Showing 9001 words to 12000 words out of 68990 words
Chapter 4 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
nata nace ta ajjiye mishi, na ƙullama ƴarta a leda kamar yadda na ƙullawa su Sulaiman, na miƙama Hindatu nasu nayi shigewata ɗaki. Ina zaune ina shan shayi da nama na jiyo muryar kawata tana tambayar bana gidanne. Ina jin Hajiyayye tana faɗa mata cewar.
"Ta koma ɗakin zaure Aure mai gidan zaiyi zai sa amaryarshi a nan ɗakin" muryarta fes cikin nishaɗi dama nasan wannan rashin darajar da Kaila yai mun dole zai faranta mata. Da sallama maman Zuhura ta shigo ɗakin da nake, taci ado irin na asalin mata gaske waɗanda maza suka amshesu har suka samu yardarsu.
"Tani kece haka a cikin wannan ɗakin mai kama da akurki?" Murmushi nayi mata kawai. Waje ta samu ta zauna, shayi na zuba mata, na miƙo mata nama leda ɗaya.
Bismillah jiya kika ce zaki shigo baki shigo ba, bismillah zauna a bakin katifa mana" Zama tayi a sanyaye.
"Tani kuma kin yarda kin amince Kaila ya fitar dake a ɗakin ki kina uwar gidanshi yasa amarya a ɗakin ki? Ya kasa bari kici albarkacin yara ma, bacin in ya mutu a halin yanzu sai dai a tsakurama matanshi da sauran yaran wani ɗan abu. Ai kinci gidan taya zaki rayu a irin wannan ɗakin ke da yara? Me yasa ba zakiy tsaiwar daka wajan ganin kin kwaci ƴancin kan ki ba, bari kiji iyayenmu bafa zasu goyi bayanki su barki ki ƙwaci ƴancinki ba ma, balle kiyi tunanin su da kansu su ƙwatar miki ƴancinki. Ya da jininki a jiki zaki zauna baƙin ciki Kaila dana kishiya ya halakaki? Yanzu fa Hajiyayye fa cikin farin ciki take faɗamun abunda ya faru. Shigowa nayi na samu suna gulma da facalarki fa. Kema Tani ƙazantarki tayi yawa, dubi jikin ki fa, ji nono yanda ya ɓata miki riga, ko rigar mama bakya sawa, kullum ke kenan cikin riga daban zani daban. Ko kitson sallah ma baki samu yi ba, kin kama ƙafarki data yara kin muku baƙin lalle wanda ake sama gishirin lalle. Wallahi in baki gyara ba, ke ma fa ba zaki ga da kyau ba. Sannan tunda kun dawo ɗakinnan kuɗin cizo ku dena kasheshi a bango dan Allah, ki ke gyara jikin ki ko kema zaki samu iska mai kyau" Ajjiyar zuchiya na sauke cikin nauyin ƙirji nace.
"Sabira bari in faɗa miki na jima da tsanar gidannan da mai gidan baki ɗaya, bani da kuzarin iya gyaran jikina, kina gani kullum zaki ganni da goyo da ciki, ni fa sai in yi wata ban kama nera biyar ma tawa ba, miji baya yi da kai, kowa ma haka ni yaya akeso in yi ne. amman yaya zanyi ne da rayuwata Aure na huɗu ne suka mutu wannan shine na biyar. Iyayena basu da wani burin daya wuce suga ina zaune a ƙarƙashin inuwar aure. Sabira dukka wannan aurarrakin da nayi suka mutu. Mahaifina ya ɗaura alhakin mutuwarsu a kaina. Gani suke rashin haƙuri ne, da kai mazajen bango yasa duk aka koroni. Dauda dana bari a Shanono tunda na bar Shanono ban sake sashi a idanuna ba Sabira. Inno dai tana zuwa dubashi in suka je ganin gida, kuma ina mai aiken duk abunda Allah ya hore mun. Yaronnan yana tsakiyar shan nono mahaifinshi ya tsigeshi a kan cinyata bazan mance ba, ya danƙashi ga kishiyata Tamaulidi ni kuma yai mun korar kare. Naga abubbuwa da dama da bana so ma in shiga labarin. Wadannan yaran zamansu nake yi bana so su yi maraici kamar yanda Dauda ya taso cikin maraicin uwa, kuma an faɗamun ba ƙaramin azaba matar uban take gana mishi ba. Inno tace in zata je wannan karon in mun je zata kaini in ganshi.
