Showing 18001 words to 21000 words out of 68990 words
Chapter 7 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
biyar. Wannan shine labarin halin dana shiga a baya" kai na jinjina nace.
Yaya batun komawarki makaranta ya akayi kika samu wannan damar, har kike kan matsayin da kike a yanzu?" Dariya tayi mun, idanunta sun yi jawur.........
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 6
Batun komawata makaranta ya samo asaline ta dalilin Hajiya Hari mai gidan abincin da nake yi ma wanke_wanke. Wata farar rana da bazan mance da'ita ba itace ranar da hajiya Hari take shaidamun ta samomun aiki a gidan wata Hajiya ƴar boko ce, kuma ta kasance mai son tsabta. Ganin tsabtata ne yasa ta zaɓeni a inje can gidan nata in yi aiki. Za'a dinga biyana albashin nera dubu biyar. Wannan labari sai naji tamkar in zuba ruwa a ƙasa in shanye dan murna. Hajiya Hari ta kaini gidan wannan Hajiya ƴar boko ta damƙani gareta.
"Habiba kin yi karatune, ko kuma matar Aure ce ke a zaune a gida?" Kafin in ce wani abun Hajiya Hari ta tari numfashina da cewa.
"Bazawarace nan mai ƴaƴa uku. Aurenta uku zaman yaƙi yiwuwa, shine ta fito neman na kai, ko dan bukatun yau da kullum" Numfasawa wannan Hajiyan tayi kawai, sai cewa tayi."
"Kinason komawa makaranta ne, ko me kika tsarama kan ki?"
Inaso Hajiya, dan auren ya gama fice mun a raina." Na bata amsa da haka. Ta umarceni gobe in zan zo in tawo da takadduna zata gani, kuma tayi mun alƙawarin zata taimakamun. Ashe wannan Hajiyar gidauniyace da ita domun tallafin mata da basu jari, masu son komawa makaranta ta sasu a makaranta. Ko da na dawo gida bance ma kowa komai ba, washe gari na kai ma Hajiya Boko takadduna ta gani, ta ajjiye a wajanta. Wata biyu da soma aiki a ƙarƙashinta na samu gurbin karatun likitanci a jami'ar Jos. Lokacin da zan tafi mahaifina ya dage akan shi ba da yawunshi ba, za'ace ya barni na tafi karuwanci Jos. Sai da amininshi maƙocinmu ya dinga bashi baki. In baku a taƙaice Amininshi ne ya bani umarnin tafiya tare da shi mun albarka. Kunji yadda akayi na zama haka kenan." Halima Bawa tace.
"To batun aure kuma fa Habiba Bala tunda dai yanzu duk namijin da zai aureki ma sai ya shirya?" Dariya mu ka yi dukka, Habiba Bala tace"
"Ina da tarin tulin zawarawa a ƙasa wanda suke jin kamar zasu mutu a kaina tsabar so. To ina lallaɓawa dai in sha Allah akwai wanda nake ganin kamar zamu iya dai_daitawa, sai dai yawan shekarunshi ne dai yake tsorata ni. Duk da nasan nafi ƙarfin ƴan matasa haka waɗanda da kadan suka haura arba'in." Hirarmu dai haka tai ta tafiya. Mu yi sallah mu dawo mu zauna mu sake baje hira. Sai da mu ka kusan raba dare muna hira, daga ƙarshe duk a ƙasa mu kai bacci saman kafet. Washe gari da rana Habiba Bala ta fita damu muka sake ziyartar sauran ƙawayenmu, ta kaimu shopping mall tayo mana siyayya sosai, sai mahriba muka dawo gida. Bayan munci abinci mun yi sallar Isha sai na ɗan shiga tattare kayana dan gobe da wuri nake son shiga Jos, ta gida zan sauka in tawo da yaran.
"Shanono kar kice na rainaki ƴan kayayyakinane nayi miki kwalimarsu, atampopi da ƴan ƙananan kaya na shan iska, da fatan kina so ko? Ke kuma Halima Bawa ga wannan babu yawa" Ta miƙa mata kuɗi ni kuma ta miƙo mun babbar leda, baki a yashe nace.
