Showing 66001 words to 68990 words out of 68990 words
Chapter 23 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
kokko. Ganin mu yasa aka ƙara yawan kofuna. Aliyu ne ya shigo da ledar ƙosai. Kowa ta danƙa mai kosai bibbiyu a hannu. Nima ta miƙo mun nawa kokko da ƙosan.
Baban yara ina kwana" Nace a sanyaye.
"Lafiya Tani. Za'a soma shiga kotun ko?" Kai na iya gyaɗa mishi kawai, dan harshena yayi nauyi. Ya nuna Yaya Use wacce idanunta su kai zuru_zuru yace.
"Kin ganta tun daren jiya take faman yin gudawa, har wayewar garin yau. Sabida tsabar tsoron zaman kotu. Idandunanta har sun faɗa. Ai irin abinda dama nake guje mata kenan. Itafa bata da aiki sai rigima da zafi, duk da a hakanma tayi sanyi" Kai ya girgiza yace.
"Allah ya kyauta. Sai kun dawo ni na fita kasuwa" Na dubi yaya Use nace.
Nima tun daren jiya zazzaɓi me zafi ya rufe ni. Gashi yau su Inno zasu dawo, ai in Baffa yaji wannan labarin daga ni har ke mun shiga uku. Barenma ni da abun lefi baya mun wuya."
"Tani na tsorata, gani nake yi bazan kuɓuta ba wallahi. Sabida tabbas na daki Hajiyayye, amman tabbas ban daki cikinta ba. Amman wa zai fitar dani a wannan ƙullin sai Allah " Kafin in yi magana Habiba Bala ta kirayi wayata.
"Shanono in shigo cikin gidan Yaya Usen ne?"
E Habiba Bala shigo muna ciki" iyakar abinda nace mata kenan. Na datse wayar. A hankali nake ɗan kurɓan kokkon. Ƙosan ma danƙama Hauwa ɗaya nayi, Balaraba ɗaya. Ruwan kokkon ma ya isheni. Da sallama Habiba Bala ta shigo. Tana sanye cikin riga doguwa fara mai shegen kyau. Ƙamshi take yi mai kwantar da zuchiyar mai shaƙa.
"Maraba Habiba Bala. Zauna ga waje dan Allah"
A ɗofane Habiba Bala ta zauna. Ta faɗaɗa murmushinta suka gaisa sosai da Yaya Use. Ni kuma ta dube ni.
"Shanono lafiya dai, naga jikin naki babu ƙwari sam. Menene damuwar?"
Hmmm babu Habiba Bala. Ya hanya?"
"To ya kamata ace ki yi wanka sai mu je ko, Yaya Use ku shirya, lokacin yayi mana a gaban kotun." Yaya Use tace.
"Kayya Habiba Bala. Tani dai ta shiga tayo wankan in zata iya. Ni kam har sai na ji yadda shari'ar zata kaya. Babban damuwata in da gaske alƙali ya tura mu gidan kaso, ni Use ya zanyi da raina Habiba Bala yarannan ina zamu kaisu?" Habiba Bala ta dube mu tace.
"Ko ɗaya Yaya Use, ai in Hajiyayye ta san farkon shari'a bata san ƙarshenta ba. Ku dai ku shirya kawai mu tafi" Da ƙyar na tashi nayo wankan na fito. Kayan jikina na mayar, ina fitowa Yaya Use ta shige ɗaki danta kintsa.
"Shanono na lura duk nasihar da nake yi miki akan ƙazanta baki dena ba. Kinsan Allah in na zuchiya ko wallahi bazan sake tako inda ma kike ba. Ke fa macece, ya kamata ki nutsu ko dan ummu nabeeha ki gyara. Na tabbatar sabida ƙazantarki ne yasa mijinku yayi miki jan fenti. Gashi ni nayi cinikin kujeru inaso in sai muku ko dan farin cikin yaranki, amman ƙila kujerun barinsu zaki yi yara su lalata a banza. Jibi kayan jikin ki, ba koɗewarba, ji dattinsu kin yi wanka tsabar iskanci kin kuma damɓarawa, meye amfanin wankan naki to? Jibi kanki dana yara duk datti. Ji Hauwa yarinya ƙarama ji tarin tulin ƙasa a kanta. Shanono sai fa kin miƙe zaki iya kwatar ƴancinki a idan duniya ma. Ki ajjiye damuwa da komai a gefe ki gyara kanki da yaranki, ki nutsu ki basu tarbiyya. Yaranki mata in kikai sake suka taso a haka wallahi kin kashe su. Suma fa korosu za'a dinga yi a gidan miji.?" Tabbas maganganun Habiba Bala sun ratsa duk jijiyoyin jikina. Kuma tabbas ita da Sabira burinsu shine su ganni cikin rayuwa da yanayi mai kyau. Nima ya kamata in faranta musu kamar yadda suke faranta mun.
