Showing 6001 words to 9000 words out of 68990 words
Chapter 3 - NA FADO DAGA BE NA ZARCE RIJIYA Complete By Badiat Ibrahim B4B.txt
guda uku nace ta kaima ummanta. Sai da na tuƙa tuwo na kwashe a leda na mayar da ruwan wanka sannan na saka katin a wayata, na ɗan sake share falona sama_sama. Ban zauna yin wayarnan ba sai da na fito wanka na kintsa tsab. Sanye nake da riga da skirt na gwanjo da azumi na siya a wajan tafsir ɗin mai shafi. Ni dama ba kananun kaya nake sawa ba, na ga kananun kaya sunfi burge Kaila ne shiyasa ma na cire ɗari ukuna na siya." Danna kiran layin Yaya Use nayi, bayan ta ɗaga nayi mata barka da Sallah mu ka ɗan taɓa hira na kashe wayata. Layin Inno na kira nayi musu barka da Sallah, daga ƙarshe na kira Yaya Karima itama mu ka yi gaisuwar sallah. Har zuwa bayan magriba ba su Kaila babu dalilinsu. whatApp na ɗan leƙa da bonus na data da glo ta bani, dan in ɗan ɗebema kaina kewa, group ɗin ƴar aljanna na leƙa mata sai turo hotunan sallansu suke su da yaransu, wasu a irin tabka_tabkan falukannan na gani a faɗe, wasu kuma a tsakar gida ma suka ɗauka, wasu a filin idi. Gasu nan dai birjik, wasu na buɗe na kashe ƙwarƙwatar idona, wasu kuma wucesu nayi. Wasu matan harda mazajensu a cikin hotunan. fita nayi a group ɗin baki ɗaya sabida naji anata kiran sallar isha. Har nayi Sallah ni dai banji motsin shigowar su Kaila ba. whatApp ɗin na koma ina hawa na ganni a cikin wani sabon group mai suna ( FGGC BAUCHI) dariya da mamaki na soma yi lokaci guda. Ina shiga na soma ganin sunayen ƴan ajinmu. Mariya Habibi, Habiba Bala, Fatima Bello, Aisha Aliyu musa Biu da dai sauransu, sauran ban sansu ba dake jiniyo kaɗai nayi daga zuwa huto aka cireni a makarantar nan komawar da ban sake yi ba kenan. Ni mamakina ma ina suka samu number wayata, duk mutanenannan ya akayi aka tattarosu" Daga farko na soma bin hirarrakinsu Habiba Bala ce ta buɗe gidan. Wani dogon voice note tayi, jikina yana rawa na danna, muryarta ce wallahi tana nan yadda nasan muryar. Nan ta faɗi manufofin buɗe group ɗin domun zumunci da ƙarfafa juna, ta bada labarin yanda akayi ta haɗo numbobinmu da dama a cikinmu, Fatima Sunusi ce ta bata number na. Mun taɓa haɗuwa da'ita ta shigo jos, lokacin ina aure a wani gidan ba gidan Kaila ba har ta ziyarceni. Haka na dinga bin saƙonnin mutane wasu a rubuce wasu voice har sai da na gaji, dan sunyi surutu fin dubu ɗaya da wani abun. Sai cigiyata ƴan ɗakinmu suke yi. Voice nayi nima na soma da gaisuwa tare da nuna farin cikina a bisa wannan gida da Habiba Bala ta zama silar assasashi, nayi musu alƙawarin in sha Allah zan halarci taron da aka haɗa domun tattaunawa na ido da ido, wanda suka tsaida rana ran huɗun Sallah,za'ayi taron a zaranda hotel. Ina turawa da saƙo duk suka fito nan muka ɓalle da hirar yaushe gamo, muna ta tuno abubbuwan dariya da suka shuɗe a lokacin baya. Ina cikin haka na jiyo muryar Hajiyayye a tsakar gidan. Sallama nayi musu kuma na miƙe. Abincinta na zuba mata na fita. Duk da nasan abune mai matuƙar wahalar gaske taci abincinnan. Ba kasafai ta fiye cin abincina ba. Nayi sallamar duniya a ƙofar ɗakin nata ba'a amsa mun ba. Ta kasan labule na tura hannuna na ajjiye mata abincin na komo ɗaki. Abincin Kaila dake jere a tire mai murtala duk tsatsa na ɗauka na fito. Da sallama na tura ɗakin Kaila na shiga. Take ƙafafuwana suka shiga rawa, ƙirjina na dokawa. Tunda nake ko a waya ban taɓa ganin tsaraici ba face na mazajen dana aura , sai gashi nayi tozali da Hajiyayye tsirara haihuwar uwarta da ubanta a saman Kaila, shi kuma sai sambatu yake yi idanunshi a kulle. Ƙaran faɗiwar tiran hannunane ya dawo dasu cikin Haiyacinsu. Da sauri na fita ina haki sai Allah kawai nake ambato, tsigar jikina sai tashi take yi. A guje na faɗa ɗakina na danna sakata ina haki. Jiyo bugun ƙofar Kaila nayi daga bayana. Ina jingine da jikin ƙofar ina tsiyayar hawaye, hoton tsaraicin Hajiyayye ƙam a idona.
