Showing 54001 words to 57000 words out of 68990 words

Chapter 19 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

Sai da suka gama kewaye gidan kana suka fita. Tabarma Sabira ta shimfiɗamun a tsakar ɗakina, ina kwanciya wani wahaltaccen baccin gajiya ya sureni, maganin da Habiba Bala ta bani harda mai sa bacci. Bani na farka ba sai la'asar. Wayata na jiyo tana kuka a tsakar gida. Da sauri na fita dan in ɗauko. Ina fita su Hajiyayye suna shigowa an sallamesu daga asibiti. Cirko_cirko mu ka yi a tsakar gidan dukkanmu daga ni har su. Cike da kallon tuhuma Hajiyayye tace.
"Ki kashe mun Ɗan Amman har ƴan sanda su sako ki. Ubanki waye tukunna a garin Jos?" Kusun uwa in na yarda me nake.............✍🏻


_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_

_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_

*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*


*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S

*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224

*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*

*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*

*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*

*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*

*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*

sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*

KAMARSU👇🏻👇🏻

*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*

DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻NA FAƊO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 15



💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*(Assalamu alaikum masoyana. Haƙiƙatan naji daɗin yanda kuke yaba rubutuna, da yanda nake tafiyar da salon labaraina. Babu abunda zance daku sai kodiya. Yau na tashi sai wasu uziri suka same ni, wanda bazai bani zarafin yin typing akan kari ba. Sai na yanke hukuncin sanar da masu bibiyar rubutuna cewar su yi haƙuri ina da uziri, ba zasu samu jina ba har sai na samu al'amura sun warware mun. Allah cikin ikonshi jim kaɗan da yin wannan maganar, saina soma samun kiraye_kirayen waya daga masoyana. Na kuma dinga cin karo da saƙonninsu wanda in na karanta wani ban isa na karanta wani ba. Duk dai ƙorafinsu shine, in taimaka zasu yi kewar Shanono. Wata tace tana cikin ɗakin jarabawa amman hankalinta na kan wayarta. Duk wanda zai yi ma rubutunka haka ai ba ƙaramin masoyinka bane. Ummu nabeeha, da su Khadija Amarya, Maman Amal, Khadija mai doki, Salma musa, Mamagee, da duk members na cikin zauren NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA. duk sun tashi hankulansu. To ga page 15 na baku. Amman zai iya kaini mako guda kafin in gama uzirin dake gaba. In sha Allah zan dawo da zafi. Nagode)*


