Showing 15001 words to 18000 words out of 68990 words

Chapter 6 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt

NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU. 5





Cikin fara'a nace
Masha Allah rayuwa tayi albarka Habiba Bala. Irin wannan daula da kike ciki haka. Ah abun yayi kyau" Murmushi ta sakar mun kawai ta nemi ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna. Muma zama mu ka yi. Halima Bawa tace.
"Ni banji motsin kowa ba a gidan, kaddai baki samu rabo bane Habiba Bala?" Wani murmushi tayi mana irin na manyan mata kana tace.
"Na samu rabo yarana uku dukka maza" Tare muka haɗe baki wajan cewa.
Masha Allah." Halima Bawa tace.
"Ismaliyya suka tafi ne, ko gidan kakanninsu nasan dai ana hutun Sallah?"
"Halima Bawa kina nan a ƴar bin diddiginnan dana sani, aikin jarida zai fi dacewa dake. To yara suna Jigawa gidan Babansu. Bani da Aure a halin yanzu. Ni kaɗai nake zama a gidannan sai Iya mai taya ni gyaran gida da jire mun gidan, ni kuma ina zuwa asibiti kamar yadda na faɗa muku a cikin taro" Jijjukannanmu gabaki ɗaya sai yayi sanyi laƙwas. Wato wannan mace_macen auren ya karaɗe Arewa sosai? Ada ƙabilar Hausa an san mazansu da riƙon Aure da haƙuri. Kamar yadda matan suke da kunya, kawaici, gami da yakana. Ni dai na rasa gane a inda matsalar take. Furucin Halima Bawa ne ya dawo dani daga zancen zuchin da ya jima da aurena.
"Hmm mazan ƙabilar Hausa na wannan ƙarnin sun maida saki tamkar ya da ledar fiya wata. Nakan yi mamaki da tunanin mai ya taɓa malam bahaushe ne haka, wannan aure da sakin yayi yawa, yawan zawarawa a ko da yaushe sake hauhawa yake yi a ƙasar Hausa, hakan yasa zinace_zinace yai yawa, duk da zina yanzu ta zama ruwan dare game duniya. Su kuma al'ummar Hausawa basa yi ma bazawara kallon tausayi, sai kallon maras tarbiyya, maras haƙuri. A cikin gidanku ma sai mahaifanka su kasa yi ma uziri, ai ta hantararka, in Aure ya mutu to fa macen itace mai lafi. Da tayi aure ɗaya biyu sai a sa mata suna, wata ma taƙi auruwa. Amman shi Namiji a kan dukkan abinda yake a kai ƙarfafa mishi guiwa jinsinshi suke, in aure goma zai yi, ij yaje nema za'a wanke a bashi. Haka Namiji da mace zasu aikata zina, ita macen ya zame mata masifa, taƙi auruwa aita goranta mata. Shi kuwa namiji sai ace mishi duk abinda yayi adone. Zina ashe zata iya zamewa ado? Wa'iyazubillah. Nima na ɗanɗani wannan rayuwar, sai da na shekara takwas ina zawarci. Duk wanda yazo wajena da iskanci yake zuwar mun. Ko ku ga da girmana yara ƙanana masu soyayyar shan minti suna zuwa. Wannan dalilin yasa na yi fatali da surutun iyaye da dangi, sai na koma makaranta na yi karatun jami'a, ban yi aure ba sai da na dafi aikina mai kyau a hannunna. Ko yau aka sake koroka a ƙalla ba zaka tagaiyara ba, kana da abun yi, ba zaka bada jikinka dan ka biya buƙatar kan ka na yau da kullum ba" Idanuwanta take suka ciko da ruwan hawayen tuno da wasu ƙunci da suka shuɗe mata a baya. Ni kuma leɓe nake cijewa kawai, irin azabar da rijalu suka ɗanɗana ma ruhina bana wasa bane.
Hmmm Allah ya kyauta" Shine abun da na iya cewa, amman tabbas Halima Bawa ta taɓo inda yake mana ƙaiƙayi ainun.