Kiyi haƙuri Habiba Bala in sha Allah Shanono daga yau ta canja, bazan sake ba, zaku sha mamakin haɗuwarmu ta gaba" Ina faɗin haka na miƙe zuwa ɗakin Yaya Use."
Yaya Use ki ban wasu kaya da zasu yi dai dai da jikina" Ba tai mun musu ba ta zaro wata doguwar riga
"Kinga wata Inno ce ta hado mun a kayan data aiko mun. Dama ke naso ba ko Karime " Godiya nayi mata tare da saka wannan kayan. Na ari hijabin ƴan matan Yaya Use na saka. Na fito, Habiba Bala tayi murmushi tace.
"Koke fa. Kema kya ji daɗin jikin ki ai ƙazanta fa babu kyau Shanono, haka ki kai ta bamu wahala a makaranta, kai kin cutar damu da warin hammata irin na sabon balagarnan. Dariya mu ka yi duka. Sai ta tuno mun da wannan Dattijuwar da muke zaman benci ɗaya a makaranta. Ranar laraba daya kasance zuwana makatanta na uku, bayan an tashi na fito daga aji, hijabina duk jirwayen ruwan nono, muna ƙarni. Wannan dattijuwa sai ta tare ni tace.
"Ƴata in babu damuwa bari in baki shawara. Muddin ki kai amfani da ita zaki ji daɗi." Tsaiwa na gyara.
"Kin ganni nan yara ɗaiɗai sai da na haifi yara goma sha bakwai a cikinnan nawa. Ƴan bibbiyu sai da na yisu sau uku. Amman bamu yi ƙarni ni da yaran irin yanda kike wannan ƙarnin ba. Ke ƴata ce, yadda zan ma ƴar cikina haka zan yi miki. Kinga ajinmu duk gulmarki suke yi. Sabida cika ajin kike da ƙarni da warin rana da kin shigo. Ƴata ki dinga tsabtace jikinki, ko dan lafiyar ki da lafiyar jaririnki. Jiya da tsarabar kuɗin cizo na koma gida, kuma nayi alƙawarin yau zan yi miki magana. Ƙazantarki tayi yawa, jibi hijabinki duk datti, littafin turanci jiya da muka haɗa aka kaima malamin da ya bamu aikin gida a ciki. Naki fa da kika ciro duk manja. Tani Shanono ki dena kin ji ko ƴata?" Ta mun jan kunne, da nuni masu dama, amman nasa ƙafa na shure. Ni ganina nake tamkar ba mace ba, gani nake yi ni kowa ma ya tsaneni, wallahi bansan abinda ke damuna ba, amman ko iyakar cunkushewar zuchiya da haki dake yawan taso mun aka barni dashi shima jarabawane. Yaya Use ce data fito ta katse mun tunanina.
"Mu janku. Ku kuma ku kula da gidan banda yawo kune manya" Adda'a yaran su ka yi mana. Manyan kuwa sai da suka ga ɓacewar motarmu tukunna. Damuwa duk ta damesu, kamar yadda muma ta damemu. Shiru kuke ji a cikin motar babu motsin komai sai ƙaran Ac da Habiba Bala ta babbaka mana. Tafiyar minti goma sha biyu ce ta kawo mu kotun wajen amingo. Muna fitowa muka ga su Hajiyayye da tawagar ƴan gidansu birjik a zaune a gefen kotun. Kaila kuma yana gefe yana waya, da ganin yanda yake suntiri na gano yayi wata sabuwar budurwar kenan. Gefe guda muka ja muka zauna. Dangin Hajiyayye suna ganinmu suka soma tsaki da harare_harare. Babu wanda ma yabi ta kansu damuwar dake damun mu ma ta ishemu...
NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA.
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 20.
