Showing 57001 words to 60000 words out of 68990 words
Chapter 20 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
guda uku. Nan ya kai Bilkisa ta dinga yabon gidan. Ɓarayin da yafi ko wanne ɓarayi tsaruwa har da na shi kanshi mai gidan nan Bilkisa ta zaɓa. Masu aiki suna ta gabatar da aikinsu, gobe fenti za'ayi kuma. Suna gamawa da nan Kaila ya kai Bilkisa gida, shi kuma ya wuce wajan sana'arshi cike da zabarin son kiran Shamwila dan jin shanyayyar muryarta. Ai kuwa yana samun sarari ya danƙoro ma Shamwila kira, tare da karonto mata adireshin inda zata same shi. Shamwila a lokacin tana kitchen ta gama abincin rana kenan. Dama a shirye take tsab. A gaban Bilkisa ta tsugguna.
"Anty ummanmu ce ta kira ni jikin Babanmu ya tashi, suna bukatar in je zan kai musu kuɗi" Bilkisa ta dubeta ta watsar, dan ita irin masu adankiya ne ( I don't care) Jaka ta ɗakko ta bata dubu biyar.
"Gashi kwa ƙara. Amman kar ki daɗe, sabida girkin dare ko? Shi kuma Allah ya bashi lafiya." Da "Ameen" Shamwila ta amsa mata. Tasa kafa ta fice. Sai A1. A harɗe a kan kujera ta samu Kaila sai cika baki da guggurun A1 yake yi, bakinshi duk madara.( Jiki duk madara 🤣🤣) Yana hango Shamwila ya shiga yashe bakinshi, harda wani kashe idanu. Waje ta samu ta zauna.
"Barka da hutawa" Baki ya kuma washe mata mata.
"Shamwila, Shamwila, kin samu karasowa kinga yanda ki ka yi bala'in kyau kuwa. Zauna da kyau yau ai rana ta ce. Me kike son a kawo miki, gugguru, ko abinci?" Fari tayi da idanunta tace.
"Soma gabatar da abinda yasa ka kirani. Dan Ɗanyan gwal taka lokaci ta bani. Abincin darenka na bisa wuyana" Murmushi yayi mai ƙayatarwa, ya kashe mata idanu yace.
"Ai sabida tsabar son abincinki da nake yi. Inason da zaran mun koma sabon gida zan sa ki dinga mun girki ko da yaushe. Ko wacce mata tayi girkinta da yaranta, nawa girkin da ban." Ido ta zare tace.
"Tayaya hakan zai faru to, alhalin Ɗanyan gwal ce ta ɗaukeni aiki?" Ƙur ya bi tsakiyar fararen dara daran idanunta da mayataccen kallo, mai firgita ƴan mata, da narkar da zuchiyar mata.
"Ni zan ƙirƙiri hakan ya faru. Ke dai naki ido Ɗanyan jini." Dariya tayi mai burgewa tace.
"Nawa sunan kenan ɗanyan jini? Ina godiya da wannan suna. Amman har yanzu fa banji dalilin zamana a gabanka ba"
"Ɗanyan jini. Sonki nake yi har cikin jijiyata. Tun kallon farko da nayi miki na jaraftu. Kuma ni aurenki zanyi, amman sai zuwa nan da shekara ɗaya. Amman zaki zama matata ta bayan fage kin gane yhah?" Yana magana irin na cikakkun ƴan duniya, waɗanda suka ga jiya su ka ga yau."
"Taya hakan zata faru, bayan matanka uku, sai dai mu yi sabgarmu a waje ina tsoro gaskiya" Gugguru ya watsa tare da taunawa, kana yace.
"Ai kema matar gidance, yanda zan turmushesu a turaka ai kema ya kamata in turmusheki a turaka" Kai ta gyaɗa tace.
"Ko in turmusheka ba, ai ni nafi karfin kab matanka" Daga haka suka shiga musayar kalaman da suka shige ka'ida. Kafin su ankara har biyar na yamma ta gota." A zabure ta miƙe. Kaila ya riƙo hannunta ya tafa mata dubu talatin, su kai sallama kowa ya kama gabanshi."
