Showing 24001 words to 27000 words out of 68990 words
Chapter 9 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
Bayan mun kammala komai Baba Rammai tace a kai ɗakin Hindatu a ajjiye abincin. Yaya Use ce ta shigar da komai, a tsakar gidan suka zauna suna cin nasu abincin. Ni kuma na shiga wanka, ina fitowa na shiga ɗaki na saka riga da zani na atampa wanda Habiba Bala ta bani. Babu abinda na shafa a fuskata. Dirin motoci da ihun yara na jiyo a dai_dai window na suna faɗin
"Kayan amarya ek_ek" Sai naji zuchiyata na son leƙawa in ga waɗanne irine matan da suka tawo jeren. Ai kuwa da sauri na matsa bakin windon na leƙa. Wasu manyan mata ƙosassun ƴan boko na gani a tsaye a bakin motar kaya, sai turanci suke yi a tsakaninsu da juna. Kaila na hango cikin girmamawa ya isa garesu, sai ɗan guntun turanci suke yi mai, shi kuma yana zare idanu gudun kar su kai shi maƙura, dan ɗan turanci nashi bai wuce cikin cokali ba, shima ya iyane a sanadiyyar zaman shagon wani inyamuri a bayan banki, shagon takalma da jakunkuna. Kamar akan gidan suke yi mishi magana dai, dan naga suna kallon gidan suna yamutse fuska, ajjiyar zuchiya na sauke na bar windon. Su Yaya Use ne da Sabira suka shigo, a tsaye suka ganni da wannan riga da zani na atampa, rigar tayi mun yawa har wuyan na zamewa.
"Baƙin ku sun iso Tani, ni naji sai turanci suke ta zazzagawa a waje." Kafin in kai da magana muka jiyo sallamarsu da wasu muryoyi masu daɗi, daga ɓangarena Yaya Use ce ta amsa musu. Suka ƙarasa zuwa cikin gidan Baba Rammai da Hindatu suka tarbesu. Daga haka muka soma jiyo muryoyin maza da shige da ficensu. Yaya Use ce ta fita, ni ko waje na samu na zauna ina fama da marurun zuchiyata. Bata jima ba sai gata ta shigo.
"Tabb lallai Kaila ya ɗebo matar da tafi ƙarfinshi gaba da baya. Yarinyarnan da zai aura daga gani ƴar masu dashi ne. Kunga kaya irin na gani da faɗe kuwa. Hmmm daga kamfanin da aka sai kayan ma aka tawo da ma'aikata maza su suke gyara ɗakin. Ji nayi wata Baturiya tana faɗama Rammai." Baki ni dai na taɓe abina. Baba Rammai ce ta ɗaga labulen ɗakina tace.
"Ai ya kamata ace kin zo kin tarbi baƙi ko Tani? Sannan ki basu abincinsu sun shawo hanya" Da To na bita tare da yunƙurawa na tashi tsaye.
"Muje in taimaka miki ke da ba ishasshiyar lafiya ba" Harara Baba Rammai ta sakar ma Sabira, taja tsaki ta saki labulen tayi gaba abunta. A ɗakin Hindatu aka sauƙi baƙin, Hajiyayye tace dangin kishiya basu isa sun zauna a ɗakinta ba. Tun muna aikin abinci tayi ficewarta daga gidan, amman ba zata wuce maƙota ba gidan ƙawayenta. Da sallama muka shiga cikin abun mamaki a cikin baƙin babu wacce ta amsa sallamarmu sai Yes kawai suka ce mana. Dauriya na aro na yafa na zauna aka gaggaisa, Baba Rammai ta nuna ni da cewa.
