Showing 39001 words to 42000 words out of 68990 words
Chapter 14 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
Maman Samira kin dawo?" Wata uwar harara Hajiyayye ta sakar mata kamar idanunta zasu faɗo ta ja tsaki. Murmushin cusa haushi Bilkisa ta sakar mata. Anty Maryam ce ta amsa ma Bilkisa gaisuwarta tana ƙarema shigarta kallo."
"Shamwila" Ta kira Shamwila da ɗan ƙarfi. Da sauri ta fito daga kitchen ɗin.
"Anty gani"
"Ki kai plate da cokali ɗakin Gwanda, in kin kai sai ki rufo ƙofar ki same ni a ɗakina" Tana idasa faɗa ta shige ciki, ta bar Hajiyayye da sakakken baki. Motsi wannan Hajiyayye ta kasa yi. Yanayin Bilkisa ya firgitata ainun. Bilkisa tafi ƙarfinta tako ta ina, in ma gasa tace zata yi da'ita ta'ina zata soma? Duk inda take jin tana da buɗewar ido. Bilkisa ita nata idon tsabar yagewa ɗayan ya haɗe da ɗayan. Da jan ƙafa Hajiyayye ta nufi ɗakinta da ko rufewa bata yi ba. Anty Maryam tace.
"Hiye irin matar da Kaila ya auro kenan ƴar boko maras kunya? Danƙari Hajiyayye akwai gagarumin aiki babba a gabanki. Domin kishi da macen data fi ƙarfinka aikine ja. Amman abinda zan faɗa miki shine kar ma ki sake ku sake hayaniya da Kaila har ta kai ki da dawowa gida. Mijin da yake da irin wannan Amaryar taku ko ya rabu daku duka kune da asara. Ni dai fatana Allah yasa kafin Babanku ya iso muji labari mai kyau" Hajiyayye tana zaune sai jijjiga kawai take ta dunƙule hannunta ɗaya tana nausan tafin hannunta dashi. Chaji kawai kanta yake ɗauka. Tunani take ta wacce hanya zata fitar da Bilkisa a gidan, dan in ita Hajiyayyen bata fitar da'ita ba. To zahiri ita zata fitar da'ita. Ita Shanono ba'a sata a lissafi dan bata ma san ciwon kanta ba, a cewar Hajiyayye wacce tayi zurfi cikin zancan zuchi.
"Ita Shamwilar da aka aika turaka da'ita tazo ne a saman gara koko yaya?"
"Ni ban sanma tsinannu ba. Nima yanda kika ganta haka nima na ganta. Anty Maryam amman kinga irin shigar da Amaryar kwana ɗaya tayi kuwa?" Anty Maryam tayi dariya tace.
"Na gani sarai kuwa. Ke dai ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki zaƙulo salo_salon kissa da hilatar miji ki ƙara akan yaƙin ki da Uwargidanku, dan wannan yaƙin shine asalin yaƙi, kinsan wannan kam sai dai ku fafata dan sai inda ƙarfinta ya ƙare. Amman ki kiyaye abinda zai taɓa igiyar aurenki, kinji dai furucin mahaifinki kunsanshi da zafi dai akan irin waɗannan maganganun. Rabi kina gani da mijin ya sakota ta dawo gida, da duka mahaifinku ya rakata har ɗakinta, wallahi ki kiyaye kema dan sunan gyatumarmu ne dake da kin yaba ma aya zaƙinta." Suna cikin wannan tattaunawa suka jiyo Sallamar malam Tsaiha mahaifi ga Hajiyayye. Ita da kanta ta fita tayo mishi iso har ciki. Rannan nashi a murtuke, bayan ya zauna ne yayi shiru kamar mai tunani har na tsawon minti biyu. Daga bisani kuma yace.