SHANONO:
Yau haka na wuni cikin farin ciki da nishaɗi, Allah _Allah nake yi monday tayi in soma zuwa makaranta. Ina ta shirye_shiryen makaranta, na zube littattafaina duka a cikin jakata. Yaran kansu suma cikin walwala suke sakamakon walwalar da suka gani tattare dani. Kuma daɗin daɗawar farin cikina shine, waya da nayi da Habiba Bala take sanar dani, zuwa gobe za'a yima Dauda tiyata yana asibiti yana karɓar kulawa ta musamman, ƴar aikinta na kula dashi a asibiti" Sai naji zuchiyata ta yi wasai. Tamkar bana cikin wata matsala. Sani da Shafi'i sai guje_guje suke yi. Allah sarki uwa, farin cikinta da walwalarta shine taga yaranta a cikin nishaɗi, haka suma yaran ganin mahaifiyarsu a cikin walwala na sanya su kazar_kazar. Haka dai yau muka wuni cikin annuri. A tire ɗaya mu ka ci tuwon dare. Bayan sun je sallar isha sun dawo muka kulle ƙofarmu. Dan tun da Hajiyayye ta dawo wuni tayi tana ƙunduma zagi iri_iri, so take in tanka ta jawo ni ta huce haushinta a kaina. Washe gari ma muka tashi zuchiyata fes. Sai dai zuwa sha biyun rana sai ga sammaci an aiko mun daga kotu. Hakanne yai silar mutuwar jikina, sukuku na wuni, sai jan ƙafa nake yi, bansan yanda shari'ar zata kaya ba. Sati biyu alƙali ya yanka mana zamu soma shiga kotu. Shikenan gidan yari za'a aimu kenan ko? Tunda da kisa ake tuhumarmu. Ban ɗaki na shiga naci kuka na na gode Allah. Da yamma Sabira ta shigo ina tsakar gida ina kaɗa miyar kuka. Sai gata da ledar inifom ta kawo mun. Ganin idona yayi jawur ne yasa tace.
"Wata matsalar ce ta afku ko me? Ba dai wani abun ya haɗaki da Hajiyayye bane, dan ina jiyo buyaginta ina tsakar gida ina wanke ganye"
Hmm daga kotu aka aiko mun sammaci, nan da sati biyu za'a gurfanar damu. Shine jikina duk yayi sanyi, kinsan sharia tamkar mace mai ciki ne, babu wanda yasan me zata haifa, sai abinda Allah ya bata." Dafani Sabira tayi.
"Da yardar Allah Alkhairi zamu ji. Tunda dai ba Yaya Use bace ta kashe yaron Hajiyayye ba. Ke dai ki dage da kai kukanki gun ubangiji Allah zai sa a dace. Kin kira Habiba Bala kin sanar mata?
A'a zan kirata dai yanzu, so nake in sauke miya." Sabira ita tai ta tausar zuchiyata. Tare da'ita muka kira Habiba Bala a waya. Hankali itama ta kwantar mun. Ta sanar dani cewar jibi zata shigo ita da lauyan da ta ɗaukar mana. Ina kashe wayar sai ga Yaya Use tana kirana. Itama jikinta duk ya mutu. Haka na kwanta cikin zulumi. Ban samu barci ba, gashi zani makaranta. Haka na tashi tun kafin asuba, tsabar zumuɗi. Duk da batun kotu ya ture mun murnar da nake yi. Yara na shirin makaranta, ni kuma ina bakin gawayi ina dumamen tuwo. Sani ne ya fito da katifarsu ya jingina yana kwara mata ruwa. Ya ɗaga butar zai sheƙa ruwan kenan. Ashe kaila ya doso. Ai kuwa yana watsa ruwannan ruwan fitsarin yai tsalle sai a jiki da fuskar Kaila. Ihu ya sake harda cewa.
"Wayyo Allah Shanono zata halakani nima"......✍🏻NA FAƊO DAGA BENE.......
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 16
Assalamu alaikum.
Allah ya nufeni na dawo. Nagode da jumurin jira. A ɗan hutun dana tafi naga zahirin irin soyayyar da kuke ma wannan littafin. Ina godiya.
