Showing 33001 words to 36000 words out of 68990 words

Chapter 12 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

Ina biye dasu ina haki, ga ciki ga goyo, ga numfashina na fita da nauyi. babban Asibitin gwamnati na Shanono muka shiga. Ganin yadda Yaya Karime ta ruɗe da kuka. Ba shiri ma'aikatan jinya suka amshi Dauda suka shige dashi wani ɗaku. Mu kuma akace mu jira a waje"


MRS BUKHARI✍🏻
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE...
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 10








*INA MIƘA DUMBIN GODIYA GA DUK ƊAUKACIN MASOYA WANNAN LITTAFIN. HAKIƘA SAƘONNINKU SUNA ZUWA GARENI. KUMA INA GANIN WAYOYINKU DAGA GARI_GARI ƘASA_ƘASA. WAƊANDA BAN SAMU DAMAR ƊAUKAR WAYOYINSU BA, SUIMUN UZIRI ABINNE DA YAWA. WAƊANDA BAN SAMU DAMAR BASU AMSOSHIN WASIƘUNSU BA, SUIMUN AFUWA SUMA DAN ALLAH. ZAN AJJIYE LINK ƊIN GROUP ƊIN LITTAFIN NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA, MAI SON KASANCEWA TARE DANI SAI YA SHIGA. KU SANI INASONKU MASOYANA A DUK INDA KUKE.*




Kaila:


wani irin farin ciki Kaila yake ciki marar musaltuwa. Tun dawowarshi da asuba, ya dawo ya samu Balkisa ta fesa ado da wata jar atampa ɗinkin riga da siket. Kayannan sun zauna mata ɗas a jikinta, kirjinta ya bayyana sosai, sai wannan hasken Amarcin irin na amaren kwana ɗaya tare da miji take yi. Kaila na ganin Bilkisa a cikin wannan ado, tuni ya mance da takaicin ganin Tani da yayi a tsakar gida. Dan bayan ya gama magana da Tani, fata yayi a ranshi dama ace Tani kar ta dawo in ta fita ta fita kenan, ko kuma ya ji labarin motarsu tayi dungure babu wanda yayi rai. Da wannan mummunan tunanin ya shigo, ganin Balkisa ya yaye mishi dukkannin cunkushewar zuchiyarshi. Tuni ya washe bakinshi tare da ware ma Bilkisa hannunshi. Da shagwaɓa ta faɗa jikin Kaila, shima ƙamshin yake zubawa kafin ya fita Masallaci sai da yayi wankan soso bayan wankan Sallah. Kan gadon suka faɗa suna dariya. Cikin so Kaila yace.
"Jina nake kamar nafi sauran maza sa'a. In ana cin ɓaure ba'a tona cikinshi Ɗanyan gwal, amman abunda zance miki shine kin sabunta mun jinina, kin sake mayar dani fresh. Dan ƙazantar su Shanono saura ƙiris ta shafe ni, ke kika ceceni. Matane gasu dai a gida, daga mai warin dauɗa da kuɗin cizo, sai mai warin baki. In Hajiyayye ta yi magana bakinta kamar shadda fa. Ke kuwa naji har yawunki ƙamshi yake yi" Dariya Bilkisa tayi na farin ciki. Ko wacce mace ta fi son mijinta a kalleta a matsayin TA FI SU, shi yasa da yawan mata basa iya takama maza burki in sun kwaso gulmar kishiya sun kawo musu. Sai dai tai ta zura miji shi kuma yana sakin layi. To ki sani yin hakan tamkar cikin ki ki ka daɓa ma wuƙa, yau ga wani gobe gareka, musamman sha'anin maza.
"Gwanda amman dai bakwa sumbatar juna in kun zo mu'amular Aure ko? Kyama har ta kama ni, ji nake uwa in yi amai" Dariyar yaudara Kaila yayi, ya gyara mata kwanciyar tata, tare da faɗin.
"Ai komai baya yiwuwa kamar yadda na faɗa miki tun kafin kizo. Ni fa duk wani soyayya da tarairayar miji a gado ban sanshi ba. Ke baki ga hakan a haɗuwarmu ta jiya ba? So fa kika yi ki buɗe mun kai" Dariya tayi mishi tace.
"Tarairaya Gwanda ai baka ga ma komai ba. Ni dai fatana shine kaci gaba da sona har izuwa ƙarshen rayuwata. Ni kuma zan baka duk wata kulawa." Nan suka shiga musayar kalaman ƙauna masu zafi, tamkar zasu koma ruwa, amman ina cikinsu na kiran ciroma, ba shiri Kaila ya miƙe dan bashi da juriyar yunwar ciki da yunwar mace.