SHANONO
Bance da Hajiyayye komai ba, sai buyagi take yi. Nazo nayi wucewata ko sake kallonta ban yi ba. Ina jiyo Yayarsu tana ƙunduma manyan zagi a tsakar gidan. Sabira ce ta shigo ɗakina da sallama, hannunta riƙe da kwanon abinci. Wayata ce ta shiga ruri a karo na biyu. Yaya Karime ce take kirana, dagawa nayi tare da kara wayar a kunnena.
Yaya Karime ina wuni?" Daga cikin wayar akace.
"Inno ce Tani. Yaya kun isa gida lafiya dai ko?"
Lafiya lau Inno yaya biki?" Dariya tayi tace.
"Ƴan uwanki sun so ganin ki. Barinma ƙawarki Shafa, yaranta goma fa yanzu, jin labarin kin shigo Shanono sai gata a gidan biki. Yaya Kaila ya yarda da zaman Dauda ba wata matsala ko?" Tsintar kaina nayi da cewa.
E ya yarda Inno." Baki ta washe tace.
"To barka ni dama dalilin da yasa na kira inji kenan. in na dawo zan zo in ɗaukeshi. Sai mu yawata dashi muna bara ina nuna ma mutane ciwon nashi. Ba karamin kuɗi zamu samu ba, kinga muma ma samu a jikinshi. In muka tattare kan kuɗin ko asibitin miya barkatai ai sai a kaishi su yi mishi aikin ko Tani?" Idanu na lumshe na tuno lokacin da muka sauka a Bamaina dake jihar jigawa, Inno ta ɗaure mun ƙafata, ta samo jini a kwata ta kwara mun a kafata, haka mu ka fita mu kaita neman kuɗi a haka. Na sha wuya sosai, Amman mun samu kuɗi sosai. Watanmu biyar kullum sai Inno tayi mun haka
A'a Inno ai Dauda wata ƙawata da mu kai karatu a Bauchi ta ɗauki nauyin biyan kuɗin aikin nashi. Yanzu haka ma suna Bauchi tare." Inno ta yi sanyi da murya, a maimakon taji daɗi, sai ma ta nuna irin ita tafison ta yawata da Dauda, sabida ba karamin kuɗi zata samu ba. Yaya Karime ce ta karɓi wayarta muka gaisa. Daga ƙarshe su kai mun sallama tare da kashe wayarsu.
"Tani ga abinci maza kici. Wai Hauwa tana Shanono ne a wajan su Inno?"
Hmm tana can, sai sun dawo zasu kawo mun ita. Nagode da hidima Sabira " farfesun kan saniya ta zuba mun da farar shinkafa. Ai kuwa naci sosai, ta bani magungunana na sha suma. Sannan nace mata.
Habiba Bala ta bani kuɗi in koma makarantar islamiyya, da boko. Kuma nima dama na riga na ƙuduri niyyar hakan. Dama jira nake in haihu, zaman rashin karatu bazai fissheni ba Sabira. Kinga kuɗin" Ƙasan fulon da nake kwance na bankaɗa na ciro kuɗin, na ba Sabira a hannunta.
Kinga kuɗin ko. Tace abinda ya ragu sai in soma ƴar sana'a domin dogaro da kai. Ke meye shawararki akan hakan? Wacce makaranta kike ganin ya dace in shiga?" Sabira dake riƙe da kuɗin a hannunta tana jujjuyasu tace.
"To tunda naga kuɗin da yawa. Inaga a shawarce ki shiga islamiyyar matan aure *UMMAHAT* Ta cikin al'iman. Kinga Mrs Bukhari ma makarantar tayi, nima gashi ita nake zuwa. Jumma'a, asabar, lahadi ne ranakun zuwan, kinga bazai taɓa makarantar bokonki ba. Kuma zaki ji larabci sosai dan ba'a Hausa, ( Allah sarki malama musriyya, malama Hajara, malama Zarah, mun sha larabci) zaki haɗu da mata wayayyu ƴan ƙarya. Nima gaskiya makarantar ta sake gogar dani na sake fahimtar yanda zan mallake Baban Mustapha. Bokon kuma zamu bincika wata makarantar matan aure dake cikin shaƙura, can unguwar rogo ƴan kwaba. Akwai wata makarantar matan aure masu jajayen wando sai mu bincika. Maganar islamiyya kuma zan sa Baban Mustapha yai ma abokinshi magana suna ɗarasawa da munir director ɗin makarantar asamu a saki a aji ɗaya. Kinga in kika gama makarantar nan har zuwa aji shida? To zaki samu takaddar zaria, zaria suke kiran takaddar, da wannan takaddar zaki iya samu admission a jami'a kai tsaye in islamic studys kike son karanta. Mu kinga saura shekara ɗaya mu gama." Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
To sabira Nagode sosai. Yanzu ni gobennan nake son mu je shaƙuran mu ji yaya za'ayi in samu makarantar nan. Tunda dai kuɗin sun samu, ba'a bori da sanyin jiki."
"Ke zaki iya fita ne da wannan kumburarriyar fuskar Tani?" Da sauri nace.
Ai ko yanzu kika ce mu je, miƙewa zanyi kawai" Dariya tayi tace.
"Goben sai mu je sassafe in Allah ya kaimu. Batun sana'a kuma mu cire sati guda mu yi tunani tukunna. Dubawa zamu yi muga menene a cikin anguwarnan yake da wuyar samu,wanda har sai mun dangana da titi, koma kasuwar ƴan tifa ( new market)?