*(Domin soyayyarku gareni da rubutuna. Akwai promo da zanyi muku na turarukan wuta da humra setine mai bala'in kyau. Kunsan dai Kanuri mune turaren wuta da humra, namu da banne, ke kanki in kika yi amfani da waɗannan set zaki gode mun. Akan farashin 10k kacal na bar muku farashin promo domin ku. Mutum ishirin kaɗai zan cire suke da damar mallakar wannan setin mai sanyin daɗi. Kuma iyakar ƴan paid group ɗina ne kaɗai zasu samu wannan garaɓasar. Ku yi hanzari duk mai buƙata ta kasance a cikin mutum ashirin da zan ɗiba.)*
Da sauri na miƙe tsaye kamar ba ni bace na wuni sukuku. Baki na riƙe kawai ina kallon Kaila. A guje Bilkisa da Hajiyayye suka fito. Hajiyayye tana ganin abinda ya faru taja wani irin dogon tsaki tayi komawarta ɗaki. Dama ɗakin nata cike yake da ƴan uwanta. Kamar yinwataccen zaki haka Kaila ya dira a wuyan Sani ya far mishi da mahaukacin duka, tamkar yana dukan ƙato. Dama haka yake musu irin wannan dukan. Bilkisa ta isa a guje ita da Hindatu, amman sun kasa ƙwatar Sani a hannun kaila. Har ya fashe mishi ɗan bakin nashi. Tsam na miƙe na koma ɗaki. Yaran suka biyoni ɗuu. Zaunar dasu nayi, ni ko na kasa zaune na kasa tsaye, ina jiyo Sani yana kirana.
"Umma ki ceceni zai kasheni, wayyo Baba wallahi bansan kana zuwa bane, wayyyooo" Kuka na fashe dashi, har muryar Sani ta dashe. Baban Mustapha ne ya burmo gidan namu. Ina jiyo muryarshi tun daga zaure. Shine ya ƙwaci Sani a hannun Kaila. Da mugun gudu Sani ya shigo bakinshi na zubar da jini da yawu, gefen idanshi ya kumbura. Ƙanƙameni yayi tsam sai cusa kanshi yake a jikina. Hannuna na ɗaura a saman kanshi ina shafawa.
Ya'isa kayi shiru kaji Yaya. Babu komai, ai mahaifinka ne hukunci yayi maka. Muje in wanke maka bakinka, ku ci dumame ku kama hanyar makaranta, kayi shiru ya'isa" Da ƙyar a ranar nasa Sani ya yarda ya tafi makaranta, bakin shi ma ya aune sosai. Ko bayan tafiyar su Sani makaranta na jima a ɗaki ni kaina bansan zaman me nake yi ba. Ni ba tunani ba, ni bansan adda'ar da zan dinga yi domin kore damuwa da baƙin ciki ba. Habiba Bala ce ta sanyaya mun raina data kira take sanar dani an yi ma Dauda tiyata cikin nasara, amman yana bacci a lokacin. Wani irin farin ciki ne ya sauka a zuchiyata. Kawai na sau ma Habiba Bala kukan farin ciki, sai jero mata godiya nake yi, ita kuma tana ta rarrashina, da haka mu kai sallama. Ina dai zaune, bani na fito ba sai wajajen goman safe. Kiki_kiki na ɗaura miyar dare, tana tafasa na kaɗa. Miyar kuɓewa nayi bushasshiya, Sai na mayar da ruwan wanka kan wutar, na soma yanke farata na, waɗanda suka cika da datti, sunyi baƙiƙƙirin dasu. Tas na yanke farcen ƙafata dana hannuna, na faɗa bayan gida, ina cuɗawa na bi da ruwa na fito. Misalin dayan rana sai ga su Sani sun shigo hajaran majaran sai warin rana suke dokawa."
"Umma yinwa" Cewar Shafi'i dama shi kam ba mai jurar yinwa bane sam. Sani da Sulaiman ne dai masu dama dama. Balaraba ita bata zuwa boko, islamiyya kaɗai take zuwa. Abinci na zuba musu su ka ci, dan zumudi ni ko abincin na kasa ci. Ƙarfe biyu bata cika ba na saka inifom ɗina har nayi goyo. Yara suka kalleni suka kwashe da dariya, Sani har yana ƙwarewa. Nima dariyar nayi bance uffan ba. Farin hijabina na saka na rataye jakata.
To maza ku yi ku gama mana. Ku je gidan su Mustapha ku yi wasanku, in lokacin islamiyya yayi sai ku je tare. Sani banda zuwa wanka rafi, dan Mustapha ya faɗa mun kana bin yaran gidan Rahilu. Ni zan je makaranta ku yi mun adda'ar samun nasara." Adda'a su kai ta mun. Raina fes na fito zauren, dai_dai Hajiyayye ta rako ƴan uwanta zaure. Turus Hajiyayye tayi kawai tana kallona. Ni ko da ganinsu gabana ya yanke ya faɗi. Dan banso nayo arba da kowa ba. Da sauri na ɗauke kaina, ina rufe ɗakina na jefa ɗan mabuɗin a jakata na fice. Yara su ka bi bayana. Da sallama mu ka shigarma Sabira. Tana ganina ta soma tafa hannaye.