"Bari in shiga gidan in samo mana abinda zamu ci ko?" Baki ta taɓe tace.
"To Allah yasa dai in iya ci Gwanda" Fita yayi daga ɗakin. Akan idon Hajiyayye Kaila ke ta faman jan rigarshi a ƙoƙarinshi na san dai_daita kanshi daga fitinar dake cin ƙasan ranshi. Wandon shi da yayi tudu tabi da idanunta. In da Hindatu take zaune tana wanki tabi da kallo, itama Kaila take kallo harda riƙe haɓa. Wani ƙaton malolon baƙin kishi ne ya tokare mata maƙoshi. Bata dawo daga duniyar takaici da zafin zuchiya ba, taji saukar sautin Kaila yana faɗin.
"Ina abincin karin Amarya Hajiyayye na ɗauka sassafe za'a shigar mata dashi, kinsan dole da yinwa ake wayar gari" Ji tayi muryarta ta dashe, ashar tayi niyyar lailayowa da ƙyar ta danne, taci gaba da wankin da ta tashi dashi yau.
"Ba dake nake ba Hajiyayye dan rashin son albarka shine kina jina ki kai mun kunnen uwar shegu, ko an faɗa miki ni sa'an wasanki ne?"
"Abinci dai banyi ba, kuma in sai Bilkisa taci abincina zata rayu sai dai ta mutu. Kayi haƙuri Kaila bana son ka taɓo ni in fa ba haka ba zaka ga jajjagen rashin mutunci, alo tsiya alo......." Tas ya wanketa ta wawan tafi. Da sauri ta dafe kuncinta tana mamaki, miƙewa tsaye tsaye tayi dafe da kunci. Shi kuma ya haɗe rai ya kumbura jiran ƙiris yake ya fashe.
"Ni ka mara Kaila sabida ƴar iskar Amaryarka?"
"In kika kuma kiranta ƴar iska sai na saki a cikin dana sani wallahi "
"An faɗa ƴar iska, an kuma ƴar iska" Cikin ɗaga murya da hargagi yace.
"Kije gidanku na sake ki. Tunda ke bakya ji, baki isa ki hanani sakewa da matata ba. Ki je gida kawai" Kuka Hajiyayye ta ruguje dashi. Wannan kukan sakin ya zame ma mata dole. Ko da mace ita ta nemi sakin, da zaran miji ya furta kalmar sai zuchiya tayi rawa gami da raunata. Amman dake Hajiyayye itama A ce, kuma ita tayi dai_dai da Kaila. Bai yi aune ba ta juye mai ruwan wankin da take yi a ka. Ta jiƙashi sharaf. Bilkisa da Amadudu tare suka fito a guje tsakar gidan, a sakamakon hargagin Kaila da Hajiyayye. Da mugun gudu yabi Hajiyayye jikinshi har yana ɓari. A guje ta fella bako mayafi daga ita sai doguwar riga. Kaila bai bar binta da gudu suna ratsa mutanen anguwa ba. Sai da Hajiyayye ta faɗa cikin wani gida jikinta na rawa. Yanda taga ɓacin rai a fuskar Kaila bata san me zai yi mata ba daya kamata. A ƙofar gidan ya tsaya yana cizon yatsanshi. Amadudu ne ya iso da sauri wajan, dashi da Baban Mustapha mijin Sabira, da wani dattijo maƙocinsu. Wannan dattijon ne yace.
"Haba Baban Sani, ya zaka take ka biyo mace da tsohon ciki waje, kana gudu tana gudu ko mayafi babu. Ai koma meye tayi maka bai dace ku fito titi ku fallashi kan ku ba. Ka duba yadda anguwa ta cika da mata, jibi can mata ne daga katanga suke leƙe fa" Kallon katangar da dattijon ya nuna musu suka yi. Mata uku suka gani sai leƙe suke yi. Anguwar ts soma cika da mutane. Dan da dama sun jiyo sautin muryar Kaila a lokacin da ya furta ma Hajiyayye saki. Haka dai wannan Dattijo ya taushi Kaila ba dan haka ranshi yaso ba ya bar ƙofar gidan yana ƙuta. Yana shiga gidan bai zarce ko ina ba sai banɗakinshi, dan takaicin bai gurje bakin Hajiyayye ba da ruwan sanyi yayo wanka. Yana fitowa ya kintsa, Bilkisa dai tana zaune tana kallonshi, so take ta bashi haƙuri amman tana jin tsoro. Ita yawan fara'ar Kaila da kashasshiyar muryarshi ta yaudara kawai ta sani. Sai gashi yau taji muryar cikakkun maza tattare dashi" Kai tsaye Kaila wajan mai indommie ya je. Kwai yasa aka toya mishi guda huɗu, ya sai kayan tea da ƙaton biredi ya dawo gida. A inda ya fita ya bar Bilkisa anan ya sameta a harɗe, jira yake ta amshi ledar hannunshi amman yaga ko gezau batai ba. Ba ta mishi ko sannu da zuwa ba. Amman dake amarya ance bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida, haka ya barta.
