙura. Amman yaya zan yi, wanda bashi da gata ai yana ruwa.
Hajiyayye dan Allah abinci zaki sanmun in ba yaran yinwa suke ji." Wani banzan kallo tayi mun. Ita da danginta suka saka shewa, kafin tace.
"Wannan abincin ba Kaila bane ya kawo aka dafa. Balle kice suma suna da hakki akai. Daga gidan ubana ƴan uwana abun alfahari na suka yo aka tawo mun dashi kin gane ko? Sabida haka bazan bayar ba." Yayarta Ta Bizaaro tace.
"Zamu haɗu a kotu nan da kwanaki zaki san kishi ba hauka bane. Gobe ba zaki sake yin kisan kai ba. Tani baki ma da kunya, kinga ƙannenmu sai haƙuri aka basu dan dakaki ma su ka so yi, nice na taushesu" Daurewa nayi dan bana fatan suga zubar hawayena. Juyawa kawai nayi da sauri. Kiciɓis nayi da Kaila a ƙofar shigowa ɓarayin Hajiyayye. Idanu muka zuba ma juna. Sai lokacin hawayen da na shanye suka shiga suntiri a kumatuna. Ƙur yayi da idanunshi a kaina, bai tanka ba, nima ban tanka ba muna tsaye dukkanmu. Kaina na sauke ƙasa nace.
Yara yinwa suke ji Kaila. Bansan da wanne kitchen zanyi amfani ba. Sannan bansan kuma inda kayan abincin suke ba waɗanda aka ɗebo daga can gidan..
"Dakata Shanono. Wannan gidan ba irin wancan tsohon gidan da muka baro bane. Duk wani tsari ya canja. Zuwa gobe zan tara ku kuji sabon tsarin da zan fitar. Kayan abinci kuma ki tambayi Hajiyayye yana store ɗin kitchen ɗinta. Kitchen ɗin falonnan zaki iya jera dattin tarkacenki, amman ki sani ba kitchen bane na kunna gawaye ba. Yana da ƙofar waje, sai ki dinga fita da gawayin ta waje. Wallahi muddin naga wani ƙazanta a cikin kitchen ɗin, to zaki koma girki a cikin ɗakin ki zai fi mun sauƙi." Yana kaiwa nan ya wuce ni, bai faɗa mun yanda zanyi da yaran ba. Nayi iya dubana ko gawayi babu ban gani ba. Haka dole na koma ɗakina. Na samu ma yara mazan sunyi bacci a katifarsu wacce aka sa ma rigar leda. Ajjiyar zuchiya na sauke, ina shiga ciki na tarar da matan ma sun yi bacci. Ni ko a darennan tunanika babu irin waɗanda basu zo kaina ba. Na gaji da irin wannan rayuwar ƙasƙancin da nake yi a gidan kaila. Na fahimci tozarcin da nake fuskanta shafi_shafi ne, kuma ko wanne shafi da salon shi. Rayuwa kenan. Babu damuwa watarana sai labari, zaman gidannan inayine domin goben yarana kawai, amman nayi imani baƙin ciki da ciwon zuchiya su za sui ajalina. Haka na kusan raba dare ina kuka da tunano rayuwar da nayi a baya. Da irin mazajen dana aura, da irin jarrabawar dana fuskanta, dama darasi, da ƙaddarar dake cikin ko wanne aurena biyar. Aure da sha'anin maza ya gama fitar mun a kaina sam.
Washe gari.
Haka gari ya waye muka tashi cikin yinwa, ni kuwa cikina ƙullewa yayi sosai, da ƙyar na tashi, na tashi yaran dan su ɗauraye jikinsu su yi sallah. Ni kuma na shiga aikin fitsari. Ruwa na yayyafa a katifun duka biyu, nasa tsumma na goggoge,abun daɗin, rigar ledar da aka rufe katifar bai ba fitsarin damar taɓa katifar ba. na fito dasu, ruwan fitsari na yarari. Kaila da Hajiyayye suna babban falo, da dukkan halama Hajiyayye itace da Kaila. Ta ɗauki wanka tayi kyau abinta. Da idanu suka bini harna fice da katifun duk biyu, na wanke zannuwan gadon da zallan ruwa na yaɓa a katanga. Ina shigowa Hajiyayye tace.
"Ruwan fitsarinnan kisa tsumma ki gogeshi, wallahi Baby bazan iya ba. Yanzu ta babban falonnan zata dinga fitar da katifa kullum?" Ina tsaye ina kallon Hajiyayye, da irin kallon tsanar da kaila ke jifana dashi. Ko da ya tashi, da zagi ya rufeni, idona ya bushe babu ko sofanen hawayen ma. Tsumma na ɗakko na goge, na basu haƙuri dukkansu na koma ɗaki. Salis na tarar a hannun Sani sai kuka yake yi. Tun cikin dare yake jan nono, amman babu ruwan nonon, kukan yinwane kawai. Sauran yaran ma sun yi jigum sai kallona suke yi, irin kallon ki yi mana rai" Salis na saɓa a baya. Idanuna duk kwantsa, kumatukana duk busassun yawun bacci na fice a gidan da karamar jakata. Jefa ƙafata kawai nake yi bansan inda ma na dosa ba. Wannan masifa dame tai kama. Ni dai na kama tafiya sai nausawa nake yi, kafin in zo titi ma ba ƙaramar tafiya bace, haka nai ta fama, ina tafe faram_faram Salis sai kuka yake yi........✍🏻