Kayan miya, musamman attarihu da albasa" Na ce mata.
"To kinga shikenan sai ki soma zuwa farar gada kina sarosu, shikenan ma muma mun huta. Kuma zaki sha ciniki sosai."
"Ɗazu da ki ka yi bacci ai gida na shiga Baban Mustapha ya dawo. Shine yake faɗa mun jiya ya ba Baban Sulaiman aron million biyu, yana son zai ƙareshi abubbuwan da bai yi ba a sabon gidanku. Wai yana son nan da sati ɗaya ku koma sabon gida. Sabida wai Baban Bilkisa ya kirashi wai ita Bilkisan ta yi ma mahaifinta ƙorafin ita wannan gidan ba zata iya rayuwa a cikin shi ba. Shine na ba Baban Mustapha shawarar tunda Baban Sulaiman ɗin siyar da nan gidan da kuke zaiyi, to ya siya kawai tunda dama zai siyar ne dan ya biya shi kuɗinshi. Na taya ki murnar zaki rabu da wannan akurkin, tunda kince a sabon gidan yara ma suna da ɗakinsu. Amman Tani zan yi rashinki da yaran baki ɗaya. Sauƙinta ma zaki soma zuwa makarantar mu" Ni dai kai kawai na gyaɗa ma Sabira, tamkar ya jin ƙosai na kasance wato a rayuwar Kaila. Ada har sai na kori Kaila yake iya zuwa gareji. Ni tunda nake aure, ban taɓa haɗuwa da masoyi irin Kaila ba. Amman jibi yanda komai ya juya, duk a sanadiyyar shigowar Hajiyayye rayuwarmu. Yawu na haɗiye kawai. Mun jima muna tattaunawa ni da Sabira. Na ce mata ta riƙe wannan kuɗin a hannunta tukunna. Sai da aka fito sallar magriba ta tafi. Bayan ta shigo mun da katifuna. Bata jima da fita ba yaran suka shigo. Nan suka dame ni da haya_haya. Bayan isha sai ga Kaila bayan har yaran sun soma bacci. Idanu ya ƙura mun kawai, yana tsaye ƙerere a tsakiyar kwanyata.
"Shanono kenan. Yaya akayi kika dawo gida, kuma wa yayi belinki?"
Ikon Allah" Iyakar abinda nace dashi kenan.
"Shi yaron da kika ɗakko a Shanono kin fitar mun dashi ne ko kuwa yana nan? In kuwa yana nan wallahi daga ke har shi baku isa kun kwana mun a gidaba. Dan bazan iya riƙe agola ba. Kema da kike zaune a gidannan dan yarane fa, amman wallahi da baki isa amsa sunan matar Kaila ba."
Kayi haƙuri, Dauda baya nan. Amma zai dawo. Kayi ma Allah kaila ka barni in rayu da Dauda. Yaron yana cikin damuwane. Fyaɗe akayi mishi kuma acan gidan Baban nashi an rasa wanda zai iya kulawa dashi ne. Yaron yana buƙatata. Dan Allah Kaila. Ƙur yayi mun da idanu yace.
"Hiye ba shakka Shanono. Acan gidan uban nashi an kasa riƙeshi sai ni ne zan riƙe shi ko? To sai ki zaɓa ai ko riƙe yaronki da kika haifa a Shanono. Ko riƙe su Sani, zaɓi ya rage gareki. Shawara ta rage ga mai shiga rijiya. Bani yaro in mishi huɗuba ni, wani irin tunani irin na jahilan ƙauye" Jiki a sanyaya na miƙo mishi yaronshi, ina tsugunne a wajan ko tausayina zai taɓa zuchiyarshi. Huɗuba yai ma yaron ya miƙo mun yace.
"Na sama yaro suna Salis, sunan mahaifin Bilkisa. Kuma bana buƙatar wani taron suna, in sun zo ma nan da wata tara zasu sake zuwa wani taron. To na gaji, kya bari kuma in ji da bikin sunan haihuwar Bilkisa in ta samu ciki, da Hajiyayye " Hannu nasa na karɓi ɗana. Shima ya fice. Mamaki nake yadda za'a sa ma ɗana sunan uban kishiyata sabida mulkin mallaka, ko turawan mulkin mallaka ai ba zasu yi wannan kama karyan ba. Da wannan surkullen tunanin nayi bacci. Nayi bacci a wannan daren sosai, irin baccin da na daɗe banyi irinshi ba. Magungunana akwai masu saka bacci.
Washe gari.
Tun sassafe nayi duk kaye_kayen daya dace. Ko da na fito tsakar gidan, sai banga buhunhunan tsunmokaranmu ba. Sai Sani ne yake faɗa mun Sabira ce ta fita dashi, su suka rakata gidan wankau ta kai mana kayan. Yarona nayi ma wanka. Ni kuma ko wankan banyi ba, bakina kawai na goge da gawayi da gishir, sai ƙunzugu dana sake. Na ɗan yi kwaskwarima na shirɓina mai mai gurguwa sai walƙiya nake yi. Ina cikin goya Salis Sabira ta shigo.
"Oya fito muje, dan ina da islamiyya yau" nera ɗari uku na ba Sani.
Ungo ka siyo muku masa kuci. Sai ku fitar da katifar fitsarinku ku sa ruwa. Mu sai mun dawo." Adawo lafiya su kai mun, muna zuwa titi mu ka hau napep na unguwar rogo.
