Showing 48001 words to 51000 words out of 68990 words
Chapter 17 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
Dauda ciki ba. Ya kamata Kaila ya fara sani tukunna." Ɗan mabuɗin na bata ta buɗe, ni kuma na shiga cikin gidan. Hajiyayye tana zaune tana soya miyar tumatur taci uban kwalliya da atampar da Kaila ya ƙwace a wajena ya bata. Lamarin da ya matuƙar bani mamaki kenan,dan ni sai yanzu ma naga kyan atampar.
"Me zan gani Umman Sulaiman haihuwa ki kayi kome, naga babu ciki a jikinki? Yaya Use ce ta shigo ciki da fara'a ta dubi Hindatu da take tambayata, hannunta riƙe da jariri tace.
"Haihuwa tayi, Shanono na biyu yazo. Sannunku da gida mun same ku lafiya?" Hajiyayye tana juya miya tace.
"Ikon Allah wai na kwance ya faɗi. Ai kuwa bamu ji ko labarin haihuwarnan ba, kuma mai gidan shi ya sani?" Yaya Use ta dubi Hajiyayye, sai naga ta kalleni da mamaki, nasan bazai wuce ganin atampar jikin Hajiyayye ba ne. Daurewa tayi tace.
"Ya sani, shine ma yace ta dawo ai"
"Allah ya raya mace ko Namiji?" Cewar Hajiyayye.
"Namiji aka samu, Hauwa an fita daga kan nono" Ta ƙarashe maganar tana yaƙe. Babu wanda yayi yunƙurin tasowa ya ga jaririn balle su ɗaukeshi, komawa ɗakina mu ka yi.
"Tani atampar jikin Hajiyayye kamar itace atampar da Inno ta bakinnan cikin bikin Sallah ko?" Yaƙe nayi nace.
A'a irinta ce dai, me zai kai kayana jikin kishiya" Ƙuramin idanu tayi tace.
"Wallahi itace Tani ɓoye mun zaki yi dai kawai. Amman akan me zaki ɗauka ki bata Inno ce fa ta baki dan tasan baki da wasu kayan fita, dan neman wajan zama shine kika ɗauka kika ba Hajiyayye matar da bata da burin daya wuce taga zubar hawayenki?" Nasan babu wata ƙarya dana isa in yi ma Yaya Use, dan tana da ƙwaƙwa sosai, tun sanda muke yara tana da saurin ɗago abu. Sai kawai na zaɓi faɗa mata gaskiya.
"Kusun uwa har lalacewar taki a cikin gidan ta kai kaila ya karɓi kaya a hannunki ya ba matarshi, ke kuma da yake lusarace sai kika bata ko, shi bai siya miki ba, wanda aka baki ya amsa? Bari kiji wallahi sai na sa Hajiyayye ta cire kayannan ta bani. In ma ke ba zaki yi amfani dashi ba, to itama bata isa tayi ba. Uwarmu ce ta nemo ta bamu domin tanason ganinmu muma fes. Wato yafi son yaga matarshi cikin ado, ke kuma ko oho." Shirin fita tayi da sauri na riƙo hannunta tsorona Allah tsorona kar Kaila ya yi zuchiya ya rabu dani, yarana bazan iya barinsu a gidannan ba. Sannan ina tsoron kar rikicin ya taɓa zaman Dauda a gidannan." Kafin in yi magana mu ka jiyo sallama da wata siririyar murya. Amsawa Yaya Use tayi, tare da ba da izinin shigowa. Bilkisa ce ta shigo, tana saye da wasu ƙananun kaya riga da wando na yadi, amman basu kamata ba, sun yi mata kyau, sai da ta cika ɗakinnan da ƙamshinta dam.
"Sannunku Anty Tani kun dawo? Maraba" Hannu tasa ta karɓi jaririn dake hannun yaya Use, amman tana ɗaukarshi tayi maza ta miƙa mata shi.
"Masha Allah, Allah ya raya shi, dama ina kwance ne a ɗakin gwanda na jiyo shigowarku shine nace bari in zo in yi muku barka, ni zan koma"
Nagode sosai Bilkisa, Allah ya saka da Alkhairi" Fita tayi da sauri, nasan hakan na da nasaba da zarni, da kuma warin da Dauda yake yi, da ƙarnin nono da jaririn shima yake yi. Yaya Use nai ma kallon kiyi mun rai. Wucewa tayi fuu zuwa tsakar gida, kai na dafe, na zauna a kusa da Dauda na shiga sauke numfashi. Banaso yaya Use tayi wani abun da zai sake jefa ni a matsala, kuma in aurena ya mutu sune na farko_farko wajan ƙyamatata da ɗaure mun fuska, amman yanzu gashi taje tana son yin rigima da Hajiyayye akan kaya. Kuma nasan rashin kunyar Hajiyayye bana wasa bane.