_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_

_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_

*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*


*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S

*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224

*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*

*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*

*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*

*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*

*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*

sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*

KAMARSU👇🏻👇🏻

*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*

DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA.
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 18









Na ci tafiya sosai. Ƙafafuna su kai busu_busu dasu. Da ƙyar na ga wani shagon yarbawa yana kallon asibitin Salman dake cikin anguwar. Na ko yi sa'a suna da gawayi, da komai. Kayan miya, da taliya, maggi, manja na siya. Dubu ɗaya na kashe, na kuma juyawa faram_faram ina haƙi. A tsakar gida na tarar da su Shafi'i suna wasan tsere ban bi ta kansu ba, na shige ciki na fito da kurfot ɗina, ta bayan lungun inda ɗakina yake a wajan na hura gawayi. Kayan miyan kuma na wanke na zuba a turmi, Sani na kira yana jajjage ni kuma ina ɗebo kayan kitchen ɗina. Babban teburina dake kitchen ɗinmu na tsohon gidanmu na jawo. Akai na jejjera ƴan tukwanena, da kwandon wanke_wankenmu. Kurfot ɗinma na kinkima na aza a saman teburin. A daren jiya na yanke hukuncin bazan yi amfani da wannan kitchen ɗin na falo ba, dan akan kitchen ɗin Kaila zai iya ƙila dukana ma, gara in kiyaye kaina in janye jikina in ƙara komawa gofe, tunda ina da iyaka a cikin rayuwar Kaila. Taliya na ɓararraka mana na baje mana ita gabaki ɗaya a tire. Ina gaba Sani na biye dani. A tsakar gida mu ka ci karo da Hindatu tana wanke wanke a bakin famfon tsakar gidan. An kawata wajan da fararen tayil masu haske. Gaisawa mu ka yi.
"Ya sabon gida Umman Sulaiman?"
Alhamdulillah sabon gida yayi kyau, yayi daɗi" Iyakar abinda nace kenan nabi bayan su Amina da suka bi Sani ɗu sunga abinci. Muna shiga falon na tarar da su Bilkisa, da kaila, da Hajiyayye"
"Shanono ki zo ke muke jira, zan yi magana daku" Nufosu nayi na samu ƙasan kafet na zauna kaina a ƙasa, su ko dake ƴan gaban goshin mijine, ɗaya na hannun daman Kaila, ɗaya na ɓarayin hagu a saman kujera. Bilkisa na sanye da kayan aikin likitanci, da halama aiki zata wuce. Itace ta gaisheni. Da fara'a na amsa mata gaisuwarta.
"Dubi idanki duk ƙwantsa Shanono. Kai Allah ya sauwaƙe miki." Ƙasa na kuma yi da kaina.
"To dalilin da yasa na tara ku anan ba komai bane face canja tsare _tsare da zanyi a gidannan. Daga yau ko wacce mace ta dinga girkin abinda take so, ko wacce zan bata kuɗin cefanenta na wata, ta sai duk abinda yai mata. Amman na dena cin abincin ko wacce mata, Shamwila ce zata dinga mun girki a kwanan ko wacce Mata. Sannan na bata ɗakin tsakar gida, zata gyara ta zauna a can. Kuma ita zata dinga gyara mun ɗakina, da wankina kamar yadda Ɗanyan gwal take sata. Ko wacce mata ta gyara ɗakinta, tayi wankinta dana yaranta. In akwai me magana tayi" Yayi shiru yana sauraren mai magana. Ni dai ai yasan banda ta cewa, ni banga ma ta inda wannan maganar ta shafeni ba da har aka tara har da ni.
"Gwanda lokaci zai ƙure, kaga ina da nisa da asibiti sai na dawo." Cewar Bilkisa wacce ta miƙe tsaye tana kallon agogon hannunta.
"Naga ƙannenki kince sun tafi sassafe, amman kuma motar da suka tawo da'ita tana tsakar gida." Idanu ya ƙura mata. Sai da ta kai bakin ƙofar fita waje kana tace.
"Dad ne ya aiko mun da'ita in ci gaba da jigilar zuwa aiki" Tana kaiwa nan ta fice. Kaila ya daɗe sosai a zaune yana bin ƙofar da kallo, har motar Bilkisa ta fice a gidan baice komai ba. Abinda na lura shine ranshi ya ɓaci. Hajiyayye ce ta katse shirun ta hanyar cewa.
"Baby me kake nufi. Yarinyar da matarka ƴar boko ta kawo cikin gida a matsayin ƴar aikinta itace zata ci gaba da yi ma girki ko ba ranar girkin uwargijiyarta ba? To ina da ja gaskiya, irin ƴan iskan yarannan ne zaka sakar ma girki, da gyaran turaka, harda wankin miji."
"Hukunci dai na riga na yanke. Yayi daɗi ko karma yayi dai dole abi. Wacce taji ba zata iyaba sai ta tafi gidansu ai." Zuruf Hajiyayye ta miƙe tace.
"Zan ko tafin. Ai gara in san aurenta kake yi zai fi mun. In san gumurzun kishi nake yi da'ita" Fuu ta wuce abunta ta bugo ƙofar ɓarayinta. Ni dai bance uffan ba na miƙe na bar Kaila a zaune yana ƙananun maganganunshi. Ni ko dan yinwa ko gani bana yi sosai haka na shiga ɗakina. Nako ci sa'a sun rage mun taliyar, na dira akai nan da nan na lashe. Ko wanke baki cikinmu babu wanda yayi. Miƙewa nayi na shiga banɗaki nayo kwaskwarima, na wanke tsumman jini, na shanya a windo. Ban wanke bakin ba, sauri nake yi in na dawo na wanke. Yaran dai na miƙo musu roba mai murfi da muke zuba gawayi dakakke da gishiri na wanke baki.
Ku goge bakin ku Sani. Ke kuma Amina ki fita waje ki yi mun wanke_wanke. Da kin gama ku dawo ɗaki ku kulle, dan Allah kar ku fita babban falo kar ku ja mun abun faɗe, ni sai na dawo." Fita nayi, na hau abun hawa sai makaranta.