"To da ƙyar da siɗin goshi mijinki ya aminta ya dawo dake ɗakin ki. A hakannma sabida darajarmu ne. Yace tunda ya bijiro da batun aurennan baki sake barinshi yayi bacci ba. Kiji fa Maryam har sau biyu tana fasama bawan Allah wayarshi salula. Sabida kawai ƙazamin kishi, ko haka taga iyayenta suna yi ohon mata. Ni gidana ko kara na ajjiye ai cikin iyayenta ba wacce ta isa ta tsallake wannan karar gabanta gaɗi. Wallahi in baki yi wasa ba sai in miki baki tunda baki da mutunci, so kike ki mayar dani dattijon banza ake ganina a matsayin wanda ya gaza wajan baku tarbiyya? Jibi abinda Rabi ta aikata itama fa. Kinci sa'a ke uwatace wallahi da sai na dakaki a cikin ɗakinnan tunda baki da hankali. Ke baki rasa ci ba, baki rasa sha ba, baki rasa suturaba da an taɓo ku ku dawo mana gida, alhalin iyayenki duk sun rasa abinda ke baki rasa ba a naki gidan mijin. Matar Bahaushe kenan, ire_irenku ke sa adadin yawan zawarawa yake sake hauhawa a ƙasar Hausa, da gangan ake ɗaura mana laifin kacokam, ai in ɓera da sata daddawa da warinta. in zaki bi mijinki ki bi mijinki, kin ganni nan aure zan ƙaro ni kaina nan da sati biyu masu zuwa, kuma yarinyace bata shige sa'arki ba. Yaushe za'aita zama da tsofaffin guzuma bayan Allah ya bamu damar da zamu more rayuwarmu." Ta inda mahaifin Hajiyayye ya shiga ba ta nan yake shiga ba. Shi ba kuɗi ba, sana'ar tashi ba wata ta kawo makudan kuɗi ba amman yana maganar cikace mata ta huɗu. Matanshi uku, yara kuwa sunfi ashirin, shagon siyar da gwanjo na yara yake dashi a kasuwar gwanjo dake katako. Yanayin sana'ar tasu hawa da sauka ne. Haka su Hajiyayye suka taso babu yabo babu fallasa, abincin da zasu ci wani sa'in sau biyu kacal yake iya ciyar da iyalanshi, na ukun sai dai iyayen su yi buga bugarsu a ƙuƙuta aci. Ko makaranta yaran da dama iyayensu mata su suka ɗau ɗawainiyar makarantar yaran nasu. Matsalolin yau daban na gobe daban. Amman a hakan yake neman yayo ƙarin Aure da ƙaramar yarinya sa'ar Hajiyayye. Mahaifin Hajiyayye yana ɗaya daga cikin mazan ƙabilar Hausa masu cisgunawa matansu da yaransu. Dalilina kuwa shine, ƙarfin samunshi bai wuce na mata ɗaya da ɗan yara ƙalilan ba. Kuma shima yasan da haka, amman dake babu sunnar da Hausawa suka fi ɗabbakawa sama data ƙarin aure a hayayyafa dan manzon Allah yai alfahari dasu ranar ƙiyama. Fahimtarsu ce ba dai_dai ba. Domin babu a inda akace a haifi yaran iska, a kasa basu tarbiyyar islama kuma ayi tunanin wai wannan yaron zai zama abun alfahiri ranar ƙiyama. Ai ko ku da kuke iyayenshi ba za kuy aifahari dashi ba. Sannan babu a inda akace sai an auri mata biyu, uku, huɗu dole, akwai mazan da auren ma ya sauka a kansu baki ɗayanshi. In kana da halin ɗaukar nauyin lalurorin mata huɗu da yaransu, kuma kana da lafiyar jiki da zaka dinga iya biyan buƙatunsu, kana da dukiyar da zaka ɗauki nauyin karatu da tarbiyyar yaranka, zaka kwatanta adalci a tsakaninsu. Alh ai baka da matsala sai kayi mata huɗu abinka. Gargadi muddin kasan baka da wannan halin to maganin kar ayi kar a soma, ko dan gudun haifar ƴaƴan iska masu addabar anguwa da sace_sace da harkar daba, fyaɗe, da sauran gurɓatattun abubbuwa. In kunne ya ji jikinmu ya tsira.
Haka mahaifin Hajiyayye yay mata tas, sai kukan baƙin ciki take yi. Tafiya su kay suka barta a cikin damuwa da tashin hankali. Rana zafi inuwa ƙuna. Gida ba daɗi, iyayenta haƙuri su ke yi da Babansu. Gidan Auren ma babu daɗi Kaila ya ƙaro samfurin rashin mutunci. Tana zaune dirshan a tsakiyar ɗakinta ta jiyo dirin shigowar lifan ɗin Kaila. Da harara tabishi ta labule ba dan tana ganinshi ba. A cikin kunnuwanta take jiyo oyoyon da Kaila ke ma Bilkisa, itama tana mishi oyoyon cikin muryar kirsa irin tamu ta mata. Yatsa Hajiyayye ta ciza. Tana ta jiran shigowar Kaila yau zai shigo, gobe ne, ko jibi. Har bayan isha bata jiyoshi ba. Ba shiri ta miƙe da cikinta a gaba ta nufi turakar Kaila.