"Halima Bawa kenan. Ke aure ɗaya ma kika yi kika fito a ɗan labarin da kika bamu. Kin ganni mazaje uku na aura amman zaman yana ƙin yiwuwa. Ku dai mu shiga daga ciki ku ɗan watsa ruwa ku huta. In muka nutsa zan dan baku a taƙaice, amman naci wuya. Jagora tayi mana i zuwa cikin ɗakinta wanda ya kasance haɗaɗɗe. Ga takalma a jajjere sunfi sawu talatin, jakunkuna suma gasu nan kaya guda a rarrataye a abun rataye jaka. Ɗakin sai wani irin ni'imtaccen turaren wuta ke tashi wanda ban taɓa jin ƙamshi turare mai sanyi irin wannan ba. ( In kina son ɗakin ki ke ma ya dinga ƙamshin gidan sarakai ki neme ni, zaki samu dukkannin nau'ikan turaruka masu sanyin daɗi 08179523215) A 3sitter dake uwar ɗakin na zauna. Hauwa na sinto a baya na na shinfiɗeta a gefe baccinta take ta shantakawa. Halima Bawa kuma mayafinta ta yaye ta yi zamanta akan gadon Habiba Bala wanda yasha shinfiɗa lallausa."
"Ga bayan gida nan akwai ruwan zafi a ciki. Ku yi wanka, sai ku yi Sallah. Bari in samu Iya a kitchin inga mai take dafawa yau ina da manyan baƙi" A haka ta fita ta barmu hatta Halima Bawa kallon sha'awa take yi mata ballantana kuma ni tukururu. Wanka mu ka yi dukkanmu tare da ɗauro alwala. Kayan jikina ni dai na mayar na yafa mayafina ina tunanin to ina ne gabas ina son gabatar da sallar la'asar wacce aka jima da yin ta. Dan yanzu ƙarfe biyar ma ta gota, amman har yanzu lokacin sallar bai wuce ba. Ina cikin wannan tunanin Habiba Bala ta shigo da ƙaton tire shaƙe da kayan abinci.
Nuna mana gabas mu yi sallah Habiba Bala." Gabas ta nuna mun, da mamaki ta dube ni tace.
"Wai da ki ka yi wankan kayan jikin ki kika mayar Shanono, har yanzu kina nan da halinki na adankiya ko? Wannan fa ƙazantace, kin sako kaya tun daga gida, kin ciyo uwar tafiya yanzu kinyi wanka kin sake mayarwa jikin ki, to meye ma amfanin wankan naki in banda abinki, baki zo da wasu kaya masu sauƙi bane na shan iska haka?"
Gaskiya banzo da kayan shan iska ba." Dariya tayi tace.
"To yi sallar bari in kawo miki ƴar doguwar riga ta shan iska ko kema kya ji dama_dama. Bauchi ana zafi ba kamar Jos bane da zaki ji sanyi kamar a masko." Dariya mu ka yi dukka. Bayan mun idar da Sallah, muna zaune, Halima Bawa tana saye da ƴar doguwar riga ta shan iska mai kyau. Habiba Bala ta shigo rike da riga ta miƙo mun. Na saka rigarnan ɗas dani gwanin sha'awa ga cikina ya sake fitowa sosai a kayan. Soyayyar shinkafa da pepper chicken Habiba Bala tasa ayi mana shinkafar taji kayan lambu da yankakkun hanta ƙananu, ga masar Bauchi da ƙuli_ƙuli shima, sai lemon kwali na tatacciyar abarba mai shegen sanyi. Ni dai sai cika bakina nake yi. Har ga Allah tunda nake ban taɓa cin shinkafa mai daɗin wannan ba. Lemon tatacciyar abarba na kora dashi. Habiba Bala tace.
""Shanono watan yarinyarki nawa ne, naga cikin naki tsoho shima ga yarinya ƙarama?" Sai da na haɗiye naman kazan dana yaga nace.
Watan ta dai to tara zance kawai duk da bata ƙarashe ba shi kuma cikin wata takwas zance. Dan Allah a matsayinki na likitar mata wacce hanya zanbi dan ganin na kauce ma samuwar ciki ina shayarwa? Ke ni yaran ma sun isheni haka inason in huta ma rayuwata, Kaila sabon Aure ma zai kuma zai sake samun sababbin ƴaƴa ƴan gaban goshi, tunda iyayen nasu suma ƴan gaban goshin ne" Tataccen ruwan abarba ta kora kafin tace.