"Ga kayan tea na siyo, ki dafa ruwa ko a kettle ne ki haɗa mana tea, akwai soyayyen ƙwai a ciki sai mu haɗa da kazar jiya" A yangance ta ɗauki ledar ta fita zuwa kitchen ɗinta na langa langa. Bata jima ba sai gata da trai a hannunta ta sako komai a kai, harda kaza mai turiri da halama ta dumamata a oven ne ko microwave, dan an danƙara mata kayan wuta iri_iri. Suna zaune suna karyawa babu mai cewa da kowa komai, sai da suka kusan kammalawa Bilkisa tace.
"Gwanda kayi haƙuri da Hajiyayye ka dawo da'ita ɗakinta, ga ciki kuma naga ƴarta ƙaramace, ɗazu ma daka fita ina jiyo kukanta a tsakar gida. In ka rabu da'ita waye zai riƙe mata yaranta" Ƙur Kaila ya mata da mayaudaran idanunshi yace.
"Tunda fa na sanar musu da batun aurenki, bata taɓa barina nayi bacci mai kyau ba. Dama fa fitinar Hajiyayye yawa ce da'ita. Ki barta kawai ta je gidan. Ala bashi in iyayenta su ka yi tunanin dawo da'ita ɗakinta shikenan." Kai Bilkisa ta gyaɗa tace.
"To shikenan ba damuwa. Abu na gaba kuma ya batun mai aiki da kayi mun alƙawarin zaka ɗauka mun washe garin ranar dana tare, kaga yau kenan. Dan gaskiya bazan iya haɗa tarairayarka da shiga kitchen ba, ga aiki in na soma zuwa. Bani ma da wannan lokacin gaskiya" Murmushi Kaila yayi yace.
"Yanzu bari in kammala karyawa sai in fita, in sha Allah da ƴar aiki zan dawo cikin gidannan. Ai ba wuya suke yi ba masu aikin. Gaskiya Ɗanyan gwal kina ji dani fa, sabida tsabar tarairayata da kike son yine kika ji girkin ma ba zaki iya yi ba." Nan dai su kak ta faman tattaunawa, daga ƙarshe Kaila ya fita, Bilkisa kuma ta koma ɗakinta. Babu abinda ta taɓa a ɗakin, kayan da su ka yi kari suna wajan, kayan da Kaila ya cire suna zube a kan gadon. Kafin azahar sai ga Kaila da ƴar aiki ya kawo ma Bilkisa. Tana harɗe a falonta tana kallo suka shigo.
"Ɗanyan gwal, wannan sabunta kwalliya haka, kai gaskiya ina morewa idona. To yanzu dai ga ƴar aiki nan na samo miki ita, sai ki faɗa mata aiyukan da zata dinga miki, da kuɗin da za'a biyata ko?" Bilkisa ta murmusa tace.
"Godiya nake ɗan maraƙin jimina gagara ɗaukar shawo. Ke me sunanki" Yarinyar tace.
"Sunana Shamwila Hajiya"
"Okey Shamwila, aikinki shine, girki duk ran girkina, wanke wanke, wankin kayana da kayan mijina duk randa yake ɗakina. Sai gyaran ɗakina da turakar mijina, sai aika haka in ya kama zan dinga yi miki. Ina ga shikenan iya aikin. Zamu dinga biyanki duk wata nera dubu bakwai. Amman fa bana son fashi in ce dai gidanku babu nisa da nan ɗin ko?" Kaila ya shiga ruɗu da mamakin yanda yaji Bilkisa ta lissafo harda gyaran turakarshi da wankin kayanshi ranar girkinta, ya soma tantamar tana da hankali kuwa? Ta ya zata sakar ma ƴar aiki girkin mijinta, da gyaran turakarshi, harma da wanki? Yarinya matashiya, mai jini a jika, kuma kyakkyawa irin haka. Shiru yayi ya ƙudurce zai taka mata burkine. Muryar Shamwila ce ta dawo dashi daga taɗin zuchin da yake ta faman yi da zuchiyarshi.