"Shanono ki buɗe ƙofar nan nace miki, bakya ji nane Shanono, kinga buɗe kiji" Da ƙyar na rarrafa na shige uwar ɗaki na kwanta a katifa na rushe da kuka ina tambayar kaina wai ni mai nayi ma maza ne suke ƙoƙarin ganin sun rabani da rayuwata ne?" Nayi kuka a wannan daren wanda bansan iyakarshi ba, bansan sanda baccin wahala yayi sama da faɗi dani ba. Na dai farka da asuba idandunana sunyi luɓu_luɓu. Ina fitowa tsakar gida da buta a hannu naci karo da Kaila, sai wani kallona a ido a ido yake yi. Ni kuwa nayi biris tamkar ban ma ganshi ba. Waƙe_ waƙen Hajiyayye na jiyo daga bayana, ina juyowa nayi tozali da'ita ta fito daga turakar Kaila daga ita sai rigar bacci iya cinya, bata ko jin kunyar bayyanar tsaraicinta. Wani ƙududune ya tokare mun maƙoshina. Bayan gida na shiga nayo fitsari na fito. Kwanukan tuwona dana kai ɗakin Kaila na gani a dokin ƙofata da tuwon da miyar duk an zube mun su a cikin tiran. Shigarwa ciki nayi na ta da Sallah. Ina sallah ina tsiyayar hawaye. Ruwan tea na haɗa shi kaɗai na iya sha da alkakin da ƙawata ta aiko mun dashi jiya. Ina jiyo ƙwaramniyar matan gida, ni dai ban bi takan kowa ba, kuma da har nayi niyyar hana Kaila abinci tunda bani na kwana dashi ba. Sai kuma na zuba ruwan tea da alkaki da naman kaza a tire na fita na kai mishi harda robar kayan ciki dana soya. Na sameshi yana waya ƙasa_ƙasa yana ganina ya sauke wayar a kunnenshi.
"Shanono ai nayi tunanin ba zaki kawo mun kayan karyawa bane, dan naga kin ƙaro wulaƙanci. Dan kuturun wulaƙanci kina fa jina ina buga ƙofa kikai biris dani sai kace wacce tazo ta kama ni ina zina da karuwa. Kai ku mata kishinku dai yayi yawa." Kallonshi kawai nayi yana gamawa nasa kai zan fice abuna. Sai yace.
"Ki same ni a ɗakin Hajiyayye yanzu inason zan yi muhimmiyar magana daku dukka kuma yanzu. Danni fita zanyi, wannan kayan karin naki ki koma dashi Hajiyayye ta kawo mun tea da biredi da ƙwoyi. Ɗaukan turan nayi na fita ba tare da nace dashi ci kan ka ba. Ina jiyo takun tafiyarshi daga bayana. Ko dana shiga ɗaki sai da na yi kuka sosai kafin na goya Hauwa a bayana na fita zuwa ɗakin Hajiyayye. Da sallama na shiga ɗakin. Suna zaune akan 3sitter na same su suna hirarsu faram_faram. A kan 1 aitter na zauna a rakuɓe bance musu komai ba, vidiyon tsaraicin Hajiyayye sai yawo yake yi a kaina, gata dai da kaya a jikinta amman ni tsirara nake kallonta. Ɗakinnan a gyare tsab sai ƙamshi yake yi. Ga kujerunta masu taushi, ga kayan kallo ga kafet mai taushe malala a ƙasa, harda buna ta turaren wuta na ƴan gayu sosai mai wuta, an juna turaren wuta yana ta buso kamshi. Gyaran murya naji Kaila yayi. Wata leda viva ya miƙo mun yace.