Gaskiya na gode sosai. Kin ji ki da faɗe Habiba Bala ai wanda ya fika ya fika. Kinga na ɗan samu na sawa, gashi kishiya za'ayo mana dama. Nagode sosai Allah ya bar zumunci" Kuɗi ta kuma bani, na dangane da batun komawa karatu ta cika mu da goma sha tara ta arziki. Washe gari ta fita damu, ni a titi ma na samu motar Jos na shiga, su kuma suka wuce zata kai Halima Bawa tashar Gombe. Idanu na lumshe motarmu sai shatata uban gudu take yi a titi. Mamaki nake yi duk da ba wannan bane na farko ba, Kaila ya saba nuna mun halin ko in kula, duk inda zani baya hanani, bazai kuma kirani a waya ba ko da shekara zanyi ban dawo ba. Ya kamata in san abunyi tun kafin Kaila ya gaji da bani ɗakin kwana da abinci ya koroni rayuwata ta sake tagaiyara a karo na biyar. Amman ba lallai abinda nake tunani ya yiwu harya tabbata ba, domun bani da wata madogara sai Allah, bani da mai taimakona ƙila iyayena su gwasaleni su ƙi ban goyon baya ma. Kaila dai nasan ba sona yake yi ba balle kishina ya ratsa ƙirjinshi ya hanani cikar burina. Wannan burin burine wanda ya daɗe da samun muhalli mai kyau a zuchiyata, mahaifane suka ruguje mun burina da nake mafarki. Kuma ba wai na yasar da burin dan son raina bane, face dan bani da yanda zanyi, bansan ta ina zan soma ba. Amman lokaci yayi da zan soma koma ta inane da izinin Allah, kuma inna soma in sha Allah sai na idasa zan tsaya, abu ɗaya ne zai yi mini cikas wannan cikin dake jikina, amman zan jinkirta har zuwa lokacin da Allah zai saukeni lafiya."
"Hajiya mun iso fa, ke kaɗai kika rage a motarnan" Cewar direban motarmu. Sakkowa nayi ina sauke ajjiyar zuchiya. Keke napep na tara zuwa layin idi mai barkono. Na kuwa taki sa'a a kofar gida na samu Inno ita da su Sulaiman, Shafi'i na riƙe da buhun bararta. Balaraba tana ganina ta rungumeni tana murnar ganina, Sani sai dariya yake yi na murna. Nima naji daɗin ganinsu sosai. Inno tace
" Ƴar nema du wannan murnar ganin uwar taki ce lallai kuwa. Dama Amina ce tawa da su Sulaimanu."
Inno bara zaku tafi, ni nama yi tunanin ba lallai in same ku a gidan ba"
"Wallahi kuwa yaranki ne suka makarar dani, amman ai da tuni ina can, Baffanku tun shidan safe suka fice da su Habu da Indo. Yarannan dai ki tafi da su Balaraba, Amman Shafi'i da Sulaimanu, da sani zasu rakani bara, inna taso komai dare zan dawo miki dasu.." Su Amina suma suka kafe sai sun bi inno .Turus nayi domun akwai lokacin da Kaila ya taɓa wucewa ta masallacin ƴan taya ya ga su Sulaiman tare da Inno suna bara yaran sun bita daga gida lokacin ana hutun makaranta. Ranar nasha baƙaƙen maganganu da zagi iri_iri, kuma yayi mun mugun gargaɗi akan kar hakan ta sake faruwa ba za'a mayar mishi da yara mabarata masu matacciyar zuchiya ba. Ni kuma bazan iya hana mahaifiyata tafiya da yarana ba. Koma yaya take uwa uwace.