"Hajiya kinga wannan itace uwar gidan Kaila. Amman bazawarace ya aureta." Naji zafi sosai, baƙin a wulaƙance suka shiga bina da kallo, ni ko murmushi nake yi, abinci muka gabatar musu da abun sha, kana muka fice a lokacin idanuna ya cika tab da ruwan hawaye. Sai zuwa yamma lis suka gama abinda ya kawo su, su kai mana sallama. Sai magriba su Yaya Use suka tafi bayan sun yi mun girki suma sunci, Sabira kuma ta ɗan jima da tafiya itama zata je ta kula da nata iyalan. Da su Sulaiman ta sake tafiya. Ina zaune muna cin abinci ni da Hauwa nake jiyo hayaniyar Kaila da Hajiyayye a tsakar gida, wannan karon hayaniyar tayi tsamari, dan ina jiyo yanda Kaila ke kutuntumama Hajiyayye ashariya, dama Kaila gwanine wajan rashin daraja, akwai shi da ruwan ashariya. Da ƙyar dai fitinar ta lafa ni ko ina ɗaki a kwance abuna ban ko leko ba ƙofata ma rufe take na saka sakata. Haka ranaku su kai ta shuɗewa ana saura kwana uku biki, gida ya cika da ƴan Wudil dangin mahaifin Kaila, da ƴan Akwanga dangin Baba Rammai. Ƙannen ƙanin Mahaifin Kaila ne kacal suka sauka a ɗakina, yara kuma suna gidan Sabira acan suke kwana. Aikin girki kuwa nice gaba_gaba taimakamun kawai jama'ar bikin ke yi, amman in ban ɗaura sanwa ba babu wanda zai fito ya ɗaura. Ana jibi ɗaurin aure aka tashi mutum huɗu biyu daga ɓarayin Baba Rammai , biyun kuma ƴan Wudil ne domun kai akwatin Amarya wanda dama ita yaba kuɗin ta sai komai domin irin yanda take ba gaye hakkinshi. Sassafe suka kama hanya domun a ranar suke son dawowa, basu suka shigo gida ba sai taran dare. Washe gari aka shiga hidimar biki gadan_gadan wanda a ranar Kaila da mutanenshi suka nufi Zaria acan zasu kwana in an ɗaura aure su tawo da Amarya da danginta. Ranar juma'a gida ya cika da maƙota ƴan uwa da abokan arziki duk sun hallara, Yaya Use da Yaya Karime tun taran safe. Mu mu kai ruwa mu kai tsaki a girkin ƴan biki. Tuwon shinkafa miyar taushe mu ka yi, sai jallof ɗin shinkafa da kaji da akai ma masu kawo amarya da abokan ango. Saye nake cikin wani lashi ɗinkin doguwar riga, yana daga cikin kayan da Habiba Bala ta bani, babu ko kwalli a idona balle in shafa mai. Yara kuma nasa musu kayan sallansu, abunka da yara sai murna da ƙiriniya suke ana biki a gidansu. Hajiyayye ma ɗakinta cike dam da ƴan uwanta da ƙawayenta na anguwa. Taci ado kamar itace Amaryar, ƙawayenta sai koɗata suke faman yi, an yi saloon, an yi ƙunshi, duk da na sallah da tayi bai gama fita ba amman akai akayi mata, har me kwalliya ƙawayenta suka ɗakko mata. Misalin ƙarfe shida da rabi na yamma motocin kawo Amarya suka soma tsayuwa a dai dai bakin windo na. Cikin ƴan mintuna yiriri_yiriri ya shiga tashi a kofar gidan. A wannan lokacin ina kwance ina hutawa ne, su Yaya Use kuma suna cikin gida suna rabon tuwon dare. Tuwon masara miyar bushasshiyar kuɓewa su ka yi. Ina jiyo takun dangin Amarya, a kunnena najiyo wata ƴar tsohuwa tana faɗin ki shiga ɗakin ki da ƙafar dama, ki yi adda'a kamar yadda muka shigo dake gidannan Allah yasa sai dai a fitar da gawarki. Murmushi kawai nayi ina dafe da cikina dake mun juyin waina. Bayan hayaniyar mata ta lafa ne na soma jiyo hayaniyar Kaila da abokanshi. Ina jiyo sallamarshi Amman bakina yayi nauyi na kasa amsawa sam.