Fitowarta daga ɗaki kenan Yaya Use ta fito.
"Hajiyayye mu shiga daga ciki zamu yi magana in babu damuwa" Wani kallon banza Hajiyayye tayi mata dan ta riga da tasan akan abinda tazo.
"Nan ma ai ya isa, babu bare a cikin gidan, ba irin gidanku na haya bane, gidan mai gidanmu ne. Yawu Yaya Use ta haɗiye tace.
"Tunda haka kika ce ai shikenan. Kayan dake jikinki nake son ki cire mun bakin ki alaikum ki miko su." Cikin gatsali Hajiyayye tace.
"In kuma ba haka ba fa?"
"Sai in tuɓe ki in ga uban daya isa ya ji dalili dan kutumar ubanki" Ina cikin ɗaki nake jiyo wannan gurmi. Ba shiri na miƙe.
Dauda ina zuwa kaji ko? Kar ka fito. Da gudu na fito, na samu Hindatu tazo ta shiga tsakaninsu.
"Hindatu ki matsa, ni ba karamin aikina bane in yima Hajiyayye zigidir a tsakar gidannan. Kaya dai ba nata bane kaya na Tani ne. Ya zama dole ta cire ta miƙo su"
"Ai Kaila ne ya bani, dan haka in kina son a cire miki kayanku, sai ki jira in yazo sai ya bani umarni amman ba dai ke ba. Kuma ni bazan haɗa kirji dake ba, ni ba fitsarariya bace wacce take yawo kwararo kwararo na bara, dama ance ƴan jagora basu da kamun kai." Abinda nake gudu shi yake shirin faruwa. Bilkisa ce ta fito daga turakar Kaila, ita da wata budurwar farar yarinya sol. Bilkisa ta shige ɗaki ita kuma yarinyar ta soma shanya. Abinda ya ɗaure mun kai gajerun wandon kaila da singiletinshi take shanyawa.
To wacece wannan kuma? " Ƙaran marin da naji ne ya dawo dani hayyacina. Hajiyayye na gani dafe da kunci. Hannu Yaya Use tasa ta fincike Hindatu kefe. Dama Yaya Use irin ƙatuwar macece, gata da ƙiba sosai. Kamo Hajiyayye tayi, nayi maza na shiga tsakani. Hajiyayye na ganin haka ta kawo naushi ya sauka a gadon bayana. Wallahi sai da ƴan hangina suka motsa tsabar zafin naushin. Nasan tana sane sarai ta naushe ni. Ni kuma nasan in na barta da Yaya Use abun bazai yi kyau ba, ga ciki a jikinta." Zagi Hajiyayye ta soma narko mana, tana haɗawa da su Inno. Idanun Yaya Use ya rufe, nan kokawa ta kaure a tsakani. Jikake tutur_tutur. Ni da Hindatu muka kasa raba wannan dambarwa, gashi har Yaya Use ta keta ma Hajiyayye riga har nonuwanta sun bayyana. Kuma bakinta bai mutu ba.
"Shegiya tsinannu masu baƙin jini. Yaran mabarata ƴan jagora karuwai waɗanda suka saba tambaɗewa" Wannan kalmar yasa Yaya Use ta raɗa Hajiyayye da ƙasa, mazaunanta suka zauna daɓas a ƙasa zaman daɓaro take jini ya ɓalle mata" Bako ɗankwali a kaina haka na fita na kirawo maƙota, a guje suka shigo. Da ƙyar aka ɓanɓare Yaya Use a jikin Hajiyayye, ta cire mata riga da zanin jikinta. Daga ita sai sikel ɗin ciki, nonuwanta gasu a waje duƙwai. Hajiyayye da taga jini na malala a jikinta sai ta shiga murƙususu tana cewa
"Nashiga uku ta kashe mun yaro a ciki, shikenan sun kashe mun ɗan cikina, a ciki ta dinga naushina. Na mutu, ku kira mun Kaila" Sabida tsabaragen makirci ba sai Hajiyayye ta sandare ba, ta soma kakkafe idanuwanta. Ita kanta yaya Use hankalinta ya tashi ainun. Kuma tsoro ya kamata. Ni kam dama nasan hukunci saki ya tabbata a kaina. Ba shiri aka kinkimi Hajiyayye sai asibiti, Hindatu ma ta bisu. Duk wannan abun da akeyi Bilkisa bata ko keƙo ba, balle tace kuyi haƙuri. Gida ya cika da mata, sai ba Yaya Use rashin gaskiya akeyi. Danme zata daki mai tsowon ciki, a ciki. Ita kuma sai rantsuwar ai ita sam bata daki cikinta ba take ta afkin yin. Jikina a sanyaye na shiga ɗaki. Sai lokacin na samu zarafin yin kuka.