"Ga ƴar makaranta, ga ƴar makaranta" Dani da yara duka muka tuntsire da dariya.
Sabira baki da dama. Ga yarannan. Sabida in na barsu a gida ba lallai suje islamiyyar ba." Sabira tace.
"Yau bana nan na fita, sai da na dawo Abban Mustapha yake faɗa mun irin dukan da Abban Sulaiman yayi ma Sani. Gashi idanunshi sun tara jini." Na ƙwafe wannan dukan sosai a raina. Sosai nake jin zafin dukan, har bana so ayi zancan. Bagarar da hirar nayi ta hanyar juyawa da gudu_gudu. Sai a zaure mu kai sallama na kama hanyar makaranta. Aji ya cika bundin, ni dai bancin ƙarshen aji na samu, mu biyu ne a bincin ni da wata dattijuwa. Mata sai hira suke yi ana tafi. Malami bai shigo ajin ba, shewa kawai kike ji yana tashi. Ni kuma sai kallonsu nake yi, ina mamakin wai yau nice a zaune a aji a karo na biyu. Bayan haihuwa ta takwas, Allah mai iko, Allah ya bani nasarar karatu. Ina cikin tunanin nan sai naji ajin ya yi tsit, ashe malamine ya shigo.
"Sababbin zuwan mu su je ajin ƴan B su mayar da form dinsu da fasfo, za'a rubuta sunansu a rijista. Ni dai na taso amman sai harɗewa nake yi. Duk inda na walga kallona mata suke yi kamar wata baƙuwar halitta. Har na fita na jiyo Muryar wata mata na faɗin.
"Baiwar Allah kuɗin cizo suna bin hijabinki ta baya" Da sauri na waiga bayan nawa ai kuwa na gansu har uku, yatsana manuniya nasa a baki na dangwalo yawu na kamo kuɗaɗen cizonnan na kashesu a ƙasa. Kab ajin ni suke kallo. Ni kuma ina ɗagowa nabi ayarin mata biyun da suka nufi B likas dan mayar da fom. Muka mayar da fom sunanmu ya shiga rijista. Da darasin lissafi muka soma ( maths) Nan dai na shiga rubutu hannuna na kakkarwa, har wani zufa hannuna ke yi dan tsoro. Abubbuwan dai gasu nan ga kamarsu gani nake tamkar ban taɓa shiga aji ba. Ko malamin turanci daya shigo ni dai ina zaune dunkum kawai. Gashi sai aikin gida suke bamu ( home work) Ni dai kwafewa kawai nake yi, wasu abun dai nakan haɗa in furta kamar mai koyon magana. Ana cikin yin darasin gona, agiric Salis ya soma kuka.
"Wacece ɗanta yake kuka? Ta fita waje in ma ta shayar dashi, ko ta rarrasheshi. Ya kamata ku dinga zuwa da mataimaka da zasu dinga kula muku da yaranku, iyakarku dasu ku fita ku basu Mama ko ruwa" Da sauri na fita, dama fitsari nake ji. Sai da na nemi ban ɗakin makaranta, ashe basu da banɗaki sai na malamai, ɗalibai sai dai su shiga maƙota. Nima maƙotan na shiga na soma yo fitsarin. Ina dawowa makaranta ana buga ƙararrawar yin hutu. Gefe na samu na yaye hijabina na dumbulama Salis nono. Yayi maza ya cabka ya shigo tsotso yana sauke ajjiyar zuchiya. hutun minti talatin muka yi. Ina gani mata sai siyayyar ƙwalam suke yi, ni kam inaa. Aji muka koma muka ci gaba da ɗaukar darasi, wallahi ji nayi bana iya fahimta, ƙwaƙwalwata ta toshe sosai. Har ƙwalla sai da na tsiyayar dana tuno ƙoƙarina wajan karatu da naci. Duk abinda ya gagari su Habiba Bala da su Halima Bawa, ni ake kawo ma, har mayya suke ce mun. Dan ina da ƙwaƙwa ko darasi akayi mana komawa ɗaki nake in ta bitar karatunnan, ko kuma in shiga ɗakin karatu na cikin makatanta wanda aka tanada domin ɗaliba, ni dai ku barni da ƙazanta kawai. Kuma ni ban ɗauka abinda nake yi ƙazanta bane, dan a haka na taso na tarar da mahaifana, da yayyena. Amman yau gani a aji bana ko gane komai. Dattijuwar dake gefena ta taɓoni.