"Shanono ki sa yara su shigar mana da Abincinmu cikin gidan Tanimu acan zamu ci, yanzu dai sallah zamu je mu yi" Da ido na bishi, sai naga kamar an sake Kaila tsabar yanda yake ƙyalli da sheƙi, saye yake da farar shadda sol sai maiƙo shaddar take faman yi, ɗinkin malum_malum na matasan zamani ce a jikinshi, kanshi saye da hula zanna bukar, ƙafarshi saye da takalmi haf koba baƙi, ga baƙin zobe ga baƙin agogon fata, idanunshi kuma saye da sabon farin tabarau, sai ƙamshin shi na tun asali yake yi ƙamshin turaren lailatus sahra, duk sanda na shaƙi wannan ƙamshi sai ƙwaƙwalwata ta shiga tariyomun faifayin bidiyon irin romon soyayyar da muka dangwala ni da Kaila. Kai kawai na ɗaga mishi halamar naji, shi ko ko a jikinshi bai damu da yasan meke damuna ba ya saki labulen yayi gaba. Zafafan hawayene suka gangaromun, sallamar Hajiyayye ne yasa nayi saurin goge fuskata, na amsa mata sallamarta. Sai gata ta shigo cikin wata jar sabuwar atampa mai kyau ta sake shiga a karo na uku. Hannunta riƙe da ƙananun bokatan roba har uku. A bakin katifata ta dure mun.
"Umman Sulaiman ga naki ke da jama'arki, dangin Amarya ne suka bamu"
An gode Allah ya ba da zaman lafiya" Baki ta taɓe tace.
"Hmm har wani roƙon zaman lafiya ma kike yi? Ni ko zuchiyata saura ƙiris ta ƙone ma baki ɗaya. Kaila ya je ya kwaso mana ƴar gidan masu kuɗi." Murmushi kawai nayi mata. Ta ja dogon tsaki ta fita abunta, tare da Yaya Use su ka ci karo, ita zata fita, ita kuma zata shigo.
Ga kayan cin_cin nan in ji dangin Amarya, ku ɗibi naku" Bubbuɗe robibin tayi. Ɗaya cike da cin_cin ɗayar cike da alkaki, ɗayar cike da nakiya sai ƙamsin kayan ƙamshi take zabgawa. Leda Yaya Use ta ɗakko ta zuba nata dana Yaya Use, ta ƙulla na Sabira dana Inno, sauran ta bar mana ni da yara. Ƴan uwa masu daɗi sai bayan isha suka mun sallama suka tafi, bayan Yaya Use ta sallami Kaila da abokanshi da abinci. Ni ko ina yin sallar isha na ɗan ci tuwo na ba Hauwa taci ta ƙoshi, dani da'itan a wajan mu kai bacci ko hannu ban wanke ba, balle in wanke bakina. Dake na gaji ainun ban farka ba har sai da asuba, kuɗin cizo sun sha jinunmu sosai hakama sauro. Mayar da Hauwa nayi kan katifa ni kuma na fita dan ɗauro alwala. Mata ƴan biki duk sun firfito anata alwala, nima alwalar nayi na gabatar da salla, kana na fita na bi ɗaki_ɗaki ina gaisawa da dangin Kaila. Da gari yayi sha kuma na dafa tea na toya wainar ƙwai na dangin Amarya. Yaran ƙanwar Baba Rammai ce suka kai musu. Mu kuma ruwan bunu muka sha da biredi. Ni dai ina gamawa na yi komawata ɗakina. Yara basu suka shigo gidan ba sai wajajen goman safe Sabira ta tusosu gaba suka tawo. Ina zaune zaman taɓaro a ƙasa Suka shigo.
"Uwar gida sarautar mata, banga kin yi wanka kin fito shar dake ba. Na hango wulgawar Hajiyayye ta sha kamfala da ɗankwalin ashoke, ke ko ina ƙunshe a ɗaki. Balaraba ce ta zauna kusa dani.
"Umma ina kwana?"
Lafiya lau ƴan albarka" Nan suka shiga gaisheni ɗaya bayan ɗaya.
Maza ku shiga cikin gida ku gaishe da iyayenku." Da sauri suka fita harda rige_rigensu. Ledar kayan filawa da Yaya Use ta ƙulla mata nata na jawo na miƙa mata.
Ga naki kayan garar Amaryar kwa tauna ke da yara. Ina so in faɗa miki ma jibi zamu yi tafiya dasu Inno zuwa Shanono can garinmu, bikin ƴar ƙanwar Inno."
