Showing 3001 words to 6000 words out of 68990 words

Chapter 2 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

a tsakar gidan bamu daina ba, har masu zuwa aski suka iskeni ina suyan nama, nan farin ciki ya lulluɓesu har suna tsalle tare da yin waƙar gobe sallah zamu ci naman Baba Dauda. Da dariya na bisu nima soyayyar miya nayi na juye namannan a ciki dab magriba sai ga masu kitso sun shigo an ko rangaɗo musu kitson gaba da shiku, Tubarakalla sunyi kyau abinsu. Ina gama kaye_kaye na mu ka ɗaura alwala ni da su Balaraba muka shige ɗaki, su Sulaiman kuma suka tafi masallaci. Muna sallah da yara Hajiyayye ta bankado labule ta ajjiyemun kular da take zuba mana abinci in girkinta ne, ta fice abunta. Ko da na sallame nayi mamakin abunda ya sa Hajiyayye ta kawo abincin da kanta, dan yara take kira su zo su ɗauka, sau biyu Hajiyayye ta taɓa shigowa ɗakina, lokacin haihuwar Balaraba da Lokacin haihuwar Hauwa sai kuma yau."
Amina kije kichin ki ɗakko mana tran silver da muke cin abinci muci, in mu ka yi sallar isha sai kuma muyi lalle ko" Amina tace.
"Umma an sha ruwa lafiya?" Shaf na mance ina yin azumin arfa da ba dan Amina ta tunamun ba, ba fa lallai in tuna ba. Sai da na sha ruwa sannan nace mata.
Lafiya lau Aminana" Fita tayi daga ɗakin, sai ga su Sulaiman sun shigo. Jallof ɗin shinkafa da makaroni Hajiyayye tayi, sai soyayyen nama data ƙirgamu ta watso, daga fika fiki sai wuya, kwankwaso harda kai da ƙafa. Juye mana dukka abincin nayi mu kai bismillah muka soma ci. Ni dai ci kawai nake yi amman zuchiyata tamkar an ɗaura mun bulo haka nake jin nauyinta, kaɗan naci naji na ƙoshi ma. Kai da ƙafan na ɗauka naci, na bar musu sauran muna zaune a wajan har isha. Ina jiyo mashin ɗin Kaila daga tsakar gida. Sulaiman yace.
"Baba ya dawo Umma" Bance mishi ci kan ka ba nace.
Ku tashi oya aje ayi sallah maza a dawo banda wasa." Da sauri suka fice, ina jiyo Kaila yana tambayarsu ina zasu je su ka ce masallaci zasu je. Korosu yayi ya shiga sababin cewar.
"Da wannan dattin kayan zaku je masallaci kuna tafe kuna zarni, uwarku bata da aiki sai son ganin ta zubar mun da kimata. Maza ku wuce ciki kafin in dokeku" A guje suka dawo ciki, ni kuma na miƙe tsaye da ƙyar nace.
Ku yi sallar a gida ina zuwa bari in yi ma Babanku sannu da dawowa" Fita nayi tsakar gidan ina turo ciki gaba. A bakin rijiya na hangoshi Hajiyayye tana haskamai tocila yana ɗaure ƙaton ragon laiya"
Sannu da dawowa Kaila" Kafin yayi magana aka kawo wutar nefa ta haske tsakar gidan tarwai. Hajiyayye tana sanye da gajeren wando iyakarshi guiwa da wata riga mai hannun shimi, kannan yasha man kitso sai ƙyalli yake yi, lallennan ya zauna a fatarta ɗas, sai ƙamshi take faman busawa, ko ni ta bani sha'awa ballantana Kaila mijinta. Shi kuwa Gogan namu yana saye cikin ƙananun kaya masu tsada da gani a ido, idanunshi saye da tabarau fari mai kyau, sai ƙamshin turaren 212 yake yi. Kaila ƙyalli kenan ƙyalli shine inkiyar shi, wanka kam akwaishi a wajan Kaila ga iya direshi, in ya ci wanka babu mai cewa yana da aure ma balle a yi tunanin yaranshi sun kai Bakwai"
"Yanzu Shanono yarannan a haka kika turasu masallaci ɗazu? Kinga kayan jikinsu kuwa, in banda zarni babu abunda suke yi. Wannan ai wulaƙanta ni kika son yi Shanono" Ɗan Murmushin dole na ƙwaƙwulo nace.
Kayi haƙuri kayan nasu masu daman ka gansu a shanya basu bushe bane shi yasa, amman baza'a sake ba. Rago muka samu? To Allah ya ba da lada"