KAILA:
Bayan watsewar su Tani a falon. Sai ya shiga ɗakinshi, wanda yake manne da falon shanono.wanka ya shiga yayo. Ya fito ya cakuɗe jikinshi da kamshi. Ya ciro wasu ƙananun kaya masu kyau. Duk da kasancewar kayan na gwanjone, a wajan Baban Hajiyayye ya siya, amman a gwanjon ma su masu tsada ne, dan giredi ne sosai. Wani silifas yasa mai taushi, shima na gwanjonne. Ya ɓare ledar cingam ya jefa a bakinshi, ya shiga tsuna kamar tsohuwar kilaki. Wayarshi ya ɗaga ya danna number Shamwila. Ringin ɗaya wayar tayi zuruf aka ɗaga. Ita kanta dama zaman jiran wayar tashi take yi, tunda ta ji fitar Bilkisa.
"Ɗanyan jini mu haɗu dake yanzu a moonshine hotel, kinsan wajan ko, ta wajan cobe?" Murmushi tayi mishi tace.
"Ai na karaɗe hotels da dama a garinnan. Gani nan fitowa, ƙila in rigaka ƙila ka rigani" Sallama su kaima juna. Ita ta rigashi fita, amman kuma shi ya rigata isa tunda shi a abun hawa na gida yake. A wannan ranar Kaila yai rub da ciki akan Shamwila. Wa'iyazubullah a wannan ranar kaila da Shamwila sun aikata abubbuwa masu yawan gaske. Amman dake Shamwila mai wayo ce, sai da ya bata kuɗi masu tarin yawan gaske, kafin ta bashi kai bori ya hau. Abunka da aikin shaiɗan nan take yaji dukkan matanshi ashe salab suke shi bai sani ba, sai daya haɗu da gogaggiyar ƴar bariki sannan ya sani. Nan Kaila ya shiga rawar jiki akan Shamwila. Tsugunnawa yayi akan guiwarshi .
"Ɗanyan jini yaushe zaki kaini wajan Abba ne? Wallahi a yau ne nake jin dai_dai da kwana ɗaya bazan iya jure rashinki ba. Ni gara muyi aure hankali a kwance." Dariya tayi mishi.
"To ya maganar ginin ɓarayina, ba kace zaka yi mun ginin daya zarce wanda kwashi kwarab ɗin matanka suke ciki? Aure kam ai zamu yi ka soma gamawa da ginin tukunna" Shiru Kaila yayi yasan a yanzu baida kuɗin soma yin wani gini, nan da shekara guda ma ba lallai ya samu kuɗin soma yin sabon gini ba. Wannan ɗin ma daya aka ƙare. Rarrashin shi Shamwila ta shiga yi, tare da yi mishi alƙawin kasancewa tare dashi a duk daren duniya. Haka ne kuwa yaci gaba da kasance.