Kaila:
Shi kuma Kaila a dai_dai wannan lokacin yana zaune Bilkisa na bashi abinci a baki. Sai washe mata baki yake yi. Yana shigowa gidan ta jashi bayan gidan ɗakinshi, dama tasa Shamwila ta haɗa mai ruwan wanka. Yana fitowa ya wuce masallaci, bai shigo ba sai da akayi isha.
"Amman Ɗanyan gwal yarinyar ta iya abinci babu laifi. Ni tunda nake ban ma taɓa cin soyayyar taliya ba, ga kazar ta ɗau maggi da tafarnuwa." Murmushi kawai tayi mishi tace.
"Nima da na ci abincin na yaba mata. Kaga bani da wata fargaba ko ran girgikina in na samu aikin kwana, Shamwila zata yi maka duk abinda ya dace, ba tare da na shiga hakkin abokan zamana na ɗaura musu hakkin da ba nasu ba." Dariya yayi yace.
" Ƙwarai ma da gaske, Shamwila za tai mun komai da komai daya dace. Da kike maganar ɗaura hakki, ai Shanono ce kaɗai zata iya yarda tayi wannan aiki ko ba ranar kwananta ba. Hajiyayye ai baza ta taɓa yarda ma tayi ba. Wannan da kike ganinta ƙwayar boris ce zafi gareta fa sosai."
"E babu shakka an zauna ana kwance mun zani a gaban kishiya. Tur da kai Kaila wallahi . " Suka jiyo saukar muryar Hajiyayye a kansu, sai jijjiga take faman yi, basu ji shigowar tata ba ma. Kaila yace
"Zaki fita a ɗakinnan ko sai na turaki gidan tsoho kin je kin ɗan ja koriyar miya ne? Nifa shi yasa naso a barki a gida, ko nima na huta amman mahaifinki ya dinga mun magiya darajarshi na duba har kika ganki a tsaye a kanmu" Hajiyayye tsabar kunya sai taji kamar ƙasa ta tsage ta faɗa. Masu iya magana na cewa, in baki yasan me zai furta, bai san me za'a mayar mishi ba. Jibi yanda Kaila ya tsinkata a gaban kishiya yana jifanta da kalaman da zasu zubar mata da mutuncinta. Cikin borin kunya ta ɗaura hannunta a bakinta ta shiga yi mishi ele.
"Woooo woooo wooo kaji kunya Kaila kaji kunya. Yarinyar da na yi imani sai da ka gama zakuɗa hannunka cikin ramar kayi kwaɗo kafin ka kawota cikin gidan kamar yadda nima kayi mi...." A mugun fusace Kaila ya dakatar da'ita da cewa.
"Ƙarashe kalmar da kike son fesarwa dai_dai yake da saki Hajiyayye. Baki da hankali ne, ni zaki ci ma mutunci a gaban iyalina?"........✍🏻
NA FADO DAGA BENE....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 8
_*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_
_kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_
*MUSUK*
*MADARAR TURARE*
*KAJIJI*
*ROT*
*SANDAL*
*HUMFUR*
*SANDAL FLASK*
*SANDAL WUD*
*AALUT*
*GAF-GAF*
*JANNAMI*
*ƘWALAKCA*
*MAHAHABSUFYAN*
*WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE*
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S
*ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻*
Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224
*AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA*
*AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA*
*AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA*
*AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR*
*MULATO SOAP*
*FACE CREAM*
*FACE SOAP*
*MULATO WHITENING LOTION*
*HAIR GROW OIL*
*HAIR GROW CREAM*
*KAR-KAR OIL*
*MINT LEAVE OIL*
*ANTI PIMPUS SOAP*
*AƘWAI SABULUN NANKARWA*
sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*ABIN BUKI*
*ABINCIN OFFICE*
*SNACK*
KAMARSU👇🏻👇🏻
*WAINAR MASA*
*SINASIR*
*MEAT PIE*
*CINCIN ƊAN LAUSHI*
*CUP CAKE*
DA DAI SAURANSU.
AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻
Hatta inifom mijin Sabira ne ya ɗinga musu, da basa zuwa ko ina sai gararamba a unguwa. Haka zalika shi ya sanyasu a islamiyya irin ta cikin anguwa, duk sati suna tafiya da nera hamsin, shima wannan ko da Kaila yaga suna zuwa bai ce dani komai ba, nima ban tanka mishi ba. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Sabira a karo na barkatai nace.