"Ameen Shanono" Yana faɗar haka suka tafi suka barni a tsaye, hannunshi riƙe da ƙugun Hajiyayye suka nufi turakarshi. Hannuna na wanke na koma ɗaki, bayan nayi sallah na shigo mana da katifinmu ciki. Sannan muka shige ƙurya ni da matan. Lalle na soma yi musu, kafin ma in gama musu duk sun yi bacci. Kwanciyar na gyara musu. Sannan na shiga jera seletab a ƙafata, bani na kammmala lallennan ba sai wajen sha biyu da rabi na dare. Ina zaune a gefen katifa tunani yai mun yawa, kaina sai aikin saramun yake yi. Ni bansan lokacin da bacci yayi awon gaba dani ba, sai kiraye_kirayen sallar asuba ne ya farkar dani. Lalle na na cire yako yi shar dashi. Gishirin lalle na kwaɓa da toka na shafa, yaranma na kwashe musu lallen na sa musu gishirin lallen. Cikin minti goma yayi baƙiƙƙirin gwanin sha'awa. Nan fa yara duk suka tashi muka shiga yin alwala. Muna tsakar gida na jiyo ƙamshin turaren Kaila ta bayana, wucewa yaxo yayi da sauri yana saye da farar jallabiya mai ɗaukar idanu. Hajiyayye kuma ta fito riƙe da ƙatuwar buta a hannunta tana waƙe_waƙen data saba yi in dai Kaila yayi mu'amalar aure da'ita. Ɗaki muka shige da yara mu kai Sallah. Na fito na hura wuta na ɗaura ruwan wanka. Kafin shidan safe tsakar gidan ya kacame da ƙamshin girkin Hajiyayye da Hindatu, mu kuma sai wanka muke yi. Nice karshen shiga wankan. Ina fitowa naga Hajiyayye da wani lafiyayyen leshi mai taushi ɗinkin doguwar riga, tasha ɗan kunne da sarƙa da zobe da awarwaro harda agogo tayi kyau sosai. Samira kuma tana cikin wasu riga da wando na kanti sababbi fil, kanta yasha bit itama ba laifi tana da gashi. Fati da Zulaihat da Tasi'u yaran Hindatu matar ƙanin Kaila suma suka fito cikin ankon shadda mai ruwan ƙasa su da uwarsu kowa yayi kyau. Gaisawa na tsaya mu ka yi dasu kafin na wuce, yara suna jira in fito in basu kayan da zasu saka. Kowa ya shafa mai. Wata bulu ɗin yadi na zaro ma Sulaiman da Shafi'i da Sani, Inno aka ba sadakarshi ta kawo mun, basu taɓa sawa ba, kuma sabone fil. Su kuma su Balaraba atampa na ciro musu wacce na dinga musu da ƙaramar sallah atampa roba, kowa yasa kayanshi, na basu sababbin hijabansu duk suka sa harda Hauwa, su kuma su Sulaiman suka saka baƙar hularsu ( gobe da mandiri) wacce na siya musu a kasuwar mai shafi da azumi ɗari bibbiyu. Ficewa su ka yi tsakar gida suma suka shige cikin ƴan uwansu. Ni kuma na shiga ciki na zaro wata abaya irin ƴan italiyannan itama Inno ce ta kawo mun ita tare da kayan su Sulaiman harda takalmi mai kyau ta haɗomun dashi duk da dai takalmin ya yi mun yawa kaɗan. Bayan na shafa mai na zura rigarnan doguwa mai kyau, na saka dan kunne da awarwarona, sai jar hoda Zainab dana ɗan barbaɗa akan tsumma na shafa, na bi farin idona da kwalli. Hijabina baƙi na ɗakko na maka na daƙko baƙin takalmina na saka abuna.
"Shanono shanono ki fito mana in kina zuwa, in kuma bakya zuwa mu tafi" Kaila ne yake mun magana murya a sama. Ba shiri na fito da ƴar posa ta baƙa a hannuna, ɗakin na kulle na samesu a ƙofar gida. Kaila yaci ado da wata farar shadda mai kyau, ya kafa hula da sabon takalmi fil, idanunshi saye da tabarau baƙi. Motar Abokinshi Isa na gani a ƙofar gidan. Shiga nayi kamar yadda naga Hindatu a ciki, mandiya hamshaƙiyar kuma tana gaban mota da ƴarta ta sa wani mayafi shara_shara. A bayan mun matsu sosai sabida yara amman a haka dai muka tafi zuwa masallacin idi.