"Ungo nan Shanono kafin in yi muku bayani" Hannu nasa na karɓi ledar daga hannunshi kaina na ƙasa, dan mugun kunyarsu nake ji.
"Baby riƙe naki kema ko?" Ya miƙama Hajiyayye ledarnan irin tawa. Zama ya gyara ya tattaro dukkan nutsuwarshi garemu, sai wani wauware idanu yake yi kamar wanda ya wanke makanta........✍🏻
*Akwai set na kayan ƙamshi, musamman domin masoyan wannan littafin. Zaku same su cikin rahusa da izinin Allah* ga masu buƙata sai su tuntuɓeni. Amman iyaka masoyan wannan littafi kaɗai zan siyarma, garaɓasar taku ce, promo nayi muku domin in faranta ranku kwatankwacin yanda kuka faranta nawa ran
[27/09, 2:32 p.m.] +234 803 641 9834: NA FAƊO DAGA BENE.....
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU
LAMBA TA 3.
*ASSALAMU ALAIKUM BARKAN MU DA SAFIYAR LITININ. HAƘIƘA BANSAN DA WACCE SIGA ZAN MIƘO SAƘON GODIYATA A GAREKI BA HAJIYA SUMAYYA. KE ƊIN MASOYIYACE TA HAƘIƘA CIKAKKIYA. SAƘON DA KIKA TURO MIN DASHI, NA KARƁA YA ISO GARENI, BANSAN WACCE IRIN GODIYA ZAN MIƘA MIKI BA, SAI DAI ADDA'AR KHAIRIRO. ALLAH YA BARMU TARE YA ƘARA MANA SOYAYYAR JUNA*
*HAƘIƘA WANNAN LITTAFIN YA KAINI WANI MATSAYI DA BAN TAƁA MAFARKIN RISKAR KAINA A KAI BA. BABU ABINDA ZANCE DA ALLAH SAI GODIYA. BABU ABINDA ZANCE DA MASOYANA SILAR MURMUSHINA, SAI FATAN ALKHAIRI*
Bayan ya gyara zama yace.
"Waɗannan ledojin kayane a ciki. Atampa guda ɗaya , sai mayafi, da takalmi, harda ɗan kunne da sarƙa, da nera dubu da ɗari biyar_biyar kuɗin ɗinki. Fasali ya ja kafin ya ɗaura da cewa.
"Dalilin wannan kaya kuwa shine. Aure zan ƙara nan da sati biyu masu zuwannan in Allah ya nufa. Kayane na faɗar kishiya ake ce musu ko me oho dai? Ɗanyan gwal Bilkisa ce ma na bata kuɗin ta siyo muku dan ta bala'in sanin kaya da kala."
"Kanbu Kaila Aure fa kace zaka yo a cikin gidannan, ni za kai ma kishiya Kaila? Wallahi in ka isa me nake, kinji fa umman Sulaiman baki ce komai ba Aure fa yake cewa zaiyo?" Ni dariya ma ta bani yanda naga ta haƙiƙance tana kumfar baki, harda miƙewa tsaye. Saina tuno da iriyar muguwar wulaƙancin dana fuskanta a lokacin da Kaila yake neman aurenta. Waya babu dare babu rana, a kan kunnena suke musayar kalaman da suka shige ƙa'ida yana fallasa mata asirin zuchiyarshi da inda gangar jikinshi ke mararin jin duminta. Daga yanda suke wayar basa jin kunyar yin batsa hakan ya sake tabbatarmun suna haɗuwa su watse, in dai Kaila bai kusanceta a waje ba, to haƙiƙa babu inda bai zakuɗa hannunshi a jikinta ba. Amman haka duk na ɗauka na jure, duk dan in samu wannan auren nawa na biyar ya ɗore. Ni banma samu arzikin kayan faɗar kishiya ba, kazalika bai zaunar dani baki da baki ya sanar dani bikinshi ba. Da lokaci yayi kawai ganin ƴan Akwanga nayi dangin mahaifiyarshi sun cika gidan tab, dangin mahaifinshi suma suka yo nasu zugar daga wudil. Haka na shiga cikin jama'ar biki akayi dani. Tunda aka auro Hajiyayye bata sake barin zuchiyata ta samu nutsuwa ba. Ga shigar banza da rashin kunya, a gabana take tsotse Kaila. Shi namiji dama kunya ba isarshi tayi ba ko a jikinshi. "
"Umman Sulaiman baki ce komai ba fa wai Aure zaiyi. Yaushe_yaushe na shigo cikin gidan ciki na biyu ne a jikina fa. KAILA ashe kai mayaudarine ban sani ba? Ka mance alƙawarurrukan da kaimun a waje cewar daga ni babu ƙari nice maganin matsalarka kana son mace ƴar gaye?" Kaila yace.