"Akwai hanyoyi da dama da mace zata yi tsarin iyali, domun jikin mace yana da buƙatar hutu da hakanne komaɗar mace zai dawo. Amman ta yaya ma zaki zama ƴar gaban goshi a wajan miji. Kullum cikin ciki da goyo, yau ƙarnin jinin biki, gobe ƙarnin nono haba. Akwai allura ta tsarin iyali, akwai wanda ake sawa, sannan akwai ƙwayoyin da ake haɗiya, duk in ba wannan ba akwai hanyar da zaki iya yin tsarin iyali ta hanyar ƙirgen kwanaki, ina nufin kwanakin sakkowar ƙwai, in muka ƙirga kwanakin al'adarki zan ɗauraki a kan hanya in wannan ɗin kike so. Kinsan mutane da dama na gudun matsalolin da tsarin iyali suke haifarwa ga lafiya. Amman yana da kyau tsarin iyali musamman a wannan ƙarnin da muke ciki na yawan mace_macen aure, da kuma yanda a wannan zamanin mazanmu na Hausawa basu cika tsaiwa akan ƴaƴa ba, hakan shi ya jefa Arewa a cikin musibu iri daban_daban." Gaskiya ne dukkan maganganun Habiba Bala, a raina naji na gamsu zan yi tsarin iyali ko dan nima jinin jikina ya dawo, so nake in daure in zama ƴar kallo a tsakankanin Kaila da abokan zamana. Duk da dama ƴar kallon ce. Hakan zai yiwu ne in na dakatar da haihuwa zuwa wani lokacin, suma su miƙe ƙafa suita zubo yaran, wala Allah su ya kula dasu da kyau, ni kuma in ci gaba da kulawa da nawa yaran." Halima Bawa tace.
"Wallahi hakane maganarki Dr Habiba Bala. Ni kaina daga wannan haihuwar dai in sha Allah ni na dena haihuwar baki ɗaya ma, wallahi da da hali ma mahaifar zan juya, wadanda na samu ma Allah ya raya mana su da imani. Yanzu mazan mu basa iya sauke ratayayyen hakkunan iyalansu daya rataya a wuyansu, mafi yawancinsu duk haka mazan suke, ɗaiɗaikune na kirki. Babban abinda yake bani tsoro shine ba ga gidan mai sani ba, ba ga gidan jahili ba, mata kuka suke ta ko ta ina kawai. Allah dai ya iyar mana kawai." Habiba Bala tace.
"Ni zan faɗa miki wannan Halima Bawa. Kun ganni aurena na fari malami na aura, wanda yake da sani sosai ta ɓangaren addini. Ni abinda ya fara jan hankalina a game dashi ma kenan. Sabida a tsari da zubinshi bai yi mun ba har ga Allah. Tunanin samun kwanciyar hankali, da kwaɗayin gurje soyayya yasa na shiga wannan gidan, dan kunsan ance ustazai akwaisu akwai iya soyayya da kwantar da hankalin mace" Dariya muka kwashe dashi ni ko har da tuntsurawata. Sai da mu ka yi mai isarmu sannan ta ɗaura da cewa.