"Amman Tani ni ina ganin akan yara bai kamata mu dinga nuna ma maza dole sai mun rayu dasu ba. Kinga wannan maganar zaman yaran da aka ƙirƙireshi a cikin kabilar Hausawa ita ta ja kusan rabi da kwatan matsalolin matar Bahaushe. Da ace yanda kika haƙura kika tafi kika bar Dauda kuma baki sake waiwayarshi ba, da hakan ki kai ma Kaila ki zube mishi yaranshi ki samu ki shaƙi iskar ƴanci" Murmushi nayi mata wasu hawaye suka surnano mun. Sabira bata san raɗaɗin dake zukatan iyayen da suke rayuwa a wata duniya, ƴaranta suma suna rayuwa a wata duniyar ba ne. Da tasan irin tashin hankali da uƙubar dazan tarar a gida, da irin tsangwamar da ƙabilar Hausawa ke ma bazawara da bazata ce in kashe auren ba. Nashiga kunci rayuwa kashi daban_daban wannan yasa banason shiga cikin ainihin rayuwar dana tsinci kaina a gidajen sauran mazajen nawa huɗu. Mahaifina har cemun yayi na zama karuwa in ɗanɗana wannan namijin, in fito in ɗanɗana wani, auren sha'awa kawai nake yi da mazajen. Babu sanda aka taɓa jana a jika domun in samu sauƙin zugin zuchiyata. Haka Sabira tai ta bani baki tana bani haƙuri akan cewar wataran sai labari. Ni kaina ina roƙon Allah yaimun tsawon ran da zanga ranar labarin. Sai da ta ɗan kwantar mun da hankali sannan tace mun zata tafi. Samosa ta kawo mun cikin leda, har bakin ƙofar gida na rakata ta tafi. Ina jiyo Kaila da Hajiyayye suna cin uwar sabada, a wannan daren Kaila yayi jaraba da masifa tamkar zai doki Hajiyayye ina ji yana cewa gobe ta tafi gidansu taje ta koyo tarbiya. Ina kwance ina fama da marurun zuchiyata. Sassafe Kaila ya ƙanƙasamun ƙofa ya miƙo mun Samira har zai wuce nace.
Zanje wunin gida yau. Sannan dan Allah inason zuwa gobe zani Bauchi akwai wani taron ƴan makarantarmu da za'ayi." Ranshi a haɗe ya juyo yace.
"Ni dai bani da kuɗin dazan baki zuwa wani Bauchi hidimar aure ce a gabana, in kina da kuɗin mota ki je in baki dashi ki haƙura."
Ina dashi dama izini nake nema" Nace a sanyaye.
"To kije kwana nawa zaki yi to?" Nace mishi.
Bazan wuce kwana ɗaya ba ƙarƙari ƙwana biyu zan dawo" umarnin zuwa ya bani, nayi mishi godiya. Da wurwuri na kammala aikina nayi wanka naima Hauwa. Goyata nayi a bayana na saka hijabina na fito hannuna riƙe da leda da Samira. Kulle kofata nayi, na miƙa ma Hindatu Samira. Nan taso ta neme ni da gulma, tana son sanar dani abinda ya faru, tafiyata nayi na barta nan da Samira a hannu. Ina isa titi na tari keke napep zuwa layin idi mai barkono (Allah ya jaddada rahamarshi gareshi). Tun daga titi na soma gaisawa da maza_mazan anguwar da suka sanni nazo na wuce gidan mariyagi idi mai barkono a raina nace Allah sarki iya ta lungu mai maganin gargajiya na kashin jarirai alkhairin Allah ya kai miki. Da sallama na shiga gidan namu. Da Baffa naci karo shi da Habu yana mishi jagora da dukkan halama bara zasu fita. Yana jin muryata ya caɓe abunka da makawo akwaisu da gane murya ballanta na kuma muryata.