"Dukka wannan garar amarya leda guda haka, ai yayi yawa Tani. Murmushi nayi nace.
Haba Sabira ai ko duka na zuba miki kin cancanci hakan ne. Kuma kinga fa bokatannan cike aka kawo mun, wannan amarya akwai maiko a hannun iyayenta gaskiya " Dariya tayi mun tace.
"Gaskiya kam ai ko da ganin danginta, da gani basu san meye talauci ba ma sam. Batun komawar yara makaranta fa? Naji ana sanarwa a gidan rediyo cewar ran monday makarantun gwamnati zasu koma karatu, to yaran zaki barsu a wajena amman ko? In an Koma makaranta sai su soma zuwa kafin su dawo, ga islamiyya ma ran monday zasu koma" Ni kam babu abinda zance da Sabira da mijinta sai dai adda'ar kairiro, domun maƙotane na gari sosai. Shi ya soma kama hannun su Sulaiman ya jefa su a makarantar gwamnati mai suna islamiyya pilot primary school makaranta ce ta gwamnati, to bayan yayi hakan ne, Kaila ya sai musu fensir da takadda...........✍🏻
MRS BUKHARI
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FADO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 8
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU👇🏻👇🏻
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻
Hatta inifom mijin Sabira ne ya ɗinga musu, da basa zuwa ko ina sai gararamba a unguwa. Haka zalika shi ya sanyasu a islamiyya irin ta cikin anguwa, duk sati suna tafiya da nera hamsin, shima wannan ko da Kaila yaga suna zuwa bai ce dani komai ba, nima ban tanka mishi ba. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Sabira a karo na barkatai nace.
To zan bar miki su, zan haɗo inifom ɗinsu Sani zai kawo miki. Zaki sha bari_bari kenan bakin ki sai yayi tsini ashe kafin in dawo. Dariya tayi tace.
"Su Mustapha da Umar fa da kike ganinsu wallahi sun fi Shafi'i da Sulaiman rigima, Sani shi bai da yawan ƙiriniya magana ma bata isheshi ba. Kullum a cikin raba dambe nake."
Hmm suma ko da yaushe aikin Kenan." Mun jima muna tattaunawa kafin muka fita domun ɗora girkin rana. Ƴan Wudil kam har sun fito tsab zasu koma, ƴan Akwanga suma ina ji suna cewa da sun yi azahar zasu tafi. Sallama nayi ma ƴan Wudil, muka shiga hidimar abincin rana. Girkin dangin Amarya daban Sabira tayi shi. Tuwon shinkafa miyar ganye tayi musu da kaji. Ita tayi komai da komai, kuma ta ɗauka ta kai musu. Bata jima ba ta fito. Ƴan Akwanga suna cin abinci suma suka kama gabansu, harda Baba Rammai dan an bogo waya an yi musu haihuwa. Sabira da Hindatu ne suka yi wanke wanke da gyaran gidan. Fes suka wanke tsakar gidan yayi kyau sosai. Misalin huɗun yamma muna tsakar gidan ina ɗaura sanwar miyar dare. Sai ga dangin Amarya su biyu, sun sa Amarya a tsakiya. Suna zuwa in da muke suka tsaya.
"Bayin Allah muna neman ɗakin uwar gidan gidanne, zamu kai amarya bisa doron al'ada." Sabira ce tayi musu jagora zuwa ɗakina ta nuna musu taburma. Ni kuma na kirawo Hajiyayye da Hindatu, tare muka shiga ɗakin, na shiga na same su sai yamutse fuska suke yi, ba shakka zarni ne ya ishesu. Bayan an yi ƴan gaishe_gaishe wata farar mata tace.
"Wacece uwar gidanne a cikinku?" Hindatu ce ta nuna ni tana dariyar ƙeta, ta nuna Hajiyayye a matsayin ta tsakiya. Baki suka sake su kansu, ƙila sun yi tunanin mai aikin gidan Kaila ce ni, dan sun gagganni face_face ina shan uban aiki kamar jakka tun zuwansu."