To zan bar miki su, zan haɗo inifom ɗinsu Sani zai kawo miki. Zaki sha bari_bari kenan bakin ki sai yayi tsini ashe kafin in dawo. Dariya tayi tace.
"Su Mustapha da Umar fa da kike ganinsu wallahi sun fi Shafi'i da Sulaiman rigima, Sani shi bai da yawan ƙiriniya magana ma bata isheshi ba. Kullum a cikin raba dambe nake."
Hmm suma ko da yaushe aikin Kenan." Mun jima muna tattaunawa kafin muka fita domun ɗora girkin rana. Ƴan Wudil kam har sun fito tsab zasu koma, ƴan Akwanga suma ina ji suna cewa da sun yi azahar zasu tafi. Sallama nayi ma ƴan Wudil, muka shiga hidimar abincin rana. Girkin dangin Amarya daban Sabira tayi shi. Tuwon shinkafa miyar ganye tayi musu da kaji. Ita tayi komai da komai, kuma ta ɗauka ta kai musu. Bata jima ba ta fito. Ƴan Akwanga suna cin abinci suma suka kama gabansu, harda Baba Rammai dan an bogo waya an yi musu haihuwa. Sabira da Hindatu ne suka yi wanke wanke da gyaran gidan. Fes suka wanke tsakar gidan yayi kyau sosai. Misalin huɗun yamma muna tsakar gidan ina ɗaura sanwar miyar dare. Sai ga dangin Amarya su biyu, sun sa Amarya a tsakiya. Suna zuwa in da muke suka tsaya.
"Bayin Allah muna neman ɗakin uwar gidan gidanne, zamu kai amarya bisa doron al'ada." Sabira ce tayi musu jagora zuwa ɗakina ta nuna musu taburma. Ni kuma na kirawo Hajiyayye da Hindatu, tare muka shiga ɗakin, na shiga na same su sai yamutse fuska suke yi, ba shakka zarni ne ya ishesu. Bayan an yi ƴan gaishe_gaishe wata farar mata tace.
"Wacece uwar gidanne a cikinku?" Hindatu ce ta nuna ni tana dariyar ƙeta, ta nuna Hajiyayye a matsayin ta tsakiya. Baki suka sake su kansu, ƙila sun yi tunanin mai aikin gidan Kaila ce ni, dan sun gagganni face_face ina shan uban aiki kamar jakka tun zuwansu."
"To uwar gida kece babba ga Bilkisa mun kawota domun ku gana, ba Domin mun kawo muku amanarta ba, amanarta na hannun wanda ya rabota da garinta da ahalinta. Bilkisa ki buɗe fuskarki abokan zamanki su ganki ki gansu" Bilkisa tana saye da wata lafaya mai adon duwatsu faca_faca hannu tasa tayi baya da mayafin. Wallahi bani ba hatta Hajiyayye da take jin ita shahararriyace sai da ta ƙware. Bilkisa gaskiya tana cikin sahun kyawawan matan hausa fulani, uwa uba gata da haske sosai, ga iya kwalliya da zabin kalar daya dace da launin fatarta.
"Ina yininku Anty da Anty?" Wani ƙwallon kishi na haɗiye nace.
Lafiya lau Amarya Bilkisa ya baƙunta?" Murmushi kawai tayi mun bata ce komai ba. Iyakar abinda ya faru kenan, sai shaida mana cewar yanzu zasu tafi da suka yi. Fatan sauka lafiya nayi musu Hajiyayye dai in kun tanka ku masu karatu to itama ta tanka, tunda Bilkisa ta buɗe fuskarta Hajiyayye ta daskare a zaune. Ana cikin haka Kaila yayo sallama ya shigo, sai faman dariya yake yi, yana doro.
"Anty Zinaru baku wuce ba ashe?" Sai wani dariya yake yi harda wani sin_sin da kai. Ita wacce ya kira da Zinaru tace.
"Munkaila yanzu zamu tafi, ka kula da Bilkisa sosai kar ka manta da sharaɗin da Mahaifinta ya gindayama tun kafin ma tafiyarku ma tayi nisa. Bayan kwana bakwai zata ci gaba da zuwa aikinta, an yi magana an gama mata komai aikin kawai zata soma zuwa." Dariya yayi yace.