Gefe guda muka samu mu ka zauna. Kaila sai yawo yake a filin kotun yana ta wayarshi. Can lauyanmu ya ƙaraso a gurguje. Isowarshi ke da wuya aka buɗe kotu tare da bamu umarnin shiga. Wallahi ƙafafuna da ƙyar suka ɗauke ni izuwa cikin kotun. Wannan shine karon farko dana shiga kotu, ina fatan na ƙarshe in sha Allah. Kujeru ne a jejjere kamar makaranta. Sai wani gidan katako daga sama, da ɗan akwaku a gefe. Kowa ya nemi waje ya zauna. Lauyoyi suna gefen wajan zamansu.
"A yau ashirin da biyar ga wata. Wannan kotu mai alfarma zata yi shari'ar Hajiyayye wacce take unguwar layin ɗanmaraya, gida mai lamba Z2110. Inda ta shigar da ƙaran kishiyarta Tani, da Yar kishiyarta Use, akan kashe mata yaro da su ka yi a ciki sanadiyyar lakaɗa mata na jaki da su ka yi" Yaya Use ta zare idanu tare da riƙe ciki.
"Gudawa nake ji Tani. Nashiga uku" Cikin raɗa take magana. Kafin in san abinda zance sai mu ka jiyo Alƙali na faɗin.
"Lauyoyin duka ɓanrarorin biyu in sun halarci zaman su gabatar mana da kansu, kafin mu soma amsar hujjoji" Lauyan su Hajiyayye ya miƙe.
"Sunana Barister Safwan Sammani. Lauyan gwamnati, nine wanda nake kare waɗanda suke ƙara. Nagode mai shari'a" Zama yayi. Lauyan da Habiba Bala ta ɗaukar mana ya miƙe.
"Sunana Barista Suwiɗi Zakariyya, daga Aminci chamba. Nine wanda yake kare waɗanda akayi ƙara" Shima yana gama faɗar haka ya zauna. Bayan shiru na sakwanni ya wakana, sai Alƙali yace.
"Akwai wani jawabi da lauyan masu ƙara zai mana a matsayin shinfiɗa?" Ni dai jikina ya gama jiƙewa sharkab da zufa. Habiba Bala sai ƙarfafani take yi. Yaya Use kuwa ta durƙusa cikinta ya gama birgewa.
"Ina da shi ya mai shari'a. Hajiyayye dai har ƙofar ɗakinta Use ta je ta sameta, kuma ta cakaleta da dambe, suka haɗu ita da ƙanwarta Tani suka zaune Hajiyayye da tsohon ciki, basu suka ɗagata ba sai da su ka ga jini na zuba tukunna. Ya mai shari'a ina son wannan kotu mai alfarma ta kwato ma Hajiyayye hakkinta, a biyata hakkin jinin ɗanta daya salwanta. Likitoci sun tabbatar mana buguwa tayi a cikinta dalilin mutuwar yaron kenan. Wanda hakan yasa sai tiyata akayi mata aka cire mata gawar yaro. Nagode ya mai shari'a " Lauyan su Hajiyayye ya zauna. Kuka mara sauti na fashe dashi, shikenan mai fitar damu a cikin wannan matsalar sai Allah. Ƙila su Baffa da muke gudun su sani dole su sani, tunda in aka kullemu a gidan yari dole labari zai je har shanono ma. Lauyan mu ya mike yace.
"Ya mai shari'a ina da ja a bisa jawabin abokin aikina. Domin har yanzu zargi akeyi ba'a tabbatar ba. Bai kamata ya dinga jingina laifin ga waɗanda ake tuhuma ba kai tsaye. Sannan abinda yai sanadiyyar har Use ta daki Hajiyayye shine. Hajiyayye cikin kaifin harshe ta zazzagi iyayen su Use tare da aibantasu dan kawai sun kasance nakasassu. Ya mai girma mai shari'a, kowa yasan duk wani ɗa na halas yana kishin iyayenshi ko da kuwa iyayennan nashi masu taɓin hankaline. Wannan lamarin shi ya haddasa turka_turka a tsakanin Use da Hajiyayye. Amman Tani bata sa hannu a jikin Hajiyayye ba. Ita kanta Use bata zauna a ruwan cikin Hajiyayye ba, kuma bata naushi cikinta ba."
"Ina da ja ya mai shari'a. Use ta zauna a kan ruwan cikin Hajiyayye, a tsakar gida akayi abun. Maƙota sun shigo a daidai lokacin da Hajiyayye take kwance a ƙasa jini na tsiyaya a jikinta. Sannan a gaban matar Ƙanin mijinsu mai suna Hindatu akayi. In kotu na son in gayyato mata Hindatu, a zama na gaba zata zo. Domin ta faɗi abinda ta sani game da hakan. Akwai takaddar asibiti data tabbatar da cewar buguwa Hajiyayye tayi shine yai sanadiyyar mutuwar abinda ke cikin nata." Lauyan su Hajiyayye ya miƙa takaddar asibitin i zuwa ga mai shari'a. Bayan ya duba takaddar sai yace.