"Amman dana shiga gidan nashi abun mamaki ashe ni nawa kallon kitse naima rogo (na ɗauka irin dacen da Mrs Bukhari tayi nima irinshi nayi. Dan nata ustaz ɗin sune mayun soyayya da tsantsar sanin darajar mace irin na ustazan asali) Wata na farko dana biyu duk lafiya. Daga wata na uku muka soma samun saɓani. In kwananane sai yayi ƙundumbala ya faɗa ɗakin uwar gidana, ni kuma babu haƙuri dan wannan ai rainin hankaline tsantsa, kuma duk macen da akaima haka tabbas sai ta zargi kanta da cewar ANYA NI CIKAKKIYAR MACACE KUWA? In na shiga na same shi yana cin abinci a ɗakin uwar gidanshi, da nayi mishi magana cewar kwanan nawa ne fa, sai yace ya sha'afa amman in yi haƙuri tunda yaci abincinta gobe ya shigo ɗakina. Daga haka matsala ta soma tun yana shigowa ɗakina wallahi har ta kai ta kawo ko iya ɗaga ido ya kalleni bayayi. Da nayi magana sai zagi da hantara, har ya dinga ce mun shi aurena bai amfaneshi da komai ba tunda ni ba haihuwa nake yi ba. Bazai dinga asarar ruwan jikinshi ta hanyar yin mu'amular Aure dani ba, ina mai asarar ruwa a banza yana bin rariya. Sai da na shekara biyu cib a gidanshi baya ko ɗaga labulen ɗakina. Abinci sai Babanmu ke aiko su Mansura su kawo mini. Dana je gida, sai su dawo dani raɓe_raɓe tare da faɗar wannan kalmar ta gadon mata (ko wacce mace zaman haƙuri take yi a gidanta. Amman duk macen da kika ganta a gidan mijinta akwai wani abun da mijinta yake yi mata wanda bata so) haka za'a tusoni gaba in dawo. Daga ƙarshe dai yai mun sakin tozarci. Yaronshi ɗan shekara uku ya aiko mun da takaddar sakina saki uku. Sai na dawo gida. Nan ƴan uwa da dangi suka dira a kaina. Biki ko suna sai da suka gagareni shiga. Mahaifiyata kuwa wallahi kamar sauyamun ita akayi, wani irin tsanata tayi, ko gaisuwata bata amsawa. Shekara guda nayi a gida sai na samu bazawari. Sakamakon tsangwama da son barin gaban iyayena yasa na auri wannan miji daya nuna yana sona. Dan ko bincike ba'aiba aka wankeni aka kaini gidan miji. Ashe madokine shi kuma. Ga matanshi tamkar karnuka kullum cikin haushi suke. Daya zo sai ya haɗa mu yaita labta tamkar Allah ne ya aiko shi. Ba dama kuyi magana ta arziki. To watan aurennan biyar ya mutu mus. Hmmmm" Hawaye ne ya gangaro a kumatun Habiba Bala, ni kuma nayi jigum ina saurarenta dan ko kwatan kwatan azabar da nasha a hannu maza bata ci ba sam, ni bana ma ƙaunar tuno da baya, banga abinda zai sa in zauna ba da labarin aurarrakin da nayi a baya ba. Na tabbatar labarin zai karya zukatan al'umma da dama, mata zasu zubar mun da hawaye sosai, maza da suke tunanin matsalar a mata ne, zasu sama ma mata lafiya. Habiba Bala ta share hawayenta taci gaba"
"Dana koma gida, na miƙa ma mahaifiyata takaddar sakina. Sai ta fashe da kuka, ni kaina kukan nake yi, shikenan na dawo gidan jiya. Ni ba mutuwar auren bane yafi ɗaga mun hankali ba, a'a irin zaman da zanyi da mahaifiyata da ƙannena shi nake tunani, dan hatta maƙota in suka shigo gidanmu sai sun yada mun habaici kafin su fita. Mahaifina a ranar ko runtsawa ya kasa yi, ni dai haka naci gaba da rayuwa a cikin gidanmu. Rana tsaka mahaifiyata take sanar dani mahaifina ya janye duk wani taimako da yake mun. Dangin su sabulu, man shafa, abinci, suttura. A ranar nayi kuka ainun, amman ya zanyi, sai na nemi mai gidan wani abinci ina mata wanke_wanke tana biyana ɗari biyu da abinci dafaffe. Da ɗari biyunnan zan sai sabulun wanki, dashi nake wanka, da ɗan man kaɗanya ko man alaiyadi su nake shafawa. Ina cikin wannan halin kwatsam wan mahaifina yazo daga ƙauye can Jigawa. Anan ya samu labarin mutuwar aurena na biyu. Ni dai bansan yanda suka ƙareba, bayan kwana biyu da tafiyarshi, sai ga Asabahu ɗanshi wai an turoshi ne ya ganni, in nayi mishi sai mu sasanta, in ban yi