"Babu ai komai Anty Zinaru ni dama ƴar bokon naso shi yasa na biyota kuma na aminta da komai. Zuwanta cikin rayuwata aikhairine mai girma, gidan zai ɗau saiti sosai, nifa yanzu ne na san nayi auren kece raini. Ina godiya sosai da karramawa" Nan su kai mana sallama suka fice, ni maza sun dena bani mamaki tuni. Hajiyayye ce tayi kasaƙe tana kwasar ruwan mamakin Kaila. Fitar Amarya da ƴan uwanta ke da wuya Hajiyayye ta miƙe tsaye tace.
"Aikin banza aikin wofi ni Kaila zai wulaƙanta sabida ya auro ƴar boko, wallahi zaman lafiyar Kaila da kilakin daya auro ya ƙare. Fuuu ta fice kamar kububuwa, Hindatu ta bi bayanta tana faɗin.
"Allah ya kyauta, wannan cin fuska dame yai kama ne ni ƴasu?" Sabira ta dubeni, nima ita nake kallo, murmushi nayi mata kawai muka koma bakin aikin mu, amman zuchiyata a cushe take ainun. Zuwa yamma gidan babu kowa sai mu mazauna gidan, yara suna gidan Sabira ta haɗe kansu dasu Mustapha sun tafi, Hauwa tana bayana. Ina kan yin shanyar kayan Hauwa dana ɗan ɗauraye sai ga Kaila ya shigo gidan, kici_kici da manyan ledoji yana shirin wucewa ɗakin Amarya.
Sannu da shigowa *Ango* Jin na kirayeshi da Ango yasa ya washe mun bakinshi har kunne.
"Sannu Shanono da hidima da jama'a fa" Murmushi nayi mishi, Hajiyayye tace.
"Inason yin magana da kai Kaila kafin ka shiga ɗakin Baturiya" Dubanta yayi yana nazartarta kafin yayi wani malalacin murmushi wanda ni nasan na muguntace.
"To yau dai kwanan Amaryane baki da hurumin da zaki ce dole sai kin yi magana dani." Yana kaiwa nan ya burma ɗakin Amarya ya rufo ƙofa garam. Numfashi kawai naja, ina gama abunda nake yi na yi alwalar magriba nayi shigewata ɗaki na danna sakata."
KAILA:
Yana shiga ya tarar da Amarya a harɗe a kan kujera tana kallon tashar Mbc action, ana wani film na soyayya. Baki ya buɗe yana dariya. Itama juyowa tayi ta yi mai murmushi mai burgewa.
"Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida. Ni na ɗauka zan zo in tarar dake akan gado a harɗe kin rufa da mayafi kina jiran in sai bakin ki?" Dariya tayi mai tace.
"Siyan baki kuma? Sai kace wadda bata waye ba. Ai ni na ɗauki wannan abun a matsayin ƙauyanci, Shekara guda muna soyayya sai yau kawai in rufe maka fuskata haba mana Ƙyalli " Murmushi yayi haƙiƙa Kaila sai ya ji Bilkisa ta sake burgeshi, irin macen daya jima yana nema kenan. Amma a baya bashi da damar mallakar irinsu, duba da yanayin rashi da yake ciki. Amman a yanzu sai hamdala, sana'arshi dai shine gashin kajin gidan gona, kuma wajan gashin nashi babbane, a rana ya kan siyar da kaji guda ashirin ko sama da haka, banda masu siyan pat_pat irin su cinya, ƙirji, kai da ƙafa da sauransu. Kuma shike kiwata kajin a gidan gonarshi da kanshi, ga kashin kajin da yake siyarwa buhu_buhu. Zama yayi a kusa da'ita yasa hannu ya jawota jikinshi tare da lumshe idandunanshi. Itama idan nata a rufe yake, taushin fatarta da irin ɗumin jikinta yayi daban da na matanshi baki ɗaya. Iya hakan ya fitar dashi daga hayyacinshi sosai. Bilkisa ba tai aune ba taji Kaila yai ma bakinta riƙon alawar yara. Abunka da wayayyar mace tuni itama ta fara mayar mishi da nata martanin, cikin wani irin salo mai gigitarwa. Kaila kusan suman zaune ya kusan yi yanda yaji Bilkisa na wasa da harshenta a cikin bakinshi. Kota ina a jikinta ƙamshine har bakinta, hatta numfashi in ta fitar ƙamshi yake korowa. Wannan masoya sun jima suna shaƙar ɗumin juna, dana bisani Kaila ya zare bakinshi a