"Tani kema kin iso kenan? Yanzu shigowar Use kamar tare kuke." Tsugunnawa nayi har ƙasa na gaisheshi duk da nasan ba gani yake yi ba. Da fara'a ya amsa mun gaisuwar tawa.
"Ya mai gidan naki Kaila ince dai kina zaune lafiya kuma kina mishi biyayya ko? Gara ma ki haƙura ki dena wannan auren ɗanɗanen dan wallahi duk ranar da kika zo mun gidannan da sunan yaji ma, wallahi zaki sha mamakin abunda zanyi miki Tani. In auren kika kaso karma ki nufo gidannan dan wallahi zaki sani in aikata miki abunda ƙila sai dai in ƙarashe rayuwata a firzin." Ni dai da to Baffa naita binshi harya gama mun nasihar.
Bara zaku je ne Habu, har hutun sallar ya ƙare?" Baffa yace.
"To in bamu fita ba Tani wa zai bamu abinci? Kwana biyunnan dana zauna a gidan duk babu daɗi sam, dan ma matan gida da maƙota sun kawo mana abinci da sadakar nama shi yasa na ɗan huta. In muka zauna a gida babu mai bamu muci. Rannan ma Kaila ya biyo ta wajan barata ya bani ɗari ko Habu ɗari biyar ce ko?" Habu yace.
"E Baffa ɗari biyar ya ajjiye mana a kwanon barar"
"To kinji kya yi mishi godiya" Wasu hawayene suka gangaro akan kumatuna shar_shar_shar, cijewa nayi nace da Baffa.
Zan yi mishi godiya sai kun dawo Baffa. Ga wannan ɗari biyar ɗin kwa yi cefane" Karɓa yayi yana ta yi mun addu'o'in masu daɗi. Shiga cikin gidan nayi na samu su Yaya Use a barandar ƙofar ɗaki a zaune akan tabarma suna dabdalar cin farfesun kan rago. Mu namu kan ragon Hajiyayye aka ba takai ma iyayenta da fatar ragon waccen laiyar ma ita aka ba.
"Kaga matar Kaila mai tukubar gashin kajin gidan gona da zabuwa" Cewar Yaya Use kenan uwar barkwanci da tsokana. Dariya nayi mata na zauna a hankali na sakko da Hauwa ja'ira idanta biyu akan cinyar Inno na ajjiyeta.
"Inno ina wuni anyi Sallah lafiya?"
"Lafiya ƙalau ya mai gidan da abokiyar zamanki, da facalarku kowa lafiya dai ko?" Dariya nayi nace
Lafiya lau Inno, ina yaran suke?" Inno tace.
"Na aikesu ƴan dankali gidan wata Hajiya kira tayi a waya tace in tura Indo tayi kwalima ta karɓo mun kaya. Shine fa yarannan su kaita magiyar su sai sun bita shine fa na basu kuɗin abun hawa suka tafi." Kai kawai na girgiza na juya muka gaisa da Yaya Use da Yaya Karime. Yaya Use tace.
"Tani rannan Baban Abas ya siyo mana kaza a tukubar Kaila gaskiya dole ma Kaila ya dinga uban ciniki gaskiya ya iya gashi sosai." Dariya nayi mata nace.
Babu laifi kam ya iya ciniki kam yana yi gaskiya tunda yanzu da kanshi ma yake kiwata kajin nashi, zabi da kajin gidan kuma daga ƙauye mahaifiyarshi ke turo mishi da yajin gashin ma duk ita take aiko mishi dashi. Yaya Karime matar babban direba Baban jafaru ya dawo kuwa?" Murmushi tayi ita ba mai son magana bace tace.