mishi ba to" hmmm Asabahu yace banyi mishi ba, wallahi mahaifiyata ta zaunar dashi ta dinga cewa ya rufa mata asiri, dangi sun sata a gaba ita kaza_ita kaza. Da haka ta jawo hankalin Asabahu ya amince da aurena. Ni ina gefe kamar yajin ƙosai, bani da bakin furta komai. Haka aka sa rana, aka kawo kayan aure a cikin baƙar leda viva. Ranar wata asabar aka ɗaura aure. Babanmu da kanshi ya kaini har wannan ƙauye. Dama nasan ƙauyen ni ba baƙuwa bace a ƙauyan. Nayi kuka sosai ganin yanda mahaifana suke neman kai dani. Ina cikin maraya haifaffiyar maraya sabida kawai ba sa son a zagesu ace sun kasa bani tarbiyyar da zanyi zaman Aure, shine suka kawoni ƙauye suka juye. Iya wuya naci wuya nice daka, nice zuwa gona, nice_nice_nice dai, ga ƙauye da gori wannan tambarin aure biyu fa yana nan anata yaɓa mini magana. Ni dai nasa audiga na toshe kunnena. Ta ɓangaren Asabahu babu daɗi, ta ɓangaren abokan zamana kuwa lafiya muke zaune dasu sosai. Shi kuwa babu dama yayi ba dai_dai ba in yi magana sai yace shifa dole akayi mishi alfarma yayi mun. Haka naita wannan zama na alfarma harna haihu. Sannan iyayena suka sake dani a bisa doron fishi da suke yi dani. Akayi suna ƴan uwa da suka zo daga Bauchi suka koma. Ni kuma naci gaba da shayar da Sani. Watan sani huɗu na samu wani cikin. Laulayi da raino ya haɗe mun. Hmm karfa ku mance a lokacin ni har ma nafi ƴan ƙauyannan munin kama wallahi, sabida rayuwar babu daɗi. Wata tara na haifi Auwal. Daga nan kishiyoyi suka sani gaba, wai na haifi maza biyu, nazo ina baƙuwa inason kwace dukiyar Asabahu. Hmm gashi shi kuma ya ɗauki son duniya ya ɗaurama Sani da Auwalu. Ni dai dama bani da wata daraja a wajanshi, bani kaɗaiba irin dai wannan ɗab'ar ta da yawan maza ta raina ƴaƴa mata, gani suke amfaninmu shine su huta damu suyi mana ciki, mu renan musu ƴaƴa. Daga lokacin da abokan zamana suka sauya mun, sai matsatsin gidan ya takureni, dan su suke debe mun kewa, mu yi daka tare, mu je roro tare. Sani da da shekara biyar na sake haihuwar ɗa Namiji ranar suna yaci sunan mahaifina Tasi'u ( Bala) Aifa nan komai ya caɓe mun. Ai mun ai ma yarana, yara babu damar su fita tsakar gida dan bala'i fa. Shi kanshi Asabahun bashi da aiki sai zaginsu da dukansu, da hantara kuma duk wannan son su da yake ya dena. Kullum a cikin kuka da lallaminsu nake. Haka kurum Asabahu ya sake ni da wata farar safiya saki biyu a karo na uku. Kuma zan tafi suka hanani ɗa ko ɗaya, yarana suna kuka ina kuka haka na baro ƙauyannan. Tunda na sauka a tashar Bauchi gabana yake ta dokawa hankalina a tashe nasan abun da zan tarar a gidan ba mai daɗi bane. Ai kuwa ilai abunda ya faru kenan. Kwararam_kwararam na shiga gida da tulin tsummokina ina kukan fitar rai ko zasu ji ƙaina su sassauta mun. Abun mamaki mahaifina nan ya rufe ni da duka, ya farfasamun jikina ko ganin girmana bai yi ba. Sabida baƙin ciki da takaici na sai da hawan jini ya kama shi. Ni kuwa na kasance tamkar mujiya, ko sallama akayi za'a shigo Mama sai ta turani ɗaki bata son mutane su ganni sabida su basason su ji kunya a wajan mutane. Sun dai zaɓi ni su karya mun zuchiya. Ga rashin iya zaman Aure, ga tsangwamar irin wacce kabilar Hausawa suke ma Bazawara, ga rashin ƴaƴana, shi kanshi jawarcin raɗaɗine dashi. ( Zawarawane kaɗai zasu gane wannan batun. Zawarci fa bashi da daɗi sam. Shi yasa wasu matan suke kashe kansu a gidan Aure, sabida gudun zawarci, da gujema tsangwama) Haka nai ta rayuwata babu wani mashin shini, na zama tamkar bora a gidanmu, aiki ake ledamun tamkar jaka, kuma fa haka na koma wannan gidan abincin na ci gaba da wanke_wanke tana bani wannan abinci dafaffe sai ƙarin albashi da tayi mun daga ɗari biyu zuwa ɗari

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login