"Sabida son mace ƴar gayen ne yasa zanyi wannan Auren. Bayan na sameki ne saina gane ba mace ƴar gaye kaɗai nake da buƙataba. Ina son mace mai aji ƴar jami'i ƴar kwalisa. Allah cikin ikonshi Ɗanyan gwal Bilkisa duk ta haɗa dukkan wannan abun da nake nema, fiye da ma abinda nake nema. Dan a yanzu hakannan da nake magana Bilkisa ma'aikaciyar jinyace, unguwar zoma ce ta asibiti, ƴar gaye mai turanci kamar a fadar Queen alizabet sarauniyar Ingila aka yayeta, kinga ke iyakarki sakandare, ita kuwa Shanono iyakarta ƙaramar sakandare bata samu damar kammala karatun sakandaren ba ma ita, kunga ai iliminku in aka haɗa bai wuce rabin cokali ba ko?" Dariya ce taso kubce mun yanda naga Hajiyayye na ƙanƙance idanta, kafin ya gama ta shiga lailayo ruwan ashar tana dannama Kaila. Dana fuskanci ranshi ya soma ɓaci sai nace.
To ka gama dani ne in tafi?" Dubana yayi yace.
"Tukunna dai Shanono. Abunda nake so dake shine ɗakin ki da kike ciki nake buƙata a nan zan saka Ɗanyan gwal Bilkisa, da wancan ɗakin zauren zan gyara mata. Amman tace mun tana da kaya da yawa kinga ɗaki ɗaya bazaiyi mata ba. Bugu da ƙari ƴar manyan mutane ce, Babanta babban mai kudine. Tunda ke babu uwar komai a ɗakin ki sai tsummoki da gaiyar kuɗin cizo da ƙwarƙwata, ku tattare ke da yaran ku koma ɗakin zaure, nan da kwana biyu haka, dan masu gyaran wajen jibi zasu zo. Zan sa su yi miki fenti in sun zo. Ɗakin ma ko kin fita sai an yi mishi wankan maganin kuɗin cizo" Dim naji gabana ya tattake ya faɗi. Ni dai na rasa me nayi ma maza basu karɓeni ba . Wai yau ni Kaila yake cema in koma ɗakin zaure ni da yara mu rai takwas. Me Yasa baice Hajiyayye ta koma ba ita mai ƴa ɗaya? Nice ba mace mai daraja ba ko, ko dan a bazawara ya auroni ne shi yasa? Murmushin takaici nayi nace.
To shikenan babu komai zan koma yau ba sai gobe ba ma. Sannan inaso Hajiyayye taci gaba da kulawa da kai har zuwa lokacin da Allah zai saukeni lafiya tunda sai na haihu zata haihu, ita da Amarya sai suci gaba da kulawa da kai. Allah ya sanya alkairi yasa abokiyar zamanka ce na har abada"
"Lallai umman Sulaiman ban san ke wawuya bace sai yau, ashe rashin ajin naki har ya kai ki dinga ma miji fatan alkhairi dan zai ƙaro aure?" Cikin gatse nace.