"Ya dawo a gida yayi Sallah, amman yanzu haka motarshi tana kan layi a farar gada ana mai lodin kayan gwari zuwa Port Harcourt, ai matan direbobin manyan mota, da matan masu kaki sai dai mu yi ta haƙuri kawai." Nan na shige cikin ƴan uwa mu kai ta hira, da dariya Inno tayi ta binmu, wanda ya kama tasa baki takan sa. Farfesun kan ragonnan nima na zuba kaɗan na sha yayi daɗi gashi yaji kayan ƙamshi. Ana haka sai ga Indo dasu Sulaiman da kaya niƙi_niƙi a buhunhuna sun shigo. Nan na shiga washe baki dan nasan zamu samu kwance ko da ɗaɗɗayane, dan yawancin kayan nawa Inno ce take bani kwancensu. Dan tunda na haifi Balaraba Kaila bai sake mun zani ba, ko na sallah baya yi mun, sai wanda ya bamu jiya na faɗar kishiya. Yara suna ganina suka shiga murna. Anan tsakar gidan Inno ta zazzage kayan tana wawwarewa, gaskiya wannan karon kayan suna da kyau sosai, harda su mayafai na ƴan gayu da takalma. Carab na riƙe wani mayafi baƙi mai kyau, ashe Yaya Use itama ta hangoshi ganin na rigata ɗauka yasa ta bar mun. Atampa da leshi Inno ta miƙo mun da ƙarin mayafi ɗaya. Na karɓa ina murna dan kayan kamar sababbi, gashi ɗinkunan jikin kayan bana banza bane ɗinkunane masu tsada. Ta wari wani ta miƙa ma Yaya Use, ta sake warema Yaya Karime nata itama. Ta ware ma Indo ma. Daga baya ta sake ƙara mana kala bibbiyu, ni nawa riga da skirt na wani jan yadi ta bani, da shadda mai surfani a jiki, na samu mayafai har uku takalmi kala ɗaya ne yayi daidai da ƙafata wani ɓaki. Yaya Use ce ta more takalma dake ita ƙafarta da girma naji daɗin kayannan sosai dama harna tawo da ƴar atamfar da Kaila ya bamu ta faɗar kishiya zan ba wata maƙociyarmu ta ɗinka mun in samu na zuwa Bauchi dan bani da wasu kayan fitar kunya in ba wannan abayar dana sa ran sallah ba. Sai gashi na samu kaya masu kyau sosai. Haka dai muka wuni na ba su Yaya Use ɗan ƙullin nama tsoka uku uku, na ba Inno nata itama ba wani yawa nawa kason ne ma na bata ni na haƙura, su Yaya Use kuma a cikin na yaran na cira musu.
"Tani saura sati biyu bikin Momiyo ƴar wajan Shafa ƙanwata ya kamata wannan karon aje Shanono dake, daga nan dai mu je kiga Dauda. Daɗi sosai naji a raina dan ina kwaɗayin son ganin Dauda sosai dannewa nake dan gudun kar in jawo ma kaina jangwam."
Allah ya kaimu. Nima gobe nake son zan je Bauchi. Ɗaliban makarantar kwana ta Bauchi da nayi ne suka haɗa taron ƙarfafa juna shine zani. Kuma sati biyu masu zuwa Kaila zai ƙara Aure." Su Yaya Use ne su ka ji wani iri, Inno kuwa saima washe baki da tayi tace.
"Ayya namijin duniya to Allah ya baku zaman lafiya. Kar dai kice zaki yi wani zafin kishi ki je ya sako ki a banza. Wallahi in ma ya sakoki kisan tayi dan Baffanku yana jirace ne dake, nima a wannan karon ba barinki zanyi ba. Aure biyar fa sai kace wata karya. Babu abinda yara suka sani na biyayyar aure in banda sakarci da hauragiya. In ce dai da yardar shi zaki je wani Bauchi ko? Dan na sanki sarai da ƙulafacin son makarantar yahudawa." Jiki a mace nace.
E da yardar shi zanje. Kuma in sha Allah babu abinda zai sa in bar wannan gidan sai in gawata za'a fitar, in dai yi nayi bari na bari shine aure to da izinin Allah sai dai a fitar da gawata, ko na mutu Lokacin mutuwar baiyi ba, ko kuma wa'adinane ya cika" Ai da faɗar haka Inno tace ina wuta ta tsolma ni. Nan ta shiga mun faɗa tana cewa dama duk take_takena ya nuna so nake Aure na biyar ɗin ma ya mutu in sake auran wani, wai na gaji da ɗanɗana Kaila inason ɗanɗana wani. Nayi kuka ainun wannan kalmar fa iyayena ke jifana dashi bansan kuma mai mutanen waje zasu ce dani ba. Ban karashe wunin da daɗi ba, kafin magriba duk mu ka ɗauki haramar komawa gidajen mazajenmu, har zuwa lokacin Baffa da Habu basu shigo gida ba, har barar dare suke yi wani sa'inma a bakin kasuwar suke kwana ko bakin masallacin ƴan taya a cikin ƴan cirani dake dako a ƴan kwalli.....✍🏻
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FADO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA 4.