Shikenan aurena ya mutu. Sai da na hanaki amman kika ƙi hanuwa, yanzu wa gari ya waya? Allah kaɗai yasan irin sharrin da Hajiyayye zata yi a wajan Kaila. Ba'ayi abu ba ma ta ƙirƙira tace anyi, kaila ya ci zarafina akai, balle an yin" Yaya Use nan ta shiga zagina tana hargagi.
"Dalla rufa mun baki, ni banje da zummar dukanta ba. Amman wallahi bata isa ta zagi iyayenmu in tsaya ina kallonta ba. Kina jin mugayen maganganun da take fesarwa, ni zata nuna ma rashin kunya ina ƴar gajora?" Gani da tayi hankalina ya tashi da yawa ne yasa ta sassauta murya ta shiga lallashina.
"Ki fito da maganin Dauda a dafa, zuwa anjima ya soma amfani dashi. Wadannan kayan kuma ki adana."
A'a Yaya Use, ki tafi dasu dai." Jakata na buɗe na bata ƙullin magangunan. Tare muka fita, kurfo biyu muka ɗaura, ni na ɗaura sanwar girki ita kuma ta ɗaura ruwan zafi. Sabira ce ta shigo da sallamarta, da alama daga anguwa take"
"Maraba lale umman Sulaiman an dawo? Yaya Use ke aka bari da ɗaura ruwan jegon?" Yaya Use tayi yaƙe kawai, dan hankalinta baya tare da'ita.
"Tani abunda naji a anguwa gaskiya ne, wai kun haɗu ke da yaya Use kun zauna a ruwan cikin Hajiyayye zaku kasheta? Wai ranga_ranga aka kaita asibiti, ance ma sai an yi mata tiyata" Daga ni har Yaya Use salati muka saka, jikina yana rawa.
Wallahi Sabira ba haka zancan yake ba" Nan yaya Use ta labarta mata yadda akayi"
"Hmmm da kin sani baki neme ta da faɗa ba. Muguwar makirace. Kuma kinga Tani a dofane take a cikin gidannan, wannan maganar zata iya zama babba sosai ta ɓangaren Baban su Sulaiman dama dangin ita Hajiyayyen, dan na lura yayyenta suna da fitina sosai" Tare muka haɗu mu ka shiga jimami a tsakar gidannan. Sai zuwa can bayan isha sai ga su Sani sun shigo. Sai murnar ganina suke yi, ni kuwa sai dariyar yaƙe nake yi musu. Sallama Sabira tayi mana akan sai gobe zata shigo. Taliya na ɓararraka musu, na baje musu ita a tire.
Yaya maza kuje ku ci, Dauda Yayanku yana cikin ɗaki a kwance bai da lafiya, kuje ku ci tare" Shafi'i yace.
"Umma dama ba Yaya Sani bane babban yayanmu ba?" Murmushin dole nayi nace.
Dauda ya girmi Sani sosai ma, ɗan uwanku ne ni na haifeshi, kuje ku ganshi " Sani yace.
"Umma shi Babanshi da ban ko?" Wannan maganar ta daki zuchiyata sosai da sosai, amman haka na kanne nace.
E Babanku ba ɗaya ba. Amman duka ni na haifeku" Shafi'i zai sake jefo tambaya, Yaya Use ta koresu. Jikin Yaya Use a sanyaye tace.
"Tani je ki watsa ruwa ki fito ki samu kici abinci. In sha Allah sharrin Hajiyayye kanta zai koma. Kuma banyi da niyyar in jefa ki a matsala ba. Asalima nayi ne domin ƙwato miki ƴanci ta yanda gaba ba zasu yi miki milkin mallaka ba, daga ita har Baban Sulaiman ɗin. Amman kiyi haƙuri ƙanwata" zuchiyarta ce ta sake tsinkewa, bance komai ba na je nayo wanka na fito. Hindatu ce ta shigo da sallamarta. Da sauri na isa kusa da'ita.