Ke da kike da ajin ai bai hana ya hango wata zai auro ba ai ko, ba'a aure ke aka auroki kika zo kika miƙe ƙafarki kuma? Yarinya meye matsalarki da aurenshi? Ta huɗu ma tana ƙofar gida ai in dai namiji ne" Ina kaiwa nan na fita abuna. Ɗaki na koma na saki kukan baƙin ciki. Hajiyayye kuwa muryarta har dakina ina jiyowa, daga karshe Kaila ya fice fu a gidan ya barta tana ta zage_zage a tsakar gida tana faɗin bai isa ya kawo mata wata ƴar iska a matsayin kishiya ba. Mikewa tsaye nayi na shiga aikin sintiri a filin tsakar ɗakina, ina tuna farkon haɗuwarmu da Kaila, da kalma mafi soyuwa daya faɗamun yasa na sakankance zan samu farin ciki mai dorewa a gidanshi. A lokacin da nake Amarya sai da Kaila ya maisheni sarauniyar mata tsabar so, ko da yaushe yana liƙe dani muna zuba soyayyarmu. Amman jibi yanzu yanda bolar gidana ta fini daraja da kima. Kaila ya mance meye ya zama silar kafuwar sana'arshi, har shi kanshi ya samu nutsuwa a cikin rayuwarshi. Gashi sakayyar da zai mun ba'a iya yin kishiyoyi ya tsaya ba harda tozarci da ƙasƙantar dani. Iyayena suna gani sunyi biris kullum kalmar da Inno take faɗamun shine duk rintsi kar in kuskura ace aurena ya sake mutuwa a karo na biyar. Mahaifina kuwa cewa yayi duk randa na sake na kaso aurena sai dai in nemi wasu iyayen da wasu dangin ba dai su ba. Gani suke kamar ni nake yin laifin da mazan suke sakina. Ni kuma a iyakacin zamana da mazajena huɗu na baya bazan iya cewa ga laifin da nayi ma ɗaya daga cikinsu ba wanda shine yai silar mutuwar auren ba. Ko su kansu basu isa sunce ga laifin da nayi musu suka sake ni ba. Ni kawai mazan ne basu karɓeni ba, ko kuma mazan ƙabilar Hausawa ne basu ɗauki saki da mace a bakin komai ba mafiya yawansu. Ni na kasa gane kan wannan zamantakewa da kabilar Hausawa ke gudanarwa a gidajensu, ko kun ɗauka an halicci mata ne su zo duniya domun kawai su zama bayinsu? Na gane mace bata da daraja amfaninta baya wuce a samu nutsuwa da'ita, ta haifi yara ta rene su. Dai_dai da ciwo in ya kamata wasu mazan saki suke yi, ko kuma su tura mace gida iyayenta su nema mata lafiya, da zaran ta samu lafiya ya lallaɓo a bashi matarshi. Hawayena na share, a zuchiye na soma fito da kayana daga cikin wannan ɗakin. Hajiyayye tana dokin ƙofarta tayi tagumi idanunta sun yi ɓulu_ɓulu. Ni kuwa aiki na shiga yi kace_kace.
"Umman Sulaiman lafiya kuwa, naga shekaran jiyannan kika gama kwalimar sallah, ko ɓera ne ya mutu a ɗakin?"
A'a Hindatu zan sauya ɗakine kawai" Nan na barta da riƙe haɓa, ai kamar jira Hajiyayye take yi. Nan ta shiga ƙundumama Kaila ruwan ashariya nan ta labartama Hindatu halin da ake ciki. Ni dai bance musu komai ba ɗakin zaure na buɗe, ƴan shirgunan ɗakin yawanci na Hindatu ne, harda wata kujerarta 2 sitter da yadin ya yayyage. Fito da komai na ɗakin nayi na kaɗa omo. Ga ciki ga goyo, amman tsabar jin haushi bana jin nauyin komai. Wanke ɗakin nayi har bango na tsane ruwan da tsumma, na wangale windon ɗakin. Alwalar azahar nayo, na shinfida daddumata nayi sallah a tsakar gidan. Hajiyayye uwar karaɗi yau ko wanka ta kasa sabuntawa tana zaune da rigar bacci a jikinta. Dumamen tuwo na ɗaura ina kan ɗumamen ƙanin Kaila ya shigo ya shiga aikin sara rago. Yana gamawa na duƙufa aikin suya. Dana gama cin abinci na ba Hauwa taci. Sai na soma shigar da kayana ɗakin zaure. Amadudu mijin Hindatu yace.
"Yaya Tani Allah dai yasa lafiya ba auren naki bane ya sake mutuwa a karo na barkatai?" Naji zafi da ciwon maganar Amadudu amman na riga na san mazauna Akwanga, Lafiya, da makurɗi basu iya tauna zance ba, kamar fitan zawo suke Magana. Ban kai da bashi amsa ba Hindatu ta labarta mai Abunda yake faruwa. Kayana naci gaba da shigarwa cikin ɗakin. Katifata na shinfiɗa a ƙasa, katifar yara kuma na jingineta daga bango ɗaya. Buhunhunan kayanmu kuma na lodasu lungun dake ɗan gefen katifata babu laifi filin tsakar ɗakin ya ishemi. Amman kenan a haka zamu dinga gwamutsuwa dani da yara a ɗaki ɗaya, taya hankalina zai kwanta gani ga yarana a cakuɗe a ɗaki ɗaya. Irin wannan sakaiyar Kaila zaimun babu komai. Sai magriba na gama suyan naman laiyannan. A take na raba na fitarma da kowa nashi. Na ba Hajiyayye nata dana Yariman