Yaya kuka ji wannan salon tafiyar kuma? Tafiyace mai tsayin gaske, labarine mai tsawon gaske, ku bini a sannu sannu domin ganin yadda zata kaya. Ƙofa a buɗe take ga masu son magana dani. Wannan littafin zai soma zuwa muku 20 ga wannan watan in sha Allah.


GAWURTATTU UKU 👠👠👠

1 _KWAI A BAKA_

*(UMMU AFFAN)*

2 _ZULFA_

*(UMMU MAHEER MISS GREEN)*

3 _NA FAƊO DAGA BENE..._
_NA ZARCE RIJIYA_

*(BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI)*



MRS BUKHARI CE

https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FADO DAGA BENE......
NA ZARCE RIJIYA
hakkin mallakar Badi'at Ibrahim Mrs Bukhari b4b gidan ƙamshi.
Gawurtattu uku



*ASSALAMU ALAIKUM MASOYAN GAWURTATTU UKU, MASOYAN BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI. GAMU MUN FITO DA ZAFINMU A BISA ROƘO DA ƘORAFIN MASOYA DA MUKA SAURARA AYI KARATU LAFIYA.

NA SOMA DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI. GODIYA DA TABBATA GA MAMALLAKIN RAINA, WANDA YAI MUN HANCI DAN SHAN ISKA.

SAƘON GODIYA.

INA MIƘA SAƘON GODIYATA GA ƊAUKACIN MASOYAN RUBUTUNA. HAƘIƘA NAGA ƘAUNA. SHAFI ƊAYA NA WALLAFA NA LITTAFINA, AMMAN A RANAR NA SAMU WAYAYO DA SAƘONNIN MASOYA BILA ADADIN. HAƘIƘA WANNAN LITTAFIN YAZO DA WANI IRIN FARIN JINI NA MUSAMMAN. SHANONO TACE IN MIƘA MATA GAISUWA GA MASOYAN LABARINTA.

SADAUKARWA:
NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA KO WACCE BAZAWARA TA ƘASAR HAUSA.
NA SAKE SADAUKAR DA WANI KASO DA MATAN AURE IYAYE.


GAWURTATTU UKU

UMMU AFFAN
(ƘWAI A BAKA)

UMMU MAHEER MISS GREEN ( ZULFA)

MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
( NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA)