Yaya jikin nata Hindatu dan Allah?" Hindatu ta yi mun wani kallon wulaƙanci tace.
"Na baro su an shiga da'ita ɗakin tiyata, sakamakon hallakata da Use ta kusan yi. Ran danginta yayi zafi, dan sun yi rantsuwar baza su yarda ba. Kinsan dai Hajiyayye da gatanta. Kaila ma yana hanyar dawowa gidan yanzu" A nan ta tafi ta barni da wannan. Jikina ya mutu murus, hantar cikina sai kaɗawa take yi. Yaya Use dake zaune da abinci a gabanta, itama tayi kasaƙe ta kasa ƙara sa loma a bakinta.
"Tani kiyi haƙuri, da sharri suke neman mu shi yasa, ta Allah ba tasu ba. Mu je ɗaki" Hannuna taja zuwa ciki, yara sai jan Dauda da surutu suke yi. Shi kuma ya takure a kuryar katifa, sai mutsi_mutsu yake yi.
"Zauna ki daure kici abinci, jego kike yi kin sani. Dauda tawo muje in maka wanka ko ka samu ƙarfin jikin, sai a shafa maka maganin, ka sha kuma na shan." Hannunshi ta riƙe suka fita. Shafi'i ya rufe hancinshi yace.
"Umma Dauda wari yake yi kamar yayi kashin wando" Carab Amina tace.
"Ni shi yasa ma naƙi zama a kusa dashi" Ni dai ina zaune jigum na rasa abinda yake yi mun daɗi a rayuwata, nasan ba lalle bane in kwana da igiyar aure a kaina. Ina ganin rayuwa fitintinu daga wannan sai in faɗa wannan, ya Allah kafi ni sanin abinda ke jawo wannan matsalar kai mun zaɓin alkhairi, in Kaila ya sake ni Allah kai mun mafita, bani da kowa sai kai ya Allah. Ita kuma Hajiyayye sharrin da take nema na dashi Allah ka mayar mata abinta. Duk wannan magana a zuchiyata nake yi. Ga abinci a gabana na kasa ci sam. A inda su Yaya Use suka fita suka barni a haka suka dawo suka same ni."
"Kun yi sallar isha ne?" Sani yace.
"Mun yi Mama. Mama amman ba'a katifarmu Dauda zai kwana ba ko?" Yaya Use ta dubeni, kana ta dubi Sani tace.
"Anan zai kwanta ɗan uwanku ne fa Sani, wanka ne" Baki Sani ya turo gaba yace.
"Wallahi wani abune a jikinshi yake wari sosai, mu gaskiya bazai kwanta mana a katifa ba. Zata yi magana na katseta da cewa.
"A kusa dani zai kwanta, katifar ai ba zata isheku ba." Shine fa su kai shiru, da ƙyar Yaya Use ta dinga rarrashina sannan na samu na tuttura abincin. Ina zaune cikin zulumi na jiyo tsaiwar lifan ɗin Kaila a ƙofar gida. Tun daga ƙofar gida ina jiyoshi yana ta faman jaraba, kamar tare da Isa abokinshi yake.
"Shanono, Shanono zo nan?" Na jiyo muryarshi a cikin zauren, a zabure na miƙe, Yaya Use ta ce.
"Jira bari in je in mishi bayani na fahimta tukunna" Tana kaiwa nan ta fita da Hijabinta a hannu.
"Kaila sannunku" Wani irin haɗe rai yayi yace.
"Ita shanonon bata ji ina kiranta ne? Ko nima kin fito ki dake ni ne, tunda ba'a koya muku tarbiyya ba? To ina ma aka nutsu da za'a koya muku tarbiyya? A kwararo fa....."
"Kai Kaila dakata kaji ko, kul ka kawo wannan zancan. Ni ba sa'arka bace, ka sani ba ƙanwar Tani bace ni, yarta ce ko ince uwarta ce ni. Dan ina da mai shekarunta a gidan miji" Maganganun Kaila yayi dai dai da saukar aradu a kaina. Ji nayi wani abu ya tokare mun maƙoshi, sai lokacin na samu zarafin yin kuka, kukane ya turniƙeni mai ɗacin gaske. Ina jiyo muryar Yaya Use da Kaila a sama.
"To Use bari kiji, ni na fiki tashanci wallahi, a kwararrafa na girma, har za'a nuna ma ɗan kwararrafa iya shege ne? Iyayen Hajiyayye sunce ba zasu yarda da abinda ku kai ma ƴarsu ba, zasu shigar da kararku, wallahi babu abinda ya dameni tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka. Kuma ki fice mun daga gida kar ki kuma zuwan mun, tunda zuwan naki ba alkhairi bane." Muryar Isa naji yana faɗin.