"Gaskiya ina da nisa Anty. Kuma dole sai dai in dinga tawowa da ƙafa, dan in nace kullum zan cire kuɗin abun hawa kuɗin zai ƙare, kuma ni ke kula da mahaifana da ƙannena" Shiru Bilkisa tayi tana nazari. Kaila yace.
"A wacce unguwa kike haka, sannan mahaifinki bashi da rai ne da yarinya ƙarama dake nauyin iyayenki da ƙannenki yake wuyanki?" Shamwila sai ta saka fuskar tausayi tace.
"Mahaifina yana kwance ba lafiya shekaru biyar kenan. Kuma mu masu ƙaramin ƙarfine sosai. mahaifiyata girma ya kamata. Shine nake buga _buga ina ciyar damu, danginmu dukka suna Niger mu Sadaka yalla ne, waɗanda ake mana laƙabi da muna bara muna karuwa. A layin ƴan ƙarya muke da zama can kusa da babtis." Kaila ya girgiza kan shi kawai. Balikisa tace.
"To a gida za'a barki ki dawo nan da kwana, in yaso ranakun asabar da lahadi kya dinga komawa gida? Sabida yanayin nisa, duba da cewar kuna cikin wani hali, zan baki nera dubu goma duk wata, amman zaki samu ƙarin aiki" Shamwila ta zube tana ta faman godiya. Kaila shi kuma aka barshi da mamaki.
"A ina zata dinga kwana kenan to?"
Balkisa da take magana a gadarance tace.
"A ɗakina ga falo wadatacce, Gwanda sai ta dinga kwananta a kujera ai, tunda kai kana da turaka" Kai ya jinjina yana tunanin taya kyakkyawar budurwa haka za'a turota aiki harda kwana a gidan aiki? Tsabar haushi a wajan ya fice ya barsu. Shamwila kuma ta kama aikinta ka'in da na'in. Dan a wannan rana ita ta gyare ɗakin Kaila tai ma ɗakin turaren wuta, ta wanke toilet, da kayan da suka cire. Tayi sharar tsakar gidan da wanke_wanke fes. Hindatu sai kallon ikon Allah kawai take yi. Bayan ta kammala ta tsugunna a gaban Bilkisa da take kwance tana charting da Kaila tana tambayarshi wai ina ya tafi ne tun safe?.
"Anty inaso zanje in kwaso kayana kuma in faɗa ma Ummata."
"Yauwa Shamwila dama inason zan miki aike kasuwa. Kaza nake son ki siya mun, da kayan miya, sai kayan lambu" Bilkisa ta lissafama ma Shamwila duk abinda take buƙata, ta bata kuɗin mota ɗari biyar. Ba'afi awa biyu ba, sai ga Shamwila niƙi_niƙi da boron kayanta gari guda, da ledar cefane. Bilkisa ta nuna mata bayan lungun show glass ɗinta tace sai dai ta ajjiye a nan.
"Inason ki dafa mun jallof ɗin soyayyar taliya da pepper chicken. Akwai kayan zoɓo a kitchen ki mun zoɓo mai daɗi" Nan Bilkisa ta tusa Shamwila a gaba suka shiga kitchen ta nunnuna mata abinda ya dace ta nuna mata. Anan ta bar Shamwila tana mamakin yanda aka narkama kitchen ɗin langa_langa dukiya haka, da tunane_tunane, da burika fal ranta ta shiga aikinta ka'in da na'in. Cikin ƙanƙanin lokacin gida ya soma tashin ƙamshin albasa da tafarnuwa."




SHANONO:

TANI:
Allah kawai nake ambato, naƙuda ma nake ji kamar inayi. Matan ƙannen Narani ne suka Iso, Shehulle na biye dasu faram_faram, ga Iya mai Fura itama tana tafe. Ni kuwa zuchiyata sai tsalle kawai take yi.
"Ina Daudan yake, a wanne halin yake?" Cewar Shehulle kenan cikin ɗaga murya. Yaya Karime ce ta mishi bayani, tare da nuna mishi inda aka shiga da Daudan. Ni ko hawaye kawai nake fitarwa bana ko iya ganin gabana, kaina naji yayi wani gingiringin. Wata ma'aikaciyar jinyace ta fito daga cikin ɗakin da aka shiga da Dauda. Ina gani duk suka rufu kanta, ni ko ina zaune ina haki, dishi_dishi ma nake ganinta.