"Baiwar Allah an tashi fa, bani wuri in wuce" jakata na raruma na matsa mata, nan na shiga kiciniyar goyon Salis, wannan dattijuwar ta dubeni tace.
"Wannan goyon ai ɗanyene, kuma zai barki kina fahimtar karatun kuwa?" Ɗan murmushi nayi nace.
To zan jaraba dai, amman ban fahimci duk abinda akayi ba ma yau. Ƙila sabida na daɗe rabona da shiga aji "
"To ki dinga tawowa da wacce zata dinga miki renon yaron. Ke kuma sai ki nutsa kiyi karatun dan yana da matuƙar mahimmanci sosai. Kuma nan ai makaranta ce duk wanda kika gani koyo yazo yi. Duk abinda ya shige miki ki yi tambaya ko malami ko ɗaliban ilimi. Sai gobe ko?" Godiya nayi mata, muka fita a tare kowa ya kama gabanshi. Inata ta tafe, kwasham_kwasham bani na samu abun hawa ba har sai da na nazo kan babban titin zangon baƙi tukunna, Minti goma ne ya kawo ni bakin layinmu.
Da shigata gidan nayi maza na buɗe ƙofata na ƙule bana son kowa ma ya ganni. Kayan makarantar na tuɓe na mayar da kayan gida. Salis yana kwance yana baccinshi rai ɗaya. Da Bilkisa naci karo tana riƙe da ƙatuwar leda.
"Umman Sulaiman kin dawo ashe? Nazo har sau biyu baki nan" Yangar maganar Bilkisa burgeni yake yi, harma nake jin kamar tafi kowa iya sarrafa harshe. Duk da naji Habiba Bala ma haka take karya murya.
Na dawo yanzu" Na bata amsa. Kaila ne ya nufo mu sai ƙamshi yake yi, cikin ado da kwalliya yake. Yana ganinmu tare ya dubeta yace.
"Wai me yake kawo ki wajan Shanono ne Ɗanyan gwal? Ni sai in ga kina shige mata da yawa ai" Da zafin harshe ya fesar da kalamin. Wani mugun kallo ta watso mishi tare da ƙare mai kallon sama da ƙasa.
"Kar ka sake ka sake ɗaga mun murya. Ko mun yi da kai duk abinda zan yi sai ka sani ne? Ni fa ko a gida banga uban da ya isa ya takura mun ba." Baki ya sake yana kallon Bilkisa data mugun haɗe ranta, kallona tayi tace.
"Kaya ne dama na fitar suna nayi miki ke da Dady na. Mummy ma tace in miki Barka ranar suna ƙanwata zata zo suna. Allah ya raya Dady." Da dariya na karɓi ledar.
Kai amman na gode sosai Bilkisa amman babu ma suna kar ki wahalar da me zuwa."
"Amman me yasa ba suna?" Ta jefo mun tambayar amman idanunta na kan Kaila wanda ya ƙula ainun. Murmushi nayi nace.
Babu kawai dai, haihuwa bata fari ba, taron bikin suna ai sai ku" Baki ta taɓe ta yi wucewarta. Tana shiga cikin gida nima na faɗa ɗakina. Kaila ya bita fuuu zuwa turakarshi.
KAILA:
Tsabar jaraba har baya iya gani. A hargitse ya shiga ɗakin ya tarar da Bilkisa a tsaye ta riƙe ƙugu.
"Ke Bilkisa yanzu dai_ dai kenan a gaban shanono ki dinga nuna ban isa dake ba? Ni fa duk na soma gajiya da lamarin zaman aurennan wallahi. Mu kenan bama kwana biyu cikin jin daɗi. Jiya ina ji ina gani kika hanani kanki a shinfiɗa............... Dakatar dashi tayi da cewa.
"Dakata mun, ni ba'a mun faɗa, kuma na gaji da aurenka tafiyata zanyi gidanmu, na gama aurenka kenan. Bansan dama kai ba adali bane a gidanka ba da bazan shigo ba ma" Hanyar fita ta shiga nema. Carab Kaila ya riƙeta ƙam. Shine harda tsugunnawa yana roƙonta tayi haƙuri, da ƙyar ta haƙura, da taga kaila na shirin zubar da hawaye. Amman sai ta shiga fishi dashi. Kiran