"Kaila baka kyauta ba. Tun a asibiti ina faɗa maka kabi komai a sannu kaƙi. Kayi haƙuri mana, abinda ya faru ya riga daya faru. Allah ya ƙaddari Yaya Use ita zata kashe yaron dake cikin Hajiyayye.Use gaskiya kema kin yi kuskure, ai ko Hajiyayye ce ta cakaleki da faɗa kya ɗaga mata ƙafa. To sakamakon dukan cikinta da kika yi, yaron ya mutu mata a ciki, an yi tiyata an ciro mata shi ba rai, kin ganshi a kwali. Danginta sunce bazasu taɓa yarda ba ƙara zasu shigar. Nayi iya yina ma a kashe maganar a gida, wallahi basu yarda ba..............✍🏻
MRS BUKHARI
Sai jibi in Allah ya kaimu da rai da lafiya "NA FAƊO DAGA BENE......
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 14
*OUM SOOFEEYYER GRAPHIC AND DATA*
*INA Marubuta da masu business*
*Maza ku hanzarta mun shirya tsaf domin kayatar da ku da graphics kalakala Kuma cikin farashi me sauki*
Logo
2d Logo
Flyer
Invitation card
Invitation vedio
Save the date card
Save the date vedio
Book cover
Account sticker
Makeup Flyer
Business Flyer
Da dai sauransu
Sannan Kuma Ina koyarwa ga duk me bukata cikin sauki
08069638776
*All netwk Data is available*
*ASIBITI*
HAJIYAYYE:
Tana kwance a asibitin dake babban masallacin juma'a mai suna MATANMI. ƙarin ruwa ne jone a hannunta. Gefenta kishiyar mamansu ce a zaune ita ke jinyarta. Tunda Hajiyayye ta dawo gayyacinta aka sanar mata mutuwar da yaro yayi mata a ciki ta shiga ruɗani. Take ta sake rikirkicewa amman fa makircine zallah. Dan har fiffisga ta dinga yi, sai da akayi mata alkurar bacci. Ganin haka ne yasa ƴan uwanta cewar su fa ba zasu yarda ba sam. Dole a ƙwatarma Hajiyayye ƴancinta kisan ɗan mutum ba wasa ba, kuma su kotu suke son a tura kes ɗin. Dan har Yaya Ta bizaro mijinta ya kawo lauya yayi ma Hajiyayye tambayoyi domin sanin makamar aiki da kuma yanda zai tunkari kes ɗin dan ganin yayi nasarar ganin Shanono da Yaya Use a ƙasa.
Shigowar su Ta Bizaro da kamar awa guda sai ga Kaila shi da ɗanyan gwal Kaila ya kawota ta duba Hajiyayye. Wani irin material ne mai stone sunfi dubu a jiki ta saka, mai santsin gaske, fari ne jikin material ɗin da baƙi, takalmi da jakarta, da mayafinta baƙaƙe ta saka masu tsada, harda ɗankunne da sarka na gwal saudi. Shamwila na biye dasu a baya da basket cike da kayan abinci da Bilkisa ta sa ta girka ma Hajiyayye. Hajiyayye na ganinsu ta yi saurin kawar da kanta, tana fatan Allah ya kawo ranar da Bilkisa zata faɗa tarkonta. Ta san ta riga ta gama da Shanono, babu makawa a halin Kaila data sani bazai iya ci gaba da zama da Shanono ba. A tunaninta saura Bilkisa itace target ɗinta na biyu, dogon tsaki mai sauti ta ja.
"Sannu Mama yaya mai jikin?" Cewar Bilkisa kenan. Baba Tumba tace.
"Jiki da sauƙi zamu ce dai. Kaila wannan itace Amaryar?" Dariya Kaila yayi harda gyara tsaiwa yace.
"Itace Tumba Bilkisa kenan. Kin ganta likita ce itama mai zaman kanta, unguwar zoma ce dan da naso in haihuwar ita Hajiyayyen ya zo ta karɓi haihuwar, amfanin ilimin mace ta yi aiki dashi a gidanta kafin ta fitar dashi waje dama. A babban asibiti take aiki a Zaria. Yanzu haka ma da ta gama kwanakin amarci zata ci gaba da aiki a babban asibitin juth na can lamingo." Hajiyayye