"Wannan yaron bashi da iyayene, ko dai tsintarshi kuka yi. Ya yaro kamar wannan za'a bari ta kashinshi ta zazzage har ta lalace haka? Ina mahaifiyarshi take?" Take Shehulle ya nuno ni. Wani kallon tsana wannan ma'aikaciyar jinya tai mun tace.
"Ke kuwa baiwar Allah kiji tsoron Allah. Shin a matsayinki na uwa, har kin mance da rainon ciki da lauwaye_laulayanshi, shin bakiyi ƙwannafi da amai bane, ina kika mance da zafin fitar kan yaro daga jikin uwa, ina kika bar buɗuwar da kwankwaso yakeyi yaro ya faɗo. Ga raino, ga shayarwa? Kina ma yaronnan wanka ace har baki san halin da yake ciki ba, har sai da ya soma tsutsa da ɗiwa tukunna? Anya kece kika haifeshi kuwa?" Duk illahirin jikina babu inda baya rawa. Maganganun ma'aikaciyar jinyarnan sai huda mun tsoka yake yi, take tsigar jikina ta soma tashi yar_yar_yar."
"A'a kar ki zargi mahaifiyarshi. Domin tun yana tsumman jinjirantaka ubanshi ya kwaceshi. A hannun matar uba yake. Ita ta hofantar da rayuwarshi. Dan Allah yarinya yanzu meye abinyi, wanne taimako ya dace abashi?" Yaya Karime ke magana cikin taushin murya. Dangin Narani kuwa kamar ruwa ya cinyesu haka suka dawo.
"Aiki za'ayi mishi. Amman aikin zai lashe kuɗi masu yawa. Shawarar da zan baku shine ayi gaggawar kaishi cikin gari, domin sun fimu ƙwararrun likitoci, da kayan aiki. Muna bashi agajin gaggawa dai a yanzu. Ke kuma baiwar Allah kiyi haƙuri, wallahi na zaci sakaci ne irin namu. Ashe muguntace irin ta iyayen riƙo. Amman duk wanda yai ma yaronnan wannan aika_aikan ya kamata lallai ku haɗashi da hukuma" Nan aka shiga ciku_cikun yanda zamu kai Dauda asibitin Birni. Baffa da Inno tuni sunji labari. Inno da Kawu Junaidu har sun tawo. Shehulle kuma ya fita samo mota. Ranga_ranga aka sa Dauda a mota, yana jikina sai ajjiyar zuchiya yake yi, ni kuma na rungumeshi kamar jariri. Hauwa tana bayan Yaya Karime. Da Yaya Use zamu, sai Shehulle. Su kuma su Inno banda su. Ta tagar mota Inno ta zuro kanta, ta danƙama Yaya Use dubu huɗu tace.
"Gashi in ji Baffanku yace in baki Use. Sai munzo. Ke kuma Tani kar ki tashi hankalinki kinga juna gareki. Naranin yana ma cikin garin Kanon yace zaku haɗu a asibiti." Ido na lumshe kawai, idona yayi jawur dashi nama rasa abinda ke mun daɗi. Ga marata sai faman ɗaurewa take yi. Haka muka kama hanyar Kano, baka jin ko tari a cikin motar, sai ajjiyar zuchiya da nake faman saukewa a kufi_a kufi. A farfajiyar asibitin Murtala muka haɗu da Narani yana jiranmu. Dauda ya zare a hannuna suka yi ciki shi da Shehulle. Mu kuma muna biye dasu a baya. Wallahi har nafi Yaya Use dauriya, dan tunda muka tawo take rera kuka mai sauti. Cikin wani dogon falo muka shiga, a lokacin Narani sun shige ɗakin jinya shi da wani ma'aikacin jinya, Shehulle da halama dakatar dashi sukayi.
"Shehu cewa su kayi ka tsaya anan?" Cewar Yaya Use, Shehulle yace.
"E Narani kawai suka ba damar shiga. Dauda ya faɗi wanda yai mishi wannan aikin?" Banza nayi dashi dan kowa haushinshi nake ji a gidansu Shehulle. Dan su su kai ruwa da tsaki wajan banƙaremun hannuna a ƙwace Dauda a yayin da akeson raba uwa da ɗanta.
"Ya faɗa Shehu. Amman baza mu yadda ba, dole hukuma tayi aikinta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login