"Tani. Ga shawara akan lamarin fitsarin yarannan. Ni ina ganin kinga katifunku dukka ko? Ki siyar dasu gaskiya sai a sai wasu na hannu a bayan masallaci, tunda Habiba Bala ta baki isassun kuɗi. Sai mu sai ledar fitsarin kwance, yarannan kuma Tani ki dinga daurewa kina tashinsu yin fitsari mana. Kayanku na kai gidan wanki, saida na yayyafa musu fiya_fiya kinga kuɗin cizo yanda suke gudu a kayan kuwa? In an wanko sai ki tsince waɗanda suka yayyage dan Allah ki zubar ko ki ba almajirai. Ni bana son kuje sabon gida da kuɗin cizo kuna ɓata bango, maganar gaskiya ran kaila fa ba zai yi daɗi ba. Ga makaranta zaki shiga. Kina zuwa a ƙazance daga malaman har ɗaliban rainaki zasu yi, ki gyara ke ma kiji daɗi mana"
To Sabira in sha Allah zan gyara." Haka mu kai ta tafiya har zuwa bakin lungun da zamu ɓulle zuwa cikin makarantar. Muna tafe ina adda'ar Allah yasa su ɗauke ni. Makarantace ta gwamnati babba, mai suna G S S UNGUWAR ROGO. amman sabida yanda sha'anin kasar tamu ta zama ne yasa ake kiran makarantar da suna shaƙura, tsabar yanda malamai suka ƙi tsaiwa su yi aikinsu, sai dai ɗalibai sui ta buga tamaula. Itama gwamnati taƙi tsaiwar daka wajan ware kuɗin malamai. Sai makarantar ta zama gata_gata. Duk fa da haka ɗaliban shaƙura sunfi ɗari, in aka tashi cika titin mota suke haka zaku gansu kamar fari. To ita wannan makaranta ta matan aure a cikin shaƙurar take. Wasu malamai masu zaman kansu ne suke kula da makarantar, sai in ɗaliban shaƙura sun tashi misalin ƙarfe biyun rana. Sai makarantar matan auren a soma biyu da rabi, zuwa ƙarfe biyar a tashi. Kamar yadda wani malami yake yi mana bayani. Form muka yanke nera ɗari biyar, yace in cike ran monday ma zan iya soma zuwa, sai in dawo da fom da fasfo guda biyu. Na biya kuɗin karatu na zango na ɗaya wato S S 1nera goma. Sai jerin littafai daya rubuto mana wanda zamu je bayan banki mu siya, dana rubutu dana katatu. Muka gama komai tas. Kai tsaye sai gamu a bayan banki. A wajan inyamuran bayan banki muka sisiyi littattafan da aka rubuta mana duka, na sai jakar gwanjo, da baƙin sandal shima na gwanjo, da safunana biyu farare tas. A wajan mu ka yanki yadin inifom jan wando, farar riga da farin hijabi. Sabira ta ban shawarin yankan yadin inifom ɗin islamiyya shi kuma mai ruwan toka ne duka, sai baƙar safa da baƙin takalmi, sai ta kaini akai mun fasfo. Dan murna zuchiyata har tsalle take yi. Duk muka sai abunda ya samu. Sha Allah sai muka dira a gidan mai ɗinki, ta mun duk gwajin daya dace. Kuɗinta dubu da ɗari biyu ta cajemu. Muka yi da'ita gobe da yamma Mustapha yazo ya karɓa mana. Bamu muka shigo gida ba sai tara da rabi. A bakin ƙofar gida mu kai sallama da Sabira, dan tayi lattin makaranta tara dai dai suke soma kilas. Ina sa ƙafa ina shiga cikin zauren Kaila ya hankaɗoni waje, na tafi taga_taga amman cikin ikon Allah ban faɗi ba. Sai ji nayi Bilkisa tace.
"Baki ji ciwo ba ko umman Sulaiman?" Ashe tare suke taci ado na tada gari, kallon kaila nayi, ashe farin takalminshi na na taka mishi. Gashi hatta kafata ƙurane bajaja balle takalmina. Ajjiyar zuchiya nayi nace.
Banji ciwo ba Bilkisa. Kaila kayi haƙuri bansan ka tawo ba. Da sauri na zamo kallabin kaina ina shirin goge mai takalmin dan gujema tozarcinshi ya dakatar dani cikin ɗaga murya.
"Kar ki sake ki ba ɗa mun ƙwarlwata. Jeki nagode, kece kina tafe bazar bazar, kamar akuyar ballagaza, kinga kuwa ina akuyar ballagaza zata samu nutsuwa?" Tsaki ya ja ya dubi Bilkisa yace.
"Ɗanyan gwal jirani in sako takalmi. Wannan ɗin sai a ba Shamwila ta wanke." Buu ya shige ciki. Bilkisa tace.
"Kiyi haƙuri dan Allah ummun Sulaiman. Banji daɗin abinda yayi miki ba" Ɗan dariya nayi mata nace.
La ai babu komai. Ai ibadar aure ta ƙunshi abubbuwa masu tarin yawa." Ɗan murmushi tayi itama tace.
"Dama Gwanda ne yace yana son ya kaini gidan da yake ginawa in gani. Kinsan ai sati mai zuwa zamu koma sabon gida ko, kuma kinsan ya siyar da wannan gidan ko?" Dariya nayi nace.
Na ji dai a bakin ki yanzu.
To Allah ya sanya alkairi yasa a koma a sa'a." Ina faɗin haka na shiga ciki tare da cewa da'ita.
Sai kun dawo."