Anan na bar yaran akan in na dawo zan yo kiran waya Habu ko Indo su rakosu." A titi muka rabu da su Yaya Use kowa ya nufi gidan mijinshi. Ina shiga na hango Hajiyayye a zaune a tsakar gida tana alwalar magriba idanun nata taci kuka na fitar hayyaci da gani.
"Kin dawo umman Sulaiman?" Ni mamaki ma nayi sosai dan Hajiyayye ko ni na kulata sai ta ga dama take kulani.
Nadawo Hajiyayye sannunku da gida. Key na ɗakko na buɗe ɗakina na shiga na ko ci sa'a akwai wutar nefa. Shinfiɗe Hauwa nayi na fito tsakar gidan dan yin alwala. Ina zaune akan sallaya na idar da sallah sai ga Hajiyayye ta shigo da sallamarta, waje ta samu a bakin katifa ta zauna. Da ido kawai na bita, to yau Hajiyayye ce a zaune a ƙazamar katifata mai wari?".
"Umman Sulaiman ni dake so nake mu haɗe kanmu ta hanyar gasa Kaila a cikin gidannan duk inda ya yi yaji babu daɗi, nifa ina gani bazan bar wata macen ta shigo gidannan ba ko da tsirara zanyi yawo. Kuma ita matsiyaciyar da yake nema zan ɗakko mana number ta mu yi mata kashedi da barazana mai ƙarfi na tabbatar zata fasa auren. Wannan bazai faru ba sai na samu haɗin kanki. Jiya da daddare sabida na fasa mishi wayarshi suna waya shine fa Kaila yasa hannu ya wankeni da mari, har nayi yaji ma na je gida, dawo dani akayi a bisa tilas ba son raina ba. Yanzu in banda maza da shegen kwaɗayi bamu isheshi ba mu biyu? Gamu farare babu wacce za'ace tana da muni jibi yawan gashin kanki dana yaranki fa me Kaila yake nema ne?"
Ai ya faɗa miki abunda yake nema da irin macen da yake burin son mallaka. Kinga kuwa dani dake in aka haɗemu bamu kaita ba ko kusa. Ni da zan baki shawara ki ɗauka ko, da kin fita sha'anin batun aurennan in dai kina son tsira da igiyoyin aurenki. A lokacin da Kaila zai auroki da ban kwantar da hankali ba da tuni bana cikin gidannan. Naga hanyar da kike son bi ba mai ɓullewa bace, in Kaila zai kwana yana waya da budurwa ke kuma sai ki kwana Sallah. Kin mance lokacin da yake nemanki kusan kwana waya kuke yi ne, ai a lokacin kinsan yana da mata a gida, yanzu dan yayi menene ai ke kika lalatashi kika kuma nuna mai hakan wayewa ce. Ni kin ganni ina lallaɓa igiyar aurenane babu ruwana da duk abunda zaki yi akan hana Kaila Aure"
"Au haka zaki ce ma dan kinga nazo inason mu haɗe kanmu?"
Haka na ce ma Hajiyayye." Ina faɗar haka na miƙe na tada kabbarar sallar isha. Fuu Hajiyayye ta fice. Bayan na idar na zauna nayi azkhar sannan na jawo wayata na buɗe data na faɗa group ɗinmu na FGGC. Anata magana da tsare_tsaren yanda za'a gabatar da taron. Magana nayi musu akan goben zan shigo nima dani za'ayi taron" Sunji daɗi ainun nan su kai ta nuna farin cikinsu. Mayafi na yafa na shiga cikin gidan a tsakar gida na samu Kaila a gaban lifan ɗanshi yana duba tayunsu.
Sannu da dawowa" Shine kalmar dana ce dashi.
"Yauwa Shanono " Iyakar abunda shima yace