To shikenan Inno sai kun dawo, ni zan tafi gida. Kwa gaishe da Baffa." Tare muka fito titi Inno na cogala ƙafarta, Inno irin masu ƙafa ɗaya da rabinnan ce, a duƙe take tafiya hannunta ɗaya dafe da ƙafar mai lalura. Shi kuma Baffana makawone, a wajan yawon bararsu tun a Shanono suka haɗu Allah ya ƙaddari aurensu. Mun zauna a garuruwa da dama wanda yawon bara ke kaimu. Amman tunda muka zo Jos Baffa yaji sanyi da daɗin garin yace yaga wajan zama, a lokacin muna yara Yaya Use ce kawai babba a wannan lokaci. Keke napep na tara muka zo muka wuce su, Su Sulaiman suna ɗaga mun hannu. Dan Inno basa hawa abun hawa duk inda zata a ƙafa take zuwa tana yi tana bara, Indo na mata waƙa. Ina jiyo sautin muryoyin su Shafi'i suna ma Inno amshin waƙar bara. Wacce muma muka taso da ƙwarewarta. Hawayene ya gangaro a kumatuna, da sauri nasa gefen mayafina na sharce hawayen. A bakin layinmu na sauka na ƙarasa. Tun daga baƙin ƙofar shiga cikin gidan nake jiyo muryar Ba Rammai Mahaifiyar Kaila, da hausarta irin ta Hausawa mazauna Akwanga , maganarta dama a sama take yi da tsawa da hargowa, kuma ba faɗa bane. In kuwa faɗan zata yi duk maƙota sai sun fito. Gabana ya yanke ya faɗi dan bata da sauƙi musamman a kaina. Ajjiye kayana nayi a ɗaki na shigo da sallama cikin gidan. A kan taburma na samu Baba Rammai da Kaila, Hajiyayye tana daga bakin ƙofarta, Hindatu kuma tana aikin sharar tsakar gida, yaran na wasansu."
Sannu da zuwa Baba Rammai kece a tafe, maraba" Ban kai da zama a kan taburmar ba, cikin hausarta ta Akwanga tace.
"Yau ga burun ubaaa ni kike cema a tafe sai kace sa'ar gurguwar uwarki Inno? Lallai Kaila ka yi ƙoƙari da kaci gaba da ajjiye wannan tsohuwar bazawarar da taga maza kala_kala." Turus nayi a durƙushe a gabanta, ji nayi kamar ta ɗauki wuƙa ta luma mun a cikina. Wai mai Hausawa suka ɗauki kalmar zawarci ne da aure_aure? Ni naga ko karuwai basu cika fuskantar irin matsin da Bazawara ko mace mai caccanja miji take fuskanta ba. Buɗar bakin Kaila sai yace mata.
"Wallahi Rammai sabida yaranta nake ɗaga mata ƙafa, bana son in ɗauketa a kansu dan babu wanda zai kula mata dasu sai dai itan. Wannan dalilin ne yasa na bata ɗakin zaure ita da yaran, ita kuma Bilkisa na bar mata nata kuma yafi ko wanne daki girma" Haƙiƙa maganar Kaila yayi dai dai da zafin fitar rai daga gangar jiki. Wato ni amfanina ciki da rainone, da ba dan hakan ba da tuni a karo na biyar ɗin ma koroni za'ayi. Ya Allah ka bani jumurin dauriyar ci gaba da zaman gidannan ko dan in bama yarana tarbiyyar data dace, sune kaɗai sanyin idaniyata, Dauda ma dana fita a gidan mahaifinshi na barshi ina mishi adda'a da fatan nasara a rayuwa. Iska na fesar na ɗago muka haɗa idanu da Hajiyayye wani irin Murmushin nasara take yi mun, Idanuna ya kaɗa yai kamar gauta. Da ƙyar na haɗiye wani kakkauran yawu kana nace.
Ina kwana Baba Rammai kin zo lafiya?" Sai da tayi tsaki sannan tace.
"Su yaran fa suna ina?" Kaila daya kafeni da mayaudaran idanunshi waɗanda ada suke da matukar tasiri gareni yace.