*KAILA*
Yana shiga ya tarar da Shamwila ɗare_ɗare a kan gadonshi tayi goho tana lailaye mishi. Mazaunanta yabi da idanu, sai wani muskutasu take yi suna tanjan_tanjan. A zuwan bata san da shigowar Kaila ba. Kuma tana sane fes. Jikinshi taji ya haɗe da nata. Tayi wata iriyar zaburar da babu inda bai kaɗa ba a jikinta ba. Tsam Kaila ya ƙanƙameta yana kokawa da numfashinshi wanda yake shirin ɗaukewa. Da ƙyar ya lalubi kunnenta yace.
"Kaila ne. Kar ki yi ihu nine. Grayan gado kike yi?" Yanda yake jan maganar ba ƙaramin gigita Shamwila yayi ba. Dama Kaila gwanine wajan iya sace zuchiya. Saurin fisge jikinta tayi a nashi, tare da faɗawa kan gadonshi, tana wani irin ja da baya, ga wawan zama da tayi. Ba shiri Kaila ya bita. Ƙaran wayarshi ne ya ankarar dashi aika aikar da yake shirin yi. Babu shiri ya fasa bin Shamwila ba dan hakan yaso ba. Wayarshi ya miƙa mata.
"Samun number ki anan. Zan kiraki anjima ki je A 1 ki same ni ko S F C." Da sauri Shamwila ta tiyfa mishi numbernta ta bashi wayar, bayan ta tabbatar hannunsu sun haɗe dana juna. Takalmi ya sake a gurguje ya fice." Kama hanyar filin sukuwa su ka yi anguwar da Kaila yai gini kenan. Unguwar masu kuɗi da amare, unguwa mai tsari marar hayaniya. Da a wajan ake yin polo ( KWALLON DOKI) A lokacin turawa ke yin wasan. Sai masu talle da ke ai kayan sana'arsu. Daga baya gwamnati ta yanka filin, jama'a su kai ta tururuwar saye. Cikin ikon Allah unguwar sai ta shahara, ta zama babu irin unguwar a cikin garin jos, sai dai ta bayan gari can. A wannan unguwa Allah ya hore ma kaila katafaren gida mai ɓarayi uku. Sai ɗakuna falle falle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login