"Zamu je hutu na minti talatin kafin mu dora" Daga nan ya buga guduma, mu ka miƙe tsaye dukkanmu. Sai da ya shige wata ƴar ƙofa kafin muka soma fita. Yaya Use da gudu ta fita, mu ka bi bayanta. Wani gidan sama dake jikin kotun ta shiga da mugun gudu. Gudawace ta koreta. Muna zama na sau kuka mai sauti.
"Lallai Hajiyayye sun shirya ganin sun kai ku ƙasa sosai. Kuma mun yi magana da Suwiɗi fa akan daga zaman kotun ya ƙare zamu je asibitin da suka karɓi haihuwar Hajiyayye. Suwiɗinne ya iso inda muke, duk muka miƙe tsaye.
"Tani ki dena kuka. Amman abunda na fahimta da wannan shari'ar, shari'ace wacce akeson ganin an kaiku ƙasa, dan kes ɗin yana da girma. Amman mun miƙa ma Allah lamarinmu, ku yi ta adda'a. Habiba Bala ita kanta jikinta yayi sanyi balle ni Shanono. Habiba Bala tace.
"Amman barista kana ganin zamu yi nasara? Likitoci fa sun tabbatar da cewar buguwace tai sanadiyyar mutuwar yaron a ciki." Dariya yayi yace.
"Ke dai ku kwantar da hankulanku, zamu yi iya yinmu, Allah shi ne zai iya mana. Ina Use?" Sai lokacin muka hangota tana tafe tana ɗingishi. Su Hajiyayye ma magana suke da nasu lauyan. Kaila ma yana tsaye a kusa dasu. Sabira muka hango tafe. Yaya Use ta ƙaraso in da muke.
"Ni nasan ma kurkuku zasu kaimu. Wallahi narantse da wa billahillazi huwarrahmanu ban daki Hajiyayye a ciki ba. Na dai fyaɗa ta da ƙasa. Idonane ya rufe kuimun rai " Sai kuka. Sabira ta iso wajanmu jikinta a sanyaye sakamakon yanda taga idanuwanmu sun yi jawur, dan hatta Habiba Bala a yau sai da hawayen idanunta suka zuba. Minti talatin na cika muka koma ciki. Kafinnan fa sai da yaya Use tayo gudawa sau biyu. Gabaki ɗaya ta galabaita ta fice a hayyacinta. Lauyanmu ne ya soma magana.
"My lord inaso wanna kotu mai alfarma ta duba lamarinnan, tayi duba a kanshi. Sannan ina neman alfarmar wannan kotu mai alfarma data ɗage shati'arnan zuwa wani lokaci, domin tattaro hujjoji. Nagode my lord" Lauyan su Hajiyayye ya miƙe tsaye.
"My lord, nima ina roƙo kamar yadda ɗan uwana ya roƙa a sake saka mana lokaci. Kafinnan inason kotu ta tsare Tani, da Use a gidan kaso har zuwa ranar da za'a dawo zama na biyu. Domin su masu lefine, kuma kisan kai ake tuhumarsu dashi my lord. Ko belinsu da aka bayar ba bisa ƙundin tsarin doka aka ba da belin nasu ba." Baki dukkanmu muka buɗe. Zuruf lauyanmu ya miƙe tsaye.
"My lord ina da ja" Shima lauyan su Hajiyayye ya miƙe a zabure yace.
"Nima ina da ja. Bai kamata ace su Tani su yi kisan kai ba kuma a barsu suna bacci a gida hankalinsu kwance. Wanda in da yazo da ƙarar kwana ita kanta uwar jaririn zata iya rasa rayuwata" Lauyanmu yace.
"Ya mai girma mai shari'a. Inaso wannan kotu mai alfarma ta ji ƙan su Tani ta barsu a gidajensu. Tunda har yanzu ba'a tabbatar su su kai kisan kan ba. Ta yiwu wani abunne da ban ya kashe yaron su kuma suka taka sawun ɓarawo. Ta yiwu yaron ma ya jima da mutuwa a cikinta. My lord ina roƙar musu alfarma a matsayinsu na mata masu rauni. Kuma dukkansu a halin yanzu ba ishasshiyar lafiya garesu ba, sannan ita Malama Tani tana da ɗanyan goyo, ƴan satittika tayi da haihuwa, sanyi zai iya illata mata lafiyarta, sannan a dubi shi jaririn" Alƙali ya dube shi yace.