"Ai na ɗauka ta gidan zaki biya ki tawo dasu ko? sai nagan ki ke kaɗai ya'isa haka ai ko. Ni kar aje ma a dinga fita ma da yara yawon tumasanci suje zuchiyarsu ta mutu su ce sunga sana'a" Duk dauriyar da na dinga yi gudun kar in yi kuka a gaban kishiya, da facala, sai da zuchiyata ta gaza tayi wani irin raunin da bansan sanda na fashe da kuka ba. Hauwa'u na sauke na dangwarar musu na tafi ɗakina. Ina jiyo shewar Hajiyayye, ita kuma Baba Rammai ta shiga farfaɗan miyagun maganganu akan bara, ina ji tana cewa daga ranar kar a kuma kai mata jikoki gidan guragu da makafi kar a koya musu maula. A kan katifata na kwanta a rigingine ina kallon rufin ɗakin, hawaye kuwa sai makanta ganina yake yi. Wallahi bansan rashin darajata a rayuwar Kaila ya kai hakan ba, yau da ba dan gudun tsinuwar iyaye, da gudun tofin Allah ya tsine daga bakunan mutane ba, wallahi da babu abinda zai sa in ƙara ko awa ɗaya a cikin gidannan"
"Ke Shanono dan wulaƙanci Rammai tana magana bata sallameki ba shine kika dangwarar mun da ƴa kika yi tafiyarki, wato ga mahaukaciya ko? To nagode Allah mahaifiyata ba mabaraciya bace mai kwana a bakin masallaci ba. Yara kuma ki yi waya a dawo mun dasu. Sannan muddin kinason kici gaba da amsa sunan matar Kaila, ki je ki tsugunna ki ba Rammai haƙuri har sai ta hakura sannan. Abu na gaba wannan kayan da kika saka a jikin ki ranar da zaki Bauchi ki fito mun dasu ki kawo mun, muna ɗakin Hajiyayye " Yana kai ƙarshen maganarshi ya fice kamar kububuwa. Sai da nayi kukana ma'ishi na kusan minti ashirin, sannan na share hawayena zuchiyarnan a cunkushe babu wani sassauci dana samu. Maganganun Kaila na ɗazu dana yanzu su suke ta faman yi mun amsa kuwa. Jakata na buɗe na zaro wannan kaya da Inno ta bani na fito. A tsakar gida na samu Hindatu tana ta waƙar kujerar tsakar gida.
"Umman Sulaiman sannu da dawowa, ina aka baro mana su Sulaiman?"
Yauwa sannu." Iyakar abunda nace mata kenan, ai tasan inda suke kuma duk abinda aketa taunawa ba tana ji ba."
"Tohh iko sai Allah wai na kwance ya faɗi. Me yayi zafi shi ba wuta ba, ai bani na kar zomon ba rataya aka bani." Shigewata nayi ɗakin Hajiyayye da sallama. Hajiyayye na tsugunne tana haɗa ma Rammai tea. Ga yarinyar Hajiyayyen a cinyarta, Hauwa kuma tana yashe a ƙasa, harta soma ɗan kuka, Kaila yana harɗe a kujera yana aikin daddanna wayarshi. A gaban Baba Rammai na durƙusa bakina na ɓari.
Baba Rammai dan Allah kiyi haƙuri. Nayi kuskure bazan sake ba in sha Allah, Allah ya huci zuchiyarki." Ai nan tace ina wuta ta tsoma ni. Ta dinga faɗa tana ihun da babu makawa maƙota duk suna jiyowa, ta dinga dawo da bara bana. Ai rannan da tazo ma banko yi mata fara'a ba bani da kunya dake na saba da maza, kuma idona ya buɗe da rashin kunya irin na yara ƴan jagora. Ni dai kaina na ƙasa ina haɗiɗiye zuchiyata, Hajiyayye ranta fes dashi har Murmushi take yi, ni dai ban gushe ba har sai da tace ta haƙura na mata godiya, wajan Kaila na wuya.
Kaila ga kayan" Bai ɗago ya kalleni ba, sai yace.
"Hajiyayye karɓi kayannan, shikenan rigima ta ƙare dai ko?" Ni kuwa binsu nayi da idanu cikin ɗaurewar kai ban gane rigima ta ƙare ba, rigima tayi akan kayan shine ya sa na kawo dan ya bata ita tasa ko me suke nufi?"
"Rigima ta ƙare Baby, ai kayanne suna da tsada super ce fa kuma babbar" Kallon Hajiyayye kawai nayi na sauke kaina ƙasa. Rammai ce tace.