"To uwar gida kece babba ga Bilkisa mun kawota domun ku gana, ba Domin mun kawo muku amanarta ba, amanarta na hannun wanda ya rabota da garinta da ahalinta. Bilkisa ki buɗe fuskarki abokan zamanki su ganki ki gansu" Bilkisa tana saye da wata lafaya mai adon duwatsu faca_faca hannu tasa tayi baya da mayafin. Wallahi bani ba hatta Hajiyayye da take jin ita shahararriyace sai da ta ƙware. Bilkisa gaskiya tana cikin sahun kyawawan matan hausa fulani, uwa uba gata da haske sosai, ga iya kwalliya da zabin kalar daya dace da launin fatarta.
"Ina yininku Anty da Anty?" Wani ƙwallon kishi na haɗiye nace.
Lafiya lau Amarya Bilkisa ya baƙunta?" Murmushi kawai tayi mun bata ce komai ba. Iyakar abinda ya faru kenan, sai shaida mana cewar yanzu zasu tafi da suka yi. Fatan sauka lafiya nayi musu Hajiyayye dai in kun tanka ku masu karatu to itama ta tanka, tunda Bilkisa ta buɗe fuskarta Hajiyayye ta daskare a zaune. Ana cikin haka Kaila yayo sallama ya shigo, sai faman dariya yake yi, yana doro.
"Anty Zinaru baku wuce ba ashe?" Sai wani dariya yake yi harda wani sin_sin da kai. Ita wacce ya kira da Zinaru tace.
"Munkaila yanzu zamu tafi, ka kula da Bilkisa sosai kar ka manta da sharaɗin da Mahaifinta ya gindayama tun kafin ma tafiyarku ma tayi nisa. Bayan kwana bakwai zata ci gaba da zuwa aikinta, an yi magana an gama mata komai aikin kawai zata soma zuwa." Dariya yayi yace.
"Babu ai komai Anty Zinaru ni dama ƴar bokon naso shi yasa na biyota kuma na aminta da komai. Zuwanta cikin rayuwata aikhairine mai girma, gidan zai ɗau saiti sosai, nifa yanzu ne na san nayi auren kece raini. Ina godiya sosai da karramawa" Nan su kai mana sallama suka fice, ni maza sun dena bani mamaki tuni. Hajiyayye ce tayi kasaƙe tana kwasar ruwan mamakin Kaila. Fitar Amarya da ƴan uwanta ke da wuya Hajiyayye ta miƙe tsaye tace.
"Aikin banza aikin wofi ni Kaila zai wulaƙanta sabida ya auro ƴar boko, wallahi zaman lafiyar Kaila da kilakin daya auro ya ƙare. Fuuu ta fice kamar kububuwa, Hindatu ta bi bayanta tana faɗin.
"Allah ya kyauta, wannan cin fuska dame yai kama ne ni ƴasu?" Sabira ta dubeni, nima ita nake kallo, murmushi nayi mata kawai muka koma bakin aikin mu, amman zuchiyata a cushe take ainun. Zuwa yamma gidan babu kowa sai mu mazauna gidan, yara suna gidan Sabira ta haɗe kansu dasu Mustapha sun tafi, Hauwa tana bayana. Ina kan yin shanyar kayan Hauwa dana ɗan ɗauraye sai ga Kaila ya shigo gidan, kici_kici da manyan ledoji yana shirin wucewa ɗakin Amarya.
Sannu da shigowa *Ango* Jin na kirayeshi da Ango yasa ya washe mun bakinshi har kunne.
"Sannu Shanono da hidima da jama'a fa" Murmushi nayi mishi, Hajiyayye tace.
"Inason yin magana da kai Kaila kafin ka shiga ɗakin Baturiya" Dubanta yayi yana nazartarta kafin yayi wani malalacin murmushi wanda ni nasan na muguntace.
"To yau dai kwanan Amaryane baki da hurumin da zaki ce dole sai kin yi magana dani." Yana kaiwa nan ya burma ɗakin Amarya ya rufo ƙofa garam. Numfashi kawai naja, ina gama abunda nake yi na yi alwalar magriba nayi shigewata ɗaki na danna sakata."
KAILA:
Yana shiga