Lamba ta 2
A filin masallacin idi mu ka yi sallar idinmu, zukatan al'ummar musulmi cike yake da farin cikin wannan rana. Yara da manya kowa ka kalla a cikin ado da kwalliya yake. Inata kallon yara ƴan gata yara sa'annin Balaraba da Amina da jaka da agogo harda tabarau na yara duk an sai musu, kansu cike da bit kamar ba da kuɗi ake siye ba. Kaila ne ya iso inda muke muna jiranshi shi da Abokinshi Isa. Gaggaisawa akayi, nan Isa ya bi ko wanne yaro da goron salla na sababbin ɗari biyar_biyar, mu kuma ya bamu dubu ɗaɗɗaya.
An gode Baban Nana Allah ya saka da Alkhairi " Idanu Kaila ya ƙuramun cikin kallonshi na yaudara, nayi saurin kawar da kaina, yaran duk suka mimmiƙo mun kuɗin hannunsu. Muna tafe zamu je inda muka ajjiye mota Balaraba tace.
"Umma siya mana askirin" Dariya nayi mata, Hindatu ta shiga yi mata tsiya. Ɗari biyar na zaro na ba Sani nace.
Yaya maza siyo muku dukkanku na duka." Jikinshi har rawa yake yi ya karɓi kuɗin ya zura da gudu ya siyo musu. Mota muka shiga muka koma gida. Muna isa Hajiyayye ta shiga rabon abinci.
"Umma! umman Samira tace ki kawo kular abincinki, da kwanon da zata zuba miki nama da cincin" Cewar Shafi'i. Yana gama faɗa ya fice a guje. Mayafin doguwar rigar jikina na yafa na fito a lokacin Kaila na kiciniyar fita da rago. Yaran kuma ashe Hundatu ce ta zuba musu shinkafa da miya a katon trai suna ta ci, harda zoɓo mai sanyi. Kula na shiga kitchen na ɗakko da kwanon nama na kai bakin ƙofar ɗakin Hajiyayye. Tana fitowa data ganni da doguwar rigarnan sai tayi wani turus ta kasa ɓoye mamakinta dan rigace mai kyau da gani kuma zata yi tsada. Kafata ta kalla sai ta haɗe ranta tace.
"Hmmmm" Ni dai ina tsaye ta zuba mun fried rice ɗinnan da koslow a kwano. Sai naman kaza da cincin, da meat pie. Cike da mamaki na dubeta ganin nama da kayan fulawar data zuba mun kamar ni kaɗaice a ɗakina banda yara.
Hajiyayye ki ɗan karamun naman da kayan fulawar kinsan muna da yawa"
"Dan kuna da yawa? Ai ba dan ku nayi ba, nayi ne sabida Baby da abokanshi ba sabida ke da yaranki nayi ba, mtwss" Taja tsaki. Ban tanka ta ba na ɗauki kwanon naman na ɗaura a saman kular abincin, na sa kwanon koslow ɗin akan kwanon naman na ɗauka. Sai ga Shafi'i ya biyo ni da lemon kwalba 7up guda huɗu. Ajjiyewa yayi na dubeshi nace.
Maza kuci abincin kuzo ku tafi ku kai ma su Inno abincin Sallah maza. Nan Shafi'i ya shiga murna a guje ya kirawosu, sai gasu har suna rige_rigen shigowa. Ƙatuwar samira ta kasan na cika ma Inno da abinci dam, samirar tsakiyan kuma nasa mata nama da meat pie. Na samu ɗankwali mai ɗawisu na kulle musu samirun dashi, na samu leda ɓaka mai ƙarfi na zura samirun a ciki, na ɗakko 7up guda biyu na zuba. Ragowar meat pie da lemun kwalbar nace musu su ci kafin su tafi, dan in sun tafi sai an gama bikin sallah ranar da naje wunin sallah na gida nake tarkatosu mu dawo tare. Suna gama ci su kai mun sallama suka fice. Hauwa kuma sai bacci take yi. Zama nayi na zuba abinci a plate na soma ci, gaskiya abincin yayi daɗi sosai, Hajiyayye ta fini iya girki nesa ba kusa ba. Bayan na gama cin abincin saina ɗan shingiɗa a bakin katifa har bacci ya soma ɗibata na jiyo muryar Kaila a tsakiyar kaina.
"Shanono ki taso ki gasa mun hanta ga kayan ciki nan na shigo dashi ki soma aiki. Kallonshi nayi nace
Kaila ai girkina sai zuwa bayan la'asar zai shiga Hajiyayye ce da kai har yanzu"