"Ɗauki ƴarki kuje ya'isa haka kuma" Dama zaman ya gundureni gudun kar in kuma yin laifine yasa na zauna ina kwasar baƙin ciki, Hajiyayye kamar zata koma cikin jikin Kaila, shi kuma sai wani lallashinta yake yi. Hauwa na sunkuya na ɗauka tare da fice wuf a ɗakin, ina shiga ɗakina na kuma ɓallewa da kuka. To mai Kaila yake nufi ne dani, meye dalilin da zai karɓarmun zani ya ba matarshi alhalin ni bashi ya sai mun ba? Kuma wai har ake faɗin rigima ta ƙare, ita kuma tana faɗin kayanne da tsada super ce. Dole na ture wannan damuwar domun akwai matsalolin da suke da mahimmanci fiye da wannan su suka fi damuna. Haka na wuni cir a ɗakina a takure, ragowar soyayyen naman sallana naci na sha ruwa, Hauwa kuma bacci take yi. Wajajen biyar na yamma dai na daure na fito tsakar gidan dan ɗaura girkin dare, Hauwa sai kuka take yi na rasa kukan na meye dan har jikinta ya soma zafi. Ni kaina jikina ya ɗau zafin zazzaɓi kau, ga wani irin mugun ciwon kai dake damuna. Zulaihat na aika shago ta siyo mun omo. Ni kuma na zauna ina jiran wuta ta ruru, Baba Rammai tana kwance tayi bacci a kan taburmar, Hajiyayye Hindatu kuwa sai shewa suke yi.
"Gobe nima yace za'a haɗa da ɗakina ayi fentin. Kuma zai sake mun kujeru, kinga inna siyar da wannan kujerun na ɗakina, nima sai in yo suturu duk da jiya ya kawo mun kala shidda. Amman zan ƙaro wasu ni da tsinanniyar amaryar tashi sai dai mu zuba, bata isa ture mun matsayina a zuchiyar Kaila ba" Cewar Hajiyayye kenan. Hindatu tayi shewa suka tafa tace.
"Ai naga sai bala'i kuke yi, jiya ma fa haka kika fashe mai wayarshi sai wata ya siyo. Naga duk ya rikirkice sai lallaɓaki yake yi" Ni dai ina jin hirarsu amman harkokin gabana nake yi. Zulaihat ce ta shigo ta kawo mun omon dana aiketa. Ina tsaka da tsintar shinkafa na jiyo muryar Kaila daga zaure yana rangaɗamun gigitaccen kira. Kafin in miƙe har ya shigo cikin gidan abunka da tashi da ƙyar zama da ƙyar. Ihun kiran sunanane ya farkar da Baba Rammai. Bol yayi da tiran dake hannuna Allah yaso na juye rabin shinkafar a roba. Tirannan ya faɗi ƙasa gwangwarangwannnnnnnn...... Ƴar ragowar shinkafar ta tarwatse. Ya cika gidan da ƙara yana huci yace mun.
"Sabida kin ɗaukeni ɗan iska shine zaki tura mun yara gidanku su dunga fita yawon bara kamar ni Shanono? Yanzu na dawo daga ƴan taya, wucewa nazo yi Shafi'i ya riƙe mun riga yana ce mun babiye Allah ba tare da yasan ko wa ya riƙe ba, ina juyowa ya ganni, Sulaiman shima yana can wani kirista na bashi sadakar nera ɗari. Dan iskanci da raini sau nawa na faɗa miki kar a sake zuwanmun da yara wajan bara?" Ni dai tunda ya soma wannan tonon sililin jikina ke rawa, ada in ma masifar ce a ɗaki yake yi mun kisan mummuƙe, amman a yanzu a gaban kowa tozartani yake yi, yau na ji na mugun muzanta a idanun kishiya da, facala. Salati suka shiga rabkawa dukka Baba Rammai harda tattafa hannaye. Hakan ya kuma tunzurashi yace.
"Kar a kuma ɗaukar mun yaro a kai mun shi gidan makafi ni dai na faɗa miki. Ke daya zame miki dole sai ki je. Kuma yanzu_yanzu ki je ƴan taya ki ɗakko mun yarana wallahi in ba haka ba a gidanku zaki kwana, bara harda su Balaraba an baza su a titi ana son kashe musu zuchiyarsu. Wannan wanne irin masifa ce nayi ni dai nadamar auro ki da nayi, wannan ai kece kara da kiyashi." Baba Rammai tace.
"Ɗaukar marar sani ba. Ai ni tunda kace mun aurenta huɗu nasan ba za'ayi abun arziki ba. Amman dake a lokacin sun yi ma asiri kana saurayinka da kai zarkaɗeɗe a rasa wacce zaka auro sai bazawara mai Aure huɗu mai yaro. Ke kuma ai sai ki bi umarnin mijinki ki je ki ɗebo mishi yaranshi tun kafin