"Wannan kotu ta ɗage wannan ƙara zuwa ashirin ga sabon watan da zai tsaya. Wanda zai kama ranar laraba. Zaman zai kasance na ƙarshe, dan haka lauyoyin duka ɓangare biyu ko wanne ya tanadi hujjojinshi. Duba da dubi da wannan kotu tayi, da nazari da tayi. Kotu zata sa a tsare Tani, da Use a gidan yari zuwa ranar da za'a yi zaman ƙarshe..........." ANAN NA KAWO ƘARSHEN LITTAFI NA ƊAYA 1 WANDA KUMA YAYI DAIDAI DA KAMMALA FREE PAGE ƊINA. DUK MAI SON JIN KARASHEN LABARIN SHANONO, SAI MU TARA DASHI A PAID GROUP, IN DA ZAN KAWO MUKU BOOK 2, DA BOOK 3. TAFIYAR FA NA FAƊA MUKU TANA DA TSAYIN GASKE. YANZU NE ZAMU SOMA LABARIN MA. KAR KU MANCE SHANONO BATA LABARTA MANA TARIHIN RAYUWARTA, DA TARIHIN AURE_AURENTA BA. KUMA NA SAN KOWA NA SON JI. MU HAƊU DAKU A GROUP ƊIN KARATU. NAGODE. GA NUMBER NA GA DUKKAN MASOYA MASU SON YI MUN GYARA, KO MASU YABON ALƘALAMINA, DAMA MASU SUKAR ALƘALAMIN DUK ƘOFA A BUƊE TAKE. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI TAKU CE.
08179523215
DOMIN SAMUNA KAI TSAYE GA NUMBER NA.
*SANNAN INA ƘARA JADDADA MUKU PROMO NA TURAREN TSUGUNNO, DA TURAREN TURAREN ƊAKI, DA TURAREN TURAREN TURARA KAYA, DA HUMRAR GASHI, DA HUMRAR FESAWA A KAYA IN ZAKA TURARASU, DA HUMRAR MATAN AURE, SUNE SETINMU DA NA FITAR MUKU DA PROMO AKAN 10K DUKKA SETIN KACAL. GARAƁASANE GA MASOYAN ALƘALAMINA IYAKAR ƳAN PAID GROUP ƊINA KAƊAI KE DA DAMAR MALLAKAR WANNAN TURARUKA MASU SIRRIN DAƊI, KUNSAN MU KANURI MUNSAN SURRUKAN ƘAMSHI IRI IRI. NA MUTUM 20 KACAL ZANYI SETIN IN SHA ALLAH. KI YI HANZARI KAR A BARKI DA CIZON YATSA.
GAWURTATTU UKU 👠👠👠
1 _KWAI A BAKA_
*(UMMU AFFAN)*
2 _ZULFA_
*(UMMU MAHEER MISS GREEN)*
3 _NA FAƊO DAGA BENE..._
_NA ZARCE RIJIYA_
*(BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI)*
_Littafi ɗaya; 400_
_Littafi biyu; 800_
_Littafi uku; 1000_
Ga masu son turo kuɗinsu ta account sai su tura a wannan account ɗin 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
0037219728
Fatima Rabi'u Sunusi
StanbicIBTC Bank
Sai ku tura da shaidar biya ta wannan number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
08104335144
Masu tura kati kuma sai su turo screenshot na katinsu Mtn ta wannan number 👇🏻
08104335144
*GA MASU SON A TALLATA MUSU HAJARSU A DUKKANNIN SHAFINMU NA Facebook, whatApp, telegram, YouTube, groups, status, zamu tallata muku ne a kan farashi mai rahusa 10k ne kacal sai ku tuntuɓi numbobinmu kamar haka 👇🏻
08104335144
07068606171
08179523215
Domin tallata muku hajojinku a cikin na sati guda ya kama👇🏻
2k kacal
Sati biyu
3k ne
Idan kuma kanason har mu gama book mu dinga ɗaura maka ya kama
10k kacal.
Muna godiya da zaɓar GAWURTATTU UKU ako da yaushe. Siyan nagari mai da ƙudi 🙏🏻.
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU👇🏻👇🏻
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