"Ke dai babu dama ayi magana ki ce to. To Hajiyayye tana can tana zuba ma abokaina abinci, kuma ta gaji ita tai ta yin hidima jiya, in zaki taso ki taso ni dallah sai shegen sa'insa mata ba dama ace mata abu ɗaya. Allah yana gani ni nayi nadamar auroki da nayi" Ficewa yayi fuu. Babu shiri na biyo bayanshi, har sun gama aikin ragon, yana jikin bangon ɗakin Hajiyayye a banƙare. Wuta na haɗa a korfo, na shiga cakuɗa hanta da maggi da yaji da kayan ƙamshi, nan na shiga gashi. Ina jiyo shewar Kaila a ɗakin Hajiyayye da abokanshi, harda shewar Hajiyayye Babu kowa a tsakar gidan sai ni, Hindatu tana ɗaki da mijinta suna kallon wakokin ado gwanja. Haka na gasa hantarnan tas nayi sallama a ƙofar ɗakin Hajiyayye. Fitowa tayi ta karɓi plate ɗin ta shige ciki. Nan na duƙufa gyaran kayan ciki, nazo na yayyanka bayan na gama na zuba a tukunya na aza bisa wuta, na zuzzuba duk abinda ya dace, na koma ɗaki ina nishin gajiya, na tarar Hauwa ta farka sai kuka take yi. Ɗaukarta nayi na zura mata nono a baki, nan ta shiga tsotso tana sauke ajjiyar zuchiya. Nima ajjiyar zuchiyar nake saukewa zuchiyata cike da tunanin shin haka mazan ƙabilar Hausawa da yawansu suka lalace wai, so suke ƙarfi da yaji su mayar da mata baya can zamanin jahiliyyah. Kuma abun takaicin shine ba ga masu sanin ba, ba ga jahilan ba. Tunda ni na auri malami na gani, jahilin ma na aure shi shima naga kalar tashi rawar, ga tsaka tsaki shima na aura naga irin tashi rawar da yake takawa. Wai mu mata ina zamu tsulma ranmu ne muji sanyi, haba maza iyayenmu ya kuke son mu yi da ranmu ne? Gashi in ƙaddara ta samu mace tayi aure ɗaya zuwa biyu ta fito, sai ƙabilar Hausa su sa mata jakar tsaba, wasu su kirata da maras tarbiyya, wasu suce mata mai ruwan ido, wasu su kirata da kwaɗayayya. A gidanku ma baka huta ba a wajan iyaye da ƙanne, tsangwama daga ko wanne ɓangare babu daɗi. Wannan dalilin shike tilastama wasu mata zaman dole wanda ka iya zama ajalinsu, ko silar shigarsu wuta. Ni kaina a wannan auren nawa karo na biyar na ɗau alƙawarin duk rintsi duk wuya zan zauna ko da wuya da ciwon zuchiya za sui ajalina. Tuno mazajena na baya na yi da dalilan mutuwar Aurarrakina. Numfashi naja mai ƙarfi dana tuno da yanda akayi na haɗu da Kaila a hanyar kasuwar taminus wajan da Baffa yake zaman Bara a masallacin ƴan taya. Wasu zafafan hawayene suka gangaro kumatuna. Ƙauri na soma jiyowa da sauri na fita na sauke tafashen kayan cikin. Man gyaɗa na gani kwalba biyu a kofar ɗakina an ajjiye mun a wulaƙance. Ɗaukowa nayi na juye a bojuwar suya na soma suyan kayan ciki. Hindatu itama tana tsakar gidan tana suyar hanji wanda Kaila ya dibar musu. Wani kurfo na dakko ƙarami na zuba gawayi da gaushi a kai. Ina suyar nan na tsai da sanwar miyar tuwon dare, na ɗebi tafashasshen kayan cikinnan na zuba a cikin ruwan miyar da ruwan tafashen. Zuwa bayan la'asar na kammala suya tas na juye a roba mai murfi bayan ya huce.
Assalamu alaikum Hajiyayye dan Allah ɗan miƙo mun key ɗin turaka zan ajjiye namannan ne" Naji shiru dama a rufe naga ƙofar amman dake na saba ganin hakan a wajen Hajiyayye sai ta saka Kaila a ɗaki ta rufe shi da ranar Allah gida fal yara bata ko jin nauyi. Hindatu ce ta fito daga bayan gida take ce mun.
"Ai basu daɗe da fita ba, ɗazu da kika shiga ɗaki ɗakko robar da kika juye kayan ciki tai mun sallama sun fita." Dawowa nayi da robar naman a hannuna, basu tasarma fita ba sai da suka ga kwanana ya shiga. Roba na samu na cika ma Hindatu da kayan ciki duk da nasan an bata ɗanye. Kunyace tasa ina dawowa ta biyo ni da cincin da soyayyen naman kaza harda zoɓo mai ɗan karen sanyi. Godiya nayi mata na ajjiye a ɗaki. Sallar la'asar nayi na jawo wayata inga ko an kirani, ai kuwa miss call ɗin Yaya Use na gani. Ina jiyo muryar Zulaihat a tsakar gida na fita da nera ta ɗari.
Zulaihat zo ki siyo mun katin glo a shagon mahi" Da gudu tazo ta karɓa taje siyo mun. Ni kuma na shiga yin talgen tuwo. Ina zaune a dokin ƙofata ina cin kayan ciki da zoɓo sassanya Zulaihat ta dawo daga siyo katin, na ganta da alkaki cike da baƙar leda tace mun.
"Maman Zuhura ce tace in kawo miki wai zata shigo inta gama tuwo. Kuncewa nayi na bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login