SHANONO:
Ina dawowa daga islamiyya na samu Kaila ya ba Sani dubu uku wai kuɗin abincinmu ni da yara na wata ɗaya. Ban dai yarda da abinda Sani yace ba, na adana kuɗin ina jiran in ya dawo in tambayeshi. Na riga nayo mana cefanen ɗan kayan masarufi daya sauwaƙa. Garin rogo da ƙuli kuwa na siyo su da yawa sosai. Gari na jiƙa mana, muna cikin sha Habiba Bala ta kira ni. Gata ta shigo jos. Kwatance na dinga yo mata harta iso. Itama ta zo mana da tsarabar sabulan wanki, dana wanka, harda man shafawa. Nako ji daɗi sosai, dan harna siyo sabulu da omo na wanki a cefanen da muka yi. Video call ta kira mai aikinta, suka haɗa ni da Dauda. Yana kwance ya sake ramewa, da gani yana jin jiki, dan sai da na zubar mishi da hawaye. Yaran na kira duk su kai mishi ya jiki. Sai tambayata yayi.
"Innata yaushe zaki zo?" Daurewa nayi na haɗiye kukana nace.
Zan zo Dauda kaji. Allah ya baka lafiya mai ɗorewa, ubangiji Allah ka raya wannan bawa naka" Habiba Bala ta kashe wayarta. A wajanmu ta wuni cur.
"Sabon gida ba zarni sai kaɗan Shanono. Akwai turaren wutan tsinke na sako miki ki yi kokari ki dinga kunnawa. Kuma ki yi kokarin gyarawa, ki dage da karatu. Sannan ki binciki sana'ar data dace dake" Godiya nayi mata sosai. Tayi mana sallama akan sai mun haɗu a kotu gobe." Wunin ranar sukuku nayi shi dan tsoron zuwa kotu gobe.
Ko da Yaya Use ta kirani itama jikinta duk a sanyaye haka dai mu ka yi wayar. Da yamma lis nasa yara mazan su yi wanka. Ni kuma na tafi baya dan yin girki. Wuta na hura na dawo ciki. Hauwa da Salis nai ma wanka, su Amina da Balaraba da kansu suke yi. Ni da kaina na ciro musu kayan da zasu saka, ba kamar yadda na saba barinsu su zazzage buhun kayan a ƙasa ba. Dana tsayar da sanwar miya, nima sai na shiga bayan gidan nayo wanka, nayi wankin tsumma. Wajajen magriba na haɗu da kaila a tsakar gida, ni kuma na fito daga baya da tukunyar miya a riƙe.
"Shanono Sani ya baki dubu uku ko?"
E ya bani.
"To sai ki jalauta kuɗin abincinku na wata guda kenan. Sai kisan yanda zaki tanana ya kai muku. Kina sane da batun zaman farko a kotu gobe ko?" Numfashi na ja.
E ina sane Allah ya nuna mana. An gode Allah ya saka da Alkhairi " Na wuce ciki abuna.
Ni fa a wannan daren Wallahi masu karatu banko runtsaba, nayi kukan harna gaji. Na yi tashin hankalin, har zazzaɓi sai da ya ci nasarar kama ni dan farbaga......✍🏻





_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_

_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_

*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*


*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S

*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224

*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*

*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*

*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*

*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*

*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*

sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*

KAMARSU👇🏻👇🏻

*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*

DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 19



Washe gari sassafe ni da yaran muka fice a gidan. Basu ci gaba da zuwa makaranta da islamiyya ba sai gobe in Allah ya nuna mana. Ni kaina ba lalle bane in iya zuwa school yau ba. Dan zazzaɓine magashiyan a jikina, ga wani irin sanyin mashasshara da nake ji. Gidan Yaya Use muka wuce. A tsakar gida na same su harda Baban yara. Yaya Use tana raba ma yara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login